ANA MALIK HAUSA NOVELS BY HUMAYRA BULAMA .doc

Author :  Humaira Bulama Category :  Top Hausa Novels 2025

Chapter   16 / 33

45K to 48K   out of 98.8K words

bashi dama ya kare kansa ba sai yau, su Innna basu lura da gawar matar wadda ke yashe a bakin k ofar gidan ba filla-filla sai da addar Oscar ta sake bada sauti wajen raba cinyarta da sangalalinta tukuunna idanuwansu suka kai gurin.
Wani Irin salati Inna ta saka mai sautin gaske sai kuma jikinta ya sake k afafuwanta suka gagara d aukarta jikinta ya hau karkarwa ta tafi zata zube a wajen idanuwanta suna jujjuyawa..Da wani irin sauri Minu ya durk usa ya kinkimeta ganin tana shirin zubewa ya bar wajen da ita, yana shiga gida ya ajjiyeta a d aki ya rufo k ofar d akin ya fito&
Ai kuwa kamar had in baki, abunda yake cikin ransa kusan shine a zuciyar gaba d aya waenda suka ji da waenda suka gani dan ya na fitowa ya dinga cin karo da samarin layin suna nufar gidan su Ma ah! Masu wuta a iceee daban masu petir a gallon daban, masu tayoyi rirrik e a hannu daban& .


BULAMA
'?
0806 402 1951
ANA MALIK!!
Book 01.
Page 13.

Humairah Bulama.
Mikiya writers Association.

Dije tana sauk a daga napep ta wuce gida da sauri, ko ta kan mai Napep d in wanda ya biyota yana yi mata maganar kud insa bata bi ba dan ita bata ma jishi ba kuma ta manta da ana biya tsabar yadda hankalinta yake a tashe ranta yake a b ace, so take kawai ta ganta a gida.

Allah ya taimaka Ya Kamal wanda dawowar sa kenan daga nemanta ya ga sauk arta daga Napep d in da yadda mutumin ya biyota dan haka ya k arasa ya sallamesa yana shirin shiga gida ya sameta ya ji ba asin Ina ta je ya ga ana ta nufar gidan su Ma a.

Usso wanda ya fito a buge! Ya tare ya tambaya, a bakinsa ya ji komai dan haka ya wuce cikin gidan a mugun fusace ya wuce d akin Iyya ya d auko wata zabgegiya wuka& & & .


Minu yana fita Inna ta samu ta tattaro duk wani ragowar kuzarinta ta mik e da kyar ta bi bayansa amma sai ta tarar ya kulleta ta waje.
Sosai ta saki kuka ta durk ushe a wajen dan ta san zafin zuciya irin ta Minu da kuma yadda ta ga ya fusata bata da tantama gidansu Ma a za su ce za su koma shi da ragowar samarin Unguwar.

Sama-sama ta ji ana tab a k ofar kafin a zare sakatar a bud e k ofar aka shigo, da sauri ta tashi ta shiga k ok arin gane wayene da yake babu haske a d akin..dai-dai nan kuwa kamar an san abunda take nema aka kawo hasken wutar nepa.
Maimakon ta rungumeta ko ta yi mata magana kawai sai ta sake fashewa da kuka!
Kukan itama Dije ta saka ta rungume Innar tata tana mai tambayarta  me yake faruwa a layin? Na ga su Ya Aminu suna ta jidar tayoyi da itace.
Zabura Inna ta yi ta fita waje tana kwala kiran Minu dai-dai Iyya itama ta biyo Ya Kamal a baya tana kiransa bai kulata ba, haka itama Maman Sagir ta biyo nata d an amma suka fice da gudu suka banko k ofar suka datsa k atuwar sakatar dake a ta waje sukayi gaba abinsu zuciyar kowa a wuya& .

Babu shiri su Inna suka fara k ok arin b alle k ofar dai-dai nan Mallan ya bud e k ofar suka shigo shi da wani k aninsa Kawu Isa wanda yake zaune a K auyen (Getso.)
Turuss!! Suka yi suka d an jaa baya sai kuma Inna ta matso ita ta ma manta da fushin da take yi da shi ta shiga ce masa  dan Allah ka je ka taho min da Minu ya tafi yin fad a da su Ma ah ba iyawa zai yi ba ka dawo mini da shi kar su kashe mini shi
A take su Iyya suma suka shiga kawo nasu zancen wanda hakan ya sanya Mallan d in ya gagara fahimtar ina zantukan nasu suka nufa.


