ANA MALIK HAUSA NOVELS BY HUMAYRA BULAMA .doc

Author :  Humaira Bulama Category :  Top Hausa Novels 2025

Chapter   10 / 33

27K to 30K   out of 98.8K words

addu a..tun ranar da ya shak e Mallan idi ta yi masa fad a bai sake zuwa ya zauna da ita haka ba, sai dai da safe ya shigo ya gaisheta da daddare ya lek o ya ajjiye mata abunda ya kawo ya yi mata sai da safe ya fita, shiyasa gaba d aya take a tsorace tana ta addu ar Allah ya sa bai saka abun a ranshi sosai ba gudun motsawar ciwonsa, shiyasa d azun da aka kawo mata shi zuciyarta ta kusan bugawa a tunaninta b acin ranne ya tado masa da ciwon sai daga baya tukunna ta gane ashe azaba ce, sannan sai da ta fahimci abun bai yi k arfi da tsanani sosai ba kamar last time tukunna hankalinta ya d an kwanta& ..ta san cewa she is selfish tabbas! Amma Ma aruf shi kad ai take da shi a duk fad in duniyar nan shiyasa take tsoron duk wani abinda zai janyo abinda zai rabata da shi& idan akwai abinda take tsananin tsoro shine ta ga ciwonsa ya motsa dan a yadda ya sha da kyar the last time ita kanta ba wai likitoci da suka bada tabbaci ba ta san any mistake to game over ne& & .
 Barka da dare Maama
Muryarsa ta katse mata tunaninta.
Ajiyar zuciya ta sauk e a hankali ta ce  barka, ya jikin naka?
A hankali ya ce  na warware
 Garin yaya karara ya shafeka ne wai?
Ta yi masa tambayar tana kallonsa, d an k uraa mata idanu ya yi kafin chan ya sunkuyar da kansa kawai.
Shiru ta yi ba ta sake yi masa maganar ba suka dasa zaman shiru a cikin d akin.
Kafin chaan ta mik e ta je ta d auko wani ruwa a cikin gora ta k araso inda yake ta zauna ta bud e tukunna ta mik a masa ta ce  gashi, d azu na lek a zan ba???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ka na tarar ka samu barci.
Ungo karb i ka sha da bismillah.
A hankali ya saka hannu ya karb a, ya yi bismillah ya shiga sha. Sai da ya shanye tukunna ya ce  na gode Maama.
Shafa kansa ta yi tana murmushi sannan a hankali ta ce  Allah ya k ara maka lafiya da nutsuwa
D agowa ya yi ya kalleta yanzun ma cikin muryarsa mai cike da dakiya da izza ya ce  Ameen Tukunna a hankali ya d an matso ya mik a hannunsa da yake a ta b angarenta ya rungumota ya ce  fushin ne har yanzu?
Dan ya lura da yanayinta. Girgiza masa kai ta yi kafin ta ce  tunani kawai nake yi ko sai yaushe Allah zai shirya mini kai! Ina yin addu a Ina sadaka amma Astaghfirullah har yanzu ban ga wani chanji a tattare da kai ba Ma aruf
Ta yi maganar tana mai dag owa ta kallesa sosai shima itan yake kallo da taimakon hasken kwan fitilar solar da ya mamaye koina a cikin d akin. Ya jima yana kallonta haka itama kafin chaan ya furzar da huci ya d auke idanuwansa daga gareta ya ce  a shirye nake, Allah ne bai baki ikon kallona ta fuska mai kyau ba!
A ko da yaushe a baibai kike kallona Maama
Ya k arashe maganar yana mai mayar da dubansa gareta.
 Wanne kallo kake tunanin zan yiwa mutum irinka? Ma aruf kalli jikinka! Kalli yanayin rayuwar da ka zab arwa kanka kalli mutanen da kake huld a da su& sannan duk fa yawancin fad an da ya shafi siyasa sai an ganka a wajen kuma har da kashe-kashe abun yake k unsa ka kuwa san makomarka Ma aruf?
Ta yi maganar muryarta na rawa alamun gab take da fashewa da kuka.
 Mugu d an daba kawai!!!
Muryar Dije ta yi flashin cikin kwanya da kunnuwansa kamar yanzun take fad a.
Cikin rauni d aci da jin zafin abinda za ta furta d in ta ce
 A ko da yaushe idan na tuna abubuwan da ka yi kuma na tuna ba ka da mafita ko wayon kare kanka a gaban Ubangiji tare da nauyi da girman zunubin ina shiga cikin matsanancin tashin hankali Ma aruf! Ka ce min ba ka da laifin komai in yarda da kai na zab i in yarda da kai d in sai dai kuma ba ni da hujjar da zan ce gata saboda ita na yarda da kai, Ina ganin kaina ne kawai a matsayin uwa mai tsananin son kai wadda son kanta zai kaita ga halaka saboda ba kai kad ai ba hatta ni inada nawa kamashon& 
Maganar tata ce ta mak ale sakamokon kukan da ya ci k arfinta.

