ANA MALIK HAUSA NOVELS BY HUMAYRA BULAMA .doc

Author :  Humaira Bulama Category :  Top Hausa Novels 2025

Chapter   15 / 33

42K to 45K   out of 98.8K words

in.
Babu yadda ba a yi da shi a kan ya fita ba amma k ememe ya tsaya ya ce a yi komai a gabansa kuma ya hanasu cire mata hijabi.
Da dabarun su na Likitoci sukayi amfani aka samu aka duddubata suka gano ba komai bane sai shock ya sanyata ta suma sannan jininta ya yi low sosai.

Likitan ne ya rubuta abubuwan da ake buk ata tare da bill d insu ya mik awa Ma a ya ce  ya biya sannan akwai guda d aya da basu da shi kuma yanzu za a jona mata drip ne dan haka ya yi k ok ari ya kawo, ana buk ata urgent.
Ba shi da ko sisi a jikinsa sai naira 20 gaba da baya dan gaba d aya tattalin arzik insa ya k arar a wajen hidimar fara sana arsa ta sayar da rake, dan hatta bencin da aka bubbuga musu wajen guda uku sai da suka ci masa kud i ba na wasa ba. Su Oscar sun so su d auko ko na uban waye ko su saka a yi musu a kyauta ala dole amma sai ya hanasu saboda tun ba yau ba dama ya yi alk awarin ba zai tab a ciyar da Mama da abunda bai dace ba komin k ank antarsa yana so komai ya zamo ta hanyar halal. Yanzu kuma ga Dije wadda saboda itan ne ma ya ke so ya fara sana o i sosai dan aiki ba ya a cikin lissafinsa, kuma ya san d awainiyarta dole tana buk afar kud i sab anin da wanda daga shi sai Mama.

Lissafin wajen dubu hamsin ake yi yanzu haka ga kuma wani drip na daban wanda zai je ya siyo.
Likitan yana gama bashi takardar ya juya ya fita, sai da ya gama k arewa fuskarta kallo tukunna shima ya juya ya fito wajen su Scorpion, suna ganinsa suka yo kansa suna tambayar sa  ya mai jiki!
Shiruuu ya yi kawai yana lissafi, Oscar ya matso still a buge yake har yanzu ya ce  kawo in je in gigita Rabiu mai chemist ya had o min kan komai! .
D agowa ya yi ya k ura masa ido kamar wanda ya ke so ya hango ta inda zai samo kud in rubuce a kan fuskarsa, wanda k ura masa idon da ya yi ya sanya Oscarn ya d an jaa da baya ya sunkuyar da kansa k asa.
Agogon hannunsa mai tsada wanda ya saitawa timer lokacin fara shirye-shiryen operation d in da suke da shi yau ne ya yi k ara! Dan haka ya d ago shi ya kalla lokaci..
Ya gama ganin lokacin amma bai janye agogon ba idanunsa a kan agogon kyarr!! Har yanzu, sai da ya gama lissafe-lissafensa tukunna ya ce musu  ku saka ido
Daga haka ya juya ya bar cikin reception d in.

Bayan kamar awa d aya ya dawo& ya siyo d ayan abun da suka ce basu da shi ragowar kuma yana k arasowa ya had a ya bayar da kud insu tare da kud in gado da service da kati da komai.

Nan da nan aka had a komai aka jona mata har yanzu ba ta san inda kanta yake ba!
Scorpion ne kawai a kaff cikinsu ya lura babu agogon hannunsa wanda ya fita da shi yanzun, murmushi kawai ya yi a ransa ya na mamakin Ogan nasu& &


Sama-sama take jin maganarsa kamar waya yake yi&
 Eh, mun yi har mun gama aikin yanzu haka baya ma duniyar!
Shiruu ya d an yi alamun ana yi masa magana ta d ayan b angaren ne kafin chaan ya ce
 To ko kana buk atar ganin gawartasa ne a je a d aukota?
Zuwa yanzu jikin Dije har ya fara karkarwa dan ta fahimci muryar waye gashi ta ji ta a kwance, ba ta kai ga bud e idanuwanta ba dan haka ba ta fahimci a ina take ba!&
Tsaki ta ji ya yi kafin ya ce  arresting d ina fa ya yi? So
kake in zuba masa ido in kyalesa!?
Chaan ta ji ya ce  wannan kuma aikin su Scorpion ne, su kuma b angaren d an wanchan mutumin ka barni da su ba ni buk atar ka yi komai mun riga mun gama magana da Alaji.
Cikin d an fushi bayan ya gama sauraron wanda suke wayar da shi ta ji ya ce  babban case d in ya ci uwarsa! Ka san yadda za ka yi wannan ba damuwa ta baceba!
Yama gama fad in haka ya kashe wayar ya juyo yana huci zuciyarsa tana tafarfasa. A kan hannunta idanunsa suka sauk a& ta damk e zanin gadon da take kai da dukkan hannuwanta biyu kamar zata fasa shi ne.
A hankali ya k arasa inda take ya tsaya a kanta ya k uraa mata ido, motsi ya ga idanun nata sunayi suna karkarwa da gaba d aya ilahirin jikin nata ma.
 Damn it!! Ya furta a hankali wanda hakan ya sanya ta fahimci yana tsaye a kanta ne kusa da ita! Ba ta san lokacin da ta zabura ta mik e a razane ba, jikinta yana wani irin karkarwa.

