ANA MALIK HAUSA NOVELS BY HUMAYRA BULAMA .doc

Author :  Humaira Bulama Category :  Top Hausa Novels 2025

Chapter   6 / 33

15K to 18K   out of 98.8K words

naka a d aki naga Asabe bata nan

Shiruu ya d an yi kafin ya juya a
fusace da niyyar fita suka yi kicib is da Dije ta kawo kai, bud ud u da ita kamar wadda ta yi burgima a cikin yashi..
Da mamaki suke kallonta fuskarnan ta yi jaa idanunta sun firfito waje alamun ta ci kuka.
Baba ya tab u kwarai da yanayin nata amma hakan bai hanasa d aga hannu ya d auketa da wani irin gigitaccen Mari ba!
Cikin karsashi ya ce  duk haukarki ta tsaya iya kan mutanen gida amma ko da wasa kar in sake jin fad a tsakaninki da Kaka!
Kamar zai wuce ta ya fita sai kuma ya ce  mai ya sameki kika yi kacha kacha haka? Ko kema kan yashin kika hau?
Sai a lokacin hawayen bak in ciki da takaici suka b alle mata tana yi tana jaan ajiyar zuciya a jejjere&
Sai da Inna ta daka mata tsawa  ba tambayar ki ake yi ba!!! Tukunna ta magantu ta ce  Ma a ne ya d aure mini k afafuwa da hannnu a lungun mal.mai kanti wai sai dai in taho gida a haka kamar tsutsar caterpillar, kuma suka dinga yi min dariya& 
Rasss!!! Gaban Inna ya yanke ya fad i, a ranta ta shiga had a kalmomin tana yi musu fashin bak i a cikin kanta& .Ma a kuma ya d aure ta a lungu!!  Innalillahi wa inna ilaihirrajiun ta shiga nanatawa a cikin ranta sai kuma ta jaaa hannunta suka shige d aki ta ma manta da Mallan a wajen wanda shima ya yi mutuwar tsaye daga jin zancen& tun kwanakin baya ya cewa Kaka yana so su tashi daga Unguwar amma tunda ta ji saboda Dije ne yake so a tashi d in nan ta yi tsalle ta dire ta ce  ba za su tashi ba, ko dai ta kama kanta ko kuma ta zubar ita ta sani amma ba za a wani tashi saboda ita ba kuma in aka sake yi mata maganar sai ta tsinewa mutum.

Suna shiga cikin d akin Inna ta hau duddubata sai kuma ta yi cupping fuskarta a cikin tafukan hannayenta ta ce  ki gaya min gaskiya mai ya faru??

Cikin sheshshek ar kuka dan sosai abun ya b ata mata rai, wai kamar ita Babba da ita za a d aure kuma ta gagara guduwa& ta ce  D azu ne da na dawo daga siyian y ar tsala wai dan in yi sauri sai na biyo ta lungun malan mai kanti, sai da na kusan kaiwa k arshen lungun tukunna na lura da su a zaune Yaransa suna ta shaye shaye. Wari gaba d aya lungun shine na toshe hanci wallahi ko kallonsu ban yi ba ya taso ya zo da kanshi ya saka igiya ya d aure mini hannu da sauri ta baya sannan ya saka d ankwalin Oscar ya d aure min k afafuwana wai dole in tsaya in shak i warin da nake toshe hanci shine garin guduwa na fad i na kasa tafiya wai in yi irin ta cartapillar kawai in k arasa gida a haka.
suka dinga yi min dariya, na dad e ina ta k ok arin tafiya na kasa har rana ta zo kaina shi yana tsaye a kaina su kuma suna gefe suna ta hira, shine yana gani na fara kuka kuma sai ya yi saurin kunce ni ya ce  in tafi, wai ashe ni marar kunyar k arya ce.
Ajiyar zuciya Inna ta sauk e kafin ta ce  kin tabbata shikenan? Daga haka shikenan?
Zuwa yanzu Dije ta gane me innar ta ke nufi dan haka ta ce  ko da ya zo d aurenima ni ban ji ya tab a ni ba.
Sosai Inna ta sake sauk e ajiyar zuciya sai kuma ta koma ta zauna a kan gadonta ta dafe kai.
***
Matsakaicin gida ne (a layin su Dije) mai d auke da d akuna uku da babban band aki da kitchen sai d aki mai bayi a soro shima Babba.
A d an hargitse ya shigo cikin gidan yana rarraba ido, idanunsa suna sauk a a kanta ya k arasa ya zare silifas d insa ya zauna a kan tabarmar nan kusa da ita inda take zaune tana tankad e& .

