ANA MALIK HAUSA NOVELS BY HUMAYRA BULAMA .doc

Author :  Humaira Bulama Category :  Top Hausa Novels 2025

Chapter   24 / 33

69K to 72K   out of 98.8K words

cewa akwai matsala amma tunda ba kai bane ba shikenan.
Tabbas ko ma waye ya jik a mana aiki. Saboda hawanka kan karagar mulkin nan ba tare da taimakon abun hannun Mariya ba it s impossible..

Shiruu duk suka yi kafin chaan ta ce  bari in je, za a zo nema na zuwa anjima Ina da bak i.

Da sauri ya ruk o hannunta ya ce  ban gaji da gan..
Dan ya lura har yanzu a fusace take, kuma da gaske bai gaji da ganin nata ba.
Cikin katseshi ta ce  Plss Nuraddeen, mu ji da abunda ya ke a gabanmu yanzu dan akwai matsala tafe kuma muddin ka bari Sarki ya mutu ba tare da Mariya ta baka abunda ta yi alk awari ba to ka san cewa da kai da babu duk d aya. A wajena da wajen kowa ma dan haka ka yi lissafi mai kyau ka nemawa kanka mafita.
Tana gama fad in haka ta juya ta wuce fuuu kamar zata tashi sama& & bayaga Nuraddeen mutane hud u ne manya a masarautar ta san sunada k udiri irin nata kuma duk ta bincike su ta k ark ashin k asa ta gano ba su bane ba, to wai waye haka wanda ya aikata musu wannan d anyen aiki haka cikin bazata! Tabbas an had a mata jagwal& ..
Tana wannan lissafin ta wuce ta barsa a wajen..

Ya dad e a wajen kafin chaan ya furzar da iska a fili ya ce  za ki shigo hannu ne! Duk wannan izza da rashin kunyar taki za ta kau ne za ki yi bayani& .

Sai kuma ya shiga tunani tare da lissafin waye ne mai wannan d anyen aikin haka?&
Tsaki ya yi ganin yana shirin bawa kansa headache ya ce  ko ma waye za a nemo sa ne Dan ya san dole da had in bakin Baiwa/Bawa ko Bafade ko Dogari aka yi aikin nan, kuma yin aiki da su ka barsu a doron k asa hatsari ne babba! Kai ko da ace ma ka kashesu dole a gano gaskiya ta hanyar wani ko wata d an uwa ko Abokinsu dan basu iya rik e sirri ba gasu da shegen munafurci! Gashi idan aka fara bincike a cikin masarautar har hanji ko Ina sai an dubo an gano gaskiya. Idan kuma aka gagara aka mak ale a taso mai gaiyya mai aiki ya bincika wanda in dai a k asar KHAK IL aka haifi mutun aka binne cibiyarsa kuma ya aikata laifin to fa dole sai an gano a cikin kwarya.
Shiyasa su suka tura tsohuwar Jakadiya ta nemo musu waenda bama y an k asar ba ta yadda suna gama yi musu aiki za su aika su lahira kuma duk kwakwar mai gaiyya bai Isa ya iya gano su ba tunba ba a k asar aka binne cibiyarsu ba, sannan za su tsoratar da su ta yadda ba su Isa su yi sirri da kowa ba idan ba su d in ba& ..
***************
Sai da Minu ya dawo da daddare tukunna aka san halin da Malllan ya ke ciki.
Sosai hankalin kowa ya tashi dan sam ko motsi ba ya yi dan haka aka wuce da shi emergency direct ba tare da sun san me za su bayar ba idan sun je d in dan sun yi k ak aff!! Hatta Ya Muhammad ma shirye-shiryen dawo da shi gida ake yi a hakan ba tare da ya warke ba saboda basu da kud in gado bare na magani.

Duk fushin da Kaka take yi da shi tana jin labari ta baro garin Getso a rikice dan Mallan daban yake a wajenta Halima ce take janyowa suke yin fad a ita da shi amma ba dan haka ba da an ga yadda ake ji da Yaro.

Zuwan nata ne ya sanya suka samu d an abunda aka bayar a asibitin aka ci gaba da treatment d insa wanda daa Likitocin suke shirin ajjiyewa dan ko syringe babu a asibitin sai ka siyo tukunna za a yi maka amfani da shi su kuwa basu da ko sisi.


Tijara ta so yiwa su Inna a bainar nasi dan haka Inna ta tattaro Dije suka baro wajen, tunda har an samu wanda zai d auki d awainiyar tasa to Alhamdulillah, daga haka suka fito ba su da ko kud in mota suka shiga dab awa da k afafuwansu ga dare.

