Author : Nil Category : Romantic Hausa Novels
qiris yake ya fashe!
Buɗe masu ɗakin akai wanda ya kasance bakikkirin babu kyan gani duk da rana ce amman bai hana sauro kawowa fuskokinsu hariba, seda officern ya buɗe window sannan suka samu damar zarafin hango batula wadda take tsugunne daga ita se doguwar rigar jiya data saka se hijabi wanda yakasance fari amman duk yama ɓaci da datti da ruwan hawaye.
Cike da tausayi suka nufeta batare da sun iya magana ba, baban abuja shinema yay qarfin halin kiran sunanta "Faɗimata zonan ALLAH ze fitar dake alfarmar annabi duk wanda yay maki wannan sharrin seya koma masa" cikin tashin hankali ta ɗago fuskarta ta dubesu batare datai motsiba sekuma can taja hannunta mai lafiyar ta miqe sannan ta tallafi wanda tai karayar ta nufi baban abuja aguje!
"Na shiga uku baba innalillahi wainnah ilaihirraju,un, yauni batula ake zargi da kisan kai kisanma na ƴar ɗan uwana mijina wallahi tallahi baba bani na kasheta ba,wallahi baba faɗuwa mukai dukkanmu naxo ɗaukarta baba ka fuskanceni tayaya za,ai na kasheta babaaaa!!! takai maganar tana faɗuwa luww tai qasa sakamakon rashin cin abincin datai ga tashin hankali seda aka zuba mata ruwa sannan taja numfashinta cike da tashin hankali ta rarumi hydar wanda yazama fasta a wajan.
"Yaya ka fitar dani anan ban saba ba tunda nazo nakejin tsoro yaya bani na kashe maka ƴarkaba wallahi baxan iya kashe mutum ba, yaya na yarda zan zauna dakai ina sonka matuqar ka fitar dani daganan wayyo zuciyata zan mutu......!! takai maganar kamar mahaukaciya.
Zuciyarsa ce ta karye batare dayaji kunyar mahaifinsaba ya haɗeta da jikinsa ya manneta a faffaɗan kirjinshi,yana shafa bayanta. cikin tausayi baban abuja yabar wajan hakama officer suka watse tare da karo masu qofar.
Ya ɗauki tsahon mintina yana shafa mata bayanta, ya lura kamar taɗan sami matsalar gushewar tunani cikin lallami yadinga tofa mata addu,a cikin kunnenta daya gama ya ɗagota ya shafe mata jikinta da addu,ar daya mata sannan ya zira harshansa yana laso hawayenta yana haɗiyewa abakinsa zaunar da ita yay ajikinsa sannan shima ya zauna duk da dattin dake wajan.
Matseta yay sosai a jikinsa yana fesar da numfashi.
Zira harshensa yay yana laso cikin kunnenta kafin ya soma magana cikin rawar murya kamar ze mata kuka!!
"Fatimah! zahara'u batula sayyida ina sonki matata wallahi bana zarginki da kashemin ƴata domin nasan wacece ke dan ALLAH dan son ma,aiki ki kwantar min da hankalinki ina tare dake babu abinda ze sauyani idanma sunyi hakane dansu rabani dake toni wannan qarin igiyoyin aurenmu ne, zan miki halacci zan nuna miki ni mai sonkine a kowani yanayi zanyi iya yina da kuɗina da lafiya da duk abinda na mallaka domin ganin kinyi free matata! yakai maganar yana sake rungumeta tare da fashewa da kuka wiwi kamar mace "fatima ina tausayinki kin karyan zuciya wallahi daga yau naita maki kuka kenan harse ALLAH ya wankeki daga wannan sarqar" yakarasa yana zubar da hawaye masu gudu.
Cikin mamaki na ɗago kaina ina kallon yaya hydar tare da mamakin wannan lamari lallai na yarda so ba qarya ba tabbas yaya hydar masoyine na rantse duk duniya babu mai sona seshi ƴarsafa ake zargin na kashe amman yaxo yana min kuka! nikam dame zan saka masa a rayuwa na rantse koda wannan kaɗai ya barni wallahi ya nuna qololuwar so.
Wata irin kunyarsa ce ta kamani nan da nan rashin mutuncin dana masa jiya ya faɗomin, janye jikina nai anasa ina cigaba da gunji kukan bakin ciki.
