ANA MALIK HAUSA NOVELS BY HUMAYRA BULAMA .doc

Author :  Humaira Bulama Category :  Top Hausa Novels 2025

Chapter   7 / 33

18K to 21K   out of 98.8K words

kusan tafasa tukunna wuff Asabe ta shigo Mallan tsaye a bakin k ofar ta zo ta juye ruwan a wani babban flask wai za a
kaiwa Kaka tana buk ata da wurwuri gashi ita ta manta ba ta d aura ba, kuma fa da gangan ta k i d aurawar dan har ta zo za ta d aura sai ta ga Dije tana ta fama da itace dan haka ta mak ale ta saka a ranta Wallahi har na shayin duk nata zata juye, hakanan ta koma ta yi kwanciyarta sai bayan sallah gari har ya fara yin haske tukunna da Mallan ya fara yi mata maganar ta ce masa  shaf ta manta amma bara ta juye na Dije ta ga sun d aura da wuri watak ila ma Kakar suka d auramawa.
A gabansu ita da Inna ta zo ta juye, har Dijen za ta yi magana Inna ta yi mata wani kallo da ido dan Mallan yana tsaye a bakin k ofar shiyasa itama Asaben ta yi hakan, ba dan Dije ta so ba hakanan ta ja bakinta ta yi shiruu, amma fa ta shak a dan kana kallon fuskarta za ka ganta a kumbure, tun daga nan ta hau cika tana batsewa& .


Ya Muhammad yana so zai fita da sassafe yau d in dan haka dolenta ta hak ura ta bari sai da nashi ya tafasa na Mallan ma ya tafasa (dan Asabe ce ta tafi kai ruwan) aka kai masa dan yau Inna ce da girki tukunna nata shima ya yi ta juye, lokacin har su Rakiya sun zo an d aura musu a murhunsu ya yi zafi sun d auka suma sun wuce, su da sai wajen k arfe bakwai ma tukunna suka tashi ko iyayensu basu taya abun kari ba gashi har suna shirin rigata shiryawa kuma ta san muddin ta barsu suka shiga to sai sun b ata mata lokaci da gangan, dan haka ta shiga sassarfa tana k ok arin d aukar ruwan a ranta tana aiyyana wallahi ba zata barsu su rigata shiga band akin ba.
Garin kiciniyar d aukar bokitin da take yi a hargitse ya sanya ta kelayar da rabi dan haka Inna ta daka mata tsawa  ki
nutsu mana!! Rawar kan na uban meye ne kike yi?
A hankali ta sunkuyar da kanta k asa, sai da Inna ta k araci mitar ta ta gama tukunna ta d auki bokitin ta wuce dan ta san a k a ida idan Inna tana magana ba a tafiya a bar mata wajen dole a jira ta gama tukunna a wuce.

Tana dosar band akin ta hangi Kubra har ta shige kafin ta yi wani yunk urin har ta cire hijabinta ta yi labule da shi ta hau wanka a gaggauce, saurin da ta ji tana yi ne ya sanya ta d aga mata k afa ta barta ai kuwa ko cikakken mintuna uku ba ta yi ba ta fito gefen fuskarta har da kumfa, Rakiya da Mariya suna ta yi mata dariya itama tana dariya ta zo ta wuce da sauri dan Sagir ya ce idan ta dad e zai yi wucewarsa kawai.
Tana wucewa Dije ta ga Rakiya tana shirin shiga dan haka ta kamo hannunta ta mayar da ita baya ta zabga mata harara tukunna ta wuce ita za ta shiga.
Kamar had in Baki saboda dama duk su biyun haushinta suke ji suka saka hannu (Rakiya da Mariya) suka fincikota ta dawo da baya da baya kamar zata fad i Mariya ta ce  wallahi ba ki isa ba! Hatta Zainab ta riga ki ga ruwanta chan.
K ura mata ido kawai Dije ta yi tana kallonta da b acin rai, ba ta yi auni ba kawai ta ga Rakiya ta afka cikin bayin ta cire Hijabinta ta yi makari da shi zanin jikinta shima ta cire ta yafo shi ta fara facal facal da ruwa.
Zuciya da ta d ebi Dije ba ta san lokacin da ta yaye labulen ba ta jefar a k asa ta saka hannuwanta duk biyu ta wantsalota waje daga ita sai hular kanta ba!
Allah ya sa daga ita sai Rakiya sai Zainab wadda ta k araso wajen yanzu ne a gurin amma fa k ofar d akin mazan gidan a d an bud e take dan haka a tare duk su ukun suka saki ihu Rakiyar ta yi saurin d urkushewa a wajen ta fashe da kuka, da mugun sauri Mariya ta ware zaninta ta yafa mata ita ta tsaya daga ita sai hijabin jikinta.
Wani abun mamakin liver irin ta Dije ko kallonsu ba ta yi ba ta wuce ciki ta kwab e ta yi wankan ta, kuma suka gagara fiddo ta, sai da ta gama ta fito ne tukunna suka ce ba zata wuce ba sai sun yi k asa k asa da ita a cikin chab in k ofar band akin, suka kamata suka fara kokawa har da Fati wadda k arasowarta wajen kenan labari ya isketa dan haka itama ta shiga fad an.
Allah ya taimaketa ba su kai ga kaita k asa ba su Ramma da Iyya suka k araso wajen.
Iyya ce ta raba fad an da kyar! Dan hatta su Ramma kasawa suka yi saboda su Rakiya sun zuciya yau d in da halin Dije duk shakkarta da suke yi sai da suka ajjiye tsoro a gefe suka gwabza da ita.

