ANA MALIK HAUSA NOVELS BY HUMAYRA BULAMA .doc

Author :  Humaira Bulama Category :  Top Hausa Novels 2025

Chapter   5 / 33

12K to 15K   out of 98.8K words

hannunsa rik e da kwano. Juyowa ta yi suka had a ido, cikin tab e baki ta ce  acici har ka zo ka fara sana ar kenan!

Dariya ya yi ya ce  Akuya ce ta tashe ni shine na zo na d auki ragowar abincina na jiya na cinye sai kuma ya kalleta ya kalli inda take kallo kafin ya nemi waje a gefenta ya zauna ya ce  Yaya Dije kema akuyar nan ce ta taso ki ko? Wallahi muma y an d akinmu duk ita ce ta taso mu, su Ya Muhammad suma tun d azu suke tsaki Mamana ma yanzu da na fito na barta zaginta take ta yi tana tsine mata.
Kallonsa ta yi sai kuma ta kalli k ofar d akin Asabe sannan ta d an d aga murya ta ce  shegiyar Akuya tsinanniya! Ko da yake ba laifinta bane ba yunwa take ji shiyasa, Allah na tuba dama ita kanta mai kiwon nata ma a karan kanta ta siyawa cikinta abun dad i ta ci kyashi take yi ka ga kuwa Ina Akuya Ina ita Ina k oshi?!
Dariya Umar ya yi ya gyara zama ya ce  babu kuwa

Kwafa Dije ta yi sannan ta ce  daga fa ganin Ya Aminu ya fara kiwon kaji shikenan aka tsiri kiwon akuyoyi tsabar gasa, ai kuwa alhaki kawai za a kwasarwa kai dan na san yunwa sai ta yi ajalinsu, kiwo dama ai ba na kowa bane ba, shi dai ya Aminu yana da arzik in yin kiwo yana da sana ar da zai ciyar da su shiyasa ya tsira su kuwa masu kiwon akuyoyi sai dai su yi ta d aukarwa kai alhaki, yo ba ka da gashin wance ai dama ba ka yi kitso wance ba

Umar kuwa dad in hirar yake ji dan haka ya biyeta tana yi yana tanka mata& Yaron kusan tsaran Zainab ne amma bashi da wayo sosai kuma jininsa ya mugun had uwa da na Dije gashi ita ba ta ma wani cika kula shi ba dan duk Yaran gidan ba wasa take musu ba, shiyasa yau d aya da ta biye masa ya ji abun kamar albishir, ita kuwa a halin yanzu da take neman magana ko jinjiri ne ya zo tayata yarda za ta yi.

K asa k asa ta ce  Wallahi da Ina da salatip yau da sai na manne wa akuyar nan baki da shi kunnen kowa ya huta, shegiya tsinanniya.
Da sauri Umar ya ce  Ina da shi a d akin mu bari& ..

 Ku tashi dan ubanku masu neman fad a
Cewar Kaka wadda muryar Dije ta taso ta daga barci.

Dama Dije da biyu take ta hayagaga so take Asabe ko Kaka wani ya kulata ta rama abinda suka yiwa ya Muhammad d azu da asuba!
Ba ta san tak ameme menene ya faru d azun a tsakaninsu ba amma dai ta san a kan Asabe ne Kaka ta kira shi da kwarto.

Cike da rashin kunya Dije ta ce  uban nawa dai d an ki ne! Kinga kuwa idan kika zage shi kamar kanki ki ka zaga.

 Tabbas dama na san za ki aikata! Shegiya marar kunya fitsararriya, ai ba laifinki bane ba laifin uwarki ne da ta lalata ku yanzu gashi tun ba a je koina ba kuna shirin addabar al umma!
Cewar Kaka.

Mik ewa tsaye Dije ta yi ta gyara d aurin zaninta sannan ta ce  Wallahi kaff cikin mu babu wanda zai addabi al umma, kaff cikin mu babu mai sata zina ko shaye shaye kinga kuwa mu ba abun gudu bane ba ita wacce kike son kai a kanta kike goyamawa baya ita ce take da wannan tambarin ba dai mu ba dan yanzu haka akwai d an uwanta a hannun hukuma ya je ya yi shaye shaye ya yiwa al umma b arna, kinga kuwa itace mai kashi a gindi..
Mu kam in sha Allah abun alfahari zamu zama wallahi ki rubuta ki ajjiye in sha Allah sai mun yi suna wallahi sai mun baki mamaki

Cikin katseta Kaka ta ce  eh suna a gidan karuwai ba!