"Yaya kaimin halacci kai kam wani irin mutum ne ana zargin na kashe maka ɗiya amman kana nan kanamun kuka!" nakai maganar ina kallonsa da jajayen idanuna.
Jawoni ya kuma yi tare da bani amsa da cewa "so dan ALLAH kenan yanzu muna fita zan nema mana lauya insha ALLAH, cikin lafazi mai daɗi yadinga kwantarmin da hankalina tare da gayamin manyan musalai na ɗaukar qaddara sannan ya janyeni ya miqe sabida maganar da akai masa lokacin ganina ya cika.
Koda wasa banyi gigin nuna masa naji ciwo a hannuna ba haka mukai sallama yabar ɗakin.
Komawa da baya nai ina kuka "YA ALLAH KABANI IKON YIWA YAYA HYDAR HALACCI KAMAR YADDA YAMIN ALLAH KADA KASAKA NA JUYA MASA BAYA INA SONKA MIJINA...."
*90 -91*
Cikin sanyin jiki ya qarasa wajansu baba sannan suka fita daga section ɗin tunda yabar ɗakin datake yakejin zuciyarsa babu daɗi sosai batula ta basa tausayi ba ɗan kaɗanba da haka sukai sallama da officern sannan suka nufi gida.
Cirko-cirko suka tarar da kowa na gidan sabida tashin hankalin abinda ke faruwa, a tsakiyar farfajiyar gidan suka rabu da baba inda shikuma ya nufi part ɗinsa.
Cike da sanyin jiki yake taka qafafunshi koda yazo dai dai bakin part ɗinsa yaji sakon kiran momy daga wajan na'eem qanwarsa wadda kallo guda zakai mata kasan taci kuka ta qoshi.
Juya akalar komawar tasa yay tare da nufar part ɗin momy, zaune ya tarar da ita gefenta su hafsat ne se maryam wadda take sanye da hijab kana kallonta kasan tana cikin tashin hankali kallo guda yayma side ɗin datake ya kauda kansa batare daya tankataba.
Zama yay akan qafafunshi yana mai dafe kansa da hannayenshi wanda yake barazanar rabewa biyu sabida tsabar tension ɗin daya masa ca! ɗago rinannun idanunsa yay waɗanda suka kaɗa sukai jawur! ya ɗora akan momy batare daya tankataba.
"Baba nasan kaji duk abinda yake faruwa, a gidannan amman ni abinda nai shine dai dai dan wallahi sena bi duk yadda zanyi abimana hakkin jininmu, se abu nagaba mahaifinka yace nabar masa gidannan to babu komai zan tafi amman nasan da xarar gaskiya tai halinta ze neman ne da kansa dan haka seka san inda zaka kaini dan goɗai goɗai dani baxan nufi maiduguri da sunan sakiba" takai maganar tana kallonsa.
Adaqile ya furta "Allah ya kyauta" batare daya tanka maganarta ba, sannan ya kuma cewa"ki koma gidan dake gwarumfa tunda clean yake" daman yana da wani gida acan ɗin shiyasa yace ta koma can...
Yana gama gaya mata haka ya miqe yana rintse idanunsa duk duniya babu wanda ya isa yay masa wannan cin mutuncin sannan ya zauna inuwa guda dashi idan ba itaba domin mahaifi yafi qarfin wasa yaya ze da ita duk tsiya mahaifiyarsa ce.
"Baba! takira sunansa ganin zebar wajan "maryam baxata koma gidansuba abisa umarnina ban amince taje ko ina ba yau zata koma part ɗinkama kuma ko kallon banxa ban amince kai mataba dan dame zataji idan banda rashin imani a kashe mata ƴa sannan ace ta tafi gida ubanka zatai maka agidan nasu!! takai maganar cikin masifa.
Ko qala bai ce mata ba haka yaja qafarsa yabar falon, bai koma part ɗin nasaba kawai seya dauki mota yabar gidan wajan wani abokinsa yaje wanda yay masa jagora wajan wani lauya wanda ze tsaya amatsayin lauyan batula duk wani abu seda hydar ya sanarwa da lauyan mai suna br.saddiq sannan sukai sallama akan gobe zezo ya ɗauki, hydar ɗin suje can wajan batulan danya mata wasu tambayoyi.
Itama momy sun ɗauki nasu lauyan batare kuma datai shawara da kowaba haka xalika aranar ta ɗaga tabar gidan baba inda baba yace kada ta tafar masa da ɗa ko ɗaya. haka ta wuce gidan hydar na gwarumfa batare da ko kare yay mata rakiyaba.
