Author : Nil Category : Romantic Hausa Novels
zuwa part ɗin baban abujan, falonsa cike yake da jama,a kota ina kuma kowanne ka duba fuskarsa cike take da farinciki baki ɗaya falon babu bare dukkan su ƴaƴansa ne da matansa da jikokinsa abin gwanin sha,awa cike da jin kunya na ƙarasa gabansa seda na fara gaisar dashi sannan na gaida su mama muna haɗa idanu da momy ta makamin harara wadda nasan bata komai bace ba seta gaisar dasu mama danai.
Juyawa nai na gaisar da sauran qannan ya hydar na sauran ɗakunan waɗanda na girma kuma suka gaisar dani.
Cike da jin daɗi baban abuja ya kamo hannuna ya zaunar dani a gefensa sannan ya soma tambayata yaya nake dafatan ina nan lafiya babu wata damuwa cikin jin kunya nake basa amsa.
Mama ya kalla sannan yayi mata alama data miqo masa manyan jakunku nan gefensa cike da bin umarni ta miqe ta ɗauko ta kawo gabansa..
Kallona yay tare da cemin nasa su rauda su ɗaukarmin zuwa ɗakina kayan lefena ne daba,ai minba ya haɗomin daga qasar daya dawo, cikin sauri na sauka daga inda nake na durqusa nai masa godiya sannan na miqe su hafiza ƴaƴan mama cike da murna suka matso gareni suka tayani ɗaukar kayan mukai part ɗin momy sosai naga abin mamaki domin kana kallonsu kasan a tsorace suke da shigowar tasu dan baki ɗaya gashi nan ya bayyana qarara akan fuskokinsu.
Haka mukai ɗakina dasu da wayo da dibara najasu muka zauna nan muka haɗu mu wajan bakwai muna faman buɗe bags ɗin waɗanda suka kasance guda huɗune se qarama guda ɗaya kuma babu abinda babu aciki na kayan sakawa dana ado.
Bamu muka gama komai ba se wajan magariba sannan suka miqe zasu tafi part ɗinsu rauda ce tai kalar tausayi tare da ce masu dan ALLAH sisters muyi zamanmu anan wallahi momy bayanzu zata dawo ba.
Cike da tsoro kausar mai bin hafiza ɗiyar mama tace a,a sudai tafiya zasuyi haka babu yadda muka iya muka rakasu daganan kuma hira ta qara riqemu anan mukai sallah mukaci tuwo seda mama ta dawo sannan mukai masu sallama muka bar part ɗin.
ALLAH cikin ikonsa har muka koma momy bata dawoba daman kuma yau ɗin girkinta ne dan haka muka kuma bajewa a ɗakinsu rauda muka zuba hirar duniya.
Anan take cemin gobe zataje saloon na'eem kuma zataje gidan qawarta tana sauka, rau rau nai da idanuna sannan nace masu dan ALLAH su tambayarmin momy nima na bisu kaina yayi datti.
Dariya rauda tayi sannan tace ai bakida matsala tunda baba yana nan nasan zata barki.
Miqewa nai nayi musu sallama tare da nufar ɗakina..
Bayi na faɗa nai alwala nazo nai isha sannan na kwanta bacci.
Cikin baccina naji kamar anan magana akaina ina bude idanuna waɗanda suka cika da bacci naga momy.
Riqe da qugunta tana faman zabgamin harara.
"Ke haɗomin kayan da alhaji yabaki dan ubanki ina kikaga wajan zama agidan nan bare har awani baki lefe to wallahi karɓesu zanyi"! cike da sanyin jiki na miqe na tsugunna nabata haquri.sannan na haɗa kayan tsaf nina dinga haɗa jakunkunan ina kai mata bedroom ɗinta har na gama jerasu sannan na komo ɗaki na kwanta na cigaba da baccina sabida ni daman ban saka akaina ba ɗanta ma ban damu dashiba bare wani lefen sa.
Da asuba na tashi nai wanka nai sallah sannan nai azkar ɗakinta na nufa sanin tana part ɗin baba kaɗe mata dattin gado nai sannan nai mata mopping wucewa toilet nai na wanke matashi tas sannan na koma kicin na sharosa na kunna gas na ɗora ruwan zafi.
