Chapter 16 Reading Koba So Akwai Kauna Book Complete Hausa Novels Arewa Novels

Koba So Akwai Kauna Book Complete Hausa Novels

Author :  Nil Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   16 / 28

45K to 48K   out of 83.3K words

cikin ido nakai maganar ina jan tsaki......!!
Na saka rigar wadda taimin das ajikina dayake doguwace, dayake babu madubi a ɗakin yasa na ɗauki ɗan ƙarami na jikin powder ɗina na nufi gaban window na ɗora ɗaurin kallabi sannan na koma na ɗauki mayafina wanda yayi kala da shaddar jikin nawa tare da ɗan fesa turare mai daɗin ƙamshi nayi waje tare da nufar falon ina takuna ɗai-ɗai kamar yadda anty zee taimin lecture atun farkon maganar aurena da abdul kafin ta dawo kan wannan.
Har ƙasa na ƙarasa gaban momy na gaisheta amman tai kamar bata jini ba sema ƙara haɗe ranta datayi tam kamar bata taɓayin dariya ba janai da baya kaɗan tare da zama na tanƙwashe ƙafata a gabanta ina zubawa t.v idanu.
Banfi minti ɗaya da zamaba sega rauda ta fito daga ɗakinsu tana hamma wanda da alama ko yunwa ce ta korota, tana ganina ta faɗaɗa far'arta gami da matsowa gareni cikin kulawa ta fara min magana "Lah sister fatimah yaushe kika zo?" amman mu bamu saniba wallahi" tafaɗa cikin tsananin zumiɗi gami da kawomin hannunta kamar zata rungumeni.
Ƙaƙalo far'ar dole nima nai tare da bata amsa da "jiya"sannan naja bakina na tsuke, dannifa sam bana ƙaunar halaƙa da duk wanda ya raɓi momy sabida bata ƙaunar uwata nafaɗi maganar cikin raina kamar kuma tana ji sena ɗan tura bakina gami da watsa mata wani irin kallo ta wutsiyar idanuna.
Cikin tsananin farin ciki ta mike "sis bara na kira na'eem wallahi itama bata san dake aka zoba dammu kam momy bata gaya manaba haka kuma big bros" da ido na bita tare da kauda kaina gefe ina wasa da fulawar jikin carpet, ina kallon momy tana aika mata da harara sabida lokacin ita momyn tana yin wayane.
Acikin minti kaɗan segasu kamar wasu ƙananun yara sukawani ɗanemin jikina suna shirme waisu acewarsu murna ce, wadda da can basusan hanyar gidan ubana ba seyanzu za,aimin bariki toni har yanxu banga wajan zama agidansu bama bare su saka rai daxan saki jikina dasu.
"Sis fatimah! naji muryar na'eem cikin farin cikina tana min magana mai kama da kawo gulma.
"Wallahi munyi farin ciki da aurenki da yayanmu dan ALLAH kada ki kula momy duk abinda zatai maki amman idan anty maryam tai maki wallahi ki zageta muma haushi take bamu yadda zakiga tana wani ɗaure face idan muna waje".
Tana kaiwa nan ta juya tana kallon momy kotaji mitace ganin hankalin momy baya kansu yasa ta juyo tacigaba da bani labarai marasa kan gado da tsari danni shi kansa baya gabana bare wata matarsa.
Taɓe bakina nayi tare da ɗan jan tsaki mai sauti tare da cewa na'eem ɗin "to naji" iya abinda na gaya mata kenan na kalli raudah saboda nidai araina naji nafi sonta sabida ita batada rawar kan na'eem sannan kuma uwa uba batada surutu, "Pls sis zanyi break wallahi rabona da abinci tun jiya" tun kafinma na dire abinda zance naga na'eem ta miƙe a miliyan wani lungu naga ta nufa cikin minti kaɗan segata da katon flaks na tea a hannunta bayanta kuma wannan yarinyar ta jiyace wadda ta kawomin kayana ɗaki rike da ɗan kwando agabana suka aje nan danan rauda tajawo cup ta haɗamin tea mai kauri tare da zubomin farfesun kaji duk ta ajemin agabana.
Bisimillah nayi zan ɗauka nakai bakina naji saukar muryar momy akaina kamar dirar rodi "Na'eem watakan dan kina gadara kayan gidan ubankine yasa kika ɗauko mata kayan abincina batare dakin nemi izinina bako?" takai maganar tana karasowa gabana.
Sunkuyar dakaina nai ƙasa ina runtse idanuna duk tsoro ya kamani.
