ANA MALIK HAUSA NOVELS BY HUMAYRA BULAMA .doc

Author :  Humaira Bulama Category :  Top Hausa Novels 2025

Chapter   25 / 33

72K to 75K   out of 98.8K words

tafiyar wata hud u ne , da zummar ko a ranar idan ta sami kud i zata bawa matar ta ce mata  ta tashi ga mai d aki tana zuwa , to amma yanzu kam ta chanja shawara dan wallahi tunda Inna ta nuna bata son matar to dole sai ta zauna a gidan har zuwa lokacin da zata gaji ta tafi dan kanta.
Ya zama dole ta nunawa Innaa bata fa da wata fada a gidan Mallan, sune da gida!.

Dije tana jin duk wani abunda yake faruwa amma
ta gagara tashi ma ballantana ta fito sakamokon wani irin rikitaccen tsoro da fargaba da suka lullub eta tun asubah yanzu kuwa suka nunku ko motsi ma ta kasa yi, sai rawar sanyin da ta soma yi daga fitar Inna zuwa yanzu zazzab i-zazzab i yana shirin lullub eta.
A kumbure Inna ta dawo cikin d akin tana ta kwafa. Sai da ta zauna tukunna idanuwanta suka sauk a a kan Dije. K ura mata ido ta yi sai kuma ta k arasa gareta sannan ta ce  lafiyanki kuwa?
Dama tun d azu ta lura da yanayinta musaman ma da Ya Kamal d in ya yi musu sallama kafin ya wuce masallaci dan daga chan kawai ya wuce Minna d in& ..
Wani murmushi Inna ta d anyi duk da kuwa Itanma a tsorace ta ke amma sai ta yi k ok arin aro jarumta ta shiga kwantarwa da Dijen hankali& ..

Sai da Inna ta tabbata Dije ta d an nutsu tukunna ta ce mata ta je ta ta gaida Iyya.
Da  to kawai ta amsa mata ta tashi ta saka hijabinta ta fice zuwa d akin Iyya.
Dai-dai wannan matar sabuwar zuwa ta fito da wasu kwalaye a hannunta alamun kimtsa d akin nata take yi.
Cike da shishshigi ta ce  A a y an mata kema a nan d in kike? Zuwa anjima dai duk zan lellek a mu gaggaisa a san juna a sassaba.
 Eh kawai Dije ta ce mata daga nan ta shige d akin Iyya tana mai jin haushin matar ganin yadda ta k ura mata idanu kamar wata mayya.

Cike da kulawa Iyya ta amsa gaisuwar tata tana ta janta a jiki a nan ma ta yi breakfast sannan ta fito& dan dagewa Iyyan ta yi ta ce  sai ta ci in kuma ta k i to zata d ura mata ne, ita da ya kamata su sake sabawa amma sai kuma ta fara ja baya da ita, gara ma ta sake dan sam ba zata lamunta ba.
Sai da ta ga ta sake da ita sun yi hira tukunna ta yarda ta barta ta fita& da kallo ta bita har ta fice fuskarta d auke da murmushi, tana fita wayarta ta d auki k ara dan haka ta mik e ta k arasa ta amsa kiran da sallama& .


Tana shiga d akin nasu ta tarar da Inna ta aika Umar ya je ya siyo musu y ar tsala ta naira d ari amma halin Inna na kyauta har Umar d in sai da ta ajjiye ta bashi yake zaune yana ci ga na Dije itama ta ajjiye mata amma ita bata ajjiyewa kanta ba, dama saboda Dijen ne ma ta siyo dan ta san tana da ulcer.
Murmushi kawai Dijen ta yi ta nemi waje ta zauna. Tana zama Inna ta ce  ga abincinki nan, ki d auka ki karya, mu ga kuma mai anjima za ta bayar.
A hankali ta ce mata  na ci abinci fa a wajen Iyya.
Kama Baki Innaa ta yi kawai ta tsaya tana kallonta, wanda yadda ta yi d in ya sanya Dije yin dariya ta ce  Wallahi babu yadda ban yi da ita ba amma ta ce sai na ci, k arshe ma cewa ta yi in ban ci ba sai ta d ura min wai ya kamar ban d auketa uwa ba.
Numfashi Inna ta fesar ta ce  Allah ya saka
Daga nan ta yi shiruu ta shiga tunanin& .
Ganin tunani da k unci yana shirin maye gurbin y ar rahar da suka samu kansu a ciki yanzun ne ya sanya Dije ta mik e ta je ta zauna a kusa da ita ta d auki y ar tsalar ta gutsira ta kai bakinta, murmushi Inna ta yi ta bud e bakin ta saka mata a ciki ta shiga taunawa a
hankali sai da ta had iye tukunna ta ce  yanzu idan kika tafi waye zai dinga bani abincin irin haka?
Kamar wadda ta ke jira tashi d aya hawaye suka b alle mata sai kuma ta tafi jikin Innar ta fad a ta fashe da wani irin kuka.
Hatta Umar wanda ke a d akin sai da kwalla ta zubo masa dan shima ya san idan Dijen ta tafi zai yi missing d inta.
Suna a haka Minu ya shigo cikin d akin bakinsa d auke da sallama. Da farko ya yi tunanin wani abun ne ya faru dan haka ya k arasa da sauri yana mai tambayarsu  mai ya faru?
Sai kuma ya fahimci dalilin kukan nasu dan haka shima a take duk sai jikinsa ya yi sanyi.