Ko breakfast ba ta tsaya yi ba ta shirya tsaf ta fito tana ta sauri dan suna da punishment d in da aka basu za su k arasa yau ita da Sumayya, wanda laifinta ne ita kad ai amma aka had a da Sumayyar ta shigar mata suke yi tare. Gashi ta san sai ta biya mata, Sumayya kuwa da nawa watak il zuwa yanzu ko wanka ba ta yi ba dole ta je ta azalzaleta su je su gama da wuri, dan ta na son samun lesson d in Literature d in da za a yi musu yau da safe, da ita za su fara waec gashi ba ta san uwar komai a ciki ba.

Allah kuwa ya taimaketa dan tana fita ta hangota itama ta tunkaro gidan nasu& .
Duk da an shiga an fita sai da y an ajin suka sanya aka raba mata aji da Sumayya tun suna aji hud u amma har yau k awancen su yana nan kullum kuma tare suke zuwa makaranta su dawo tare boko da islamiyya. Sannan kusan ko da yaushe ma ne suna tare d in dan tunda suka shiga ss3 yawancin periods d in nasu had e su ake yi a yi musu lessons d in tare dan haka kusan duk periods d in suna tare. Kowa yana mamakin wannan k awancen nasu dan sam halinsu bai zo d aya ba. Ita Sumayya sanyi ne da ita sosai sab anin Dije da ba a isa a saka mata hannu a yatsa ba ta ciza ba.
A b angaren Dije kuwa amana da gaskiya da rashin munafurcin Sumayyar ne ya sanya ta rik eta k awance dan sam Dije ba ta k aunar munafurci gashi ba ta iya ba shiyasa kwata kwata ba ta shiri da su Rakiya dan Rakiya Fati Kubra da Mariya gaba d ayansu munafukai ne na bugawa a jarida. A hakan wai k awaye ne duk su hud un amma kowa munafurcin kowa take yi a tsakanin su, wani zubin idan fad a ya had osu aka fara bankad e bankad e sai ka ji halin nasu kamar na y ay an shed an& ..


Suna shiga cikin makarantar suka wuce band akin direct suka fara aikinsu Dije tana aiyyana yadda za ta ci uwar Zainab dan itace musabbabin wannan aikin k azantar da take yi, fad a ne aka yi da ita ta yi mata shegen duka shine aka ce har da Sumayya aka had a aka basu punishment dan malaman cewa suka yi
dukan da aka yiwa Zainab d in ya fi k arfin ace mutum d aya Yarinya budurwa ce ta aikata shi& .ita Zainab tunda ita aka daka sai aka bata na kwana hud u su kuwa na sati d aya aka basu yau za su gama.
Kad an ya rage ba a basu suspension ba ma dan irin haka mostly a ajin Yara a ka fi samu ba wai su god ai god ai
da su ba.