A hankali ya sauk e ajiyar zuciya yana jin wani zafi yana taso masa, da kyar ya iya d aga d aya hannunsa ya sakata a jikinsa ya rungume, cikin sigar lallashi yake bubbuga bayanta& ..
Sun d an jima a haka kafin chaan! Ya sauk e wani nannauyan numfashi ya ce  ga balangu nan, na wajen Ganaye, wanda kika fi so.
Ya k arashe maganar da d an murmushi a kan fuskarsa.
Ta riga ta san maganar ce baya so kuma tunda ya sako wata to an bar wacchan kenan har abada.
Kallon ledar da ya mik o mata ta yi kamar kullum ta ce  a ina ka samu kud in
Murmushi ya yi kafin ya ce  ta hanyar halal, doyata dana gaya miki mun noma a Niger ita aka siyar
Cikin tarar numfashinsa ta ce  an dad e fa ana baka kud in doyar nan Ma aruf& 
Numfashi ya fesar sannan ya ce  sun kusan k arewa saura kad an bai kai dubu ashirin ba ma
Daga nan ya yi shiru kamar mai tauna abin da zai fad a kafin ya ce  Sana a zan fara da kud in da wanda na baki ajiya, in sha Allah
Wani irin zabura ta yi sai kuma ta fara murmushi mai had e da dariya kafin ta gyara zamanta tukunna ta yi sujjada.
Murmushi sosai shima ya yi wanda idan ba yana tare da ita d in ba to ba za ka tab a gani ya yi ba.

Bayan ta d ago ta gyara zamanta cike da farin ciki ta kamo hannunsa ta ce  Allah ya dafa maka Allah ya taimake ka Allah ya sa ka fara a sa a .
A hankali ya ce  Ameen& ..


Ana fitowa daga masallacin sallar asubah Mallan da Minu da wasu samari a gidan guda biyu Ya Kamal da Ya Musa suka tafi kai Ya Muhammad asibiti
dan zuwa wannan lokacin jikin nashi ya yi tsanani sosai.
Tunda suka tafi Inna take kuka gashi ta cewa Dije ko inda ta ke kar ta kalla ballanta ta yi mata magana& .sosai ta bawa mutanen gidan tausayi yayinda wasu suke ta jin dad i kar ma Kaka da Asabe su ji labari.

Sai wajajen k arfe goma tukunna Mallan ya amsa wayar Inna ya ce mata  jikin da sauk i an d an samu kansa yanzu haka an yi masa allurar barci baccin yake yi, ga Minu za su dawo tare da su Ya Kamal, ta bashi karin kumallo ya kai akwai maganin da dole sai ya ci abinci tukunna zai sha
Da  to ta amsa tana ta jera hamdala ta mik e ta nufi kitchen, tana shiga ta tarar da Dije tanata jefa d anwake.
Yi ta yi kamar ba ta ganta ba kawai ta juya ta fice a kitchen d in.
A hankali kwalla ta shiga zirya saman kyakkyawar fuskarta dan idan akwai abinda bata so a duniyar nan to shine Inna ta yi fushi da ita, gaba d aya ji take yi duniyar ta tsaya mata chak& .Inna bata saba yin fushi da ita ba shiyasa a duk lokacin da ta yi take jin jiki.
Sai da ta gama jefa d anwaken tass tukunna ta d an zuba mai a kasko ta rufe ta ajjiye roba ta je ta d ebo ruwa shima ta ajjiye tana jira ya gama ta kwashe.
Ganin zai d auki lokaci ya sanya ta mik e ta fita ta wuce d akinsu domin ta je ta d auko albaasa yadda tana sauk e d an waken sai ta d aura man, dan rushon gawayin su ya samu matsala, da abin girki d aya suke amfani kwana biyu.