A hankali ya nemi guri ya zauna a gefenta, ya zamana shi da Inna sun sakata a tsakiya tukunna ya shiga lallashinta shima zuciyarsa ba dad i.
Sai da ta d an yi shiru tukunna ya kalli Umar wanda fuskarsa ta yi dagaje-dagaje da hawaye ya yafito sa. Sai da ya zo ya goge masa hawayen tukunna ya zaro d ari uku a aljihunsa ya basa ya ce  ya je ya siyo musu bredi su karya , da sauri Inna ta ce  ai mu mun ci abinci
Amma still Minu ya ce  eh ya siyo ni zan ci in ya so sai ku ajjiye na san zai yi amfani.
Shiruu d akin ya kasance bayan fitar Umar kowa da abunda yake tunani a ransa, kafin chaan Inna ta ce  Ba a yi muku abin karin bane?
Numfashi ya fesar sannan ya ce, ta yi masa fanke da kunu, yana cikin napep d in Ya Musa ya shiga wanka ne yana fitowa za mu wuce.
Sai kuma ya yi wani murmushin takaici kafin ya ce  ni, ta ce idan na ci Allah ya Isa bata yafe ba, wai d anta kad ai ta yi mawa. Shiyasa na ke so in karya a nan dan na san Baba dole zai d ura min kuma maybe ya ce in rantse akan na karya idan na ce masa na k oshi.

Shiruuu duk suka yi chaan Inna ta ce  Allah ya kyauta.

A hankali Minu ya zaro kud i dubu uku had e da dubu biyar itama an had eta waje d aya ya dunk ule ya ce  gashi shi ya ma manta bai had e kud in ba a yadda aka bashi a rabe a haka ya bata duka dan ya yi alk awarin ba zai bawa Kaka ba.
Hannu Inna ta saka ta karb a a lokaci guda tana kallonsa ta ce  daga ina?
Bai kalleta ba dan ya san zata fahimci wani abun ya ce  Mallan ne ya ce a kawo muku, jiya wani Abokinsa ya zo ya duba shi shine ya bashi duba ashirin, mun kammala biyan komai ragowar kuma ya ce in kawo miki.

Warwarewa ta yi ta shiga dubawa, dama tunda ya k i kallonta ta san akwai abunda yake b oyewa. Dan haka tana gama dubawa ta kallesa ta ce  Ungo kaiwa Kaka nata
Juyowa ya yi da niyyar yin
musu ya ga ta had e rai tamau!
Cikin b acin rai ta sake mik a masa ta ce  Ungo na ce!
Ba dan ransa yana so ba ya karb a ya mik e ya fita.

Daga nan cikin d akin, su Inna suna jin yadda Minu yake ta rafka sallama amma an k i a kulashi sai chaaan! Su har ma sun cire ran zata fito sai gata ta fito tana cewa  Halima tana bi na bashi ne da zaka zo ka isheni da sallama? Sannan har yanzu baku gama munafurcin da ka shige d akin kuke yi kai da uwartaka da k anwar taka ba ka wuce ka kai abincin ba?? .

K udin hannunsa kawai ya mik a mata dan a k ule yake da ita matuk a idan ya ce zai bud e Baki ya kulata tabbas ba zata yi kyau ba.

 Bebe ka zama ne? Ba zaka bud e Baki ka yi min bayani ba dan uwarka!

 Mallan ne ya ce a baki
Haka kawai ya ce da ita kansa a gefe dan ko kallonta bai ya son yi.

K uraa masa ido ta yi ranta na gama b aci zuciyarta ta shiga tafarfasa kafin chaan ta ce  sai da kuka gama k us-k us tukunna za a wani kawo min kud i?
To ku je ku rik e ku ne matsiyata wallahi! Sannan ka cewa uwartaka na ce dan ubanta ta yi kad an d ana ya bata kud i ya ce ta bani idan zai bani abu sai dai hannu da hannu ita ba ta Isa ko da sani ne ta yi ba! Dan haka koma wanne k ullin kuke shirin k ullawa ya tsaya a iyaka kanku& .ka koma mata da tsiyarta ta had a ta rik e chaan itace talaka. Kuma wallahi ta sake gwada min wannan shirmen sai na bata mamaki.

