ANA MALIK HAUSA NOVELS BY HUMAYRA BULAMA .doc

Author :  Humaira Bulama Category :  Top Hausa Novels 2025

Chapter   3 / 33

6K to 9K   out of 98.8K words

kalleta ya ce  Inna ko kin san cewa daga makwabta aka kirani aka ce min har yanzu ba ki yi shiru ba in zo in raba fad an, haka nan na baro marar lafiya na dawo.

Cikin fad a fad a Inna ta ce  Gidan su Suwaiba ko? Shegu munafukai, bar ni da su! Da suka kira ka ka dawo to duka na za ka yi???

Dafe Kai Ya Muhammad ya yi saboda sam shi sentence mai tsaho ma juya masa kai yake yi ballanta doguwar muhawara, cikin rashin jin dad i ya ce  haba mana Inna, ya kike so in yi ne? Da wannen zan ji?
Dan Allah ki daina& 
Cikin katse shi ta ce  na ji!
Zai yi magana ta sake cewa  na ji na ce a d an hassale dan haka ya ja bakinsa ya yi shiruu.
So yake ya fad a mata sak on Mallan da ya ce  Ita da Dije su bada kud i a kai Zainab chemist amma yana jin tsoro dan ya san ba zata bayar ba kuma bala i ne zai kunno kai, dan haka kawai sai ya yanke shawarar kai Zainab d in da aljihunsa in ya so ya ce mata Inna ce ta bayar da kud in dan ya san dole Mallan zai nemi ji daga wajensu, Allah dai ya sa Yarinyar ta yarda dan a yadda aka gama kashe boss da uwarta da Innar ya san tana da
wayon da ya ci ta fahimci kud in kaita chemist ba zai tab a fitowa daga aljihun Innaa a yau ba.

Haka nan ya k arasa ya yi sallama a k ofar d akin nasu ya ce  Zainab ta zo zai kaita chemist a duba mata hancinta in da ya fashe.
Sosai Asabe ta so ta hana ganin sai yanzu ma aka kula su amma kuma kawai sai ta barta ta bishi a ranta ta ce  raba Arne da makami ibada ne.


Bayan Ya Muhammad ya fita, sallah Inna ta fara yi daga nan ta zari mayafinta sai gidansu Suwaiba makwabtansu.
Sai da ta yi musu tatass!! Tukunna ta ji zuciyarta ta d an yi sanyi ba laifi dukda kuwa rashin tanka mata d in da suka yi ya b ata mata rai amma dai ta rage takaicinta. Haka nan ta k are musu d iban albarka tare da kwakkwaran kashedin su daina yi mata shishshigi da munafurci daga nan ta juya ta fita ta koma gida..


Sai gab da sallar isha tukunna aka dawo da Minu. D akin mazan gidan shine na farko a jerin d akuna hud u da suke a hannun hagu, dan haka suka nufi nan da shi, amma sai Mallan ya ce  su dawo da shi d akinsa mai k ofa ta soro Hakan kuwa aka yi suka kai shi daga nan suka yi masa sallama suka wuce bayan wasu a cikinsu sun shiga sun lek a sun gaida Inna tare da yi mata jaje da fatan Allah ya kare gaba.

Wannan Abu da aka yi ba k aramin sake tunzura Asabe ya yi ba, dan ta gama tsarawa idan ta je turaka ne zata warware masa abunda ya ke cikinta amma gashi ya ce a kai Minu bayan yau d in ba kwanan uwarsa bane ba kwanan ta ne.

Har wajajen k arfe goma ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????na dare bata ji kuma ba ta ga an fito da Minu ba dan haka hankalinta ya sake tashi ranta ya sake b aci!!  Ta yaya ma za a d auki k asurgumin gardi a d aura a kan katifar sunnah fisabilillahi Ta aiyyana hakan a cikin ranta. Ta dad e a tsaye tana ta faman lek en d akin, da yake akwai wata k ofar shiga d akin ta inda suke shiga ita da Inna da window ya sanya ta hango yadda aka rage fitilar alamun ana shirin yin barci kenan& .
Ko mayafi bata tsaya d auka ba daga ita sai y ar hula da sleeping dress d in da matar manager ta bata a kayan kunce dan Asabe ba dai son gayu ba, haka nan ta fito rai a b ace ta Isa bakin k ofar ta saka hannu ta tura amma sai ta jita a rufe.
B acin ranta ne ya sake hauhawa dan haka ta zagaya ta Isa bakin k ofar d akin dake a soro ta fara bubbugawa& .
Ba ta wani jima ba ya zo ya bud e mata, har yanzun rawani ne da babbar riga a jikinsa alamun bai yi shirin kwanciya ba.
Kallonta ya yi kafin ya yi gyaran murya ya ce  yi hak uri ban nemeki da wuri ba, yanzu nake shirin zuwa in nemi yardarki akan Minu
ya kwana a wajena, Ina ga ba sai kin zo ba ko? Akwai tofin da nake son in kwana yi masa saboda kin san al amari idan ya shafi kai dole a bashi muhimmanci.
Ba tare da ta kalle sa ba ta ce  ban amince ba .