A gajiye suka koma ajin, kasancewar sun san lesson d in malamin Hausa mai himmar zuwa ya wuce Sumayya dan da sassafe yake yiwa y an A (ajin su Sumayya) B kuma (ajin su Dije) sai an kusan tashi, shiyasa kawai suka wuce ajinsu Dije inda ake musu lesson d in literature a daidai wannan awar& . har sun danno kai Dije ta jaa hannun Sumayya suka tsaya ba su shiga ba sakamokon jiyo muryar Rakiya da ta yi kamar tana munafurcin y an gidansu, ai kuwa tsayuwarsu ke da wuya ta ji Mariya ta ce  yo ai ke kike wannan maganar ita ma Ina ga idan aka bibiya fa mahaukaciyar ce irin d an uwan nata. Zigidir fa ta janyota ta fito da ita daga band aki ai wallahi yau ba dan an rabamu ba da sai na nuna mata nima ban girma ba na iya haukar Yarintar har yanzu tana kaina ba ta barni ba.
Dariya y an matan kusan su goma suka saka& ..da yake Malamin literature d in bai zo ba shiyasa suka had a daba a nan cikin ajin suka hau sana ar ta su ta munafurci.
Cike da dariyar mugunta wata a cikin y an matan ta ce  Ai na ci dariya da aka ce ya biyo matarsa har waje da wuk a Astaghfirullah, shegiyar Yarinya babu yadda ba a yi da ita ba akan kar ta auresa mahaukaci ne amma ta k i, sai da ta fara jiyo k amshin lahira tukunna ta farga. Ta shafawa kanta lafiya, gashi yanzu, ran Asabar d innan za a d aura mata aure da mai hankali abinta.
A hankali wata a cikinsu ta ce  ni wallahi tausayi yake bani& 
Cikin katseta Rakiya ta ce  kee!!! Waennan ba abun tausayi bane ba! Ba su san Annabi ya faku ba duk cikinsu Malan ne kawai na kwarai amma tun daga kan Innar tasu har zuwa kan Dijen ba na Allah bane ba, shi kansa mahaukacin ba na Allah bane ba.

 Na ubanki ne???
Muryarta tsaye a kansu ta sauk a garesu.

A take wasu a cikinsu suka rud e yayinda su Rakiya suka yi tsaki, suka ci gaba da hirarsu& & &
Ajijn nasu seat guda hud u ne amma mai cin mutane da yawa dan dogaye ne sosai, kuma biyu sun karye (d ayan babu k afafuwa biyu d ayan shima haka) d ayan kuma nata ne ita da Sumayya da wasu a cikin y an ajin dan haka ba a zama a kai, sai d ayan mai lafiyar shima na wata Yarinya ne maggi irin k edaran nan k atuwa masu shegen k arfi da masifa, daga Dije sai ita a masifa a kaff ajin nasu.
Cikin ikon Allah su Rakiya gaba d ayansu a kan karyayyen seat marar k afa biyu guda d aya dogo suka had a wannan dabar ta su, katako kawai suka nemo suka saka a chan k arshe da kuma tsakiya inda babu k afafun. Ta riga ta san kan seat d in shiyasa tashi d aya ta saka k afa ta ingije malejin nasu ai kuwa suka taho luuuuu kamar irin sun hau super d innan suka zube a simintin k asan ajin.
A zuciye suka taso Allah ya taimaka wani malaminsu wanda ya ji hayaniya ya zo wucewa ya shigo cikin ajin, shi ya raba damben da ya ke shirin kunnuwa dan duk yawansu d innan ko d arr Dije ba ta ji ba haka ta ke shirin shiga a dambatu Sumayya na rik eta ta na fisgewa.
A duniya Dije tana son d an uwanta Ya Muhammad kuma tana tsananin jin tausayinsa gashi kusan kullum idan ciwonsa ya tashi to ko ita ko Inna ne sila, shiyasa take dad a jin ciwo idan jahilai suka goranta masa, sannan shiyasa take bin maganarsa take kuma kare duk wani abun da zai b ata masa rai.

Wani punishment d in aka fitar da su aka sake basu, tare da bulala ashirin ashirin a dukka su goma sha hud un har da Sumayya sannan aka saka su kneel down a rana har aka tashi.
A tunanin Dije idan aka tashi za su tunkareta ko su tare mata hanya dan haka ta shirya musu tsaff, sai dai su y an matan ko kallonta ba su yi ba kowa ya kama gabansa saboda sun san dambe a hanya ba nasu bane ba dad in dad awa kuma duk akwai samarinsu a Unguwar dan haka sun san sun girma sab anin ita da kwata kwata kamar ma ba ta san me ake nufi da girma da y an matancin ba tsabar yadda ta saka fad ace fad ace da dambe a gabanta.
Sosai ta had iye takaici kuwa dan ta shirya yadda zata d ebo k asa ta tada k ura ta ci ubansu tunda ta san sun fi ta yawa.
Da kyar Sumayya ta d an shawo kanta ta saki jiki takaicin su Rakiya ya fita daga kanta da kyar, a haka ta share lamarinsu suka d an tab a hira kafin su k araso k ofar gidan su Sumayya Dijen tana ta nanata mata sak onta da take so ta taho mata da shi daga k auyensu d in da za su je gobe gaisuwa ba za kuma su dawo ba sai sun yi kwanaki hud u.