Wata mahaukaciyar dariya Asabe wadda ta fito yanzun da niyyar tankawa Dije ta yi kafin ta ce  ai dama baki ya san me zai fad a amma bai san me za a mayar masa ba

Tab e Baki Dije ta yi kafin ta ce  ai ba gaskiya ta fad a ba! Mugun alkaba i take yiwa mutane wanda in sha Allah a kanta zai tsaya ita kad ai
Sai kuma ta juya ga Kaka ta ce  wannan rashin sanin ya kamatan naki da aiki da kike yi da k aramar kwakwalwarkin nan ne ya sanya ko kad an ba na respecting d inki wallahi! Allah na tuba in banda rashin man kai wacce
kalar Kaka ce za ta yi wannan furucin ga jikarta??

Cikin fushi Kaka ta taho tana cewa  Asabe rik e min Yarinyar nan yau sai na koya mata hankali wallahi, rik e min ita in daki banza, ya kamata ta san har yanzu Inada ragowar k arfi na! Shegiya kayan banza

Nan kuwa Asabe ta shiga k ok arin rik o ta ita kuma tana zillewa tana cewa  Wallahi mai dukana sai ruwan sama

Dai dai sun rutsa ta a lungu Asabe ta tare hanya Kaka kuma ta taho da sassarfa har da had awa da gudu ita kuwa Dije ta yi wani tsalle ta bi ta kan kejin kajin Ya Aminu ta tsallake Asabe yayinda Kaka ta je ta gwaru da garu ji kake k ummm!!! Ta gwara hannu da Kai nan take ta zube a wajen bayan kanta ya bugu sangalalin hannunta kuma ya ce wani  k asss!
Salati Asabe ta kurma ta fashe da kuka tana cewa  shikenan za ta k arasa mana ita! Mallan! Mallan!! Mallan!!!!

Ita kuwa Dije ko d arr ba ta ji dan dama ita da tsoro sun yi hannun riga, cike da gadara ta ce  gobe kya sake zagin mu& ai mu Allah muka ce shiyasa duk wanda ya tab o mu yake ganin ba daidai ba.

Ba ta san lokacin da Ya Muhammad ya shigo tsakar gidan ba sai  wuce ki tafi d aki d in da ya ce mata ta ji.

Tana waigowa ta ganshi a tsaye ransa a d an b ace abunda ba ta saba gani ba dan haka ta juya simi simi ta wuce ciki zuciyarta fess!!
Har ga Allah ba ta tausayi ko jin k an Kaka saboda yadda sarai kuma k iri k iri tshohuwar take nuna musu k iyayya ko kara babu, ta tabbata in da ace babu zunubi tsaff Kaka sai ta kashesu one by one& .haka nan suke rayuwarsu su da ita kamar Annabi da kafiri.

A zaune ta tadda Inna tana yankan farce, sai da ta durk usa tukunna ta ce mata  Inna Ina kwana, ya jikin?
Dukda ta san Inna ba lalle ta yi mata magana ba tunda ba wani namijin ta kula ko ta yi dambe da shi ba amma sai da ta ji d ar-d ar&
Ilai kuwa kamar komai bai faru ba Inna ta d ago ta kalle ta ta ce  Alhamdulillah.
Ki je ki d aura mana ruwan d an wake
Ajiyar zuciya Dije ta sauk e kafin ta ce su Ramma sun jik a duk itacen kitchen d in wasu har d igar ruwa suke yi ragowar kuma ba za su ci da wuri a yi girkin a gama da wuri ba, za su bada wahala su b ata lokaci. Ko a siyo y ar tsala
kawai ko?

Tab e baki Inna ta yi ba tare da ta damu ta ji mai ya faru ita da waye ba ta ce mata  ki d auki itacen namu ki kai kan simintin waje ki shanya su, daga nan sai ki biya ki siyi y ar tsalar ki tahowa Muhammadu da shayi.
Ta yi maganar tana janyo
purse d inta ta zaro d ari shidda ta bata.

Karb a ta yi ta ce  to daga nan ta mik e ta d auki Hijabin ta har za ta fita sai kuma ta juyo ta ce  Inna in fitar da har murhun in d aura a kan kejin Ya Aminu ko? Komai na kitchen d in ya jik e
 Eh
Kawai Innna ta ce mata daga nan ta ci gaba da yankan farcenta.

Tana fitowa ta tarar an kinkimi Kaka an wuce an fita da ita da alama asibiti za su kaita.
Ai kuwa ilai tana fita ta ga anata k ok arin dannanta a motar Manager. Ko sake kallon inda suke bata yi ba kamar ba ita ce musabbabin komai ba haka nan ta wuce ta barsu suna ta hayya hayya.