Murmushi ya yi kafin ya ce  uwargida kuma amarya sarautar mata, barka da gida

Murmushin itama ta mayar masa kafin ta yi masa barka da shigowa sannan ta fara k ok arin mik ewa tana cewa  bari in kawo maka abinci
Da sauri ya rik o hannun nata ya ce  A a ba abinci ba tukunna zauna mu yi wata y ar magana& .a cikin ajiyar da aka baki jiya nake so ki d an bani rance .
A take annurin fuskarta ya d auke, ba ta zauna d in ba ta ce  dan Allah ka rufawa kanka asiri, ni da ace ina da nawa wallahi da na baka ka sani. Kud in nan da ka gani ya bani jiya yau fa yace min zai karb a& 
Cikin katseta ya daka mata wata uwar tsawa yana cewa  ke dalla malama rufewa mutane Baki! Ba wani dogon zance na nemi ji a wajenki ba kud i kawai za ki ranta min. Kin san ni yau nawa na kashewa b arnar da ya yi d azu da asubah a masallaci?& & Ki d auko mutane zan biya bashi na gaya miki zan mayar kafin ya karb a.
Ya yi maganar yana mai matse tafin hannunta wanda yake a cikin nasa..
Azaba sosai take karb a dan kamar zai karya mata hannun haka yake yi mata cike da mugunta, cikin dauriya ta ce  Allah wannan karon idan ya zo kai tsaye zan ce masa kai ne ka karb a ba zan sake rufa maka asiri ba..
Cikin tsananin b acin rai ya fincikota kuma ba kansa ba gefen taburmar ya zubar da ita sannan ya ce  idan kin fasa!! Ki tashi ki d auko min kud i na ce Ji ta yi kamar mutum a kansu dan haka ta d ago ta kalli direction d in aikuwa a take idanunta suka sark e a cikin nasa, da mugun k arfi gabanta ya yanke ya fad i karkarwar da jikinta ke yi ya k aru gashi babu damar wayancewa dan da gani ya dad e tsaye a wajen& .
Tana shirin yiwa Mallan Idi magana ko ta yi masa inkiya ta ji an fincikesa kamar wanda aka jaaa da mashin hakanan kafin k iftawar ido ta hangesu ya buga shi da bangon gabas ya shak esa yana huci!!!
Cikin mad aukakin tashin hankali ta k arasa garesu da gudu ta fara k ok arin b amb are hannunsa daga wuyansa amma ko gezau, tsabar bala i jikinsa har wani karkarwa yake yi yana huci gashi ya kafesa da idanunsa waenda suka rine da b acin rai.

Zuwa yanzu idanuwan mallan idi har sun fara k ak k afewa!!
So yake yi ya basa hak uri amma ya k i ma ya bashi damar yin hakan, ganin yana shirin aika sa lahira a take ya sanya ta daga hannuwanta duk biyu kawai ta rufesa da duka sai kuma ta fashe da kuka ganin ba ma dukan yake ji ba ta durk ushe a wajen tana cewa  ka rufawa kanka asiri so kake tsinuwar Allah ta tabbata a kanka ne???
Sautin kukan ta ne ya d an fara dawo da shi cikin haiyyacinsa, a hankali ya juya ya kalli yadda ta durkush e a wajen tana kuka, cikin wani irin rauni ya ce  ki daina kuka!
Ganin ta yi nasarar karkarto da hankalinsa ne ya sanya kawai ta mik e ta shige d aki still tana kukan, ba ta da tantama yanzu zai biyo ta& & &

Ko gama zama ba ta yi ba ya d aga labulen d akin ya shigo fuskarsa a hargitse, cikin rashin jin dad i ya k arasa inda take ya zauna ya kamo hannunta.
Fisgewa ta yi cikin kuka ta ce  tashi ka fita
Cikin rauni dan sam ba ya k aunar kukan nata ya ce  Mamaa
A fusace ta juyo tana kallonsa ta ce  me za ka ce min? Ma aruf ubanka ne fa shi!! Idan ba ka tsoron mutane zuciyarka ta k ek ashe ai ya kamata a ce kana jin tsoron mahallicin ka! Ka san me ake nufi da iyaye kuwa? So kake yi Allah ya yi fushi da kai ka sake tab arb arewa??? Kalli rayuwarka Ma aruf ko kishin kanka ba ka yi? Ba aiki ba sana a ba aure ba girma? Ko wannan fadanci da ake yi maka ganinsa ka ke yi a mazaunin girma? Ka yi karatunka ka je ka nemi aiki ko ka ci gaba da karatun ko ka kama sana a wannan rayuwar da ka zab awa kanka ba fa mai b illewa bace ba, mai ya sa su y an siyasar ba sa saka y ay ansu yin ta addancin sai kai?& .
Yadda ya runtse ido ya fara haki ne ya sanya ta fahimci ransa ya kai k ololuwar b aci, dan haka kawai sai ta kawar da kai ta k i ci gaba da cewa komai& & &
A hankali ya zame hannunsa da ke a cikin nata ya ce  dan Allah ki daina kuka
Daga haka ya mik e ya juya ya fice fuuu kamar zai tashi sama.

