Author : Nil Category : Romantic Hausa Novels
jiki sannan yay min fatan alkairi gami da yimin sallama ya katse wayar.
*********************
Cikin tausayin ɗiyar tasa ya dubi umma wadda tai tagumi tana jimanta abin itama aranta"Aisha yanzu yaya kike ganin zamuyi kadafa zainab ta illata mana ƴa munan kara zube" abba yakai maganar cikin wani yanayi murmushin dole umma tayi daman ita indai akan ƴaƴane akwai kawaici kuma tafi abba dangana sannan tafara masa magana cikin kwantar da hankali harta ɗora masa da misalin irin halaccin da baban abuja yay masu na sauya akalar auren da ɗansa.
Numfasawa yayi tare da cewa "ina zuwa Aisha nifa idan babu dama zan ɗauko ɗiyata dan tunda kikaga fatima tana min wannan kukan ba banxa ba kinsan ita barta da gandar ta amman batada yawan kuka koda ciwo take akwai dauriya nifa tunda naji tana min magiyar nan hankalina ya tashi" abba yakai maganar yana danna wayarsa ringing!! biyu aka daga wayar.
Aliyu wanda yake tare da wasu abokansa a barrack ɗin da aka saukesu yayi saurin danna line busy tare da kiran abba cikin lokaci kaɗan.gefe yaɗan matsa daga wajan abokan aikin nasa sannan yasoma gaisar da abba cikin ladabi.
Daga bangaren abba ya numfasa tare da cewa "ashe kuma kai Aliyu baka ma garin dafatan to kana lafiya kaida iyalin naka?" sunne kansa yayi a qasa kamar yana gaban abba sannan yace"wallahi kam abba ai mana addu,a muna nan dai tafe insha ALLAH" yakai maganar cikin ladabi.
"To masha ALLAH ubangiji ya dafa maka ya tsareka kaji Aliyu, daman kiran dana maka wata alfarma zan nema gareka yanzu qanwar taka taimin waya wai ita gida to shine nace tunda bakwa nan meze hana kasa akawota nan ɗin tunda daman akwai form ɗinta na f.c.e a qasa idan yaso taɗan fara zuwa kafin komai ya kammala" abba yakai maganar tare da jiran tabakin Aliyun..
Wata zuface take karyo masa ta kowani sassa na jikinsa jiwani ganganci da abba yakeson yayi masa aikam fati ita da karatu har abada tunda ta riga ta shigo gidansa.babban ma abinda ya basa mamaki ina ta samu wayar data kira abban?
Yaja numfashi tare da cewa."Abba kayi haquri ban qi maganar kaba amman aɗan yimin haquri har nakoma tukunna sena kawota dakaina ta ganku amman makaranta kam abba banajin fatie zata qara yin wata gaskiya" yakai maganar adake batare da tsoro ko qaryaba.
Ɗan murmushi abba yayi tare da gano wani boyayyen al,amari dangane da Aliyun tare da cewa" to karka damu Aliyu hakan ma nagode ALLAH yabaka ikon kula da qanwar taka ka gaisar min da maryam ɗin" can qasan maqoshi ya furta amin sannan cikin sigar siyasa yace"abba kadan turon da number da fatie ta kiraka daman tun safe nake kiran gida babu network" batare da abba ya kawo komi aransa ba yacewa Aliyu to tare da katse wayar cikin minti ɗaya ya tura masa da number.
Shikam Aliyu yayi hakane dan yagane dawata number fatima take waya dan yasan yanzu rauda babu waya a hannunta na'eem kuma yana da numberta toyana tunanin kota na'eem ɗince tunda yasan kotasha giyar wake momy baxata bata wayarta ba.
Baisha ɗumbin mamaki ba seda aka tura masa da number yaga bai santaba koda da kama jikinsa har rawa ike ya shiga neman number.
********************
Ringing ɗaya na ɗaga wayar ina cewa "bara na kaiwa baba wayar naɗan arane" firgitacciyar tsawar danaji ita tasaka na yada wayar qasa kafin naji dirin muryar wanda banyi zato ko tsammaniba kamar dirar mikiya.