Dije bata dad e da fita ba, Umar ya fito hannunsa rik e da wani k aton salatip fari, kasancewar kusan kaff gidan aka tafi kai Kaka asibiti dan wasu ma a napep suka bisu ya sanya gidan ya zamana shiruuu,???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? tsakar gidan shima ba kowa.
Wani murmushi Umar ya yi ya k arasa inda akuyar nan take wadda ta ci kuka ta galabaitu zuwa yanzu kukan nata ma da kyar ya ke fita.
Yana zuwa ya nemo kan salatip d in ya d agosa ya warwaro ya dedeta bakinta ya mannna mata, a take ta fara kiciniyar kwacewa amma ya danneta ya shiga nad a mata salatip d in nan kamar an aiko sa& .Umar d in Yaro ne gashi dukda kasancewar sa Yaron still shekarunsa sun fi wayonsa yawa sosai, gashi so yake yi ya burge Dije idan ta dawo ta tarar ya toshewa Akuya Baki ta daina kuka ya san za ta ji dad i, dan haka ya had e har da hancin akuyar ya rufe koina ruff da salatip d in nan ba tare da ya lura ba.

BULAMA
'?
0806 402 1951
ANA MALIK!!
Book 01.
Page 04.

Humairah Bulama.
Mikiya writers Association.

****************
& ..SOMEWHERE IN AFRICA& ..
Dukda kasancewar garin a waye yake hakan bai sanya d igon haske ya ratso ta cikin d akin ba! Ga wanda bai san inda kansa yake ba tsaff zai iya cewa duhun daren wata mai kwana d aya ko biyu ne, amma a zahirin gaskiya k arfe goma da rabi ne na safe.
Wata dakakkiyar murya aka yi amfani da ita wajen cewa  ki tabbata idan aka samu matsala wannan karon ranki ne fansa tare da na y ay ank i guda uku! .

Wani yawu mai tauri d aci da zafi ta had iye sannan ta ce  na yi dukkannin abinda ya dace, bani da tantama wannan karon bai isa ya tsallake ba .

 Ki tabbata idan aka samu matsala wannan karon ranki ne fansa tare da na y ay ank i guda uku! .
Aka sake maimaita mata maganar ta farko.
Ta san idan ta bari aka maimaita har sau uku hukuncin ta mai tsanani ne dan haka ba dan ranta ya so ba ta ce  Na amince!
Muryarta na rawa.

Marik in k ofar wadda ta kasance ta jar k asa mai shegen nauyi aka kama aka jaaa k ofar ta bud u wanda hakan ya bawa haske damar wanzuwa a cikin d akin tarr! Har sai da ta yi saurin runtse idanuwanta sakamokon sabawar da ta fara yi da duhun d akin.
Ficewa aka yi aka barta ita d aya kwal aka mayar da k ofar aka rufe duhun nan ya sake mamaye koina..wani Irin kuka ta fashe da shi jikinta yana karkarwa tashin hankali yana sake lullub e ta, ta san cewa ta yi dukkanin abubuwan da aka sanya ta amma Mai Martaba Sarki ZainulAbidden ba k aramin d an baiwa bane ba shiyasa ta ke cikin matsanancin tashin hankali! Ba zata iya k irga adadin tarkunan da ya shallake ba kama daga haihuwar sa zuwa yanzu ba! Ta yadda aka yi aka haifesa d a Namiji ma kuma ya rayu a cikin masarautar kanshi abin mamaki tsoro da al ajabi ne!
Kamar wata zararriya haka ta fara magana tana hawaye ga gumi kamar ana dafata sakamokon rashin b ulin da iska ko d aya zata shigo cikin d akin.  Kaicona! Ina zaune a matsayina cikin kwanciyar hankali tare da uwargijiyata gashi kwad ayin k arin matsayi tare da son abun duniya sun janyo min bala i
Numfashinta ne ta ji ya fara sark ewa sakamokon rashin iska dan ta jima a d akin ta galabaitu, a hankali ta ce  Ya Allah ko da ace wa adi na ya zo k arshe ka kub utar min da y ay ana
Dukda kuwa ta san rayuwarsu a cikin masarautar ba tare da ita ba bala i ne gasu duk k ananu amma gara dai su rayu d in akan su mutu tare da ita& .
A hankali ta fara lullumshe ido daga nan ta silale daga zaunen da take ta sume a wajen& .
Bayan kamar awa d aya, ta ji an shek a mata ruwa!
Haske ta gani tarr! An bud e k ofar Fadawa wajen su biyar suna tsaye a kanta. Kukan babbar y arta ta ji mai kimanin shekaru goma a duniya. Da k arfi kuma da sauri ta runtse idanuwanta bata kai ga bud ewa ba aka ce mata  Mai Martaba Sarki ZainulAbidden yana a cikin k oshin lafiya bayan karin kumallo da ya yi da shayi da dambun naman da kika yi masa
Bulala arba in ta hau kanki tare da y ay anki bayan nan kuma
Rayukan ku ne fansa!!
Bud e Baki ta yi zata fara magiya aka yi saurin toshe mata bakin ta bayanta da wani kyalle haka suma y ay an nata& .

