ANA MALIK HAUSA NOVELS BY HUMAYRA BULAMA .doc

Author :  Humaira Bulama Category :  Top Hausa Novels 2025

Chapter   19 / 33

54K to 57K   out of 98.8K words


Dan haka ki saka a kanki aurenki da shi abunda Allah ya tsara ne ba wai ni ko a ta silar Kaka ba.

Sannan mutum yakan iya barin k auye ya dawo birni ko kuma na birni ya koma k auye wannan duk tsarin Allah ne kuma in har ya k addara to sai an yi ko da kuwa Sarki za ki aura to idan ya k addara a k auye za ki rayu sai fa kin rayu a k auyen nan.

Abu na k arshe kuma da nakeso ki saka a kanki shine da mai kud i da marar kud i da d an k auye da mai ilimi da marar ilimi duk Ubangiji ne ya yi su!
Bawa kuma bai Isa ya shallake k addararsa ba! Dan haka ki rungumi ambaton sunan Allah ki yi ta addu a na rantse miki
baza ki tab e ba!

Maganata ta gaba itace
tun ba yau ba na lura da take-taken Ma aruf wanda ba zan b oye miki ba har da hakan ya sanya na amincewa kawunki dan gara Yusufa sau dubu a kan Ma aruf wanda na san in har ya furta yana son ki to akwai matsala! Dan ni kad ai na san me na hanga.. Kuma Dije da in bar ki ki
auri Ma aruf ki yi rayuwa da shi gara ace babu ke!&
Ilai kuwa sai gashi yau ya zo neman aurenki a wajena yanzunnan muka rabu da shi.
A firgice duk suka d ago suna kallonsa.
Jinjina musu kai ya yi sannan ya ce  dan haka dan Allah ku bani had in kai a samu a yi auren nan Dije ta tafi ta tare a gidanta tun kafin ya b allo
mana wata b arnar&
D azu Minu har kuka ya yi mini a d aki dan Allah Halima ki taimaka ki taya ni fahimtar da shi, Mun yi magana da Yusufa ya ce in sha Allah zai san yadda zai yi ta ci gaba da karatu ko da hakan yana nufin ya mayar da ita madobi ko kura ta samu ta yi polytechnic dan shima dama kasuwancinsa a tsakankanin nan d in ne.
Ya ce min in sha Allah har aiki Dije sai ta yi amma yanzu a jira a fara yin auren dan idan ya tsame ta daga cikinsu yanzun tashi d aya to akwai matsala, itama amaryarsa yanzu haka waec take rubutawa Uwargidan kuma ita ce ta k i shiyasa, dan haka kinga ba ta da matsalar karatu sannan ya ce a gida daban zai ajjiyeta yanzun ma, ba zai had ata da su ba.
Ku kwantar da hankalinku ku taya ni kwantar mata a samu a yi abunnan mu rufawa junanmu asiri dan Allah.
Idan Allah ya yi za ta yi karatu ko a k ark ashin rami ta ke za ta yi& .
Na san na gaza miki a matsayin uba amma nima abubuwan sun fi k arfina ne, da ke da y an uwanki da mahaifiyarku na san duk na gaza muku, ku yi hak uri ba ni na zab i hakan ba a haka tawa kaddarar ta zo, ku yi hak uri dan Allah ku yafewa Mahaifinku Halima ki yafewa Mijinki ki taimaka ki ce wani abun ki bani amsa dan Allah ki yi min magana.
Ya k arashe maganar yana mai had e hannuwansa waje guda abun tausayi.

Zuciya da abunda take so gaba d aya tashi d aya???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? duk sai Inna ta yi sanyi.

Sai da ta saka hannu ta sauk e masa hannunsa daga alamar rok o da ya yi tukunna a hankali ta sauk e wata nannuyar ajiyar zuciya kafin ta ce  tun a ranar da ka ce ka bayar da ita ba ni da jaa a kan hakan Mallan dan na yarda ba zaka cutar da ita ba kuma na yarda da k addara, sannan kamar yadda ka fad a Allah shine ya yi kowa duk d aya muke babu wanda ya fi wani kuma kamar yadda ka fad a idan Allah ya yi zata yi karatun to fa ko a k ark ashin dutse take sai ta yi, idan kuma ya rubuta ba zata yi ba to ko a bakin makarantar gidanta yake ba zata yi ba!
Sannan ni kaina shaida ce kuma na yarda da k aunar da Yusufa yake yi mata.
Sannan rayuwarma da ake ta buri a kanta dududu nawa take? Mu da ma bamu san wa adin mu ba.
Dan haka na amince d ari bisa d ari yanzu haka ma da ka shigo ka ganmu nasiha nake yi mata.
Kuma maganr Ma aruf ba kai kad ai ba har ni nan kaina na fara fahimtar hakan, kuma har ga Allah ba k aramin dad i na ji ba da ya kasance sai da aka gama maganar aurenta tukunna shi ya zo daga baya, ka ga dole ya hak ura kenan.