Lokacin dana fito qarfe bakwai dan haka senahau sharar falo kuɗi nagani zube akan kujera na haɗesu tas na aje mata akan t.v stand sannan na haɗa ruwan mopping ɗin falon na fara seda na gama komai tsaf sannan naje ɗakinsu rauda ko juyi basuyi ba kallon agogon ɗakin nayi qarfe takwas da wani abu nai murmushi tare da haskoni agaban umma ada sannan naja masu qofar nayi kicin.
Ruwan dana ɗora akan gas naga ya tafasa dan haka na saukesa na zuba a tea flask sannan na ɗebo dankali nafara ferayewa ina gama ferayar na yayyan kasa yadda zanji dadin suya sannan na zuba mai a kasko nasoma soya dankalin ina gamawa na sauke man na kashe gas ɗin sannan na ɗauko albasa da taruhu na gyarasu nan na mayarda miyar sourse mai kwai wadda za,a iyacin dankali da ita.
Lokacin dana gama aikin qarfe taran safiya na ɗibi nawa na jere masu nasu daman haka ta umarcan tun jiya sannan na fice nai ɗakina.
Harɗe qafa nai inacin dankalin ina kora ruwan liptom cike da kuzari na kammala cin abin sannan na kai kwanukan kicin zama nai abakin katifa ta na soma tsefe kitson kaina wanda har wajan goma ban gamaba seda na gama sannan na kaɗe ɗakin nawa na gyara se kawai na wuce bayi na haɗa ruwa mai zafi nai wanka batare dana wanke kaina ba sanin zamu fita anjima.
Rigar atamfa nasaka da mayafinta sannn na nufi falo tarar da momy zaune taci kwalliya nai tana danna wayarta.
Bayan na gaisar da ita cike da tuhuma tacemin ina na aje mata kuɗinta tsaye na miqe naje gaban stand na dauko na bata su sannan na koma na zauna tare da zabga tagumi.
Nidai naga momy tana ta ɗaga waya bini bini cike da murna akan fuskarta.
Seduk abin ya dauremin kai ana haka naga su rauda sun fito cikin shiri hannun na'eem da keyn mota gaban momy suka tsugunna sukai mata sallama tare da kallona sis taso mu wuce nidai naga momy bata tanka mana ba.
Bayan datace semun dawo abakin part ɗin baban abuja na tsaya nace masu bara naje na gaisar dashi dariya rauda tai "hmm waya gaya maki baba na tashi yanzu ai se 12" wara idanuna nai sannan na'eem taja hannuna mukai parking space.
Wata farar venz ta bude muka shiga ban gama tsinkewa ba seda naga yarinyar taja motar tare da nufar gate nan danan aka bude mana muka fice nan muka ɗauki hanyar inda zamuje.
Gidan anty hafsa muka fara zuwa mai bin ya hydar wadda bama shiri da ita.
Amman abin mamaki yau itace harda tsokanata kuma sosai ta sakarmin fuska mukaita hira da ita daman ashe itama tsoron uwarta ya hana ta kulani.
Bamu muka bar gidan ba se qarfe ɗayan rana bayan munci munsha takuma sadani da kayan kwalliya masu uban yawa wai naiwa ɗan uwanta ado.
Ahanya nake cewa su rauda wai yanaga momy bata min magana ba dazamu taho? dariya suka saki tare da cewa yau ai sister momy tana cikin busy ne yaya hydar zedawofa yau, wai anty maryam ce batajin daɗi shine ake tunanin ko haihuwa ce amman shi naji ance ze koma bayan ya kawota, dariya nayi tare da cewa haba shiyasa naga momy yau anata far,a ashe ɗan lele ne ze dawo.
Suma dariyar suka kumayi cike da surutu na'eem tace ai muma se ɗazu mukaji yana gayawa momy ina tunanin tafiyar sama taka tazo masu amman da ai ba yanzu ze dawo ba.
Haka mukaita hiranmu har muka qarasa wajan saloon ɗin, ni aka farawa gyaran kan sannan akai masu suma nan muka kuma rankayawa mukai gidan qawar rauda.
Jirgin shabiyun rana suka biyo duk maryam ta ɗaga masa hankali da kuka jiki babu daɗi driver ya ɗaukosu zuwa gida.
Part ɗin momy suka sauka bayan ta cikasu da kayan ci dana sha kala kala shikam miqewa yay zuwa part ɗin Mahaifinsa seda yayi masa barka da zuwa suka ɗan zanta sannan ya fito ya nufi bangarorin su mama suma ya gaisar dasu.