Maryam kam ta koma part ɗin hydar amman har yanzuma bata saka sa a idanuntaba, sannan ga mamy mahaifiyarta taqi zuwa kuma ta hana kowa yazo tace babu ruwanta tsuntsun dayaja ruwa shi ruwa kan duka.
Haka ta zauna a part ɗin sukuku duk jikinta babu daɗi ga bakin cikin rashin ɗiyarta.
Bai shigo gidanba se bayan sallar isha sannan yay wanka ya kuma fita, wani wajan siyan abinci yaje yasai abinci da lemo da ruwa ya nufi sitation ɗin officern yay ma waya ya basa kayan abincin sannan yabar sitation ɗin ya kuma komawa gida, kai tsaye ɗakinsa ya wuce ya kullo kansa ya zauna ya saka kuka! kamar wani yaron goye, babu mai rarrashinsa shikaɗai yasan yadda yakeji acikin ransa.
Babu yadda ummi batai da umma akan su wuce gidan, baban abuja ba amman umma taqi tace wallahi ita yanzu bata kaunar kowa na gidan sabida haka zata sauka agidan wata qawarta anan ɗin har zuwa sanda zataga abinda ya turewa buxu naɗi sannan hydar ya sakarmata ƴa tai gida da ita, dan ita a ganinta kowa na gidan yana da laifi tunda suka bari aka tafi da batula batare dasun tsayar ba.
Agidan qawartan kuwa suka sauka kuma matar mai kirki da ƴaƴanta sa,annin ummi nan aka bawa umma da ummi ɗaki aka basu abinci da komai matar qawar umma mai suna anty habiba mace mai kirki ita taita baiwa umma haquri akan tabari se gobe saji yadda abin yake, abincin dai se ummice taci amman ita umma ko ruwa bata iya shaba haka tai alwala ta kalli gabas tana miqawa ubangiji lamarinta.
Suma su abba baxu zoba se wajan goman dare cikin mamaki baban abuja ya taresu anan suke shaida masa cewar mama ce ta kira take gaya masu cikin faɗa ya dinga magana yace mai yasa aka shaida musu mezasuyi subarsa mana ai ze dauki dukkan matakin daya kamata seda abba ya shaida masa ai magana ta cika gari harma umma taji sun taho sannan kuma aka shiga tambayar ina umman take.
A,a koda baba ya tura cikin gidan mama ta shaida masa umma bata zoba tuni hankalin abba ya tashi ganin ai sun rigasu zuwa, seda ya kira anty zee sannan ta shaida masa ummi takirasu tagaya masu sun sauka agidan qawar umma, karɓar number yay awajan anty zee sannan ya adanata yana ayyana akwai dramar kenan gaba!
Cikin dubara ya nuna wa ƴan uwan nasa cewar umma ta sauka agidan qawarta ne sabida yafi kusa kuma sungaji amman bai nuna cewar wata matsalace ta tsaida ita acan ɗinba.
Cike da bakin cikin lamarin suka kwana wanda umma hydar batula yadda sukaga dare haka sukaga rana, inda ita batula tsoro bargaba ga ciwon da hannunta yake mata sune suka hanata bacci ga tashin hankalin datace ciki.
Shikam hydar tunanin sahibarsa da halin datake ciki sune suka hanasa rintsawa.
Da asuba suka haɗu dasu abba amasallaci, cike da ɗumbin mamaki hydar ya qarasa gabansu suka gaisa cikin kunyar abinda mahaifiyarsa tai yake bawa abba haquri tare da ɗaukar alwashin komai zezo cikin sauki da yardar ALLAH.
Sannan ya shaida masu da safan nan za,a fara zaman kotu sabida yafison ai shari,ar da wuri shine dalilin dayasa ya ɗauki lauya sabida bayansa ta daɗe a cell.
Murmushi abba yay sannan yace masa ai su basuga laifinshiba dan kuwa baima ƴar uwarsa komaiba illa mahaifiyarsa wadda suke fatan ALLAH ya gaggauta bayyana gaskiya sannan kuma wannan abun baxe taɓa saka zumuncinsu ya lalaceba.
Haka suka qarasa gida shikam qarfe bakwai yabar gidan dagashi se jallabiya fara, ya nufi wajan lauyan da aka haɗasu jiya br.saddiq, seda suka gama sannan shi yay gida br shikuma yay kotu dan kai report.