Mikomin hannunta tayi "bani bread ɗin hannunki aiba kabirune ya kawo ba dan uwarki aisha!!.
Cikin mamaki naɗago kaina ina kallonta da idanuna wanda ya sauya kala nan take haushi takaici baƙin ciki sune suka kamani nan take.
Amman babu damar nai wani abu akai domin ance wata fuskar tafi gaban mari!
Tsintar muryar raudah nayi cikin damuwa kamar ita akama abun tare da cewa.....
"Haba momy idan baki ragama sis fatimah ba aimu kya mana kara na sunan ƙanin mahaifinku dan ALLAH momy muna sawwaqewa zuƙatanmu duniyar ma nawa take, bareni wallahi bantaɓa ganin abban kano ko umman kano sun maki koda kallon banxa ba amman ke kullum kika zauna sekin aibatasu agabanmu haba momy ai bai dace ki zagi iyayenta agabanta ba kada gaba kizo kina danasanin hakan....!!Tas!Tas!! kakejin ƙarar sautin marin da momy ta wanke rauda dashi sannan tahau bala'i "To uwata dan ubanki harkin kai matsayin daxaki yimin faɗa!! har kin isa nai magana ki kawomin wa,azi!! tafaɗa cikin tsawa da gudu naga na'eem ta mike tana kuka tabar wajan itama raudan kuka ta saka tare da barin wajan cikin sanyin jiki.
"Allah yabaki hakuri momy" tafaɗa tana shigewa ɗakinsu.
Wani tunanine ya ɗarsamin araina wato lallai momy itake son rabamu da ƴaƴanta ashe duk ba haka sukeba su zuciyarsu mai kyauce itace kawai matsalar tinda ga ya hydar ma baya da matsala a iya jiya zuwa yau na fuskanci hakan..
Nima miƙewa nai tare da son nabar wajan sejin saukar muryata nayi "ina zakije ƴar gwall!maza ga hanyar ɗakina can kije ki gyaramin shi ki wanken ki gogen tiles sannan kizo kije part ɗin baba suma ki gyarawa maryam ɗakinta idan kin gama kije cikin masu girki ki zauna dan bana son ganin wannan baƙar fatar taki mai kama data shuni, kuma wallahi ko ɗigon haƙoranki nagani a waje da sunan dariya kinawa baba sena yanke maki baki! takai maganar cikin hargagi.
Ƙarasowa nayi sum-sum na wuce na nufi hanyar data nuna min inajin zuciyata babu daɗi, wallahi bada ban umma tayi mugun jamani kunne akan koda kwana bata nemana ba da yau ɗinnan zakara ze bani sa,a! kash to ke batula idan ma kin fita waxe baki na mota ina kuma kika san hanya yadda garinnan babu lafiya, uwa uba ma kuma a yanzu waye ze barki ki futa dan kinsan wannan mai fuskar ƙwaran baze bar masu gadi barinki fitaba zuciyata ta bani wannan amsar.
Dawannan tunanin na ƙarasa shiga bedroom ɗin nata ina mai bawa kaina hakuri sabida nasan ba komai ke ɗorewa ba watarana se labari to gwaea tun yanzu inke bawa zuciyata hakuri da juriyar danne dukkan abinda momy zatamin danna san komai akwai lokacinsa.
Babban ɗakine wanda ya laƙume ƙaton gado na royal mai kalar ruwan toka se siff ɗinsa da ƙaton ɓadubi se wajan adana takalma mai ɗan karan kyau.
Babu wani dattin kirki acikinsa sema wani ƙamshi mai daɗi dake tashi anan na kuma tabbatar da cewa lallai dole ya hydar yazama mai muguwar tsafta sabida yadda na kula momy tana ɗaya daga cikin mata masu tsananin tsaftar gaske.
Yaye bedshit ɗin nai tare da ɗauko wanda nagani daga gefen cavet ɗin mai kalar blue na warwaresa tare da shinfiɗawa akai sannan na shirya pillow case ɗin suma cikin tsari, cikin lokaci kaɗan na gama gyara mata gadon nata tsaff harda yimata wani shegen decoration danaga ummi nayi a gadonta.