BULAMA
'?
0806 402 1951
ANA MALIK!!
Book 01.
Page 12.

Humairah Bulama.
Mikiya writers Association.

Yama gama fad in haka ya kashe wayar ya juyo yana huci zuciyarsa tana tafarfasa.
A kan hannunta idanunsa suka sauk a& ta damk e zanin gadon da take kai da dukkan hannuwanta biyu kamar zata fasa shi ne.
A hankali ya k arasa inda take ya tsaya a kanta ya k uraa mata ido, motsi ya ga idanun nata sunayi suna karkarwa da gaba d aya ilahirin jikin nata ma.
 Damn it!! Ya furta a hankali wanda hakan ya sanya ta fahimci yana tsaye a kanta ne kusa da ita!
Ba ta san lokacin da ta zabura ta mik e a razane ba, jikinta yana wani irin karkarwa.
Sai da ta mik e ta bud e idanuwanta tukunna ta fahimci ashe a asibiti ta ke, wawwaigawa ta yi ta ga d akin daga ita sai shi sannan kamar ma dare ne dan haka ta matsa sosai jikin bango wani mad aukakin tsoro mai tafe da takaici yana lullub eta& &

K uraa mata ido ya yi yana kallon yadda ta ke kuka yana jin sauk ar hawayen nata kamar zubar ruwan zafi a kan k irjinsa, a hankali ya matsa kusa da ita ya zauna a bakin gadon wanda hakan ya sanya ta sake mak alewa sosai a jikin bangon ta kawar da kanta gefe ta k ame sosai dan hatta sautin kukan nata ma ya tsaya dan sosai ta gimtse bakinta, sai uban hawaye da suke ambaliya wani na korar wani.

A hankali ya ke kallonta cikin wani irin yanayi, sai da ya gama nazartarta ya gama hango tsorone tsantsa a tattare da ita, bayan ya tuna yadda Likitan ya ce masa  shock ne ya sanyata ta suma , tukunna a hankali ya fesar da wani irin huci wanda ya sanyata ta sake k ank ame jikinta ta manne da jikin bangon kamar zata tsaga shi ta shige ciki sakamokon wani irin wari da numfashinsa ya feso mata da shi! Ba wai wari na k azanta ko warin baki ba! Wani irin wari ne wanda ba ta tab a jin kwatankwacin irinsa ba amma dai ta fahimci warin kayan shaye-shaye ne sakamokon yadda ta ji kanta ya yi wani irin mahaukacin sarawa a lokacin da ya fesa mata hucin numfashinnasa ita kuma ta shak a.

A hankali cikin wata iriyar calm murya sannan a slow sosai ta ji ya ce  Ba zan tab a cutar da ke ba Khadijah.
Da sauri ta juyo ta ware kyawawan idanuwanta da suka rine ta zuba masa su wanda hakan da ta yi ya sake assasa mata tsana da matsanancin tsoronsa& kallo d aya za ka yi masa ka fahimci shi d in rik ak k en d an daba ne sannan yanzu da ta had a idanu ta shi ta sake fahimtar a buge yake mak ill!! Sai dai kuma wani ikon Allah a lokaci guda maganar ta sa ta soma yunk urin yin tasiri a kanta saboda yadda take hango zallar gaskiyar abinda ya fad a d in a cikin kwayar idanunsa wanda hakan ya bada gudummawa wajen sanyaya mata ilahirin jikinta& &

Kamar kuma wadda aka mintsina a take ta yi firgigit! Ta d auke kanta lokaci guda ta dawo cikin haiyyacinta.
Cikin takaici da tsoro ta fara k ok arin sauk a daga kan gadon gaba d aya, da sauri ya rik e mata hannu ya ce  relax, ba ki da lafiya fa
Ya yi maganar a dake.
Wani irin kallo ta yiwa hannun nasa sannan ta d ago ta kallesa, wanda hakan ya sanya kawai ya d auke hannun nasa.
 Ina y an uwa na? Mai yasa na kasance a nan tare da kai?
Ta yi masa cikin takaici tsoro da damuwa.
A hankali ya runtse idanuwansa kafin ya bud esu, sai kuma ya mik e a hankali ya juya ya fita bayan ya sake ce mata  ki nutsu ba ki da lafiya