*92 - 93*
Bai break fast ba haka ya watsa ruwa a gurguje! sannan ya fito kaya masu sauqin nauyi ya saka ajikinsa tare da ɗaukar makullin motarsa ya nufi cikin gidan.
Abakin falon baba ya tsaya ya amsa wayan br.saddiq sannan ya katse ya nufi cikin falon kiciɓus sukai dasu abba waɗanda suke shirin fitowa suma, haka suka ɗungumo zuwa haraban gidan, amotarsa ya ɗauki baban abuja, inda sauran ƴan gidan suka hau babbar motar siyana sabida yau ɗin za,a fara zaman kotu yana da kyau kowa ya halacci wajan.
Maryam da sassarfa tazo zata buɗe motar dayake ciki, bayan baban abuja yana gidan baya dama gidan gaba kuma emty ne, hararar daya maka mata ita ta saka taja jikinta tabar wajan kafin shima yaja motarsa ya baɗeta da qura.
Tafiyar mintina kaɗan takaisu babbar kotun daxa,a gudanar da shari,ar bakuma su daɗe da shiga cikiba sega motansu abba nan itama kotun tafara cika babu laifi dan seda aka gudanar da wata shari,ar kafin afara shirye shiryen tasun.
Cikin mintuna kaɗan itama momy ta shigo bata zauna wajan ko da ƴaƴanta ba seta nemi gu can ta zauna ita ɗaya kafin lauyan nata yazo su miqe su fita wadda nan da nan maryam tabi bayansu itama.
Cikin bakin ciki hydar ya sada kansa a qasa yana jin takaicin abinda momy take wanda ko wajan su abba batazo ta gaidasu ba, wannan abun ya daurewa kowa na wajan kai hatta ga ƴaƴanta.
Bayan wani lokaci mai shari,a ya nemi ƴansan dan kotu dasu je station ɗin da aka rufe batula wanda yake kusa da kotun domin su kawota sannan br saddiq ya miqe ya kaiwa mai shari,a record ɗinsu da komai sannan ya dawo ya zauna.
Zamansa da kaɗan suma su momy suka kuma dawowa cikin kotun sannan suka zauna.
Shigowar umma ita ta ɗaurewa hydar kai daman taxo bayanta ummice wadda sukai waya da abba ɗazu a wayan anty habiba yay masu direction ɗin kotun, bayan ummi anty habiba ce da mijinta.
Da qyar umma ta gaisa da baban abuja da sauran mutanan wajan sannan tanemi gu nesa dasu ta zauna tabar ummi tana gaisawa da sauran mutan gidan.
Kallo guda zakaiwa umma kasan akwai amtsala ganin kamar bata gansaba yasa ya tashi yaje gareta ya durqusa ya gaishe da qyar umma ta amsa masa tare da kauda kanta gefe.
Cike da ɗumbin mamaki hydar ya koma domin bai saba ganin hakan garetaba.
Tsakaninta da momy kam se kallo da watsa harara daman ance mai haquri bai iya fushiba sosai yadda umma ta share kowa yabasu mamaki shikam abba dayake yasan halin matar tasa idan ƴan abunta suka motsa yaja bakinsa yay gum!
Shigowar ƴan sanda mata biyu riqe da hannun batula wadda ta sada kanta a qasa bata kallon kowa shiya ɗago da umma cikin furgici ta nufi ƴar tata wanda kafin taje ummi da rauda sun miqe da zafin nama sun riqeta suna bata haquri tana kuka tana kiran sunan batula haka aka wuce da ita can kan abinda ake tsayar da masu laifi a kotu.
Shikam hydar harta wuce bai iya ɗago idanunshiba sema share wata qwallar takaici yake damma ya dakatar da duk wani ɗan jarida akan halartar shari,ar tasu
Sosai umma take kuka! inda batula ta ɗago idanunta ta zuba akan mahaifanta baki ɗayama hawayen nata ya qafe haka aka fara gabatar da shari,ar.
Lauyan su ya hydar shiya soma tashi sabida sune suka shigar da qarar tun wuri kafin su momy.