Ko wannensu sai da Fadawan nan suka yi masa bulala arba in d innan kamar yadda suka furta da wata mahaukaciyar bulala wanda tun a bugu na uku da aka yiwa y ar autarta mai Shekaru hud u da ita Yarinyar ba ta sake shurawa ba!
Jina jina haka nan suka yi musu tukunna suka fita suka barsu da Baki a toshe gashi babu ko d igon iska a cikin d akin da ya kasance na jar k asa wanda ta waje aka yi masa kamar plasta da langa langa.
Dukda bata gani sosai suna fita ta rarrafa kansu inda take jin nishi sama sama&
Da kyar hannunta yake iya lalubo mata su, ko da ta duba ta k arshen ta rasu haka shima na biyun babbar y arta ce kawai ta yi saura, dan haka ta jawo ta ta rungume suna wani irin kuka mai cin rai.
Bayan kamar awa d aya lokacin da rana ta kwalle numfashi ya yi bankwana da jikin babbbar y ar tata, lokacin itama ba ta cikin haiyyacinta ta yi sumar wucin gadi, sai da ta farfad o sannan ta fahimci rumgume take da gawa& & Rashin ventilation ga uban warin gawarwakin da wasu suke ta tsutsa da bak in ciki da azabar radad in ciwukan da suka jijji mata yayin dukansu da bulalar doki! Ne suka taru suka sanya itama ta ji zuciyarta ta yi wani irin hantsilawa sai kuma ta bada dummm!!! Daga nan ta ce ga garinku nan.
****************

Mallan bai samu ya koma gida ba sai wajajen k arfen goma na safiyar ranar sakamokon suntumewar da k afar wannan bawan Allah wanda Ma a ya yiwa b alli b alli a masallaci ta yi, dan sai da ta kaisu ga danganta shi da asibiti yanzu haka ma yana chan an dai yi dressing an nad e k afar ana kan bincike.
Yana shigowa tsakar gidan ya hango gawar Akuyar Asabe yashe a tsakar gidan baki a nannad e!
Dukda ya san ba lalle Dije ta aikata wannan d anyen aiki ba amma sai ya tsinci kanshi da fara adduar Allah ya sa babu hannunta a ciki, a zuciyarsa.

D akin Kaka ya nufa da niyyar gaida ita kamar yadda ya saba kullum sai dai kuma ko da ya Isa bakin k ofar ya kwankwasa sai ya ji shiru, bai wani jima a tsaye ba Inna ta fito tana gyara d aurin d ankwalinta, suna had a ido da shi ta d an saki fuska ta ce  Ashe kai ne Sai kuma ta d an rissina ta gaida shi dukda wadda suka yi a waya ba da jimawa ba.
Cikin kulawa ya amsa mata ta tambayesa mai jiki ya ce mata  da sauk i daga nan ya fara rarraba ido ya na k arewa tsakar gidan kallo& .
Sai a yanzu ya lura da yadda gidan ya ke shiruu kamar ma babu kowa, dan in banda Umar da ya gani a kan yashi suna wasa da Yara to bai ga kowa ba kuma bai ji motsin kowa ba bayan Halima da suke gaisawa da ita yanzun, sai ko Rakiya da ya hanga a kitchen tana shan ruwa.
Gyaran murya ya yi bayan ya gama waennan lissafe lissafen ya ce  ina ta kiran wayar Kaka tun d azu bata d auka, tana ciki kuwa? Allah dai ya sa lafiya
Ya jero mata tambayoyin idanunsa a cikin nata.

Numfashi ta fesar ta sauk e wata nannuyar ajiyar zuciya kafin ta ce  Ka yi hak uri Mallan, Kaka Dije ta biyo d azu wai za ta daketa ita kuma ta zille shine ta k ume da bango ta suma, Aminu kuma yanzu ya fita yake ce min har da gocewar k ashi a hannu .

Lumshe idanuwansa ya yi ya fara k ok arin controlling temper d insa, sai da ya samu ya d an daidaita kansa da kyar! Tukunna ya ware murya ya shiga kwala kiran  Dije! Dije!!
Cikin kwantar da murya Inna ta ce  tun d azu na aiketa siyo y ar tsala ka ga har yanzu ba ta dawo ba babu ita ba abun karin, sai Aminu na bawa ya je ya siyo mana k osai ga

5 / 33