Yadda ya yi da fuskarsa zai sanya ka fahimci maganar ta dake sa matuk a amma sai ya kawar yana shirin yin magana ta katseshi ta hanyar sake cewa
 Ban fa amince ba kuma ban lamunta ba! Ai kai Malami ne mai tsoron Allah dan haka na san ka san yin hakan haramun ne.

Dai dai nan Kaka wadda tun d azu ta ga fitowarta ta k araso wajen cikin takunta na tsoffi rai a d an b ace ta ce  yanzu ja inja za ku tsaya yi ku tarawa kanku jama a ko yaya?

Dai dai nan Minu wanda tunda ta fara maganar ya farka ya tashi daga kan kafet d in inda ya yi shimfida shima ya k araso wajen&
Da kyar kunya ta barshi ya iya cewa  Mallan bara in je da safe sai ka k arasa min.

Cikin d an b acin rai Mallan d in ya ce  wa ya sako da kai?
Yana shirin yin magana Kaka ta ce  Aminu wuce ka tafi d akinku

A hankali Mallan ya sunkuyar da kai ya kasa cewa komai.

Simi simi Minu ya zo ya wuce bayan ya yi musu sai da safe gaba d aya jikinsa babu kwari.

Cikin d an fad a fad a a hankali saboda kar a ji Kaka ta ce  ka san Allah idan ba ka daina gwada wannan son kan da nuna banbancin ba to ka tabbata za mu samu matsala da kai! Wanne irin sakarci ne haka za ka d auko k ato ka saka a d aki ranar kwananta?? Kuma idan ta yi magana sai a ce ba ta da gaskiya ba ta kara bayan kune da laifi!
Ina ce rigimar y ar uwarsa ce ta jefa shi a matsalar dan haka Ina ruwanka?? Ai dama abunda ake fad a ake guje muku kenan amma sam ba kwa ji yanzu ga irinta nan!
Ayi mutum kamar mai karin kumallo da wuta amma sam baka son laifinta ita da uwarta ai kuwa ka gamu da aiki babba wallahi..
Sannan Ina so ka jaa wa Halima kunne duk da na san ba jinka zata yi ba dan ta raina kowa amma dai ka fad a mata kuma ka yi mata kashedi mai zafi!!! D azu bayan ka fita haka nan ta wuni a gidan nan tana rashin albarka dukda kuwa kashedin da na yi mata amma bata ji ba saboda ta raina ni, ban kula ta ba a lokacin amma wallahi ka ce mata na ce idan ta k ara to ni da ita ne a cikin gidan nan, da ni za ta yi! Ai ta sanni ta san abunda zan iya aikatawa dan haka mu zuba ni da ita a cikin gidan nan tunda ita dai ta ce bata san mutunci ba.
Tana gama fad in haka ta juya ta bar wajen zuciyarta fal tsanar Inna da y ay anta.

Tana wucewa ya juya shima ya wuce ciki ya barwa Asabe k ofa a bud e ba tare da yace mata komai ba. Ya san tana fashin sallah yau d in shiyasa ya so yiwa Minu tofi da addu o in kuma har ga Allah bai yi zaton zata ji haushi ko ta ce bata yarda ba dan inda ace ya san zata yi hakan to da ba zai ma fara ba, duba da yadda Minun yake jin jiki ya sanya ya yi tunanin zata yi masa kawaici amma kalli abunda matar nan ta yi, shi kwata kwata ya rasa gane dalilin da ya sanya har gobe ita da Halima ba zasu rungumi juna su so y ay ansu a matsayin abu d aya ba.
Yana wannan lissafin ya k arasa cikin d akin ba tare da ya ko waiwayeta ba.

Ta so ta yi masa k orafe k orafe had e da lallashi ban hak uri tare da kissa amma yadda ya had e rai wanda hakan abune sabo a wajenta ya sanya ta sha jinin jikinta ta nemi gefen katifa ta kwanta& & & .