Tana fita dede Asabe tana fitowa daga band aki, ita Asaben ta ganta amma sam Dije ba ta ganta ba da yake baya ta bata.
Kwafa Asabe ta yi dai-dai Dije ta shige d akinsu, ta san ta tsani Halima kuma tana kishinta amma zuwa yanzu tabbas tsanar Dije tana shirin kere ta Halima a cikin zuciyarta, sosai take jin zafin Yarinyar& tana k arasa fitowa tsakar gidan idanunta suka sauk a a dede wajen da ta zo ta tarar da gawar akuyarta wanda Maman Fati ta tabbatar musu aikin Dijen ne, wani irin tuk uk i ne ta ji yana taso mata..Kaka ta ce kar ta yi mata magana zata yi maganinta ta hanyar sakawa a koreta a gidan amma shiru yau ma gashi har ta kwana ta hantse babu alamun zata bar gidan!..
Kitchen d in ta juya ta kalla ta ga tukunyarsu a kan murhunsu wuta tana ta ci, ba ta yi wata-wata ba ta afka cikin kitchen d in zuciya tana cinta ta shiga ta lek a cikin tukunyar&
K urawa d anwaken da yake ta tafasa ido ta yi, tana cikin tunanin me zata yi masa ta lalatashi idanunta suka sauk a a kan uban ruwa k anwa kusan cikin babban kofin sha biyu a cikin wata babbar roba, da sauri ta d auka ta juye duka a ciki har da k asa k asar ba ta rage komai ba, hankalinta bai kwanta ba ta sake d aukar gishiri shima ta juye a ciki ta saka ludaye ta juya sasai kamar mai burge miya sannan ta mik e ta juya za ta fita suka ci karo da Dije.

Wani Irin tururin wutar bala i ce take taso mata amma ta danne da mugun kyar dan ko saboda Ya Muhammad ba zata yarda ta kula kowa a gidan ba yau!
Tsaki Asabe ta yi tana jira Dije ta tanka ta ita kuma ta tada bala in da kowa sai ya ji ko dan a sake aibanta Dijen amma ga mamakinta sai ta ga Yarinyar ta wuceta ta d auko tsumma ta d auki tukunyar d anwaken nata ta fice ta nufi bakin rijiya.

Da kyar ta samu kaso biyu a cikin ukun d anwaken da ta jefe shima kuma duk ya yi laushi, dan kanwar mai k arfi ce sosai hakan ya sanya d anwaken zagwanyewa&
Tana cikin wankewa Minu ya yi sallama, ya k arasa ya ce mata ta yi sauri ta had a abincin y an asibiti yanzu zai juya Musa yana wajen yana jiransa a napep d insa.
Da  to ta amsa ta koma kitchen d in da sauri ta d aura mai sannan ta d auko flask ta fito ta ci gaba da had a kan d anwaken.
Sai da ta gama tukunna ta nufi kitchen d in domin ta zuba mai ta kammala komai.
A kitchen d in ta samu Sagir da Kubra yana tayata tsintar wake suna hira suna dariya, ba ta ko kalli inda suke ba dan ta tsani Sagir tun ba yau ha tunda ta fahimci d an iska ne ya fice mata a rai gashi uwarsa ba ta son laifinsa.
Mahaifiyar Kubran ce ta kirata dan haka ta tashi da sauri tana cewa  Na am ta fice daga cikin kitchen d in.
Tsaki Dije ta yi ta rasa dalilin da ya sa ba za a kafa dokar hana maza shigowa kitchen d in gidan ba fisabilillahi da hijab mutum zai ji ko da zafin kitchen d in da ko windo d aya babu, musamman ma da rana idan kowa ya kunna murhunsa kitchen d in sai ka ji kamar oven ga uban hayak i na masifa!
So take yi ta koma d aki ta d auko hijab d inta amma kuma ta ji ya Aminu ya ce ta yi sauri gashi ba ta so ta sake yi musu wani laifin dan haka kawai sai ta ware d ankwalin kanta ta d an yane jikinta da shi dan ta lura Sagir d in bashi da niyyar fita kuma dukda bata juya ba tana jin yadda idanuwansa suke yawo a jikinta.

Rigar bacci ce a jikinta amma cotton kuma hannunta d an dogo ne dan ya kusan rufe guiwar hannunta ma, sai zani da ta d aura a kan rigar baccin nata da d ankwalinsa, rigar baccin loose ce amma da ikon Allah ta fito da albarkatun k irjinta sosai haka nan shima zanin normal ta d aura shi amma k ugunta ya fito sosai tubarkallah.
Tsabar yadda Sagir yake sake lek ata yana kallonta har d an zillo yake yi daga nan zaune kan kujerar inda yake idanunsa kamar zasu fad o k asa, ga ta dai a gabansa amma da ikon Allah lek e yake yi ko mai zai gano
oho!.
Ya Aminu ya fito kenan daga d akin Inna zai zubawa kajin sa abinci ya ga mutum yana zillo shi kad ai a kan kujera, da ke Dije tana daga chan ciki shi kuma yana a bakin k ofar shiyasa bai ganta ba ya gansa shi kad ai.
Da mamaki ya k arasa bakin kitchen d in idanunsa a kan Sagir wanda bai ma san ya k araso ba.
Dai dai Dije ta d an tsugunna a kan k afafuwanta tana k ok arin rufe flask d in da ya k i rufuwa wanda tsugunnawar da ta yi ya taimaka wajen sake fito da hips d inta ta gefe da gefe.
Wani irin murmushin iskanci ya ga Sagir d in ya yi har da wani fito da harshe ya na sid e Baki.
Da sauri ya juya ya kalli Dije wadda ita ba ma ta san yana yi ba Allah Allah kawai take ta gama ta fita ta bar amsa kitchen d in.
Wani irin takaici da bak in ciki ne suka lullub e Minu a lokaci guda, bai san lokacin da ya juya ya zaro tsinken tsintsiyar kwakwar da
aka jingine a wajen ya tsole masa ido ba!
Dai dai Mahaifiyar Sagir d in ta fito& .abun ya faru a kan idanunta dan haka ta k arasa cikin sassarfa tana rafka salati da k arfi wanda hakan ya yi sanadiyyar fitowar mutanen gidan daga cikin d akunansu.

