ANA MALIK HAUSA NOVELS BY HUMAYRA BULAMA .doc

Author :  Humaira Bulama Category :  Top Hausa Novels 2025

Chapter   11 / 33

30K to 33K   out of 98.8K words

Yaro hakkinsa.
Ta fad i haka tana Isa kan Sagir wanda zuwa yanzu ya ware daga mutstsika idon da yake yi amma yana nan zaune a inda yake kawai yana kallon Minu irin a fusace yake da shi d innan.
Duddubashi ta yi kamar wani k aramin Yaro tana dubashi tana cewa  ya idon naka? Kana gani sosai?
Jinjina mata kai kawai ya yi, ba ta d ago ba ta ce  Shege mugun Yaro haka nan kawai zai janyo maka, ido ai ba abun wasa bane& .
Wata mahaukaciyar fisga Inna ta yi mata ta juyo da ita sannan ta ce  na rantse da mahalliccina ko da wasa idan kika sake shegantamin Yaro da k azamin bakinkin nan sai na tsinka miki mari!!!
Da sauri Sagir ya taso ya zo ya tsaya a gaban Inna fuska a had e ya ce  cikata!!
Sake damk eta Inna ta yi ta kallesa cikin fushi ta ce ba zan cikata ba dan kutumar ubanka!!!!
Yunk urawa ya yi zai yi kan Inna Minu ya yi wani irin jifa da shi a fusace ya ce  kar ka soma! K aramin mahaukaci
Ai kuwa a take gidan ya hargitse dan Sagir sake tasowa ya yi Minu kuwa ya rufesa da duka dama a fusace yake.
Da kyar bayan mazan gidan sun shigo suka samu suka kwaci Sagir daga hannun Minu amma fa ya daku dan har ya fasa masa saman ido da hanci da baki.
Sai da Iyya ta zo itama da kyar tukunna ta lallab a Inna ta cika uwar Sagir wadda take ta fisge-fisge amma ta gagara kwatar kanta daga hannnun Innar.
Ana cikata ta yi kan Sagir tana mai fashewa da kuka kafin ta d ago fuska dagaje dagaje ta fara jero  Allah ya Isa
Ya Kamal ne ya ce  mai ya faru?
Ya yi maganar yana kallon Minu.
Banza Minu ya yi da shi yana huci sai da ya sake cewa  Mai ya faru? Iyya Mahaifiyarsa itama ta cewa Minun  mai ya faru tukunna ya ce  Kama sa na yi yana k arewa Dije kallo ta juya baya, shine na tsole masa ido& 
Daga nan kawai ya yi shiru.
Kwashewa da dariya Ramma ta yi ta ce  Allah ya kyauta daga haka ta juya ta wuce ciki.
Yayinda Asabe wadda fitowarta kenan daga d akin Kaka ta k araso wajen ta ce  amma wallahi ka ji kunya Minu!
Saboda an kalli k anwarka?

Cikin zafi Maman Sagir ta taso ta ce kuma ina ita k anwar tasa ita ce ta fito babu mayafi?
Allah na tuba Yarinya ragowar d an daba ta gama karuwancinta komai ya fito rass ai dole Yaro Namiji mai lafiya ya kalla.
Ta fad i maganar idanunta jazur cikin na Inna cike da b acin rai!

Dariya Asabe ta yi kafin ta ce  maganar ki dutse.

 Eh ai ba zanga laifinki ba tunda na san Abokin mutuwa kike nema! Gara mu zargi kuke yi ashahadu a wuyanku! Yanzu idan aka ce ku kawo sheda na san wallahi sai dai a kasheku! Saboda na yarda da Dije d ari bisa d ari kuma wallahi abun kunya ba dai a kanta ba ta fi k arfin haka!!!!
Ke kuwa a gidanku ni shaida ce y ar uwarki sai da ta haifi shege ga shi chan yana yawo.

Da sauri Iyya ta matso ta ce  Halima ya isa haka gori babu kyau ko me suka yi miki ki barsu da halinsu. Sannan dan Allah kar in sake ji kince wani ya fi k arfin k addara
Dariyar rainin wayo Asabe ta yi sannan ta ce  Allah na tuba k addara kuma ta nawa? Jiya ma fa kina ji an ce har filin ball ta bisa dayake abun ya motsa tana so a sosa mata inda yake yi mata k aik aiyi!

Cikin tsananin b acin rai Inna ta ce  tsabar ke dak iyaya ce ki rasa a ina zaki yi sharrin naki sai a filin ball tangamemen waje idanun kowa a kansu? Idan kin tashi sharri ki dinga yin wanda hankali zai d auta mana!
Ko da yake ba zan ga laifinki ba dan hatta Kattime ashe da cikinta aka yi auren iyayenki sannan yanzu haka babu aure a tsakaninsu suke zaune amma har fad an kwana take yi da kishiyoyi, amaryar gidanku ma da aka saka kwanaki saboda fad an kwana da tayi da uwarki ne aka saketa bayan ita uwartaki a musulunci ma bata da kwanan sai dai zina!