"Fatie waya baki waya wallahi idan baki bani amsata ba yau zan taho komai dare naga uban daya baki waya!!!! yakai maganar cikin hargaginsu na sojoji,hannuna har yana rawa wajan kara wayar a kunnena gawani tsoro daya kamani sannan na soma masa magana"ni wallahi ta baba cefa wannan matar wadda tarakoni wajanka shine fa na ara na kira abbana" nakai maganar cikin wawanci inajin saukar ajiyar zuciyarsa wadda ta bayyana qarara tare da cewa "mi kika cewa abba ce mai kikai natafi nabarki komi?" wannan karon muryarsa taɗan kwanta ba kamar waccanba.
"Nifa ba haka nace mashi ba" nakai maganar cikin kuka!
Can ciki ya kwantar da muryarsa sosai tare da cewa.
"To gayamin ni kinga banison wannan kukan muyi magana mikika ce mashi"yakai maganar yana jan numfashi kamar mai cutar asma.
Seda na goge hawayena kamar yana gabana sannan nace......
"Yaya kaima fa kai tafiyar ka kullum momyn ka bata da aiki se zagina sakani aiki ɗazufa akan na gaisa sa mama harda kwaɗamin ludayi ni wallahi sena gudu"!!!
Nakai maganar ina sakin wani irin marayan kuka mai shiga zuciya.
Daga nasa ɓangaren shafa kwantacciyar sumar kansa yake yana runtse idanunshi waɗanda zallar ɓacin rai sukaiwa caa!! can cikin qasan maqoshin sa ya furta.
"Fatie kina son nazo yau na ɗaukeki mutaho nan?" ya tambayeni muryarsa kamar ze zubda hawaye😳 tura bakina nai gaba.
"A,a base kazoba ni kawai gida zan tafi wallahi ni ummatah" nakai maganar ina kuka!!
Cikin takaicin abinda tace masa ya fara magana cikin faɗa-faɗa kamar bashi yagama rarrashiba.
"Kekinga kirufamin wannan wawan bakin naki wallahi tunda baxaki zo wajenaba ni babu ruwana kita zama idan yaso ta dakaki ma kuma wannan shine last naga kin kuma karɓar wayan wani agidanan idan kuwa naji labari sena ɓallaki wawiya kawai...!! qitt naji ya datse kiran wanda yayi dai dai da jiyo muryar momy danai tana kwaɗomin kira wanda da alama tana ma tsayene ajikin qofar ɗakin nawa........!!!
*64 - 65*
Dawani irin tsoro wanda ya bayyana har kan fuskata na qarasa gaban qofar bayan na mayar da wayar baba cikin skirt ɗina na ɓoyeta ta yadda momyn bazata kulaba.
Buɗe kofar nayi tare da rage tsahona kaɗan "momy gani" nafaɗa ina mai saukar da qwayar idanuna a qasa.
"bakiji kiran danake maki bane ba tun ɗazu?" ta tambayeni muryarta cikin sanyi babu wannan faɗan nada.
"Eh naji momy wallahi kaina kemin ciwo shine na kwanta amman kiyi haquri dan ALLAH" Nakai maganar ina mai langwaɓar da kaina gefe nai suffar abin tausayi.
"Amman miya hana kizo kice zakisha magani wato dan kinga yau Alhaji ze dawo shine zakizo ki kwanta salon kijamin faɗa ko?"takai maganar tana zabgan harara, sunne kaina nai aqasa ina mai sake bata haquri cikin rawar jiki "momy ubangiji ya baki haquri naga idan na zauna a falon wataran ceman kike na sakaku agaba shiyasa na kwanta a dakin amman kiyi haquri" naqarasa faɗa ina share hawayena.
Tsaki taɗan ja marar sauti sannn tace."dalla taso wazaki ma daɗin baki wuce muje ki qarasa jeramin kayan abinci a daining ɗin falon alhaji" tana gama kayan haka tai ciki tana sakin mitar tata data saba.
Hamdala nai jin bata ji maganar danake ba tare da kara danne wayar ajikina sannan na nufi bayanta har nakai wajan kicin ɗin sekum na koma dakina aguje na yayo hijab na fito na biyota sabida tuna gargaɗinsa na cewar idan na fita koda falon momy ne babu hijabi ALLAH ya isan sa, ina tafe ina tuna wannan maganar tare da cewa wallahi bada ban nasan hukunci da haqqin aure ba da babu wata dokarsa dazanbi amman babu damar hakan sabida daka sani ka take gwara baka sanin bama baki ɗaya.
Cikin hanzari na fara kaiwa da komowa a tsakanin part ɗin baba dana momy inkai wannan injera inkai wancan injera haka naita faman abu guda har zuwa wani lokaci.