Ta bayan gidan su Ma ah samarin suka fara zuwa suka sassaka tayoyi kafin su zagayo ta gaba dukda yadda su Oscar suke hauka da wuk ak e (dan suna gama sassara matar nan suka koma kan y an kallo) suna gani ana sarar Jama a amma hakan bai hana mazan nan tunkarar su gadan-gadan ba.
Ta inda aka ci galaba a kansu shine su Oscar d in ba su tab'a tunanin zuciyar mutanen zata iya k'ek'eshewa su tunkare su ba dan haka basu shiryama komai ba su kuwa samarin suna zuwa tun daga nesa suka fara yi musu ruwan kalanzir da tayoyi har da masu petir..Ma'a yana ganin haka ya wuce cikin gida da guda ya kunna famfo ya jono ruwa da masifar guda dan ya san me suke shirin yi ai kuwa yana fitowa ya tarar an fara wullo musu wuta ta kama jikin Grenade sai ihu yake yi.

Tunda Scorpion ya hango Minu a cikin tawagar daman ya fahimci tabbas in ba da kyar ba sai kwanansu ya k are a yau dan ya san Ma ah zai iya yunk urin kare Minu su kuwa yadda suke a zuciyen nan da gani da shirin kashe su suka zo dan haka duk wani mistake ko sanya idan suka yi tsaff sai an ci galaba a kansu!!
Shiyasa tun wuri ya koma gefe ya yiwa Yaransa waya ta yadda ko shi an hanasa su baza su hanu ba dan ba hankali ne ma da su ba (they are always drunk) ballantana su fahimci Ma ah d in idan ya ce kar a yi.
Yana fitowa da mesar ya fara watsa ruwan a kan Grenade dan wutar ta kama shi da kuma waensu wajaje har jikin ginin gidan duk sun kama suna ta ci da wuta sosai& sai da ya fara kashewa Grenade wutar jikinsa tukunna ya saka k afa ya take wajajen rabin mesar da masifar k arfi ruwan ya daina zuwa, a gaggauce ya sunkuya ya d auki wani galan d in da aka jefo masa yanzu a cikin ruwan jefe-jefen da ake ya yi musu dan ya ji shi da d an nauyi ai kuwa yana d auka ya ga da d an dama a ciki dan haka ya zuba abinda ke a cikin galan d in ta bakin mesar ya kai kusan rabin inda ya take d in..dukda jifa da tayoyi da ruwan fetur d in da yake sha hakan bai sa ya tsorata ya sare ba gashi hannunsa ya kama da wuta dan garin zuba abun a cikin mesar ya zubar masa a hannu dan haka wuta ta kama hannunnasa amma bai sare ba abunda ya sa gaba kawai yake yi da zafi-zafi& ..
Kad an ya d an d aga k afarsa daga kan mesar ruwan ya taho, ya dededeci inda wuta ke ci, sai da ya tabbatar wutar ta bi ruwan tukunna ya kwaso ta da mesar ya d aga k afarsa daga kan mesar gaba d aya ya watsa musu, nan kuwa wuta ta tashi buuuuu!! Ta fara kama har da galoli da tayoyinsu.
Sai da ya tabbatar da ruwan ya dedeta tukunna ya kashe wutar dake a a hannunsa wanda wajen ya ji rauni matuk a.

Rikicewar da suka yi ya sanya suka yi laushi wasunsu suka gudu su kuma su Scorpion suka yi kan ragowar da basu gudu ba.
Sam! ko da wasa basu nufesu da niyyar sara suka ba da niyyar kisa suka nufesu dan a wuya da ka! Suke kai musu suka wusu kuma idan suka chaka musu wuk ar daga k asan k irji sai sun jaaa sun kai ta har k asan tumbinsu kayan ciki sun fito tukunna suke jefar da su! Hakan da aka gani ya sanya aka ci gaba da guduwa.