D ifff haka Asabe ta d auke wuta, tabbas baki ya san abunda zai fad a amma bai san me za a mayar masa ba! Ta rasa ta yaya Halima ta ke samun zafafan surrrukanta da na gidansu, wanda a duk lokacin da suka yi fad a sai an ji new update daga bakinta.
Cikin fushi Inna ta ci gaba da cewa  dan haka Zina da kike ta ambata a gindinki ta k are ke da y an gidanku da iyayenki ba dai Dije ba wallahi na fad a na k ara fad a Dije ta fi k arfin wannan lalatar dan na yarda da tarbiyyar da na bata. Kuma ba ta gada ba ba ta sha a nono ba kamar yadda yake yawo a jininku.

Ke kuma da kike cewa dole Sagir ya kalleta yanzu hakan har abun alfahari ne? Ragowar mazan gidan su mai yasa basu kalleta ba? Ko mata maza ne su? Sai shi k aramin d an iska ko?
Kinsan a tafin hannuna kike dan haka wallahi ku kiyaye ni in ba haka ba zan yi muku abunda hankali bai zata ba muddin kuka sake shiga sabgarmu.

Tana gama fad in haka ta wuce ciki ta je ta janyo hannun Dije wadda tun d azu ta k ame a kitchen d in take kuka. Suka fito suka wuce d aki aka bar ragowar mutanen gidan da k us-k us, wanda da yawa a kan maganar gidansu Asabe da Inna ta sakar musu latest suke yi. Mahaifin Asabe irin babban mutum ne a unguwar kowa ya sanshi sai dai mai kud in bahaushe ne dan shi kansa idan kika ganshi ba za ki ce ya tara ba ballantana y ay a da matansa, kusan kaso goma a cikin d ari na gidajen Unguwar duk nasa ne amma ko atamfar anko idan ta fito ba iya siyawa mata da y ay ansa yake yi ba dan abun nasa ya had e masa da matsananciyar rowa da mammak o da son tara kud i (ko wa yake taramawa? Oho masa!)
Kusan kowa ya san gidansu wannan dalili ya sa idan aka ji b im! Na gidan ake d abbaka abun a zuzuta shi! .

Suna wucewa Minu ya shiga ya d auki flask d in abinci ya fice dan sai a lokacin hankalinsa ya samu damar jiyo masa vibration d in wayarsa da take cikin aljihun jean d in jikinsa wanda yake da tabbacin Mallan ne.


Su Dije suna shiga d aki ta zube a k asa ta shiga bawa Inna hak uri, ko kallonta Innar ba ta yi ba ta wuce ta je kan gadonta ta zauna tana huci tana jijjjiga k afa dan bata gama hucewa ba.
Sun jima a haka kafin Dije ta zame ta kwanta a wajen tana sauk e ajiyar zuciya ajejjere, ba ta dad e ba bacci ya yi awon gaba da ita.