Inda ya bi ya fita ta juya ta bi da kallo zuciyarta sak e sak e kala kala& ba ta san wasu ba amma ita dai tunda ta ke ba ta tab a ganin mutum mai saurin fushi rik o da taurin zuciya da masifar taurin kai had e da zafin kai kamar d anta Ma aruf ba! A lokacin da ta haifesa bayan ta farfad o daga suman wucin gadin da ta yi ungozoma hud u ta tarar a kansa suna ta duba shi dan ya k i yin kuka sam! Ga dai idanunsa a bud e yana kallon jama a amma bai ce uffan ba, k arshe sai hak ura suka yi suka ce ta kaisa ya ga Likita& .
Sai da ya kai shekaru uku tukunna ta fahimci halayensa tsaff waenda suke matuk ar d aure mata kai wasu lokutan..
Tun haihuwarsa Mahaifinsa Mallan idi ya ke jinyar karaya, dan haka ita take fita ta je ta yi aikatau ta nemo musu abinci, barinsa da Ma a da take yi ne ya bashi damar cin zalin Yaron kamar ba shi ya haifesa ba dan har da molestation
yake had awa wanda sai da Ma a d in ya kai shekaru goma sha biyu tukunna ya gane cutarwa ne ake yi masa kuma abun bai dace ba..shi d in ya kasance Yaro mai tsananin so da yiwa Mahaifiyarsa biyayya to a duk lokacin da ta dawo gida ya tambayeta me ye hukuncin wanda ba ya yiwa iyayensa biyayya sai ta ce masa  d an wuta ne to top it all ya ga ita kanta da ya ke matuk ar so da girmamawa tana jin tsoron uban, ga uwar wahalar da yake gana masa idan ba ta nan waennan su suka taimaka wajen sake saka tsoronsa a cikin zuciyarsa. Tsoro azabtarwa da wahalhalun da Mallan idi yake basa ne suka bada gudummawa wajen jefasa a hali na damuwa sannan zuciyarsa ta tab u.
Bak in Hali da miskilancinsa da ba sa barinsa ma ya shiga cikin Yara ya sanya bai fahimci komai ba sai da Mahaifiyar sa ta harhad a kud i da kyar ta saka shi a makaranta lokacin shekarunsa goma sha biyu& & .
Musu suke yi shi da wani Yaro Antynsu ta ji shi Ma a ya ce  ko menene idan iyaye suka ce a yi dole a yi shi kuma Yaron ya ce masa  ban da sab on Allah.
Dan haka ta kirasu ta faiyyace masa komai ta yi masa bayani dalla dalla. Ko da ya je islamiyya nan ma same thing Malamin su ya gaya masa dan haka kawai ya samu Mama da maganar kai tsaye.
Da farko ba ta yarda ba sai da ta d ana tarko ta kama Mallan Idi da kanta tukunna.
Ita sam maganar wanki da ragowar wahalhalun ba su dame ta ba kamar molestation& Yanke jiki ta yi ta fad i sai a asibiti ta tsinci kanta. Ko da ta farfad o a take ta ce ba aure! Shi kuma ya ce bata isa ba
Ganin y an unguwa suna shirin maida su su zauna ne ya sanya ta tatttara kayanta suka gudu ita da Ma a.
Sai bayan shekaru goma sha d aya tukunna da kyar aka gano inda suke, ya tattaro mutane har da k aryar ciwo ya na kuka aka lallab a ta koma ba dan ranta yana so ba sai dan ba yadda ta iya dan har zuwa wannan lokacin ya ce shi fa bai saketa ba.
Ko da suka dawo ita kanta Mama sai da ta yi mamakin yadda kwata kwata Ma a bai nemi d aukar fansa ba gashi a lokacin ya zama rik ekk en d an daba& sai da aka yi watanni tukunna ta fahimci ashe petir yake bashi kullum cokali biyu kuma ya hanashi fad a, a cewarsa sai ya kashe sa silently kamar yadda ya yi masa& Allah ya taimaki Malan idi idan Ma a d in ya fita yana bi ya surka ta yadda ba za a gane ba kuma ya na gama bashi idan ya fita yake bi ya sha magani da madara.
& Bayan rabuwar su da Mallan idi shekaru goma sha d aya da suka wuce Ma a ya ci gaba da karatunsa, a lokacin da suka dawo garesa Ma a d in yana final year a university (daga wannan lokacin zuwa yanzun kuma shekaru tara kenan). Tun shekaru biyu da suka wuce (lokacin yana level 2) ya zama rik ekk en d an daba a ta sanadiyyyar goyon baya da ya samu d ari bisa d ari daga wajen wasu manyan k asa dama chan al adarsa kenan amma sai Mama ta tsawatar masa, kuma a halin da ake ciki a wannan lokacin ma ba ta gama sanin me da me yake yi ba dan b oye mata yake yi.