Grenade ne ya yi kan Minu ya sare shi da wuk a a hannu Allah ya so ba sosai
ba dan ya goce kuma ya kare sarar ne dan Kansa Grenade d in ya kaiwa hari Allah ya tak aita, garin guje-guje (wani ya taho da gudu) ya bige sa aikuwa a take ya zube a wajen, dan haka Grenade d in ya sake d aga wuk ar yana shirin sauk e masa ita a kai kenan Allah ya kawo Ma a wanda ya hangosa tunda ya nufesa ya hankad e sa ya tada Minu& mistakenly ya tura Grenade d in kan su Scorpion ai kuwa suka zube rikicaa makamansu suka fad i a k asa& wasu a cikin samarin layin kuwa waenda basu kai ga guduwa ba suka yi kukan kura cikin zafin nama suka yi kansu wani a cikinsu ya d auke zabgegiyar wuk ar scorpion bai yi wata-wata ba ya sauk eta a kan Grenade dama shi kad ai ne Allah bai bawa ikon tashi da wuri ba sakamokon k unar da take a jikinsa ya sanya dama dauriya ce kawai yake yi.
K arasowar Ma a d in shi ya taimaki su Scorpion amma da tuni suma an kasheshu, da kyar ya kwacesu ta hanyar kaiwa wajen mutun biyar sara a lokaci gudu, suma kuma mutanen dama tunda suka ga ya shiga fad an aka fara guduwa.
Suna tashi suka yi kan Minu wanda jiri ya hanasa tashi a wajen nan ma Ma a ya sake taresu ya ingiza su cikin gida, ai kuwa suna gama shigewa aka samu wani mai k arfin Hali ya biyosu ya datse k ofar.
Yayinda su kuma suna shiga cikin gidan kawai suka ga wuta tana ci kamar hauka sun cinna musu wuta ta baya ashe, ga Maama a yashe a tsakar gidan wadda tun fitarsa ta farko da ta yanke jiki ta fad i bata sake shurawa ba.
Da gudu suka nefeta duk su ukun dan shima sai yanzu ya ganta d azu da ya shigo kunna ruwa sam bai ganta ba. Yana zuwa ya d ago fuskarta, da mugun sauri ya runtse idanuwansa sakamokon yadda ya ga gaba d aya halittun fuskartata sun zaizaye sun koma gefe guda inda ta kwanta a kai& & ..
Wani irin wutar bala i ce take taso masa yana k ok arin dannewa dan ya san idan ya fita a haka tabbas sai ya kashe duk wani rai da yake a wajen nan& .
Cikin tsananin fushi Scorpion ya ce  Shi fa Yaron da kake ta karewa a yanzu inda ace zai samu dama wallahi da sai ya kasheka!!! Bai
ma fa san kana yi ba, ga gawar Grenade chan yashe a waje inaga hakan ya isa ya sanya ka fahimci idan baka daina katsemu ba to
muma duk sai an kashe mu!
Sannan ka gaya min ta yadda zaka fita da Mama a cikin gidan nan idan ba a yi clearing wajen nan ba???
Yana gama fad in hakan ya d auki waya ya kira Yaronsa yana d auka ya ce  wai dan durun uwarka kuna Ina?
A buge Saurayin ya ce  go slow ne ya tsare mu a kan gada, ka san tal udun da ka ce mu zo dole sai an bi ta cikin gadar ruwa
Tsaki ya yi ya jefar da wayar da wani irin mugun k arfi ta tarwatse bai samu ya ji na gefen saurayin wanda ya ke ce masa  mun kusa fa Oga ka d aga masa k afa a china yake shi yanzu haka ba.

Tabbas ya san in dai ba Ma ah ne ya shiga fad an nan ba to sai an kashe su su duka hud un a yau! Dan tun d azu ya fahimci ba iyaka samarin layin bane kusan kaff y an Unguwar ne suka yi musu taron dangi, yanzu haka kuma hayaniyar da yake ji a waje ya san sun ninka na farko!
Ko da ace kanshi ba ya ja ya san cewa  Sarkin yawa ya fi sarkin k arfi Ammafa dukda haka ba zai zuba ido a gaban idanunsa Ma a da Mahaifiyarsa su mutu a cikin wutar nan ba ba tare da ya tab uka uwar komai ba dan haka kawai sai ya juya ya nufi d akin Ma ah d in wanda yake a soro ya bud e ya shiga!
Sun bar wuk ak ensu a waje dan haka yana shiga wajen da ya san zai ga wuk ak e da adduna ya nufa.
Wata zabgegiyar Adda ya d auka ya d auki wata wuk a mai mugun kaifi ya sak ale a k ugunsa ya fito.
A bakin k ofar d akin ya ga Ma a a tsaye rik e da Maama a hannunsa& zai yi magana ya ga kawai ya wucesa ya ajjiye ta a d akin nasa dan nan ne kawai hayak i bai bule ba a cikin gidan& yana ajjiyeta ya d auki wuk ak e ya fito ransa a mugun b ace!
Ihu suka saka suna yi masa kirari yayinda shi kuma ya k arasa bakin k ofar gidan ya saka dukkan k arfin da Allah ya bashi ya dake ta da k afa& sau uku ya kai mata duka ta b alle ta fad i a k asa, y an wajen kuwa kamar jira suke suka hau yi musu ruwa fetur basu kai ga fara cilla musu itace masu ci da wuta ba suka yi kansu& & &
Sun fi su d ari wanda kaso goma ne kawai za a ce suka d auko makamai! Zuciya mai cike da Imani da rashin iya aikata kisan kai ya sanya suka rikice gashi wani irin chachchaka Ma a yake yi musu da hannu bibbiyu!
Tsoro da kuma ganin ana ta kashe wasu ana jiwa wasu rauni ya sanya wasu kaso hamsin a cikin waenda suka yi saura sake guduwa dan haka suka sake samun galaba a kansu! Ammafa suma an sassaresu, dauriya ce kawai suke yi da kuma sabo shiyasa basu galabaita k arfinsu ya gushe ba.


