ANA MALIK HAUSA NOVELS BY HUMAYRA BULAMA .doc

Author :  Humaira Bulama Category :  Top Hausa Novels 2025

Chapter   2 / 33

3K to 6K   out of 98.8K words

kwaso su suka kawo su nan wanda sun san tab a shi dai dai yake da rasa aiyyukan su, duk matsayin mutum kuwa.

Tunda aka yi wurgi da Ya Aminu ta nufesa ta durk usa a wajen ta fashe da kuka dan sam baya motsi gashi gefen kansa inda ya bugu da dutsen sosai ya fashe.

Kukan da take yi sai da ta bawa kowa tausayi a wajen gashi babu mai damar taimakonsu.

Tunda ta je ta durk usa a wajen yake kallonta, kafin daga bisani ya juya ya yi wani tsaki ya bar wajen.
Sai da ya yi wajen taku biyar tukunna Yaran nasa suka samu damar binsa a baya dan abun ya yi matuk ar basu mamaki! Su da suke shirin fara cin uwar Minu a hakan a yadda yake amma kalli abinda Oga ya yi!?
Sosai abun ya d aure musu kai amma sai suka yi tunanin maybe barinsa zai yi ya warke tukunna ya ci ubansa ta yadda zai fi galabaituwa! Amma kuma duba da yadda Yarinyar itama ta dad e tana yi musu hauka amma ya hana ko kallon banza ne a yi mata ya sanya suka saka kokwanto a al amarin& .
A haka dai suka bishi a baya zuciyoyinsu fal tambayoyin da basu isa su yisu ba.

Su Ma a suna wucewa kowa ya tuttulo aka yo kan Minu har da y an sandan da aka d auko takanas akan su yiwa tufkar hanci kafin a yi b arna amma suka mak ale.
Suna zuwa wajen wata tsohowa ta ce  Dalla chan malamai ku matsa daga nan, baku da amfani kwata kwata ga al aumma wallahi, ace Yaro kwalli d aya ya addabemu ya hana mu sukuni amma kun kasa tab uka uwar komai! Tsoronsa kuke ji ne? Ko
ya fi k arfin hukuma ne? .
Ai kuwa kamar jira jama ar wajen suke yi nan suka hau kan y an sandan kamar za su rufe su da duka.
Basu kula su ba instead k ok ari suka yi suka saka Minu a mota a ka wuce da shi asibiti zuciyoyinsu fal alhini! Tabbas abunda mutanen nan suka fad a gaskiya ne amma suma d in komai ya fi k arfin su ne shiyasa.

Kusan duk mutanen da suka zo da y an sandan ne suka tafi kai Minu asibiti, d aya daga cikin biyun da suka taho da shi wajen Ma a d azu  Ya Kamal kuma ya tafi kai Dije gida domin su je su sanarwa da su Mallan halin da ake ciki.


Babban gida ne gidan haya mai d auke da d akuna a k alla guda goma sha uku& ta wani dogon soro suka bi kafin su k arasa cikin gidan wanda tsakar gidan dududu ba zai iya cinye k ananan motoci biyu ba amma sai uban tarkace da igiyoyin shanya ga wata uwar rijiya da aka yiwa d ogwarago kana shiga ita kake fara hange. Band akin maza a farko-farkon dogon soron yake yayinda na mata yake ata gefe jikin k ofar shigowa cikin tsakar gidan sai kitchen a ta chaan lungun bandak in matan fuskarsa tana kallon ka idan ka kalli direction d in da yake. Daga kitchen d in har band akunan gaba d aya babu wanda ya samu arzik in k ofa sai dai in ka zo shiga bayin ka nemi zani ko dai wani kyallen ka yafa ka yi uzurin ka wanda hakan shike nunawa wanda ya tunkaro wajen akwai mutum a ciki. Siminti ne a shimfid e a tsakar gidan wanda bashi da maraba da rairayi sakamokon farfashewar da yayi ta koina.

Daga b angaren dama d akuna ne guda hud u y an fici fici a jere sai guda uku suna kallon su yayinda hud u suke a ta chan k uryar gidan a jere suna kallon k ofa sai guda biyu manya manya sosai d ayan har da band aki a cinkinsa suna kallon ukun k ofofinsu jere da k ofar shigowa amma d ayan d akin an bud e masa wata k ofar ta soro.
A tsakar gidan akwai kejin kaji mai hawa biyu da alama kiwo mai shi yake yi sannan alwai rago da akuya sabbin haihuwa ga kuma uban tulin wanki k ulli-k ulli wani a kan wani sun kai guda goma wanda kana gani ka san akwai mai wankau a gidan.