Lokacin da Mama ta fahimci abinda Ma a yake yiwa Mahaifinsa ba k aramin tashin hankali ta shiga ba! Gashi da ya ga ta fahimta d in kawai sai ya fito ya ce mata shi kashe sa ma kawai zai yi a wannan gab ar kowa ya huta dan ko sunansa ba ya son ji.
Da kyar ta lallab asa ya yarda ba zai yiwa Mallan idi komai ba amma da sharad in itama ba zata sake takura masa ba za ta barshi ya yi abinda yake so. Ita sam ba ta san b arnar da yake yi a doron k asa ba shiyasa ta amince masa aka tafi a haka amma dukda haka ya ce ko kallonsa idan mallan idi ya sake yi sai ya tsole masa ido! Kowa kawai ya yi harkar gabansa babu ruwan kowa da kowa.

A ta sanadiyyar abubuwan da aka dinga yi masa tun yana Yaro ne ya sanya zuciyarsa ta d an tab u.

Lokacin da Mama ta fara fahimtar wasu daga cikin abubuwan da Ma a d in yake yi sai da ta kwanta jinya, da tace kuma babu shi babu ita shi sai ya kwantar jinyar gaba d aya komai ya damalmale ya rinchab e! Da kyar aka samu ya d an dawo dai dai, ba dan tana so ba kuma ta san addu a ta fi k arfin komai ta zuba masa ido take yi masa addu a ba dare ba rana& & ..

Shigowar Mallan idi cikin d akin yana d ingishi ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta lula.
Bai ko kalleta ba ya k arasa jikin gadon d akin ya bud e side drawer ya d auko man zafi ya shiga shafawa k afafuwansa dan bayan shigowar Mama d akin Ma a take masa k afar ya yi da masifar k arfi tukunna ya yi wulli da shi ya bi bayanta.

Har ya gama babu wanda ya cewa wani uffan, haka nan ya mik e ya fice ba tare da ya ce mata ci kanki ba.

Yana fita Mama ta sauk e ajiyar zuciya ta d aga hannuwanta sama ta ce  ya Allah ka shirya mini Yarona .
Yara Yara da suka taso tare da Ma a a layin yanzu haka duk sun yi aure har da mai y ay a biyu, amma shi yana nan tare da y an iska! Idan an kashe wasu ya sake kwaso wasu ita ta rasa ta yaya ma suke yarda su biye masa& ..
**
Daga Inna har Dije har ma da mutanen gidan gaba d aya babu wanda bai yi mamakin yadda Asabe ba ta yi magana akan mutuwar akuyarta ba bayan ta tabbata kisan gilla ne tunda ga salatip a hanci da Baki& ..Ko da ta dawo ta tarar da akuyar a haka bayan ta shiga d aki ta d an jima kuma sai ta fito ta kira Minu kawai ta ce masa ya d auki mushen ya fitar ya san yadda zai yi da shi.

Ajiyar zuciya kawai Inna ta sauk e dan ta san tabbas akwai wata a k asa.

BULAMA
'?
0806 402 1951
ANA MALIK!!
Book 01.
Page 05.

Humairah Bulama.
Mikiya writers Association.

& BAYAN KWANA D AYA&
Kasancewar yau litinin akwai makaranta ya sanya kowa ya tashi da wuri, iyaye mata suna kitchen suna had a abin karin kumallo yayinda y an mata-matan da Yaran gidan suke ta shirin yin wanka.
Jiya kwana aka yi ana tsula ruwa dan haka garin yau sai aka tashi da wani irin sanyi mai ratsa har cikin k ashi..kaff gidan yau Dije ta rigasu tashi dan tun kafin ta yi sallar asuba ta d aura ruwan wanka a murhu da na shayi a d an k aramin rushon gawayinsu.
Sai da ya

6 / 33