Gudu sosai ake yi zuwa yanzu dan tiyagas Ma a ya koma cikin d akinsa ya d auko ya zo ya sakar musu dan haka baka iya ganin komai sai dai kawai ka ji sauk ar wuk a a ruwan cikinka, su kuwa su duka ukun akwai glases d in da suka saka mai tare hayak i.

Sai da ya yi clearing wajen ya tabbata it s safe tukunna ya koma cikin gidan da mugun gudu ya kinkimo Maama ya d auki wani briefcase dan sosai gidan yake ci da wuta! Ya fito da ita, suna fitowa gas ya yi bindiga wutar ta fi ta farko.

Da gudu ya saka Mama a mota ya bawa Oscar key ya shiga ya zauna tare da ita yana kallon fuskarta yana jin wani kalar wutar bala i da k unci
suna taso masa& .Yana shiga mota Yaran Scorpion suna k arasowa wajen!&
Har an tayar da motar Ma a ya yi kiransa.. kamar zai hanasa sai kuma abunda ya faru d azu da rijiyar da ya tsallake da baya duk a yau suka dawo masa tarr cikin kwanyarsa dan haka kawai ya ce masa  duk rintsi kar ku tab a gidansu Khadijah! Da y an gidan.
Jinjina kai Scorpion d in ya yi ya sara masa tare da addu ar Allah ya bawa Mama lafiya tukunna ya juya ya koma kan tawagar Yaransa waenda zuwa yanzu har sun cinnawa gida uku wuta.


Suna wucewa& .a hankali yake bin gidansu da kallo
yana ganin yadda yake ci da wuta kamar ba gobe! Ya san ko tsinke ba za a iya fitarwa ba dan da kyar shima yanzun ya iya shiga ya d auko Mama tare da takardun credentials d insa dukda kuwa bayajin akwai wani amfani da za su yi
masa. Sai a lokacin tukunna ya tuna yau fa tun d azu bai ga Mallan idi ba! Tsaki ya yi ya kawar da kansa a ransa ya shiga addu ar  Allah ya sa ya na ciki ya bugu yana ta uban bacci, bai ji komai ba har wutar ta cinye sa & & & & & .


A chan gidan su Dije kuwa Mallan yana gama fahimtar komai ya juya zai fita shi da kawu Isa a gigice, Kaka ta fito ta ce  Duk ku biyun idan kuka fita sai na tsine muku Wallahi, ba zai yiu in rasa y ay ana har biyu akan wani Minu wanda ba a da tabbacin ma d anka ne ba.
Ta k arfi Inna ta runtse idanuwanta tana gani??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????n wani irin dishi-dishi, a hankali ta juya ta koma d aki ta d auko mayafinta ta zo ta nufi k ofar fita.
Mallan bai motsa ba kuma bai ce mata komai ba sai da ta k araso daff da shi tukunna ya ce mata  ki koma ki zauna Allah yana tare da su
Rikitattun idanuwanta da suka rine da kuka da tashin hankali ta d ago ta watsa masa sannan ta ce  bani hanya in wuce! Idan kai zata iya tsine maka ai ni ba zata iya ba!

 Eh ai dama a tsinen kike!! Shegiya gantalalliya! Ina amfanin tsinewa tsinanniya!?
Cewar kaka

Da sauri kawu Isa ya ce  Kaka ki yi hak uri ba za mu fita ba ki koma ciki kin ji!!!

Cikin b acin rai ta ce  ai Isa yau kuma a yanzu za mu yita ta k are!! Idan ka ga na koma ciki to Mallan ya zab a ko ni ko Dije da uwarta!! Dan wallahi na gama zama da su k ark ashin inuwa d aya!!!

A hankali Mallan ya runtse idanuwansa sannan ya bud e ya ce  Kaka dan girman Allah ki yi hak uri ki tsaya tukunna a gama wannan tashin hankalin da yake wakana a waje!!!

Cikin halin ko in kula ta ce  yo ni Ina ruwana da wani tashin hankali?? Ai bai shafe ni ba tunda babu d aya daga cikinku a wajen! Abunda nake so yanzu shi za a yi idan kuma su zaka zab a to fad a min tun wuri in fitar maka daga gida in shiga gari!!
K irjinsa ne ya ji ya fara wani irin zafii ga ife-ife suna jiyowa a waje ga result d

16 / 33