Part ɗin sa ya koma yayi wanka yayi sallah sannan ya zira jallabiya ya nufi part ɗin momy, bakaramin mamaki yayiba ganin maryam ta ware sunata hira itada momy.
Zama yayi akan kujera tare da ɗora qafa ɗaya kan ɗaya.
"hajiya wai ina yaran nan ne?" cike da far,a momy tace "sun tafi gyaran gashi ne" tana gaya masa haka ta juya ga maryam suna hiransu.
"Fatiemah fa naga tunda nazo ban gantaba" yafaɗa yana kallon momy danshi danda yay fushi da ita sabida maganar data gaya masa jiya amman kuma seyaji ya kasa daure hakan
Wani sakaran kallo ta watsa masa mai kama da baka da hankali sannan tace "to maye haɗinka da ita zaka wani ce tana ina to ta bisu"! takai maganar tana maka masa wata banxar harara!.
Tsit maryam tai tana son ganin action ɗin daxe ɗauka.
Itama momyn zuba masa idanu tai cike da harara tana kallonsa.
Wani irin firgicine ya dirar masa mai cike da rudani kamar ba Aliyu ba ya miqe tsaye jikinsa har yana mazari "what!! momy ban gane ba?" yakai maganar yana zube hannayensa akan kujerar da momyn take kai.
"Eh abinda kunnenka yaji shinake sake gaya maka nace ta bisu itama ta wanke kan nata kaga yau kusan watanta guda da sati guda kanta akwai datti" takai maganar cikin bawa abun rashin mahimmanci.
Rau rau yay da fuska kamar ze saka kuka tare da kaiwa kujerar naushi "haba hajiya haba hajiya akan me baxaki gayamin ba akan me baxakice tanemi izinina ba saraifa kinsa yadda garin nan yake babu lafiya" sakin baki da hanci momy da maryam sukai suna binsa da idanu cike da ɗumbin mamaki.
"To ubana dakeni sabida nabar matarka ta fita ko oho ashe kai sontane maqure acikin ranka kai ko kunyar faɗan hakan bakai ba to idan ma dawani guntun munafurcin sonta aranka gwara tun wuri ka cire dan wallahi baxan yarda ba ni nai gaba qaryar aisha tai nasara akaina" takai maganar tana zuba uban huci.
Lumshe idanunsa yayi tare da warasu akanta "hajiya ta yaya wai zanqi fatimah alhalin itan ahalina ce jinina ce matata ce ta sunna wadda ALLAH ya haɗa aurena da ita batare dani na shirya hakan ba hajiya bafa musan mai ALLAH ya boye mana da hakan.....tas! tas! ta tsinkesa da mari akaron farko acikin rayuwarta sannan ta miqe! "wallahi tallahi ba,a isa anyi min haka ba ninasan bayin kanka bane asiri akai maka agabana zaka lissafamin wannan maganganun dagaske baba son fatima kake"tafaɗa tana cakumarsa kamar wata mahaukaciya "na shiga uku ni zainab walllahi baka isaba baxanga wannan baqar ranar ba" takai maganar tana saka wani mahaukacin kuka! cikin sauri naga maryam ta miqe tai ɗakin momyn itama tana wani irin kuka mai taɓa zuciya.
Saka hannunsa yayi akan kafaɗun momy murya cike da tarin damuwa "hajiya kidaina kuka akaina ALLAH ze fushi dani amman ina son ki nutsu momy mu ɗauki qaddarar mu haqiqa aurena da fatimah darasine akanki dan ALLAH momy kibarni naji da abinda yake damuna ƴar da bakya so bakya son mahaifanta ita ALLAH ya jarabci ɗanki wanda kika fiso fiye da komai a rayuwarki yake bala'in so wallahi momy akan fatima zaki iya rasani wallahi momy zan bar maki garin nan akan fatima momy zan dauketa mu gudu" yakai maganar kamar ɗan maye.
Jada baya momy tai tana kara mutstsike idanunta can kuma ta kamo hannunsa ta ɗora akan kirjinta sekuma ta rungumesa tana sakin kuka "baba kada kaimin haka tabbas senaje an karya maka wannan sihiri wallahi baba asiri sukai maka bakai bane ba wallahi baxanga wannan baqar rana ba" daɗa rungumeta yayi yana jin wata iriyar masifffiyar soyayyar batula acikin ransa jiyake kamar ya zauce akanta.