Tunda dare ya yi dama Dije ta sha jinin jikinta, kana ganinta ka san a tsorace ta ke, ai
kuwa ta fara bacci
kenan ta ji sauk ar wayar radio& & Gashi babu damar ta yi ihu.
Sai da Inna ta zane ta da wayar radion nan kamar wata y ar Yarinya tukunna ta rufeta da fad a baki da kumfa, sannan ta ce  daga yau ko a hanya ne idan ta ga Ma a to ta chanja tata hanyar
Sam Inna ta ma k i ta tsaya ta ji bayanin Dije da take ta cewa  k arya Zainab ta yi mata Ma a bai rik eta ba Ya Aminu bai bashi dama ba
Dama ita Innar ta san da hakan, ita kawai abinda ya fi damunta shine  Ma a d in wanda ta lura ya fara sakawa Dijen ido dayawa kamar sauran samarin layi, gashi ita kuma mahaukaciyar Yarinyar a nata shirmen tsayawa take yi ta ce zata yi fad a ko ta biye masa& tun kafin Dije ta kai haka Inna take addu ar Allah ya kareta daga sharrin maza, gashi Yarinyar tun lokacin da ta fara al ada gaba d aya ta bunkushe kullum komai nata sake fitowa yake gashi surarta mai matuk ar d aukar hankali ce, shiyasa kwata kwata ko da wasa bata k aunar abunda zai had a ta da wani d a Namijin idan ba su Aminu ba, dan haka take a tsaye idanunta a kanta sosai wannan dalili ya sanya ita kanta Dije in dai ta san an ganta da wani ko wani ya biyo ta to a d ari-d ari take wuni, idan kuwa ta san an ganta da Ma a to a tsorace ta ke kai dare dan ta san wayar radion Inna na nan tana jiranta.
Ba Inna kad ai ba hatta su Ya Aminu da Mallan ganin Yarinya suke yi mata har yanzun, sannan karatu suke so ta yi a halin yanzun ba wai tara samari tun bata gama secondary school ba. Shiyasa sam ba su bada goyon bayan ta kula samari ba, musamman ma Minu wanda indai kana so ya daina ganin mutuncin ka to ka ce  kana son k anwarsa Dije .


Washegari da safe ta kasance Asabar, ranar hutun mako ta farko, ranar da al umma sukan d an kwanta su huta saboda babu fitar safe..ga kowa kusan hakan take amma ga al ummar wannan gida kuwa za a iya cewa yau d in tun Asubar fari suka fara tashin hankalin nasu wanda ya zame musu tambari a unguwa.



BULAMA
'?
0806 402 1951
ANA MALIK!!
Book 01.
Page 03.

Humairah Bulama.
Mikiya writers Association.

Tun kiran sallar farko da aka yi Ramma ta tashi bata koma ba, tana ta fama da k ullin fanken siyarwarn ta wanda ya k i tashi sam! Dama tun jiya da daddare bayan ta kwanta ta d an ji sanyi-sanyi da iska a garin sai da ta tashi yanzun tukunna ta ga ashe hadari ne a kwance gashi kuma sai da ta duba sai ta ga ashe yeast d in marar kyau ne, dan haka ta karb i wani a wajen Maman fati ta k ara sannan ta d aura ruwan d umi a murhunta dan ba ta ga alamun rana zata fito da wuri ba yau d in.

Kasancewar ta san idan ta fita k ofar gida tuyar fanken to ba lalle ta gama ta dawo da wuri bane ya sanya ta koma d akinta ta shiga k imtsawa.
Mijin Ramma bai dad e da rasuwa ba ya rasu ya barta da Yara uku..Y ay anta biyu mata Fiddausi da Rakiya, Fiddausi na da shekara goma Rakiya kuma sha biyar sai Usama na tsakiyar su mai shekaru sha uku& .
Y an matan suna kwance suna ta sharar barci ta shiga ta kimtsa ta gyara ta share koina ta tattare ta linke kaya, gadon da suke kwance kawai ta bar musu idan sun tashi su gyara sai
kuma tallar fanken da idan ya yi saura Fiddausi za ta tafi ta kaiwa wata makarantar koyon d inki Umar kuma shi zai yi wanke wanke Rakiya kuwa ba ta uwar komai dan har girki ba ta cika yi ba Ramma ce ta ke yi, Ramma irin matan nan ne masu masifar son y ay ansu da sangarta su gashi bata so su wahala musamman Rakiya .
Ba su dad e da dawowa Unguwar ba Mijinta ya rasu yau shekaru biyu kenan, tun daga nan ta d auki nauyin y ayanta uku daman kuma daga danginta har na marigayin Mijin nata duk ba masu zumunci bane ba dukiyar marayun ma da bata fi miliyan biyar ba gaba d ayanta wani k aninsa ya handame yanzu haka ana kotu. Babu yadda ba ayi da Ramma ba akan ta bar y ay anta suma su yi sana a amma furr ta k i! Ita ce wankau ita ce suyar fanke asabar da lahadi Litinin zuwa Juma a kuma akwai wata makarantar boko da take yi musu nanny. Rakiya ta iya kitso amma har shi uwarta ta hanata yi a ganinta y ay anta suna da gata tunda suna da ita dan haka ba za su wahala ba.
A kaff gidan za a iya cewa daga Inna sai Ramma a masifa! Irin masifaffun matan nan ne gata wata y ar firit da ita sai shegen k arfi da masifar d aurawa kai& &