GIDAN SU DIJE.
Asalin Mallan cikakken Bahaushen garin Kano
ne, k auyen Getso.
Kaka su biyu kacal Allah ya bata Mallan (Bashir) da d an uwansa Kawu Isa wanda shi har yanzu yake zaune a k auyen Getso yayinda Mallan dama shi tun lokacin da ya baro garin ya taho neman ilimi yake zaune a gidan Malaminsu, wanda zuwa yanzu Allah ya yi masa rasuwa.
A nan ya had u da Inna (Halima) wadda babu kalar abunda Kaka bata yi ba dan kar a yi auren amma da yake rabo ya rantse sai da aka yi..Da taimakon Mahaifin Mallan wanda yake tsananin son had in ba dan komai ba sai dan fahimtar da ya yi Halima ita ce sanyin idaniyar d an nasa ita ce farincikinsa, dan haka ya tsaya tsayin daka har sai da ya ga auren tukunna hankalinsa ya kwanta, wanda ana yin auren da wata d aya ciff Allah ya karb i ransa, (shekaru talatin da d aya kenan yanzu).
Anan Mallan ya sayi gida bayan an raba musu gado, wanda nan ma iko da kud irar Allah kad ai ta sanya aka sayi gidan nan dan babu yadda Inna ba ta yi ba amma ya sayar da gonar sa ya zo ya sayi gida babba mai d akuna da yawa a unguwa uku, dan Mallan ya so tara y ay a barkatai hakan shine burinsa, dukda kuwa ya saka a ransa in sha Allah Halima ita kad ai ce matar aurensa amma ya tsara zata haifa masa akai-akai in sha Allahu har sai haihuwar ta tsaya dan kanta.
Bayan rasuwar Mahaifinsa Kaka k in ci gaba da zama a Getso ta yi ta tarkato ta dawo gidan Mallan da d amarar korar Inna daga gidan ta ko wacce hanya.
Kwata-kwata Mallan bai san cewa Kaka ba ta son Halima ba dan ta k ark ashin k asa take yin komai. Sai da Inna ta samu cikin Ya Muhammad tukunna true colour d in Kaka ya fito fili ras! Dan kasa ci gaba da danne tsanar Halima ta yi, hankalinsa ya tashi kam a wannan lokacin dan k iri-k iri Kaka ta nuna ba ta son cikin k arshe ma ta ce ba na Mallan d in bane ba, sai da ta saka Inna ta rantse a gaban mai unguwa tukunna aka samu ta sarara mata.
Tun daga nan kuwa hankalin Mallan bai kwanta ba, dan tunda Inna ta fahimci Kaka bata k aunarta itama ta botsare dama itama fitinanniyar ce ta bugawa a jarida shiyasa kwata-kwata sai aka gagara samun sauk i ta ko wanne b angare, kullum cikin rigima suke babu mai d agawa wani k afa.
Sai da Kaka ta kwanta jinya a lokacin da aka ce mata Inna ta haifi d anta Namiji fari sol da shi kamarsu d aya sak! Kamar ta yi kaki ta tofar( lokacin shekara d aya da auran Inna da Mallan).
Bayan ta warke ta je Getso ta dawo, ita dai Inna har gobe Kaka take zargi akan rashin lafiyar Ya Muhammad dan tunda ta dawo ta d aukesa ta shige d akinta da shi daga baya ta dawo mata da shi shikenan Yaron ya fara shisshhid ewa a take idanunsa suka k akk afe& .sai da aka kai ruwa rana tukunna da kyar aka samu kansa a asibiti, ai kuwa tun daga nan ko kuka ya yi mai tsaho sai sun yi sama da sati a asibiti, sai da ya yi wayo tukunna aka fahimci ashe abun hauka ne, dan Idan ya motsa har duka yake yi kuma burinsa kawai ya kawar da duk wani da ke a kusa da shi, to idan ya lafa kuma sai ya zama kamar wani zombie kafin a hankali a hankali kuma ya warware.
Da aka haifi Ya Aminu nan ma sai da Kaka ta kusan zaucewa wanda hakan ya yi matuk ar bawa Mallan mamaki da tsoro kuma ya sake tabbatarwa tabbas ba ta son Inna.
Tun daga nan ta tayar da ballin  sai Mallan ya k ara aure
A ganinta tunda ta kasa ita kad ai idan aka yowa Innar kishiya kishiyar zata tayata su fitar da ita cikin sauk i.
Asabe y ar k awar Kaka ce dan tunda Kaka ta dawo layin suke shiri a lokacin sune manyan layi, ita Kaka d anta yana da gida mai d akuna dayawa ita kuma mahaifiyar Asabe Mijinta yana da kud i.
Daga baya baya dai Ita mahaifiyar Asabe ta d an ja jiki lokacin da duniya ta fara yiwa Mallan zafi, dan shi bai yi karatun boko ba, kuma tunda Malaminsa (uban gidan sa) ya rasu komai sai ya jaa baya.
Sai dai kuma Kaka tana zuwa da zancen aure ta yi karaf ta amince dan a lokacin Asaben ta yi laifi Mahaifinta yana shirin aurawa wani Yaronsa ita kuma Yaron nasa a Sumaila yake matansa uku ita ce ta hud u, gashi dama ta san Asaben tana son Mallan, fad a ne kawai ba su yi ba a ganin uwar hakan zubar da girma ne.

Sai da Inna ta yi da gaske tukunna ta iya rik e kanta da auren ya taho gadan-gadan. Shi Kansa Mallan d in ba so yake yi ba babu yadda ya iya ne, haka nan Kaka ta yi ruwa ta yi tsaki sai da ta ga Asabe a d akin Mallan tukunna hankalinta ya kwanta.
Lokacin auren Mallan da Inna shekaru 15 kenan.
Babu kalar gorin da Inna ba ta ji ba, har da cewa  A bawa Asabe d akuna hud u dan ita d in tana da dangi da nasaba an san za a yi mata kayan d aki
Sai gashi Asabe ta zo daga ita sai wani gado low class a lokacin, da wata yololuwar katifa, ai kuwa nan itama Inna ta samu na yi ta tisa su gaba da nata gorin dan ko ita da take ba uwa ba uba ba dangi kayan da ta siyawa kanta a lokacin aurenta ya fi na Asabe.
Ganin wannan gorin bai ci ba sai Kaka ta fara maganar haihuwa dan a lokacin shekarar Inna goma sha biyar da auren Mallan amma y ayanta biyu tana da cikin Dije. Kullum Kaka bata da abin fad e sai  a matsa ga mai cika gidan nan ta zo .
Sai gashi sai da aka yi shekaru hud u lokacin har Dije an Haifa ta yi wayo sosai tukunna Asabe ta samu cikin Zainab da kyar kuma tun daga kan Zainab haihuwar ta tsaya mata ita ma Inna haka wanda zuwa wannan lokacin duk sun fahimci Mallan d in ne bashi da rabon haihuwar da yawa.