Bayan na kammala naje ɗakinta seda nai nocking bayan ta bani damar shiga na raɓe daga gefe gami da sada kaina qasa sannan nace mata nagama abin da tasakani.
Babu yabo babu fallasa tace to naje na ɗauki magani akan furji sannan na bude lokar kicin ta gefe na ɗauki abincin ranata a kwano sena naci, godiya nai mata kamar wata almajira sannan nabar ɗakin.
Seda na ɗauki abinci sannan naje na dauki maganin duk daba yunwa nakeji ba amman nasan idan taga ban ɗauka ba yanzu zatace sharri zan haɗa mata dannaga baba ze dawo shiyasa na dauka nakai ɗakina na adana sannan nafice wajan baaba
Cikin farin ciki najawota gefe na bata wayar tata sannan nai mata godiya tare da ce mata insha Allah zan bata kuɗin kati, da sauri baban tace min ita dan ALLAH tabani badan nai mata wata hidima ba.
Murmushi nayi mata sannan na kuma yi mata godiya kana na koma part ɗin momy.
Jin anata kiran sallar la,asar kawai sena nufi bayi nai alwala na fito na data sallah, seda na ɗora harda azkar ɗin yammaci sannan na kuma kowama bayi na haɗa ruwa mai ɗumi na tube kayan jikina.
Ɗan shafo wajan da momy ta kwaɗamin ludayi nai wanda harya ɗan kumbura kaɗan sannan na soma wankana ina mai jin tausayin kaina.
Towel na ɗauro bayan na gama wankan na fito sanin babu wanda ke shigomin ɗakina yasa na tube towel ɗin jikin nawa na nafara goga mai a fatar jikina wadda taketa faman sheqi domin duk bautar da momy ke sakani baya hanani yin wanka da gyara jikina dan watarana ma da kanta take cemin naje nayi wanka idan taga banyi ba, dan a ɗan zamana a gidan na fahimci momy irin mutanan nan ne masu tsananin tsaftar gaske.
Atamfar holand na ɗauko mai kalar yellow na saka riga da skirt sannan na kafa ɗaurin kallabina na ɗauki sarqa da ɗan kunne na saka tare da yafa wani yellon mayafi wanda ya shiga da kayan jikin nawa.
Turare na fesa sannan na ɗauki hanyar fita daga ɗakin batare dana gyara katifata ba sabida tun ɗazu naji dirin motar su baba.
Abakin qofar na zira takalmina flate sannan na qarasa falon momy.
Tunda nataho momy wadda take zaune riqe da waya a hannunta ta zubamin idanu ko qiftawa batai sanye take dawani ɗanyen boyel ja da baqi wanda yakusan zautar dani dan seta komamin kamar wata balarabiya dan tsabar kyau wallahi baxaka taɓa cewa tahaifi yaya ba, kuma anan seka marsu tai mugun fitowa dashi hatta kallonsu na qasan idanu ashe iri ɗayane.
Har na qarasa gabanta na zauna a qasan carpet momy bata daina bina da kalloba.
Itakam anata bangaren tsananin mamakin yadda batula tai mugun kyaune ya kamata daman haka yarinyar take da kyau da ɗaukar ado wanda tashi guda kyanta yake bayyana idan tayi ado yazama dole ta takama wannan adon burki kafin ya rufta da ita.
Dan yadda taga jikin batula yana kaɗawa ta ko ina tabbas zatai saurin ɗaukar hankalin ɗan nata wanda hakan ze jawo mata gagarumar matsala!!
Seda ta numfasa sannan ta dubeni "Ke! waya baki damar kwalliya agidannan nanfa gidan bauta ne ba gidan ƴanci ba" takai maganar tana zafgan harara.
Ɗauke kaina nai ina ayyana lallai barewa bata gudu ɗanta ya rarrafa ba tabbas wannan hararar ta ya hydar bai ɗauka abanza ba ashe gado ce.
"Ke"! naji takuma daka min tsawa "bada ke nake magana ba kona fara wasa dake! takai maganar idonta cikin nawa.
Nima yau sam bana jin daɗin jikina tunda kuma mukai waya da abba yau ƴan shagwaɓar tawa suke kusa dan haka cikin sangarta nace.