Kamar daga sama suna cikin tafiya ta ji an ce  Khadija
Tana juyawa ta ga Ya Kamal ya biyosu yana d an haki alamun da kyar ya cimmusu.

A take kunya duk sai ta lullub e Inna dan tabbas ta san bai kamata Dije ta fito ba da saninshi ba.
Sai da ya rissina tukunna ya gaida Inna itama ta amsa cikin jin kunyar da bata tab a kawowa zata yi ta a Kamal d in ba.
Cikin rashin jin dad i ta ce  ka yi hak uri ta fito ba da sanin ka ba ko? Jikin Mallan ne ya motsa shine duk muka fito
a d imauce ni na ma matan w
Da sauri ya ce  haba dai Inna, ba komai wallahi Allah ya bashi lafiya, nima Iyya ce ta kira take sanar min shine na biyo sahu shigata ba wuya kuma Minu ya ce min yanzu kuka fita, shine na ce bara in duba.
Bismillah mu je in k arasa da ku ga mashine d in chan.
Ya yi maganar yana mai waigawa ya nuna musu inda ya yi parking.

Murmushi Inna ta yi ta ce  ba komai ku je zan k araso ni.

Shima sai a lokacin lissafinsa ya bashi baza ta iya ta bisu a machine d in ba dan haka ya wuce ya tarar mata napep ta shiga ya biya kud in suka wuce.
Dije ji tayi kamar ta bita su tafi a kan cinyarta amma Napep d in a cike take tap da mata biyu da y ay ansu Innar ma da kyar ta samu waje.

Sai da ya ga wucewarsu tukunna ya juyo ga Dije wadda ta diririce a take ta hau kame-kame.
Murmushi kawai
ya yi a ransa yana mamakin yadda duk suka sauya daga ita
har Innar kamar ba su ba. Ko da yake ya san in komai ya wuce za su dawo kamar yadda suke a daa in sha Allah idan komai ya yi settling hankali
ya kwanta dan mai hali ba ya fasawa. A ransa ya ce  zan sha daru! Fuskarsa tana baiyyana murmushin da yake nuni da nishad in da zuciyarsa take a ciki.
 Mu je ko?
Muryarsa ta katse mata hanzari.
A hankali ta sake sunkuyar da kanta k asa ta juya ta wuce inda ya nuna musu machine d in nashi.

Sai da ya hau tukunna ya karkata mata itama ta hau sannan ya kunna suka wuce, yana jin yadda ta matsa sosai chan k arshe duk dan kar jikinta ya gogi nashi. Kad an ya rage bai fashe da dariya ba lokacin da akazo wajen speed bumps dan sosai ta saka hannayenta a tsakankanin k irjinta da bayansa yadda k irjinta ba zai bugi bayansa ba.
Har suka k arasa gidan babu wanda ya cewa d an uwansa k ala! Yana sauk eta ta fara k ok arin shigewa cikin gida& har ta hau kan d an dakalin k ofar gidan nasu ya yi sauri ya ce  Khadija yana mai daidaita parking d in mashine d in nasa.

A hankali ta ja ta tsaya kafin ta juyo, a take ta ji gabanta ya yanke ya yi wani irin mahaukacin fad uwa sakamokon idanu biyu da suka yi da Ma ah tsaye a bayansa.
Idanuwanta ne suka wani Irin ciccikowa k irjinta ya hau dukan uku-uku jikinta ya fara karkarwa tana mai jin wata kalar tsoro da tsanarsa suna lullub eta.
Ya kafeta da idanuwa sam ko kyaftawa ba yayi kuma bai yi motsi ba sannan bai ce komai ba yana nan a yadda yake wanda hakan ya sanya ta fara tunanin ko dai Aljani ne dan ita a iya saninta ma Ma ah d in baya Unguwar baya ma garin.
Karkarwar jikinta ne ya k aru gashi tsigar jikinta ta fara tashi a ta sakamokon kallon k urillar da yake yi mata da taimakon hasken kwan fitilar nepan da ke a k ofar gida, ga wani irin tsoro da fargaba dan haka ta yi sauri ta juyaa zata shige cikin gida ita sam ta ma manta da Ya Kamal a wajen wanda ya k araso izuwa gareta ya tsaya yana kallonta yana mamakin yadda jikinta ke karkarwa haka tashi d aya.
Caraff! Ya yi ya ruk o hannunta da sauri ya juyo da ita wanda hakan ya sanya Ma ah d in ya yunk ura kamar zai yi kansu sai kuma ya d an dakata.
A hankali yana kallonta ya ce  mai ya faru? Ba ki da lafiya ne kema? & ..