Zame momy yayi daga jikinsa tare da zaunar da ita.
Ya tsugunna gabanta yana gaya mata kalamai masu sanyi cike da siyasa ya kwantar mata da hankalinta amman ransa yana ga fatimansa.
Miqewa yay momy tajawosa kaiwa ALLAH baba kada ka sake nakuma jin ka furta soyayyar wannan ƴar agabana sannan kada ka sake ko hannunta ka kama bare akai ga zance kwanciya.
Haɗiye miyau yayi sannan ya qaqaro murmushin dole ya maka mata hajiya karki damu indai dan wannan ne.
Yakai maganar yana ficewa a falon yabarta da zancen zuci.
Number raudah ya fara nema danya kira yaci uban fati yaji kuma wata tambaya ta fita batare daya bata damar hakan ba sama da awa uku suna titi......!
Ringing! wayar tasa ta shigayi amman shuru ba,a ɗauka ba qwafa yayi tare da sake kira a wannan karon aka ɗaga wayar.
Cikin rawar jiki raudah ta ɗauki wayar tare da rissinar da kanta a qasa kamar yana gabanta.
"Assalamu Alaikum, yaya barka da rana?" lumshe idanunsa yay waɗanda suka cika da zallar ɓacin rai tare da furta "gidan uban wa kuka je"! yafaɗa cikin wata iriyar tsawa mai shiga jikin mutum! da sauri rauda ta haɗiye miyau sannan tace "yaya ai mungayawa momy wallahi gyaran gashi mukaje" takai maganar tana kallon su batula waɗanda duk sukai tsaye suna jin yadda sautin qarajinsa ya cika wayar.
"Nabaku minti goma ku dawo gida idan kuka ɗara wallahi se ranku yayi mugun ɓaci"! yakai maganar tare da qatse wayar tasa qitt!
Wata zubace takaryo ma rauda sannan ta sharce ta juya ta kalli su batula"todai kunji abinda yaya yace saboda haka kawai muwuce gida kada mu tsaya shiririta ya jibgemu" takai maganar tana kallonsu.
Nikam lumshe ido nai tare da ce mata "dan ALLAH barsa wallahi muyi zamanmu har mugama abinda zamuyi daga zuwansa zewani ɗagawa mutane hankali" naqarasa maganar ina jan tsaki! zaro idanu na'em tai sannan ta kalli raudah "nikam kunga tafiyata wallahi bazan tsaya ya lafceni a iskaba itama rauda bin bayanta tayi tare da kamo hannuna "sis zomu wuce mana kin tsaya kingafa keyn yana hannunta kada ta wuce tabarmu wallahi na'eem ba hankali gareta ba" takai maganar tana jan hannuna turjewa nai na tsaya "kinga dan ALLAH kuje kawai nifa sena koma wajan nan anyi mani kitso dan wallahi bazan tafi da kaina babu kitsoba dan gidanku babu wanda ya iya bare aimin" ɗan jimm tai sannan tace "to mu yanzu kenan mu wuce ko yaya?" taqarasa tana kallona dan taji mezance mata ,kaɗa kafaɗata nai alamun ko ajikina sannan nace "kawai kutafi ai da ragowar kuɗi a hannuna zan gane gida na taho" kamar zatai kuka haka taja jikinta ta faɗa mota na'eem ce ta dubeta "a,a yanaga sis ta tsaya lafiya dai?" gaya mata yadda sukai da batula tai jimm na'eem tayi sannan ta tayar da motar suka bar wajan.
Juyawa nai na nufi wajan da akai mana saloon ɗin bayan na shiga muka kuma gaisawa da matar sannan na gaya mata abinda nake buqata, cemin tai na zauna naɗan jira agamawa wata mata sannan mufara.
Jarida ta miqomin wai na karanta sannan ta bani lemo da ruwa cike da farin ciki na karɓa nai mata godiya sannan na zauna ina nazarin jaridar hannun nawa kafin a soma min.
Cikin minti 30 aka kammalawa matar sannan nima na matsa aka soma yarfamin wanda na zaɓa qananu mai ɗan karan kyau.
Tafiyar mintuna goma takaisu gida abakin gate sukai horn mai gadi ya buɗe masu suka harba kan motarsu cikin gidan.