"Ya mai girma mai shari,a sunana BR.SADDIQ A YUSUF! nine mai shigar da qarar maryam wadda taiwa kishiyarta fatima kabir uba! sharri akan ta kashe mata ɗiyarta!.........yabada duk wani labari wanda ya gabata a shafukan mu na baya dangane da yadda akai batulan ta ɗauki ƴar wanda ya samesu a wajanta ajiya bayan hydar yay masa jagora sannan ya ɗora da cewa" ko mai girma mai shari,a ze bawa wadda ake zargi damar muji ta bakinta?" gyaran murya mai shari,a yay kafin yace "kotu ta baka dama" murmushi br yay kafin yace "ina godiya" sannan ya juya gareta "malama muna son muji sunanki da tarihinki ataqaice sannan kuma munason ki gaya wa kotu yaya akai wannan lamarin ya faru har wannan kishiyar taki ta jefeki da wannan bakin qazafin"!
"objection my lord!! lauyan su momy ya miqe tsaye, "sunana br wada usman nine wanda nake kare maryam wadda wannan kishiyar tata ta kashe mata ƴa ina son wannan kotu tamu mai adalci datai watsi da wannan qara da br saddiq ya shigar ta kuma bamu, tabamu damar ɗaukaka qara zuwa mataki nagaba duba da yadda fatima ta zalunci maryam ta kashe mata jinjirarta da ganganci ƴar kwanaki biyu da haihuwa" sannan ya koma ya zauna.
Ɗan rubutu mai shari,a yay kafin ya dubi br wada "kotu bata amince da wannan qorafin nakaba harse kun bamu manyan hujjoji da shaidu waɗanda zasu tabbatar mana da zarginku ga fatima gaskiyane" sannan ya juya ga br saddiq yace "kotu na sauraranka br" miqewa tsaye br.saddiq ya kumayi a karo na biyu sannan ya dubi batula wadda tunda aka soma take kuka! "malama fatima inason kiyi haquri ki fawwala ALLAH komai insha ALLAH inda muna da gaskiya ALLAH baxe bamu kunya ba, sannan ki ɗago kanki kiyiwa mai sharia bayani cikin nutsuwa wannan kotu mai adalci ce insha ALLAH zaki samu mai shari,a da maki adalci" yakai maganar yana kallonta
Ɗago kaina nai ganin yawan muta nan cikin kotun su suka sake hargitsani dubana makai ga umma wadda ta kafeni da ido kamar zata aro bakina sannan na kalli ya Hydar wanda yaketamin alama da idanunsa akan nai magana!
"Sunana fatima kabi uba magini, amman ummammu nacemin batula inada shekara goma sha takwas da haihuwa,sannan naja numfashi na shaqi majina! kuma ina auren Aliyu muhd uba magini! wanda ina faɗin haka yaya ya ɗago yana min kallon tausayawa! nidai wallahi tallahi mai shari,a ban kashe masu ƴarsuba amman nasan munfaɗi lokacin danaga tana kuka a falo zata faɗo daga saman kujera naje danna bata taimako senaji kamar anjani da abu mai santsi wallahi ban kuma sanin komaiba seji nai momy na cewa ƴansanda su tafi dani" sannan na ɗago hannuna mai karayar na nuna masa"kalla kaga hannuna ya karye ta dalilin bata taimako amman duk da haka ban tsiraba seda aka jefeni da baqar lamba wadda zatai ta bina" kallon momy nai"mai yasa momy zaki zaɓi cimin mutunci da min qazafin kisan kai akan dalilin qin da kikemin? miyasa baxaki umarci ɗanki ya sakeni ba shine harsekin ɓatamin raina da sunana dana dangina wallahi tallahi momy ko duk duniya zaki haɗa akan na yafe maki wannan qazafin wallahi baxan yafe maki ba har abada" ina kai maganar naga kowa ya kalloni musamman shi wanda idan ba idona kemin gixoba kuka yake! watsar dashi nai na juya ga maryam"kekuma bakin haɗan sharriba akan mijina ya qini duniya ta zagen mizaki aduniyar ke! mi kike nema wanda yakaiki ga jefa ɗan uwanki musulmi a masifa to idan mijine gaki gashi amman kisani koda kotu ta yanken hukuncin kisa ina roqon ubangiji daya taramu agabansa domin ya bayyan mai gaskiya tsakaninmu kuma kije da yardar ALLAH yadda kika ɓatan rai kika ɓata na mijina dangina iyayena alfarmar annabi s.a.w kema sanaki yayi fiye da nawa" ina kai maganar na dubi alqali "yamai girma mai shari,a abinda zance maka bani na kashetaba amman dan ALLAH idan baku yarda ba bana son ku wahalar da iyayena kawai ku kasheni na huta da wannan rayuwa