Wani ɗan lugu na juya na ɗauko tsintsiyar laushi da abin kwasar shara nazo nafara gyara mata cikin ɗakin seda na sharesa tas na kwase ɗan dattin naje na watsar sannan na nufi toilet ɗin nata sabida bana son nai mopping sannan na shiga banɗakin zan lalata sharar danayine abanxa
Baƙaramin mamaki nayiba lallai inda kuɗi yake akwai kallo jibi yadda iya banɗakin momy ma ya laƙume waɗannan kayan wanka masu kyau da tsari kamar baza,a mutuba lallai inda ranka kasha kallo nafaɗa ina kallon jaguzin cikin bayin wanda yake ɗaukar idanun ga wasu irin madubai da aka jere tarkacen kayan wankin baki akansu juya nai sosai cikin mamaki komaye na kai madubi bayi oho,ganin zan ɓata lokacine akan wannan shirman yasa na mayar da hankalina ga fara gyaran bayin seda na gama tsaf na goge dukkan maduban da glasan wajan sannan na fito waje bayana ke faman amsamin na rashin sabo ga hannuna duk ya ƙage sabida sanyi.
Seda nai minti biyar sannan na tsoma mopar a boket na fara mope ɗakin nata cikin tsautsayi ruwan santsi ya kwarfemin ƙafata banyi aune ba seji kake fam!Na kife a wajan wata ƴar ƙara na saki gwanin tausayi gawani irin zafi daya ziyarci ƙuguna haka na miƙe da ƙyar na gama na haɗa kayan nakai inda zankai nayi hanyar fita.
Cikin ladabi na ƙarasa gabanta yanzu tare suke dawata mace da alama kaya ta kawo mata dannaga matar tanata fito da kayan jiki na mata kala-kala gaisar da matar nayi sannan nacewa momyn na kammala.
Dawani irin kallo ta dubeni sannan tace naje wajan firjin can ta nunan da hannu wai na ɗauki biredi da tea nasha sannan na wuce part ɗin maryam na gyara mata.
Cikin miƙa wuya ga abinda ta umarcen dashi na tashi naje gaban firjin wata ƙwallace tazomin ganin ɗan shayin dabefi amir ya kurɓeba babu yadda na iya haka na ɗauka na wuce ɗakin da aka saukeni na zauna awajan zamanma seda nai ƙara sabida yadda ƙuguna ya amsamin dan baƙaramar buguwa wurin yayiba.
Cikin ƙanƙanin lokaci nagama da tean wanda ko gefen cibiyana bai jeba na tattare cup ɗin na kai karamin kicin ɗin falon danaga na'eem ta ɗaukomin break fast ɗin ɗazu.
Gabanta naje na tsugunna tare da ce mata momy na gama cikin tsawa tacemin wai ubana ne ze rakani part ɗin maryam cikin hargitsa na ɗago kaina na kalleta tare da kawar da kaina gefe ina jan hucin takaici tare da danne abinda yazomin wuyana, murmushi baƙuwarta tai tare da cewa "hajiya zainab kimata a hankali kinsan ƴaƴan namu se hakuri" wani banxan kallo tabi matar dashi tare da hayowa kaina "Maza ɓacemin daga wajannan kije kinemi part ɗin nasu mana banxa mai surfar kwaki" takai maganar tana hamɓarina da ƙafarta da gudu na miƙe nai hanyar waje na buɗe kofar falon na fita seda naci kukana a abakin kofar sannan naja jikina nai part ɗinsu yaya.
Baƙaramin ɓata lokaci nai ina danna ƙofarba kafin azo a buɗemin haɗa ido mukai da anty maryam wadda take sanye da wasu shegun riga da wando na barci iya gwiwa se wata riga mai hannun shimi, raɓeta nai na wuce cikin dauriya.
Cikin zafin nama tabiyo bayana tare da fincikoni gabanta har ina dan dukan cikin dake jikinta kadan wanda yake gaf da haihuwa.
"Ke dallah malama ina zakije kin wani zo kin shigemin falo kamar daga gidanku kika zo dashi".
Ɓanɓare hannunta nayi daga jikina saboda idan har na tsaya gabanta komai ze iya faruwa sabida yadda bana jin dadin zuciyata a halin yanzu tsakiyar falon naje tare da raba idanuna ina neman ɗakinsa danshi kaɗai nasan xan iya gyarawa muhallinsa ba wata ƙatuwaba.
Inajin yadda ta biyo bayana tana antaya min ashar amman haka na cije naki kulata nabawa banxa ajiyarta nai hanyar room ɗin danake tunanin nashine.