Duniya ta yi zafi, babu tayi yawa, wannan dalilin ya sanya Mallan ya fara raba d akunan gidansa a haya saboda su samu abin rik e kansu, su dinga rufawa kansu asiri, dan shi Mallan bai iya sana a ba sam bata karb esa ba, Ya Muhammad kuma bashi da Isashshiyar lafiya, Minu ne kawai da ya taso yake sana ar carpinter, sai ko kiwon kajin da ya fara, wanda kud in duk a registration da handouts ya yi ta tafiya, dan yanzu haka ya kammala buk inda ya karanci geography service yake shirin farawa.
D akuna goma sha uku ne a gidan, biyun farkon na Mallan ne da Kaka, sai na farko da yake cikin d akunan hannun dama kuma na mazan gidan ne, duk wani Namiji tun daga kan Ya Kamal har zuwa kan Umar duk a d akin suke. Na kusa da shi kuma d akin Maman Fati ne, Maman Fati tana da Miji Yunusa cirani yake zuwa Lagos yana da wata a chan, ya kan yi wata bakwai bai zo ba, kuma idan ya zo bai fi ya yi kwana biyu ba ya koma.
Baban Fati irin masifaffun mazan nan ne shiyasa wani lokacin ita kanta Kaka take shakkarsa. Ita kuma Maman Fati munafurci da fuska biyun da ta kware a kai ne ya sanya take iya zama da shi, dan hatta matarsa ta chan chanjawa yake yi baya tab a iya yin shekara d aya da mace saboda halinsa na zuciya da saurin fushi da fad a.
Y ay ansu biyu, Fatima (sa ar Dije da Umar sa an Zainab).

Sai d akin su Dije, Dije shekarunta sha shidda, Ya Aminu ashirin da hud u, sai Ya Muhammad talatin, Dije tana ss3 yanzu haka Ya Aminu ya gama University amma shi Ya Muhammad da kyar aka samu ya kammala diploma daga nan shi da kansa ya ce  ya hak ura dan karatun duk a daddafe ya yi gashi sai yayi ta zubewa ana kwaso shi.
Aure kuwa sau biyu ya yi sa shima daga nan ya ce  ya hak ura
Dan bayan wadda aka sani ya aura a nan unguwa uku, Mallan ya nema masa auren wata a Garko aka d aura ya tare sai dai ko kwana ita kam bata yi ba ma aka fitar da ita a sume! Dan dama a tsorace yake tun da yaga an d aura auren yake gudun abunda zai je ya dawo, kuma tsoro wahala da b acin rai su suke triggering ciwon nasa.

Sai Maman Kubra, ita kuma tana da y ay a da yawa amma rasuwar Mijinta ya sanya aka karb e su aka barta da k ananun kawai y an biyu Kubra da Usman (Usso), unfortunately Usman yana shaye-shaye sosai an kasa rabasa da shi haka nan ake ta fama, Kubra a k alla yanzu shekarunta sha takwas amma rashin dai dai ita a cikin gidan ya sanya ta shiga group d in su Rakiya. Doguwa ce sosai fara sol da ita dan asalin Mahaifinsu Igbo ne, yanzu haka duk y an uwanta suna hannun Kakarsu wadda itama ta tsani uwarsu kamar mutuwarta saboda kasancewarta Bahaushiya ita kuma ta fi so a auri ta su. Wannan rashin jituwar da ke tsakanin Kakarsu da Uwarsu shi ya yi sanadiyyar yanke hatta zumuncin da ke tsanin su Kubra da y an uwansu.

D akunan da suke kallon k ofar shigowa tsakar gidan kuma (guda hud u) D aya na Asabe ne, d aya Empty ba kowa a ciki, sai na kusa da shi kuma d akin wata copper ne (Grace) ita kam ba ma ta zama sosai
Kullum sai dare take dawowa ta kwana da safe k arfe tara take
fita. Copper nan tana ganin ikon Allah a cikin gidan dan hatta band aki idan ta shiga ta fito sai an yi masa wankan tsarki, gashi su yi ta munafurcinta da Hausa dan ita bata ji ammafa tana fahimta, dan suna farawa ta san me suke yi, gata shiru-shiru da ita babu ruwanta amma hakan bai hanasu nuna mata wariyar launin fata ba. Bayaga aikin da ya yi mata yawa da

11 / 33