A tsaye cirko cirko suka tarar da mutanen gidan Yara da manya da y an mata..tsakar gidan ya cika taff da jama a tubarkallah har da mak wafta.
Zainab ta hanga a tsakiyarsu Yarinyar da ba zata haura shekaru sha biyu ba, hankalin kowa a kanta tana ta zuba bayani dalla dalla, duk inda ta kai aya ta dire sai a hau salati da sallallami ana tafa hannu sai kuma a yi shiru ita kuma ta d aura daga inda ta tsaya.

Tsabar yadda hankalin ilahirin jama ar yake a kan Zainab babu wanda ya lura da shigowar Dije da Ya Kamal, idanunsu ya rufe daga jin labarin A bu wanda yake kamar busharar shiga gidan aljannah a zuciyoyin wasu.

Ganin yadda aka bata muhimmanci aka yi mata k awanya kowa ya bata hankalinsa ya sanya Zainab d in ta fara had awa da k arya da sharri har da cewa  da Ma a ya janyo Dije sai da ya rungumeta ya shafa mata k ugu tukunna da kyar ya Aminu ya finciketa daga jikinsa
Wata y ar budurwa tsarar Dijen ce a wajen ta ce  Anya kuwa A bu wannan ba k arya kike yi ba? .
Nan kuwa ta hau rantse rantse matan gidan suna tayata da cewa  Ai A bu ba ta k arya, tunda ta fad a to an yi hakan& 

Babu wanda ya ga tahowar Dije sai ingije jama ar wajen da ta ke ta faman yi wajen k ok arin ganin ta isa ga A bu ne ya fargar da wasu.
Kafin su ankare kuwa har ta isa ta finciko wuyan rigar A bu! Bata yi wata wata ba ta d auketa da Mari ji kake tasss!!! Dama a zuciye take ranta a b ace yake.

Cike da masifa uwar A bu wadda take wajen ta fara zaginta tana kai mata duka sai dai cunkoson mutanen wajen bai sanya dukan ya shafeta ba.
Cikin lokaci k alilan waje ya hautsine dan Dije ta damk i wuyan A bu kamar mai shirin aikata lahira tana danna mata ashar ta uwa ta uba tana kiranta da mak aryaciya tsinanniya& &

Wata uwar tsawa aka daka  Dije!!! Wanda hakan ya sanya kowa ya sha jinin jikinsa yayinda wasu kuma suka hau k unk uni musamman mahaifiyar A bu.

Da mugun k arfi Dije ta runtse idanunta dan bata so Allah ya kawo mai raba ta da A bu ba a yau d  in nan! Yarinyar ta sha k ulla mata munafurci kala kala dama tun ba yau ba. Ita babban abunda ya fi k ular da ita ma shine shafa mata k ugun da aka ce wai Ma a ya yi! Mutumin da ta tsana kamar mutuwarta& .

 Za ki cikata ko sai na k araso???

Shiruu haka wajen ya d auka baka jin k arar komai sai na sheshshek ar kukan A bu wadda hatta bakinta ya fashe.
Tana haki tana huci zuciyarta a wuya ta cika ta ta d an ja baya ta sunkuyar ta kanta k asa tana k ok arin hana kanta kuka dan kwata kwata dukan da ta yiwa Abu bai gamsar da ita ba.

 Wuce ki tafi d aki
Ya ce da ita idanunsa a kanta.

 Allah gafarta Mallan gaskiya yau dai sai an bi mana hakkin mu
Mahaifiyar Zainab ta fad a tana kallon gefe tana harare harare.

Ba tare da ya kula ta ko ya kalli inda take ba ya juya ya bar wajen ya nufi k ofar d akinsa dake a soro.

Ido ta had a da Ya Muhammad tsaye a gefen Ya Kamal wanda ya rakota gidan duk sai ta ji babu dad i. Mallan yana wucewa Ya Muhammad shima ya juya ya bi bayansa yayinda Ya Kamal ya k araso wajen ya ce  Inna bata da lafiya haka Minu shima kuma duk a ta sanadiyyar ki ne amma kalli abunda kika sake aikatawa.
A harzuk e Mahaifiyar Zainab ta ce  yo ai gada ta yi! Ka ga laifinta? Ai ta san tana da d aurin gindi ta ko wanne b angare ne shiyasa take abunda ta ga dama, to dai gashi maza sun fara latsata kuma gashi ba a son laifinta dan haka ban san yaya zata kaya ba! Mu dai Allah kiyaye mu da ganin abun kunya.
Cikin fushi Dije ta ce  uwark.
Da sauri Ya Kamal ya ce  Au Allah??? Da k arfi cikin katseta sannan ya ce  wuce ki tafi kafin in yi ball da ke a wajen nan wallahi.