Cikin zafin nama na budesa tare da mayar da key na datse nan na karasa cikin ɗakin mai ɗan karan kyau da tsari gadon nafara gyarawa sannan shima baɗan shirya tarkacen kasan wajan loptop ɗinshi dake a ƙasa na ɗauka na aje masa akan sopa sannan na gyara masa toilet ɗinshi na kammala komai na fito na rufo kofar ina jan kafata sabida yadda jikina yake wani ciwon gajiya ga ɗakin nashi daɗan kura kaɗan.
Banganta a falon ba hakan yayimin dadi dan haka nayi gaba abina koda naje part ɗin momy banga kowa afalon nataba yasa nayi dakina na nufi bayi babu abinda nake buƙata a halin yanxu kamar naɗan gasa ƙuguna da ruwan ɗumi dan haka na nufi bayi na haɗa ruwa mai ɗan ɗumi na gasa jikina sannan na ɗauro towel na fito waje babu abinda jikina keyi se zafi wanda har yaɗan sakamin zazzaɓi gashi dai nayi wanka amman har yanxu ban daina jin yadda kuguna da bayana ke amsamin ba kuka na saka tare da hayewa katifar nai ruf da ciki ko towel din jikin nawa ban cireba haka nahau kuka ina dafe ƙuguna da hannuna.
Nidai banji ƙarar buɗe kofar ba sejin mayar da ita danai anrufe bangama dawowa daga tunanina ba naji alamun motsin mutum akaina.
Saurin mirginowa nai ina dafe towel ɗin jikina da hannuna tare da zuba masa matsakaitan idanuna ina kallonsa dasu waɗanda suka jiƙe da ruwan hawaye.
Batare daya cemin komai ba ya nemi gu agefen katifar ya zauna ya saka hannunshi guda ya dafe kuncinsa dasu ganin yayi haka yasa nima na juya masa baya ina sakin wani irin marayan kuka!
"Ni wallahi yaya bazan iya zaman gidannan ba ai ba haka kukai da abbanmu ba idan baxaka iya rikeni ba kawai ka sakeni ka sawwaqemin kamayar dani gaban iyayena tun kafin akashe masu ni"!
Nakai maganar ina jan majina kaɗan kaɗan.
Ɗago rinannun idanunshi yayi ya zubasu akaina batare daya saki fuskarshiba muryarsa can ƙasan maƙoshi yacemin "Kada na kuma jin wannan banzar maganar abakin ki yanzu mi akai maki?" yajefomin maganar face ɗinshi babu walwala ko kaɗan.
Juya masa baya nayi ina cigaba da kukan danake batare dana tankasa ba.
"Malama gaba zaki jiyomin ba baya ba ki tambayi maryam ni mace ƙarya take ta juyamin baya"! yafaɗi maganar cikin jan tsaki yana fiddo da wayarsa daga aljihun wandon jeans ɗin dake jikinsa.
Idon sa naga kan waya bai kuma ƙara cemin komai ba baya ga wannan maganar daya furta min.
Ringing wayar taketa faman yi wadda ya ƙaro sautinta kafin naji saukar muryar umma kamar daga sama.
Cikin wani ladabi wanda ya sakani a kwana naji yana gaisawa da umma sannan ya ɗora da ce mata ɗazu yaga kiranta baya gidane yanxun nan ya shigo gidan.
Jinai umma tana ce masa ba komai nan dai suka kuma gaisawa sannan naji ta sako maganata wai hala dai bana shirmen nawa, murmushi mai sauti yayi tare da cewa "haba umma yaufa kwananta guda aiko gama shirya kayanta ma inaga bata gama ba" yakai maganar cikin raha.
Ce masa tayi dan ALLAH idan ina kusa yabani wayar mana jim yayi kadan sannan naga ya mikomin wayar yana zabgan harara!
Nima juya baya nai alamun baxan ansaba can kuma sena cafka har ina hadewa da hannunshi sannan nahau mata kukan shagwaɓa.
Nakai minti kusan biyu ina wannan kukan kafin na furta.
"Haba umma yanxu daman kun shirya bazaku taho dasu ummi ba amman kuka kasa gayamin har aka sa na saka raina da zuwan nasu".
Kwantar da murya tayi nan tafara min magana cikin tattausan lafazi tare da gayamin manyan misalai na hakuri da zaman aure sannan tace na kwantar da hankalina suna nan zuwa ai indai anyi hutu.
Shaƙar majina nai tare da kallon saitin dayake ganin baki ɗaya hankalinshi ba,a kaina yakeba yana can kan ɗaya wayar tasa yana danne danne yasaka na rage volume tare da cewa umma.