Magana Ya Kamal yake yi mata amma kwata-kwata hankalinta baya a garesa dan haka bama ta jinsa gaba d aya idanunta da hankalinta suna a kan Ma ah wanda take hango tsantsar b acin rai da tashin hankali a cikin kwayar idanuwansa& Ya Kamal yana da kirki fiye da zato ba zata ce tana son shi ba a yanzu dai kam amma ta san zata so shi a gaba a matsayin Mijin aurenta! Tabbas idan wani abu ya same shi ata sanadiyyarta to bata jin za ta iya d auka! A hankali ta ce  Astaghfirullah sai kuma a take hawaye shaa suka kwace mata.
Rikicewa ya yi ya shiga tambayar ta  mai ya faru? wanda hakan ya sanya hawayen suka k ara dad uwa kamar an kunna famfo.
Ganin yadda jikinta ke karkarwa gashi sai kuka take yi ne ya sanya kawai ya janyota ya saka ta a jikinsa yana bubbuga bayanta alamun rarrashi.
Da wani Irin mugun speed Ma ah ya juya ya bar wajen kamar walk iya& & .

Da kyar Dije ta iya cewa  Ya Kamal mai ya sa ka yarda ka aureni? Kar wani abun kaima ya sam& 
Shiruu ta yi ta kasa ci gaba da maganar saboda yadda kuka ya sake taho mata da k arfin gaske mai yawa.

Bai san lokacin da murmushi ya sub uce masa ba, kenan ta damu da shi& gashi har tana kuka bata so wani abun ya same shi kenan.
Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauk e kafin ya ce  Khadija babu abunda ya Isa ya sami bawa sai da izinin Ubangiji, Ma ah bai Isa ya yi mini komai ba sai abunda Allah ya riga ya rubuta kuma ina so ki saka a ranki ma ba shine yake kashe waenda aka yi baikon ki dasu ba, kar ki bari nauyin guilt d in kowa ya hanaki yin walwala, kin ji ko?
Ya yi maganar a hankali cikin sake sakata a cikin jikinsa wanda hakan da ya yin ne ya sanya ta tuna a ina take dan haka ta yi saurin jaa daga jikinsa ta matsa gefe sosai.
Murmushi ya yi ya sake kamo hannunta a karo na biyu ya ce  ki kwantar da hankalinki, kin ji ko? Sannan kar ki tab a bari guilt ya yi tasiri a kanki zai tarwatsa miki rayuwa ne, ki yi min wannan alk awarin.
A hankali ta jinjina kanta tana mai dudddubawa ganin bata ga Ma ah ba ya sanya ta d an nutsu bayan ta saka a ranta maybe ko kwakwalwarta ce take yi mata gizon sa.
Juyawa ya yi ya kalli inda take kallo ganin bai ga kowa ba ya sanya ya kawar da tunanin ya ce  gobe da sassafe zan tafi Minna, Iyya ta ce in je in nema mana inda za mu zauna sannan in sanarwa k aninta halinda ake ciki (in person) tukunna, dan daa tare zamu tafi to amma ta san za su ce suna so su zo su d aukeki hakan babbar Al ada ce a garemu dan haka baza su so ta sub uce musu ba&
In sha Allahu ba zan wuce 1 week ba zan dawo tare da su sai mu wuce ko? Zan had o miki har da lefen ki in taho miki da su in sha Allah.
Ya k arashe maganar yana murmushi yana kallonta.
A hankali ta sunkuyar da kanta k asa sosai sannan ta ce  Allah ya kiyaye hanya, sai ka dawo.
Jinjina kai ya yi ya ce  za mu dinga waya ta wayar Inna.
Ba zan yi miki alk awarin waya yanzu ba saboda akwai abubuwa da yawa a kanmu amma idan muka yi settling kika ci gaba da makarantar a chan zan siya miki in sha Allah.
Jinjina kai ta yi ta ce  na gode
Har zata wuce sai kuma ta ce  Allah ya tsare hanya.
A hankali ya ce  sai na dawo
Sai kuma ya kamo hannunta ya yi kissing wanda hakan ya sanya ta d an zabura har ta so bashi dariya sannan ya zaro dubu goma dama da ya yi niyyar bata kafin ya wuce ya ce  gashi ki rik e a hannunki, ko?
Da kyar kuwa ta karb a tukunna ta wuce ciki jikinta sanyi k alau!& & .
Bata yi tunanin tadda kowa a tsakar gidan ba dan 12 ma ta kusa, amma tana shiga ta tarar da Rakiya da Kubra da Maman Fati suna ta k us-k us. Tana jin Rakiya tana cewa  Wallahi har da kiss, hmm Yarinyar nan ai ta cucesu ko da ba a kashesa ba ya kwashi ragowa, ki ga fa yadda take nuna tana cikin damuwa amma ta kasa hak ura dan bala i a k ofar gida fa.
Sarai kuma ta san sun lura da ita sun ga shigowarta zuwa yanzu.
Kubra ta ce  yo abune an riga an saba, kinga kuwa ai ba za a iya d aga k afa ba.
A take duk suka kwashe da wata y ar iskar dariya kamar ba dare ba.
Har zata kula su sai kuma kawai ta rabu da su ta yi shigewarta cikin d akinsu zuciyarta a cunkushe& & & ..