Bayan sunyi parking suka qarasa cikin gida seda suka kusan qarasawa part ɗin momy sannan rauda ta dubi na'eem sis anya bamuyi mistake ɗin barin sister acan ba?" alama tai da hannunta na ko'in kula sannan ta dubi rauda "nifa tsiyata dake tsoro wai ita yarinyace daba xata iya kawo kanta gida ba aidai munfuta haqqinta" takai maganar tana yin gaba abinta.
Tundaga bakin qofar falon momy suka hangosa yakai ya kawo da alamun kamar yana jiran wani abunne da sassarfa suka qarasa gabansa suka tsugunna "yaya mun dawo" yaji saukar muryarsu acikin kunnensa! juyowa yay yana bin kowannensu da kallo kafin ya dire idanunsa akan rauda! "ina fatie?" ya jefo masu tambayar batare daya amsa maganarsu ta farko ba.
Gabaki ɗayansu suka dafe kirjinsu sannan rauda tai qarfin hali "munce tazo mutafi gida tace ita setai kitso tana can HANAN SALOON mun barta acan" takai maganar tana sada kanta a qasa.
Waro idanunsa yayi yana ɗan shafa sumar kansa mai uban yawa sannan ya kuma dubarsu "dan kutumar ubanku wayace kutafi da ita uban waye yace kubarmin mata acan ehe!!! ya buga masu wata mahaukaciyar tsawa wadda ta amsa ilahirin gidan baki ɗaya, da gudu suka miqe suka fara neman hanyar ɓuya ganin yadda ya hauro kamar zedake su Cikin wani irin zafin nama wanda se sojan kaɗai yasan dashi sabida horo wajan training ya cafkosu suduka biyun ya haɗa kansu waje ɗaya yakai musu wani mahaukacin bugu! ahaɗe suka saka kuka suna basa hakuri amman ina ran ƴan mazan ya ɓaci seda ya dakesu iya duka ba maceci sannan ya gwarasu da bangon qofar ya haure ya bar wajan tare da qara gargaɗinsu akan kada koda wasa sukuma futar masa da mata waje.
Da wani irin gudu har suna gware suka bar wajan sukai ciki kai tsaye ɗakin momy suka faɗa suna wani irin gunjin kuka kamar babu gobe....!
Da,azama momy tasaki maryam wadda take kwance bisa cinyarta tana aikin kukan abinda hydar yay ɗazu, tare da qarasowa gaban ƴaƴan nata har zaninta yana kwancewa.
"waya tabaku daga ina kuke?" takai maganar a hargitse!
Jikinta suka faɗa sannan suka fara labarta mata abinda ya faru cike da qufula momy ta dubesu "ina shi baban yake wata kan akan wannan baqar kadarar yakeson illata min ku to wallahi bara yaxo daga shi har itana se ransu ya ɓaci baxan yarda a illataminku ba"! cike da kuka na'eem ta ɗago "a,a momy bafa laifin anty fatima bane yaya ne kawai da zuciya amman maye abin duka anan" takai maganar tana sakin kuka!"
"Dalla can matsa waye babban munafuki idan ba itaba taje tai asiri anason haukata mun ɗa shine zakice min haka bayan akanta yakeson illata mun ku" takai maganar tana daɗa matsesu ajikinta tare da ɗaukar alwashi akan batula mai tsauri.
Tsaki maryam taja cike da ɓacin rai da kishi mai zafin gaske tabar ɗakin tana jin yadda ɗan cikinta yake juyawa sabida ɓacin rai.
Dawani irin sauri kamar banasa ba yabar gidan koda yaje parking space d a zafin nama ya shige wata baqar mota yana dannan horn kamar ze kunna gidan da gudu aka bude masa motar yabar gidan yana wani irin mahaukacin gudu na fitar hankali.
Allah ne yakaisa lafiya danma titin abuja bakamar na nan ba da ɗan qarancin motoci.
Abakin wajan yayi parking batare daya kashe motarba ya futa daga ciki ya nufi cikin HANAN SALOON ɗin kasancewar wajan ba boyayye bane ba agarin na abuja.
Daga wajen wajan ya tsaya sabida wajene na mata sannan ya ɗauki number mai wajan yafara nemanta a waya.
Cikin kamala matar ta ɗauka sama sama suka gaisa sannan ya gaya mata cewar ta turo