Ita dai Sumayya a tsorace ta ke da wannan sak o na Dije amma sanin da ta yi cewa idan ba ta kawo ba tsaf za su iya samun matsala ya sanya ta amsa mata da  to suka yi sallama suka rabu bayan ta yi mata Allah ya kiyaye hanya, dan ba lalle su sake had uwa ba Sumayyan ta ce  kasuwa za su je yau ba za ta je islamiyya ba dama tun jiya ta d auki excuse na tsawon kwanakin da za su yi, gobe kuma fitar asuba za su yi.

& BAYAN KWANAKI HUD U&
Asabar.
Sai da Kaka ta yi kwana biyar a asibiti tukunna aka sallameta. Ba dan Likitocin sun so ko dan ta warke ba sai dan shegiyar tsirfa da iyayin da take yi
musu kamar wata consultant, gashi ta kawo wani daga Getso shi ya gyara mata ma hannun har da cewa wai
su zo su koya daga wajensa shi d in tshohon hannu ne, idan aka bata magani bata sha sai
tsumin wannan mutumin kawai take sha sannan ba ta yarda da drip ba! Ganin ta cike musu waje ya sanya kawai suka ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????sallameta suka ce ta je gida ta k arasa jinyar a chan, ba damuwa.
Minu kusan shi ne ya yi jinyarta shi da Asabe dan shi yake d aukarta ya kaita bayi idan za ta yi uzuri a cewarta wai bata iya tashi ba zata iya yin tafiya ba sai ka ce a k afa ne ta samu gocewar k ashin.
Sannan duk wani aike shi ne kuma da kud in sa yake yin na motaa amma hakan bai hana Kaka aibanta Inna da Dije tare da zaginsu su a gaban kowa ba. Tun yana jin haushi yana ji kamar ya mayar mata har ya zo ya rabu da ita dan tabbas zuwa yanzu ya fara yiwa Kaka kallon kwarkwar.
Inna ta je sau d aya washegarin ranar da sassafe ta tafi da abincin kari amma sai da Mallan ya rabata da su da kyar ya maidota gida Kaka har da kukanta wai  Halima ta rainata kuma ta mallake mata d a Bayan ita ce ta fara zaginta tana shiga ko zama bata bari ta yi ba ta hau zaginta ta uwa ta uba sannan ta dinga yiwa Dije baki da fatan karuwanci, ita kuma Inna ta ce  In sha Allah Dije alkhairi kawai za ta gani sannan idan ta sake zaginta wallahi sai ta rama tunda ba ta san ta girma ba ..Asabe ta sa baki Inna ta buge bakin shiyasa da Mallan ya ga dambe yana shirin kwacewa ya yi sauri ya fitar da Haliman ya maidata gida, kuma shima ya yi mata tatas ya ce  ko da wasa idan ta sake mayarwa da Kaka magana wallahi sai ranta ya b aci ko me kuwa Kakar ta yi mata. Shiyasa tun daga ranar Inna ba ta sake komawa ba kuma ta d auki fushi da Mallan d in a ganinta ya yi son kai sun had e mata kai.

Yau tun safe Dije take cikin farin cikin da Inna ta kasa fahimtar na menene, suna kitchen su biyu suna jefa d anwake tare suna d an tab a hira Sumayya ta yi sallama wanda sai da sallamar tata ta sanya Dije ta kusa kifar da tukunyar d an waken garin mik ewar da ta yi ta a zabure cike da gand oki.

Tsayawa kawai Inna ta yi ta zuba mata ido wanda hakan ya sa ta d an sha jinin jikinta.
Ta d an jima tana kallonta kafin ta d auke ido kawai ba tare da ta ce mata komai ba. Ta gane me Innar take nufi shiyasa ta gyara jikinta ta sake nutsuwa tukuna ta nufi hanyar fita dan har Sumayyan ta k araso tana k ok arin sako kai.
Gaisawa suka yi da Inna tukunna Dije ta sa hannu ta jata tana mai cewa  Inna bara mu je d aki.
Jinjina kai kawai Inna ta yi ta ci gaba da jifan d anwaken ta.

Sai da ta fito tukunna ta d auki ruwa a buta ta d an wanke hannunta tukunna suka wuce ciki.
Suna shiga Dije ta ce  Bani da sauri in b oye tukunna sai mu gaisa
Ta yi maganar jikinta har wani rawa yake yi.

Dariya Sumayya ta yi ta ce  ai ban samu ba

 Bar batun wasa mana.
Dije ta ce cikin zak uwa.

Dariya Sumayya ta yi ta fito da

7 / 33