"Umma nikam idan kunxo biyoku zanyi wallahi umma yau tunda na tashi momy take sakani aiki nan na kwashe komai na gaya mata hattaga ciwon danaji da abinda maryam taimin da ciwon da ƙuguna yakemin da yadda momy ta bani break fast tas na zayyanewa uwata batare dana ma tuna yana wajan ba nakuma kara da ɗaukar alwashin wallahi suka takuramin guduwa zanyi.
Umma danne abinda yake taso mata aranta tayi tare da kiran sunan batula da ɗan ƙarfi kaɗan. nan tahau yi mata faɗa sosai akan kada ta kuma gaya mata duk abinda momy zata mata sannan kuma ai momy mahaifiyarta ce koda babu auren ali akan ta bare kuma yanxu datake surukarta sannan tace mata kada ta sake ta gayawa kowa wannan maganar koda kuwa hydar dinne sannan kuma komai momy zata mata tai hakuri banda rashin kunya.

Sosai jikina yayi sanyi da kalaman ummata haka mukai sallama ko waigaya banyiba na aje wayar a gefensa na juya na kifa kaina akasa ina sakin kuka ƙasa-ƙasa.

Duk abinda take gayawa mahaifiyarta yana jinta kuma duk abinda umman ta gaya mata yana ji sedai yadda ya basar ne baxaka taɓa cewa yaji mi sukace ɗinba.
Sosai maganganun umma suka birgesa nan ya kumajin kaunar matar da ƙimarta sun sake masa caa! acikin ranshi gakuma ɗunbin mamakin halin momyn wato seda dai ta azabtar da yarinyar ɗin kenan bayan fitarsa bayan dukkan magiyar daya gama mata kafin ya fita dazun.
Lumshe idanunshi yayi kafin kuma ya waresu akanta jin yadda take kuka! yasa ta karya masa dukkan wani lakar jikinsa shi mutumne mai tausayi baya kaunar yaga mutum ya shiga damuwa musamman kukan mace wanda bakaramin ɗaga masa hankalinsa yake ba.
Tattausan hannunshi mai yalwar gargasa da santsi ya saka agadon bayanta tare da birkito da ita gabansa ya tsareta da manyan idanunshi yana binta dasu cikin wani irin yanayi.
Jin hannunshi abayana yasaka rawar jikina ta ƙaru ban jure yadda yake bina da kallo ba dan haka se kawai na rufe idanuna gam ina zubar da ƙwallah.
"Mi momy tayi maki ɗazu?" naji amon muryarshi akunnena. girgiza kaina nai alamun babu komai sabida nasihar umma gareni yakaɗani dambu taliya naƙi gaya masa komai daga karshema sena ƙara sautin kukan danakeyi.
Banyi auneba naji ya ɗagani cak! gami da ɗorani akan cinyarsa, abinda ya sakani a ɗimuwa yadda naji saukar hannunshi akan ƙuguna yana murzamin cikin wani irin salo mai wuyar misaltawa.....
Zullo nayi gami da ƙoƙarin dira daga kan cinyar tasa sakamakon wani irin bakon yanayi dana.....!!

Na saka rigar wadda taimin das ajikina dayake doguwace, dayake babu madubi a ɗakin yasa na ɗauki ɗan ƙarami na jikin powder ɗina na nufi gaban window na ɗora ɗaurin kallabi sannan na koma na ɗauki mayafina wanda yayi kala da shaddar jikin nawa tare da ɗan fesa turare mai daɗin ƙamshi nayi waje tare da nufar falon ina takuna ɗai-ɗai kamar yadda anty zee taimin lecture atun farkon maganar aurena da abdul kafin ta dawo kan wannan.
Har ƙasa na ƙarasa gaban momy na gaisheta amman tai kamar bata jini ba sema ƙara haɗe ranta datayi tam kamar bata taɓayin dariya ba janai da baya kaɗan tare da zama na tanƙwashe ƙafata a gabanta ina zubawa t.v idanu.
Banfi minti ɗaya da zamaba sega rauda ta fito daga ɗakinsu tana hamma wanda da alama ko yunwa ce ta korota, tana ganina ta faɗaɗa far'arta gami da matsowa gareni cikin kulawa ta fara min magana "Lah sister fatimah yaushe kika zo?" amman mu bamu saniba wallahi" tafaɗa cikin tsananin zumiɗi gami da kawomin hannunta kamar zata rungumeni.
Ƙaƙalo far'ar dole nima nai tare da bata amsa da "jiya"sannan naja bakina na tsuke, dannifa sam bana ƙaunar halaƙa da duk

16 / 28