"Nifa momy ba kwalliya naiba kuma naga kowa agidannan yau yana farin cikin zuwan baba shiyasa nima na sauya"! sakin bakinta tai tare da kama haɓa "iye yaushe yazama baban naki ki duba a ƴaƴan gidan nan kaf akwai baqi dazaki ce kinga baba yadawo babo ba baba ba munafuka mai baqar fuska" kallonta nai can qasa yadda baxata jiba nace."insha ALLAH ajikokin ki se ansamu baqi tunda baki haifi baqin ba ai shima kuma bakin halitta ce daga ALLAH" na tsinci bakina da faɗar hakan batare dana bari tajiba, tsaki naji ta kuma ja tare da ɗaga wayarta sannan ta ajeta a gefe ta fita.
Zama nai gami da makawa tv idanu ina daɗa nanata wannan tsana mai tarin yawa da momy take min.
ALIYU ya kaiwa iska naushi tare da furzar da wani huci daya zo masa lallai yazama dole ya takawa yarinyar nan burki danya fara kaiwa bango da wannan tsanar tata garesa, shifa ɗanso ne qarewa ma shi abun sone ga kowa tayaya za,ai yarinyar nan ta kafa masa karan tsana ada baya damuwa da qinta garesa amman yanzu yana aurenta yana kwaɗayin ya haɗa zuriya da ita kodan mahaifansu amman kuma ita daga nata ɓangaren kullum wani boren take kuma bullo masa( kanka ka sani kenan ashe babu daɗi😛😛😛 ) wannan fa dalilin shiya hana yacewa momy ta bata waya idan suna waya sabida baya son abinda ze ɓata mashi good mood ɗinshi tabbas seya horar da ita ya kuma koya mata sonshi da qaunarsa sannnn yaxo ya gasata da wannan soyayyar tasa wadda watarana idan bata gansa ba setai kusan hauka.( ji mugunta 😭😭 ) tabbas seya nuna mata shiɗin zakine kuma gwarzone agida da jeji sekuma ya nuna mata shiɗin cikakken namijine mai isa da izza wadda da kanta seta raina kanta harta kawo kanta garesa shinefa mai gara manyan mata suna kuka wiwi akansa bare kuma wannan ƴar shilar wadda bada ban darajar aure ba da ko kallo bata ishesaba amman yanzu ta dalilin aurensu yasaka tunaninsa yafara sauyawa akanta har yana tunanin haɗa shimfiɗa da ita kuma yana marmarin yaji kalar tata baiwar ta ɗiya mace wadda idan akai sa,a ya dace yasami ɗa ko ƴa daga gareta yana son ALLAH yafara basu ɗiya mace da ita mai kalar fatarta mai kalar shagwaɓarta amman bamai sangartarta ba, ayanzu haka babban burinsa ya gama aikin gabansa cikin satin gaba yahaɗo maryam su dawo gida burinsa kullum yasanya ta a idanunshi ( tofa 😳) lalubo busassun yawunsa yayi tare da haɗiyewa sannan ya furta "i miss you ƴar rigimatah" cikin sanyin jiki ya koma wajan abokan aikin nasa suna cigaba da aikin gabansu.
Har aka kusan kiran magariba banji ɗuriyar momy ba danna haka naja qafafuna na nufi ɗakina inje inci abinci sannan nai sallah tunda bani da gatan daxa,a kirani naxo naiwa yayan mahaifina barka da dawowa dan gidan gashinan tsitt hatta su rauda basuma shigoba suna can wajan mahaifinsu cikin dadin rai nikuwa wannan mugun ya rabani da nawa iyayen ya kawomin bursuna.
Ina gaf dazan kai cikin ɗakin naji wayar momy tana ringing! da sauri na koma baya ina ayya bara na ɗauka na kai mata ko ALLAH yasa inga baban abuja na masa sannu da zuwa.
My Boy naga anrubuta da manyan harufa duk tunani nama ko ɗaya daga cikin qannan yaya ne dan haka sena ɗaga burina na isar masa da cewar tana ɗakin baba amman bara na miqa mata dan kar aita kira kuma nasan daga qarshe laifina xata gani tace ina kallo ana kiranta amman naqi miko mata dan tsabar bakin hali.
Da sassarfa na miqa hannuna tare da dannan wajan ɗaga kira "assalamu alaikum momyn bata kusa amman bara na kai mata tana part ɗin baba" nakai maganar gaba ɗaya kuma ajere.