Washegari da sassafe sama-sama Inna ta ji Kaka tana yiwa wata mata interview& tsabar matar ta raina mata hankali wai a Jigawa aka haifeta iyayenta duk sun rasu a chan, achan ta taso sai dai bata da aure yanzu Mijinta ya rasu ya barta ita da y arta d aya Saddik a, amma wai ta fad i sunayen unguwanni uku a garin Jigawan ta gagara!.
Jin da Inna ta yi Kaka tana shirin bata makulli ne ya sanya ta yi wuff ta fito, suna had a idanu da matar ta ji tsigar jikinta ta wani tashi yaaammmmm! Gabanta ya yanke ya fad i.
Da sauri ta yi ta a uzi ta shiga karanto sunayen Allah tukunna ta d an nutsu dai-dai Kaka ta mik a mata makullin ita kuma ta mik o mata kud i za a yi hannun kuturu da makaho.

Da sauri Inna ta k arasa ta wafce makullin ta tura mata hannunta jikinta mai
rik e da kud in ta ce  Malama tashi ke da y artaki ku fice daga gidan nan bama son rainin wayo.
K urrrr! Matar ta yi mata haka itama Inna ta yi mata k urrr da nata idanun duk da kuwa yadda take jin fargaba da tsinkewar zuciya amma bata janye idanunta a cikin na matar ba sai ita matar ce ta janye nata idanun tana mai mamakin Inna.

Mari! Kaka ta kawowa Inna a fusace ta yi saurin gocewa cikin fushi ta ce  dan ubanki har yaushe kika fara shiga sabgata a cikin gidan nan?.
Ko da yake baki ma da uban ai ballanta idan an zage shi ki ji haushi.
Ba ni makullin nan kafin mu kwashi y an kallo ni da ke da asubar farin nan.
Ta k arashe maganar tana mai daka mata wata uwar tsawar.

A take sai Inna ta ji duk ta muzanta& Tabbas kam bai kamata ta shiga harkarta ba, bai ma kamata ta fito ba bama ta san me ya fito
da itan ba. To amma kuma ai dai matar tare da su zata zauna a cikin gidan dan haka idan ma wata annobar ce ai abun har ita ya shafa& .
Har ta yunk ura zata yi
Magana sai kuma wata zuciyar ta ce mata  ta bari kawai ta samu Mallan da maganar, idan ya ji sauk i, dan ta san tunda ta nuna bata son matar to ko aman wuta aka ga matar tana yi Kaka sai ta barta ta zauna a cikin gidan ko dan ta k untata mata! Dan haka yanzu ko ta yi wani abun ma a banza. Dan haka gara ta bari Mallan ya dawo ya bincika ya gano wacece ya yiwa Kaka bayani cikin salama a sallameta dan bata da tantama tabbas matar nan ba ta kirki bace ba& &

BULAMA
'?
0806 402 1951
ANA MALIK!!
Book 01.
Page 22.

Humairah Bulama.
Mikiya writers Association.

Saboda hatta y ar da ta zo da ita kana gani ka san ba tata bace ba, dan babu kama ko kad an gashi kana kallon Yarinyar tashi d aya zaka fahimci a tsorace take.
Nufota Kaka ta yi a zuciye dan haka ta mik a mata makullin kawai da sauri ta juya ta wuce d akinta tana jinta tana ta zage-zage tana goranta mata har da cewa  shegiya, ke da ba kya aikin fari ballatana na bak i daga ke har y ay anki, idan ba a karb i kud in nata ba uban waye ne kike tunanin zai biya ragowar kud in asibitin Mallan?
Ita dai Innaa bata biye ta ba ta yi wucewarta ciki abunta&

Ita kanta Kaka tunda Matar ta tare ta a k ofar gida tana shirin shigowa (dawowarta daga asibiti kenan) gaba d aya ta ji matar bata yi mata ba. Dalilin da ya sanya ta amince ta karb i matar kud i take da buk ata ne urgent na treatment d in Baba gashi ko kwayar shinkafa basu da ita shiyasa ma ta karb i na wata uku ta ce mata  akwai mai d akin ta yi

24 / 33