Ba ta yi minti ashirin ba ta kammala kimtsa d akin ta fito hannunta rik e da tsintsiya da abunda ta kwaso shara a ciki.

Ba ta kai ga kaiwa bolar ba ta hangi Asabe a cikin kitchen d in ta bud e mata tukunya tana ta d ibar ruwa daga wani botiki tana zubawa a cikin tukunyar.

A yadda ta bar tukunyar tata cike taff da ruwa ta san ko
kofi d aya ba zai yiu a k ara a kai ba tukunyar za ta yi anbaliya amma gashi da ikon Allah Asabe ta kusa juye rabin bokiti amma tukunyar ba ta cika ba.
Kwana ta yi ta nufi kitchen d in hannunta har yanzu rik e da tsintsiya da katin d aurin auren da ta kwaso sharar d akinta a ciki ta nufi kitchen d in tana adduar Allah dai ya sa ba ruwan fankenta Asabe ta tab a ba.
Kasancewar gari bai fara yin haske ba ya sanya sai da Ramma ta shiga cikin kitchen d in tukunna ta lura da Zainab d aure da zani a tsaye tana rawar sanyi..

Tana shigowa Asabe ta d ago a d an zabure sai kuma ta dake ta ce  Au Ramma ke ce? Ruwan ki ne?
Zuwa yanzu Ramma ta gama gasgata tabbas ruwanta Asabe ta kandame yanzun kuma take mayar mata da mai sanyi dan haka ta gyara tsayuwarta ranta yana gama b aci ta ce  A a na uwarki ne!
Cikin tsananin fushi Asabe ta ce  durun uwa salatin arna, kina da isashshen hankali kuwa? A kan ruwan zafi za ki sako uwata a cikin shirmenki?
Ta yi maganar tana mai k arasawa daff da ita tana dukan k irjinta.
Dai dai nan Iyya ta shigo cikin kitchen d in hannunta rik e da buta da fitila tana salati, cikin takun ta na tsoffi ta k arasa kusa da su ta ce  haba mana Asabe me ye haka ne kuke yi, gari fa ko fara wayewa bai yi ba?
Cikin zafi masifa da d acin zuciya Asabe ta ce  wai dan uban wannan matar har ita ta isa ta sako uwata a cikin haukan ta? Kin ga fa Zainab ce zazzab i ya rufe cikin dare ta kwana tana amai jiya ita kad ai a d aki shine yanzu ina shiga na tsinceta kwance shame shame cikin k azanta ga zazzab i ruff a jikinta. Shine wai dan na tab a ruwanta na yi mata wanka yanzu na mayar mata har take da bakin zagina!
Dan ubanki kitchen d in na Tanimu ne?
Salati Iyya ta yi sannan ta ce Ramma ba ki kyauta ba iyaye sun fi k arfin wasa sannann larura ce ta sanya ta tab a miki ruwa ba son ranta ba, ke kuma Asabe dan girman Allah kar in sake ji kin sako mamaci a cikin fad an ku hakan ba dacewa bane ba!& 

Wani Irin huci Ramma ta ke yi zuciyarta tana wani irin tafarfasa, sai da Asabe ta kai aya tukunna ta saka dukkannin k arfinta ta ingije ta cikin zafin nama ta isa inda Zainab ta ke ta d aga gaba d aya sharar d akinta wadda ta kwaso a cikin katin d aurin auren nan ta juyewa Zainab a cikin gashinta da jikinta sannan ta durk usa ta dumbuzo rairayin k asan kitchen d in har da toka ta watsa mata a jiki.

Kukan kura Asabe ta yi ta yo kanta dai dai nan Ramma ta yi saurin gocewa ta tafi ta afka kan tukunyar gaba d aya ruwan ciki ya kelaye a kitchen d in ya jik a koina da duk wani icce

3 / 33