Bai dad e da fita ba lokacin Dije har ta gama shirin fecewa wata nurse ta shigo, juyin duniya amma Dije ta k i zama a asibitin nan ta ce  ita Gida zata tafi. & ..
Dai-dai ta fito su Oscar suka taso dan su ya barwa jiranta amma kallon da ta yi musu ta k ara sauri ya sanya suka gagara tsaida ita dan sun san basu Isa tsawatar mata ko su rik eta ba& .a baya dai Scorpion ya bita ya ga ta tsayar da abun hawa ta fad a masa inda zata je ta shiga, tukunna ya koma ciki ya na mai gwada layin Ma a wanda tunda ta fito ya fara k ok arin kiransa amma tun lokacin layinsa engaged.

Da niyyar zuwa gidansu ya fita domin ya taho mata da ko da Minu ne dan ya lura a mugun tsorace take da shi wanda hakan ya sanyashi dana sanin abubuwa da yawa a karon farko na rayuwarsa.
Yana fita kiran Maama ya shigo cikin wayarsa, dan haka ya amsa& .
 Ka zo yanzunnan ta ce da shi cikin sheshshek ar kuka!
Sai da gabansa ya yanke ya fad i kafin ya ce wani abun ta kashe wayar.
Gudu-gudu sauri-sauri ya k arasa bakin titi, dan already ya aiki Grenade da motar da suka taho da ita ta dpo.
Napep d in da ya tarar akwai mutane a cikinta amma haka ya fincikosu ya watsar ya shige suma kuma basu yi yunk urin yin komai ba saboda yanayinsa da suka gani.
Shi kansa mai Napep d in a tsorace yake da shi dan haka ya dage ya dinga tsula uban gudu kamar yadda Ma a d in ya umarcesa.

Yana shiga cikin gidansu tun daga soro wajen d akinsa ya fara jiyo muryar wata mata tana cewa  to ni dai bari in yi sauri in tafi kafin ya zo, dan ya saka mana dokar zuwa cikin gidannan kamar yadda na gaya miki yanzun. Kuma wallahi ya kula da kanshi dan wannan karon kam ba zamu yarda ba
Kuka sosai Mama take yi yayinda matar take k ok arin saka slippers d inta dan haka duk basu lura da Ma a wanda ya shigo a zuciye zuciyarsa tana wani irin tafarfasa ba.
Sai da matar ta gama saka slippers d inta ta d an yo gaba kawai ta ji ta k ume da k irjinsa gab!
Kamar wani dutse ko
motsi bai yi ba amma idanuwansa kad ai idan ka kalla sun isa su gigita ka.
Inda-inda ta farayi ganin yadda ya kafeta da idanuwa sai kuma ta fashe da kuka kawai tsabar tsoro..ta durk usa a gabansa tana kuka wiwi tana cewa  ka rufa min asiri inada jikata guda d aya ni kad ai gareta bamu da kowa idan ka kasheni za ta tagaiyyara
Wata mahaukaciyar shak a ya yi mata ta mik e tsaye ganin yadda take sake ruru wutar tsanarsa a idanun Maama, yana d agota bai yi wata-wata ba ya d auke ta da wani
Irin mahaukacin gigitaccen Mari dama tun d azu a k ule yake ga kuma Dije da ya fahimci ita tsoronsa ma take ji yanzu kuma ga Maama.