Shiruuu suka yi kowa ya kasa cewa komai, a haka Minu ya shigo a zuciye ya same su kamar zai fashe.
Ba wanda ya kulashi ya k arachi masifar sa shi kad ai ya juya ya fita kamar zai tashi sama, bayan ya bawa Inna kud in ta k i karb a itama
ta ce  ya kaiwa Mallan d in in yaso sai ya bawa Kakar da hannusa kamar yadda ta ce.

Yana fita Inna ko bi ta kansu bata sake yi ba ta kamo
hannun Dije ta shiga yi mata nasiha& &

Sosai ta nutsu tana sauraron Innar kamar daga sama suka ji salatin Maman Fati.
A hargitse duk suka firfito, a take gabansu ya yanke ya fad i a tare rassss!!! Sakamokon ganin k ofar d akin Iyya da suka yi cike taf da jama ar gidan anata lek awa ciki ga waya kare a kunnen Maman Fati tana cewa  ga dai number nan da ta kirata last ta shiga, bari mu ji mai ya faru haka ya firgitata har ya kai ta ga suma Allah dai ya rufa asiri, ya sa ba wani abun ne ya samu Kamal d in ba.
Dai-dai nan su Gwaggo suka fito da Iyya wadda take a sume suka shimfid eta a tsakar gida (kan tabarma) suka shiga yi mata taimakon al ada na gaggawa.

Dishi-dishi Dije ta fara gani k afafuwanta suka shiga karkarwa sosai dan kana ganinta zaka shaida hakan.
 Ameen wa alaikassalam, bawan Allah ka kira wannan number mun zo mun samu mai wayar da wayar a hannunta a sume, lafiya dai ko?
Muryar Maman Fati wadda Dije take iya jiyota a chaaaan nesa sama-sama ta karad e gidan.
Salatin da ta saka ta fashe da kuka ne ya sanarwa kowa halinda ake ciki! Daga nan ita dai Dije duhu ne ya maye gurbin ganinta kunnuwanta suka yi wani irin dummmm! Ta tafi ta sulale ta fad i a wajen sumammiya.

BULAMA
'?
0806 402 1951
ANA MALIK!!
Book 01.
Page 23.

Humairah Bulama.
Mikiya writers Association.


Rabon da hawaye su zubo daga cikin idanuwansa har ya manta!&
Sosai kansa yake wani irin sarawa zuciyarsa tana bugawa da k arfi da k arfi yana jin tashin hankalin da bai tab a tsintar kansa a ciki ba& .Bak in ciki danasani da kuma tashin hankalin da yake ciki a yanzun sune suka taru suka bayarda gudummawa har hawaye suka samu damar zubowa daga cikin idanuwansa.

A hankali wani Abokin huld ar tasu  Tiger ya ce  Dama na dad e ina gaya maka mutanen nan duk bakinsu d aya siyasa ce kawai ta sanya suke rainawa mutane hankali.
Kai kuma da ka fahimta, ka je ka gansu ka kuma ji abubuwan da suke tattaunawa Ma aruf kamata ya yi ka bar gurin ka zo a san abun yi ba wai ka tsaya biyesu ba! Yanzu wa gari ya waya? .

Da wani irin masifar k arfi ya runtse idanuwansa jijiyoyin kansa suka sake baiyyana fiye da daa, bai tab a tunanin akwai abunda zai tab a d aure masa kai irin wannan ba!
Adadin y an daba kai har ma da mutane waenda suke a k ark ashinsu da suka rasa rayukansu a ta sanadiyyar rashin jituwarsu baza su k irgu ba! Amma wai it turns out to be ashe su d in best friends ne saboda siyasar su ne ya sanya suke pretending suke yin hakan, sannan dan ya nuna musu b acin ransa har suna da guts d in da zasu hana shi Mahaifiyarsa wadda ko motsi bata iya yi bama ta san waye a kanta ba!
Tabbas yau za a mutu! Dan muddin ya gama tabbatarwa Maama bata cikin gidan nan wallahi sai ya fasa gas a ciki uban kowa ya mutu!.