Ba dan ta so ba ta juya ta wuce cikin d akinsu inda Inna take jinya amma wallahi ta ci alwashi sai ta mayar wa da Asabe martani tunda ita dai bata san ya kamata ba& .
Haka nan ta shige d akin tana jinsu ita da y an koron ta suna ta yayata maganar suna sake assasa abun.
Turuss!! Haka ta ja ta tsaya sakamokon ido biyu da ta yi da Inna a zaune Anty Sakina tana yi mata allurar jijiya.
Da sassarfa ta Isa gareta tana duddubawa kafin ta d ago idanunta da har sun d an sake kad awa ta ce  Inna jikin dai? Sannu.
Jinjina mata kai kawai Inna ta yi tana mai sauraren zage zage da d ibar albarkar da Asabe take zubawa har yanzu, gashi sai aibanta Dije take yi ana ta mayar da magana ana cewa  Ma a ya rungumeta ya shashshafeta yau d in ita kuma tana sake rurawa abun wuta tana sake d abbaka zancen.

Ya Muhammad ne ya shigo cikin d akin hannunsa d auke da wani kwano wanda Mallan ya gama tofi a cikinsa yanzun ya ce ya kawowa Inna ta sha.

A gabanta ya durk usa sannan ya mik a mata ya ce  gashi in ji Mallan.
Jinjina kai ta yi ta ce  ya ake ciki da al amarin Aminun?

Wata nannuyar ajiyar zuciya ya sauk e kafin ya ce  ban je ba tukunna, ki kwantar da hankalin ki zai samu lafiya in sha Allah.

Jinjina kai kawai ta yi dai dai nan Sakina ta gama juye mata ruwan allurar a cikin jijiyar ta ta zare sannan ta fara k ok arin tattare kayanta, sai da ta had a komai tsaff tukunna ta sake yiwa Inna jaje tare da addu ar neman sauk i daga nan ta mik e ta fita.

Tunda ya Muhammad ya shigo cikin d akin Dije take ta faman sunne kai kamar wata ta kirki.
Sakina tana fita ya zuba mata manyan idanuwansa farare k all kawai yana kallonta ba tare da ya ce mata komai ba.
Kusan minti d aya suka kwashe a haka ganin bashi da niyyar yin magana ya sanya ta magantu da kanta, ta ce  dan Allah ka yi hak uri, Inna ku yi hak uri ba zan sake ba
 Ba zaki sake me ba?
Ya jefo mata tambayar idanunsa a kanta.
Inda inda ta fara yi kafin ta ce  duka biyun.
Ajiyar zuciya ya sauk e sannan ya ce  jiya jiya aka gama case d inki da Kaka, damuwa ta haifarwa da Inna ciwo amma kalli yau ma issue har biyu Dije duk a kanki ke kad ai? Idan an yi magana ki ce kina son mu kina tausayinmu, an ya kuwa Dije??

Hawaye ne suka shiga sintiri akan fuskarta da kyar cikin jan hanci ta ce  sune fa suke tsokanata

K uraa mata ido ya yi na y an mintuna kafin chaan ya ce  ko da wasa kar in sake ganinki a nesa da Ma a ma ballantana kusa da shi!
A hankali ta ce  Yaya shine fa ya tare min& 
 Shiiii ya ce da ita yana mai d aura hannunsa a kan lips d insa kafin ya ce  abunda na fad a kenan
Daga haka ya fara k ok arin mik ewa yana mai cewa  Inna bari in je wajen Minu.
Duk sai a lokacin suka lura da yadda sam hankalinta baya a kansu kwata kwata.

Lumshe idanuwa ya Muhammad ya yi ya bud e kafin ya ce  Inna dan Allah ki rabu da su kar maganar su ya dame ki

 Ai dama kina ganin yadda take kumbura kwana biyun nan kin san akwai dalili! Shegiyar Yarinya ashe latseta ake yi bamu sani ba! Ta fito tana ta juya mana mazaunai ita nan ga mai diri nan kuwa ba na Allah da Annabi bane ba& ..
Muryar Asabe ta ratsa kunnuwansu.

Zurufff! Inna ta yi ta mik e tsaye, da sauri ya Muhammad ya runtse idanuwansa, kafin ka ce kwabo har ta fice waje& ..


BULAMA
'?
0806 402 1951
ANA MALIK!!
Book 01.
Page 02.

Humairah Bulama.
Mikiya writers Association.