Aliyu wanda rabuwarsa da abokan aikinsa kenan ze shiga gida ya ɗora hannunsa akan ɗan dakin ɗin dake qofar gidan nasa na barrack ɗin tasu tare da lumshe manyan idanunsa yana sauraran daddaɗar muryarta wadda ayanzu yake fatan ya kasance da ita har ransa.
Sannan yaɗan lashi qasan lip's ɗinsa cikin basar da feeling ɗinshi akanta yace "ke kina miye to a falon dagajin sound ɗinnan ke kaɗai ce?" naji dirin muryar wanda banyi zato ba, cike da jin haushi daman kuma a haushin nake nace "To ina ruwan bare acikin shiga cikin Ahali" nabasa amsar cike da baqar magana.
Ɗan waro idanunsa yayi waje cike da mamaki daman ba sabga da yara ba rainin tsiya yanzu tunkafin ma taga girmanka harta fara gasa maka magana zuciyarsa ta karanta masa hakan amman seya basar tare da cewa.
"Ke malama kama bakinki tunkafin na bayyana gabanki na zubar maki da ruɓaɓɓun haqoranki wawiya ni zaki gayawa maganar banza i say me kike ke ɗaya anan?"!! ya bugamin wata iriyar tsawa.
Razana naɗanyi kaɗan tare da matse idanuna na rufesu ruf kamar yana gabana sama- sama nake mayar da numfashin tsoro batare dana ce masa komaiba.
Daɗa kara wayar yayi sosai acikin kunnensa yana jin yadda take saukar da numfashi kamar na mai cutar asma cikin murmushi kaɗan yace "farar kura kenan ga tsoro ga rashin kunya baxaki gayamin ba na kashe wayata ko kinga anata kiran sallah" naji saukar maganarsa wannan karon a hankali babu hayaniyar da.
Buɗe idanuna nai sannan na furta "kaine ai"
"Nine me" yayi saurin katseni tare da fiddo idanunsa waje.
Tura bakina nai kamar koda yaushe.
"Kaita min faɗa kana dakamin tsawa kaiko tausayina bakayi sannan kaje kayi zamanka kabarni anan anata bani wahala yanzuma fa momy cemin tai wai niba ƴar babanku bace kuma duk ƴan gidannan babu mai baqar fuskata".cike da jin haushi da takaicin maganar wadda ta maqalen a makoshina nakai maganar.
Lasar qasan lip's ɗinshi yayi kaɗan tare da furta "Ya ALLAH" aqasan maqoshinsa wai miyasa momy take hakane yatake qoqarin yada qimarta tare da tasa ne ga yarinyar nan yanzu dan ALLAH maye zata gayawa fati haka wannan ma ai salon raini ne.
"Fatie naji yaja sunana a hankali" share hawayena nai tare da furta "na,am" sanin baya son yay magana ai masa shuru.
"Kina jina kiyi haquri da momy nah dan ALLAH ki kwantar min da hankalin ki idan kuma baqar fuska ce ai yanzu zatai ta ganinta qarewa ma insha ALLAH se masu baqar fatar nan sunyi wasa a kan gadonta ƴaƴan daxan haifa dake kuma ina roqon ALLAH ya ɗora mata mugun sansu fiye da wanda take man" yakai maganar cikin rashin jin daɗi wanda na lura kamar baiji daɗin abinda taimin ɗinba.
Tura bakina nai gaba "ni wallahi yaya sakina zakai baxan haihu a inda ba,a sona ba nifa ba sonka nakeba kuma ai se da son juna ake zama" nakai maganar cike da jin haushinsu su duka.
Rintse idanunshi yayi tare da ɗan shafa jijiyar kansa wadda ta miqe yanzu jin wannan mummunan furucin nata dayafi saukar dalma zafi acikin zuciyarsa.
"Wallahi fatie ki kama kanki aurena dake HAƊIN ALLAH ne babu saki babu yaji haka zakita zama momy na bautar dake da aiki ni kuma ina moreki agado kuma da izinin ALLAH duk shekara ki haifar min ƴaƴa kinga baki da damar fita kenan" yakai maganar tare da datse kiran baki ɗaya.
Wanda ina tunanin fushi yayi dani cike da mamaki da sanyin jiki nace "to maye abin jin haushi danna ce banayi dakai...."
Maganar ce ban gama kaiwa ba naji sakon kiran baban abuja daga wajan raudah wadda take tsaye akaina yanzu.....!
*66 - 67*
Numfasawa nai sannan na miqe nabi bayanta