Tana k arasawa ta rufe Minu da duka& .
Matar ta tsufa sosai ya san ko yunk urin hana ta ya yi tsaff zata kife a wajen shiyasa kawai ya rabu da ita ya saka hannunsa ya kare jikinsa ita kuma tana ta dukansa tana kuka tana cewa  Wallahi idan wani abun ya samu idon Sagir sai na yi shari ah da kai. Mugu kawai shegen Yaro

Inna ba ta so shiga sabgar kowa ba yau amma duk yadda ta so sai abun ya gagareta, dan haka ta tashi ta fito fuskarnan a had e tamau kamar ba ta tab a dariya ba.

Ba su san ta k araso wajen ba sai da ta shiga tsakanin Minu da matar ta rik e mata hannu tukunna.
Murya cike da b acin rai ta ce  Ana barin halak ko dan kunya, fisabilillahi ko me ya yi miki kuma ko me ya faru ai bai kamata ki dinga d aga murya kina sheganta mini Yaro ba! A gidan ubansa fa kike haya.
Yanzu kuma idan na saka baki sai ace na cika fad a a ga laifi na bayan kune kuke shiga sabgata.

Har da d an gudu gudu Kaka ta fito ta ce  ai tun jiya na gaya miki ki nemo ubansu ba dai d ana ba dan haka ki daina wani hak ilo kina ik irari& 

Cikin katseta sannan a tsawace Inna ta ce  Dakata malama ban sako da ke ba! Ko kinga na tanka ki tun jiya? Kina so ki san dalili?
Ba ta jira ta bata amsa ba ta ce  saboda maganarki ba ta kai in tsaya in sakata a mizanin hankali ba shiyasa, in da ace maganar mutane masu hankali kika yi da sai in saurareki amma ba ni da lokacin shirmenki ne shiyasa ban biye ki ba kuma duk mutum mai hankali ba zai biye miki ba ko kinga shi Mallan d in ya biye ki?
Nan ma bata jira me zata ce ba ta ce  saboda ya san me yake yi. Jakai, dak ik ai sannan munafukai sune suke biye ki suke bawa zancenki mahimmanci.
Ni nan kin ganni tunda har ba Mallan ne da kansa ya furta wannan zance ba to idan kinga dama Hadiza ki d auki loudspeaker kina bi layi layi kina fad a wallahi ko a jikina.
Ta k arshe maganar tana dukan cinya cike da bala i.

Kuka Kaka ta fashe da shi ta juya ta shige cikin d aki tana cewa  ko uwar da ta haifeta ba ta kiran sunanta saboda sunan mahaifiyarta ne amma yau ga suruka ta ambaci sunanta bayaga kiranta da mahaukaciya da ta yi, wallahi ba zata zauna ba bar musu gidan za ta yi yau za a yi ta ta k are Mallan sai dai ya zab a dan wallahi ta gama zama gida d aya da su Dije.

Asabe da Maman fati ne suka bi bayanta suna rarrashinta yayinda Inna ta doka wani uban tsaki ta juya kan Maman Sagir ta ce  ke kuma me Minu ya yi miki? Wadda ba ta san alkhairi ba!

 Ya kike magana kamar wadda ta ba ni waje na zauna a kyauta? Haya fa nake yi?& 

Cikin katseta Minu ya ce  Anty ki yi hak uri a bar maganar nan, Inna dan girman Allah kema ki yi hak uri ki kyaleta ya wuce.

Cikin fushi Maman Sagir d in ta ce  eh ai dole ka ce a bar magana tunda mu ka cuta, to wallahi ba ka isa ba! Dole a biwa

10 / 33