Inna tana fitowa wasu suka yi shiru yayinda Asabe ta ci gaba da magana kanta tsaye tana aibanta Dije.
Cikin mad aukakin b acin rai Inna ta ce  sannu tambad ad d iya wadda ba ta san ya kamata ba! Yanzu ke abinda kike yi tarbiyyar kenan? Kin tara Yara da muna manyan cikin gida sai zancen batsa kuke yi a gaban Yara k ananu, haka ake tarbiyyar a garin ubanki? .
Da sauri Asabe ta ce  a kul d inki Halimatu! Wallahi a k ul d in ki!! Kar ki
kuskura ki sake ambato mini iyaye da k azamin bakinki, sannan ai gara mu zancen batsa da iskancin muka yi ba aikata shi muka yi da jikinmu ba.
Daff da ita Inna ta matsa sosai ta ce  waye ya aikata iskancin? Waye d an iskan??? Ta yi mata tambayar cikin tsattsareta da manyan idanuwanta tana huci dama tun jiya take neman wanda zata sauk ema takaicin Kaka a ka.
Duk tsageranci irin na Asabe tana shakkar Inna, ta san sarai yanzun sai ta lakad a mata dukan mutuwa ba k aramin aiki ta bane ba yin hakan, dan haka sam sai ta gagara ambatar sunan Dije kamar yadda ta yi niyya taketa kuma fad a tun d azun. Sai kawai ta yi tsaki ta juya ta shige cikin d akinta zuciyarta fal takaici, ga abunda Mallan ya yi mata a kan Dijen yanzun sannan gashi ita da kanta ta yada kanta a gaban mutanen gidan ta sake bawa Halima girma a idanunsu tunda dai gashi k iri k iri ta gagara tanka mata.

 Ki dawo ki tanka mana! K aramar marar kunya k aramar munafuka. Ku kuma y an koronta munafukai mu zuba da ni da ku a cikin gidan nan kar ku fasa fita daga harkata ni da y ay ana wallahi wahala za ku sha

Da sauri wata y ar kyamurmurar mata (Maman Fati) ta ce  Wane mutum! Ai ko giwa ta fad i ta fi k arfin kiyasai su ja gawarta. Su Maman Sagir ne dai y an koronta amma mu ai mun san dai dai mun kuma san gaibu.

D aya bayan d aya aka fara watsewa bayan kusan rabin matan da suke tsakar gidan sun taru sun taushi Inna sun nuna mata su babu ruwansu kamar ba da su aka gama gutsiri tsoma a tsakar gidan yanzun nan ba.
Asabe tana ciki tana ta kwafa tana lissafa mutanen da suke ta bawa Inna hak uri suna cewa  ta rabu da Asabe ba sa ar ta bace ba, kar ta bari ranta ya b aci saboda Asabe
Tana aiyyana kalar yadda itama zata gurza musu tunda ba su san mutunci ba.


Umar da Usama ne kawai suka rage a tsakar gidan dan kowacce ta shige cikin d aki, masu fita yawon Juma a kuma sun fice amma har zuwa wannan lokacin Inna tana nan zaune a tsakar gidan tana bala i da masifa dan tana gama waya da Minu da ta ji jikinsa da sauk i Alhamdulillah nan ta fito ta ja kujera ta dasa a inuwa ta shiga k arewa Asabe d iban albarka, gori kuwa kala kala kamar ita ta yankewa k asar garinsu cibiya& .Kasancewar wata k anwar Asabe ta tab a yin cikin shege, a cikin yayunta maza kuma akwai mai shaye shaye wanda kowa in dai a Unguwar kake to ka san Yaron da shaye shaye da sace sace!Hakan ya sanya Inna ta samu abun yi dama ta saba goronta mata akan hakan amma na yau ya fi na kullum ga kuma wasu sabbin surrakan gidansu waenda ita kanta Asaben ba ta san ta ya aka yi Innar ta ji ba, haka nan dai ta yi mata tatass! Ta tsigale ta ta yi mata tumb ir dan har sai da ta saka Asabe kuka ita kad ai a d aki.
Tukunna da kyar Ya Muhammad wanda ya dawo daga wajen Minu, yau d aya ya ci nasarar mayar da ita d aki lokacin har sallar la asar an yi an idar.

Wunin ranar Asabe a d aki ta yi shi gashi babu wanda ya lek ota dan Inna tana gamawa da ta mik e ta shige d aki sai ragowar matan gidan da basu fita ba suka taru a d akin Ramma aka dasa faifan munafurcin gidan su Asaben! Dama yanzu haka ma akwai wata k anwar ta bazawara da ta fito daga gidan miji kuma matar tana da d an tara zawarawa ga shegen yawo, to ga kuma sabbin abubuwan da suka ji daga bakin Inna yanzun, dan haka topic d insu na ranar sai ya kasance a kanta.


Jikin Minu da sauk i, an yi masa dressing na ciwonsa inda ya yanke a ta sanadiyyar dutsen da Yaron Ma a ya cillashi a kai, yanzu haka ma ruwa ake k ara masa zuwa bayan sallar la asar zai dawo tare da samarin layin da suka yi cincirundon kaisa kuma har yanzu suke a tare da shi, kud in asibitin ma sune suka yi karo karo suka biya& &


Suna shiga d akin Ya Muhammad ya

2 / 33