Cikin b acin rai Scorpion ya ce  ai kuwa sun janyowa kansu bala i dan yaudarar mu da suka yi da abunda suka yi na b oye Mama da kuma kisan da suka saka aka yiwa Oscar wallahi wallahi ba zai tab a tafiya a banza, sai na lahira ya fi su jin dad i
A d an fusace Tiger ya ce  Au inda ka sha da kyar nan zaka koma gaba gadi? Scorpion sojoji ne suke gadin mutanen nan masu amfani da harsashi waenda kafin ka k arasa sun d aukeka da bindiga kamar yadda suka yiwa Oscar, ka tsaya ka nutsu.
Mu rabu da su for now mu san abun yi tukunna.
Sannan batun gawar Oscar inaga gara kawai mu bar musu, suma ai musulmai ne na tabbata baza su tab a barinsa a haka ba duk tsiya za su saka a yi masa sutura a binnesa& .
Cikin tarar numfashinsa Scorpion ya ce  Baka gama fahimtar su waye mutanen nan ba har yanzu kai kenan ko?
Girgiza masa kai ya yi ya juyo da shi sosai suka fuskanci juna ya kama kafad unsa ya ce  Scorpion Sarkin yawa ya fi sarkin k arfi sannan power is everything!!! Idan muka tunkare su yanzu mu ne a ruwa, sannan Mama fa tana hannunsu!
Sai kuma ya d an yi shiruu kafin ya ce  wai ta yaya ma aka yi kuka barta ita kad ai har suka samu damar chanja mata waje?.
Cikin runtse ido dan sosai bullet d in da ke mak ale a d antsen hannunsa yake dad a azabtar da shi, Scorpion d in ya ce  operation suka tura mu jiya tsakar dare, a chan ne ma muka ji komai ai, muna komawa kuma muka tarar da su tare muka ji conversation d insu, to I think da suka ga mun ji kuma ranmu ya b aci shine suka yi saurin ce mana sun turata England a cikin daren, which nake suspecting a tsakankanin lokacin ne suka tura aka chanja mata waje, dan muna fara nuna musu b acin ranmu Alaji ya tashi ya fita da waya kare a kunnansa& .to a wannan time d inne inaga suka chanja mata waje saboda su yi amfani da ita against us tunda sun san mun fahimci komai.
Ni dama tun shekaran jiya da Alaji ya ce mu dawo Kano gaba d ayanmu ta nan jirgin zai tashi jikina ya fara bani akwai munafurci da b oye-b oye a al amuransa.

Da k arfi Ma a ya damk i bedsheet d in gadon da yake a kai kansa yana wani irin juyawa tsabar bala in da yake a ciki, idan ya ci gaba da zama a haka tabbas bak in ciki zai iya kumbura masa zuciya ya mutu kafin ya yi abunda ya yi niyya, dan haka kawai ya juya ya bud e drawer da ke a gefen gadonsa ya shiga dube-dube.
Ba tare da ya kalli Scorpion ba ya ce  wuce ka tafi asibiti a rabaka da abun hannunka.
Clinic d in baya inda muke zuwa nan zaka je.
 Tam, Oga!
Scorpion ya ce da shi yana mai sara masa wata kwalla tana zubo masa dan ya san da tare za su yi masa hakan shi da Oscar, cike da alhini bak in ciki da b acin rai ya juya ya fice daga cikin d akin dai-dai Ma a ya gano abunda yake nema.
Wata rikitacciyar kwayar gari ce ya d auko. Ya kunna coal a kasko ya fara k ok arin zubawa a ciki, da sauri Tiger ya k arasa garesa ya rik e masa hannu ya ce  wai da wanne yaren kake so in yi maka bayani tukunna ka fahimce ni ne? Ka gaya mini ribar yin hakan idan ka yi, ka nutsu kar ka bari ka birkice na tabbata idan aka bincika watak ilan ma Mama tana chan England d in kamar yadda aka tsara, raina maka wayo kawai suke yi, ka tsaya ka nutsu mu san abun yi ba wai ka rikice mu rasa tudun dafawa ba.
K uraa masa idanuwa ya yi kafin chaan ya ce  Maama ba ta chan basu kaita ba na gaya maka, Tiger treatment zamu je ba batun wasan y ar tsana ba, ka gaya min ta yadda za su iya kammala duk wasu shirye-shirye su turata a cikin y an kwanakin da suka gabata ana shirin& .
Tabbas na tafka babban kuskure da na bar ragamar d awainiyar kula da ita a hannunsu, dana sani da nayi mata iyakar iyawata na barwa Allah komai.
On top of everything kuma jiya na sake barinta na tafi wani banzan operation!
Ya k arashe maganar yana mai kama kansa kamar mai shirin fasawa, wani abu mai zafi yana dakar k irjinsa, ji yake yi kamar ya kurma uban ihu! Bai ma san ta Ina ne zai fara ba gaba d

25 / 33