Matar tana zubewa a wajen dai-dai Maama itama ta durk ushe ta fashe da wani irin gigitaccen kuka!
Jikinsa ne ya hau karkarwa ya yi kan Maama zai rik eta ta mik e ta fara jaa da baya tana cewa  Ashe har yanzu zalincin naka yana nan Ma aruf? Ashe har yanzu baka daina kashe mutane ba? Ashe har yanzu zuciyarka babu Allah?
To wallahi tallahi bari ka ji in gaya maka da kaina nan zan mik a ka ga hukuma in yaso sai in ga uban da zai kwatoka! Ma aruf a gaban uwa ka kashe mata d anta! Ya kake tunanin zata ji? Ya kake tunanin zan ji idan wani ya kashe mini kai a gaban idanuna????
A hankali ya sake tunkararta hankalinsa a masifar tashe ta ce  kar ka matso kusa da ni!!
Cikin tsawa sannan ta ce  babu ni babu kai daga yau! Ka ji abunda na fad a maka ko baka ji ba???
A da Ina tunanin har da sharrrin K uruciya da zafin abunda ya faru da kai ne sanadi hakan ya sanya na nad e hannu na yafe maka b arnar da ka yi a baya nake nema maka sassaucin azabar girman zunubinka a wajen Ubangiji amma yanzu kam baka da wani excuse Ma aruf!! Kuma bari ka ji in gaya maka ya zama dole ka amsa laifukanka kuma a hukunta ka ko da kuwa hakan yana nufin zan rasa ka ne!
Idan ka kasance d an daba wannan zan iya yi maka addu a idan ka yi kisan kai a lokacin k uruciya wannan shima zan iya d aga maka k afa amma bazan zama selfish in nad e hannu in zauna Ina gani kana kashe rai da hannayenka ba! An yi an gama ta faru ta k are!!! .
Wani irin mahaukacin karkarwa jikinsa ya shiga yi yana jin wani kalar birkitaccen tashin hankali yana dad a bijiro masa. A hankali ya matso kusa da ita wannan karon kam ihu ta yi jikinta ya na karkarwa idanunta jazir! Ta ce  na ce maka bana so ka tab a ni ko? Ba na son ganinka!!!
A hankali ya runtse idanunsa ya d auke numfashinsa na wasu y an sakanni sannan ya saki yana jin tashin hankalin da bai tab a jin kwatankwacinsa ba.
Juyawa ya yi da niyyar cin uwar matar nan ko ya samu ya huce ya hangota dai-dai tana fita daga gidan&
 Sannan na baka mintuna ashirin ka dawo da Yarinyar da ka yi Garkuwa da ita gidan iyayenta
Cike da rashin fahimta ya juyo yana kallonta dai-dai nan kiran Scorpion wanda yake ta yi masa babu k ak k autawa ya sake shigowa cikin wayarsa dan haka ya amsa yana shirin yin magana a fusace ya ji Scorpion d in ya ce masa  suna waje, yana son ganinsa. A k ule ya ce  ka tabbata ka
tare min matar da ta fito daga cikin gidanmu yanzunnan.
Yana gama fad in haka ya kashe wayar ya d ago zai yiwa Maama magana ya ji ta d aukesa da wani irin gigitaccen Mari.
Cikin mad aukakin b acin rai take magana tana kuka  idan suka tare maka ita kasheta itama zaka yi? Ma aruf ina yi maka magana amma still kana cin k asa? Ya kake so in yi? Ka san me nake ji kuwa? Da wanne kake so in ji? Ka san ya nake ji idan na tuna ni da kaina zan mik a ka ga hukuma kuwa?
Ta k arashe maganar tana mai durk ushewa a wajen ta sake fashewa da wani irin kuka.
Sosai ya dunk ule hannuwansa yana jin wani kalar zafiii a k irjinsa, tabbas idan bai sumar da matar da ta kawowa Maama zancensa ba yau to bai cika d a ba.
D urkusawa ya yi zai yi mata magana ya kai hannu zai tab a ta ta yi sauri ta buge masa hannun cikin zafi ta ce  na ce ka je ka kawo musu Yarinyarsu kafin a zo a tafi da kai
Tunda ta fara magana shi har ga Allah sai yanzu ya fahimci Dije take nufi.
Cikin matsananciyar kasalar da take taimakawa wajen danne b acin ransa ya ce  Maama ban yi garkuwa da kowa ba! Dije ce ta suma d azu kuma ba zan tab a iya tsallaketa in tafi in barta a wannan halin ba, shine na kaita Asibiti
Cikin tarar numfashinsa ta ce  k arya kake Ma aruf
Sai kuma ta yi shiruu kamar mai tunani kafin ta d ago ta kallesa ta ce  kar ka ce min Dije ta wannan Unguwar wannan layin itace Yarinyar da kake so za ka aura, dan ko da ace Allah ya dubeka ka tsallake ba a kasheka ba wallahi baza a tab a yard
Da wani irin mugun sauri ya mik e ya fita tun kafin Maama ta yi masa bakin da zai tarwatsa rayuwarsa.


Da sauri sannan zuciya tana cinsa ya fito daga cikin gidan, sai da ya kai kusan rabin gaban gidan ma tukunna idanunsa suka fara ganin dai-dai, a mugun cike taff ya ga layin amma chan nesa mutanen suka tsatstsaya, sai kuma ya ci karo da su Oscar sun yiwa matar nan cut 5 filla-filla abun tashin hankali!
Har da Grenade wanda shi shigowarsa k asar ma kenan ya zo wajensu Ma ah d in ya aikesa da ya dawo kuma yanzu ya kwasosu suka yo nan a motar dpo wadda suke shirin cinyewa k arfi da yaji.

Da k arfi ya runtse idanuwansa
ya kawar da kai da sauri ya juya da nufin komawa cikin gida ya ci karo da Inna da Minu suma sun kawo kai za su shiga cikin gidan nasu& .
Tunda Ma ah yake a rayuwarsa bai tab a jin an yi abu ya so a

15 / 33