Jinjina kai Mallan ya yi yana mai fitar da wani huci mai zafi, sai kuma ya d ago ya kalleta yana murmushi& .Ba k aramin dad i ya ji ba dan sai da ya yi hawayen farin ciki, sannan ya shiga jero mata albarka da addu o i masu tarin yawa& &

A tsari dama sai an d aura aure da sati d aya tukunna za su tare, dan yanzu haka ma ginin gidan nata inda za ta zauna flasta ake yi ba a kai ga yin ko fenti ba, shima kuma Mallan dama ya ce musu su bashi sati d aya ya yi siyayya. Ya san dan sati d aya dai Kaka zata yi hak uri ta k ara musu, za a sha daru kam amma ya san za ta k ara musu kuma ma Mahaifiyar Yusufa ta ce tun ana i saura kwana biyar d aukar amaryar za ta taho dan haka ya san ba shi da matsala tunda ba laifi suna shiri da matar idan ta ga dama.

Adduarsa d aya Allah ya basu zaman lafiya Allah ya bawa Dije farin ciki ya had ata da marar adadin alkhairi.


Ba laifi Inna ta d an sake dan sai da suka gama lissafin komai har aka kusa shiga sallah, suka shirya akan gobe zata je ta siyo komai na kayan d aki tukunna ya mik e ya nufi k ofa yana mai ci gaba da saka musu albarka, sosai ya ji kaso hamsin na damuwar da yake a ciki ya yaye da ya samu Inna ta kulashi kuma ta bashi goyon baya.

Ta so ta yi masa maganar k in d aukar wayarta da replying message d inta da yayi kuma mai ya sa ya turo mata Asabe amma kawai sai ta basar dan kwana biyun nan komai ya sure mata a ka
ga rashe-rashen da aka yi sun sake sanyayata& ..


D azu da Mallan ya zo shiga d akin Inna bayan ya shiga sai ya mayar da k ofar ya rufe, wannan dalili ya sanya har ya taso ya iso bakin k ofar ya sa hannu ya bud e sam Asabe da Kaka basu san ya k araso ba.

A mugun zabure suka d an matsa da suka ga an bud e k ofar sai kuma suka d ago a tare wanda hakan ya janyo suka k ume k ummm!!!

A gigice Kaka take sosa wajen tana kallonsa yayinda Asabe ta kawar da kanta gefe ta shiga kame-kame.
Yatsine fuska ya yi cike da kalar tausayi irin mai yasa kike haka d innen yana daff da yin magana cike da borin kunya ta ce  dan ubanka to ba lab e muka yi ba!

Ya riga ya makara sosai dan gashi ma ya ji har wani ya fara kiran sallah dan haka ya wuce da sauri yana mai cewa  ni ban ce komai ba Kaka, bari in tafi masallaci na makara.


Yana fita Dije ta fashe da wani irin kuka, sosai Inna take jin tausayinta kwana biyun nan dan haka ta janyota jikinta ta rungume ta shiga lallashinta..wanda sai da ta yi da gaske tukunna aka samu ta yi shiru.
Wai yau ita Dije ce zata auri Yusufa mutumin da ko muryarsa ba ta son ji!
Ai kuwa d an halak d in nata a take kiran wayarsa ya shigo wayar Inna dan ita bata da waya.
D auka Inna ta yi
suka gaisa daga nan ya fara kame-kame, murmushin da ya fi kuka ciwo ta yi kawai ta mik awa Dije wayar ta mik e ta fita dan ta je ta yo alwallah, ai kuwa ko gama fita ba ta yi ba Dijen ta kashe wayar kamar yadda ta yi jiya da shekaran jiya, Allah ya sota Innar ba ta ganta ba ta k arasa fita daga cikin d akin abunta.

Bayan fitar Inna Yusufa ya kira ya fi sau goma amma ta k i d agawa kuma ta goge misscalls d in k arshema kashe wayar ta yi gaba d aya da Innar ta dawo ta ce mata chaji ne babu.

Bayan ta je ta yi alwallah ta dawo, a hankali ta koma ta kwanta ta lumshe idanunta a take lissafin Ma ah ya fad o mata& . Mugu kawai! Ta fad i hakan a ranta tana shafa hannunta dai-dai inda ya tab a rik ewa kwanaki wanda sai da wajen ya yi kwana uku ciff yana yi mata zafi-zafi!!&
 Haka kurum na aure shi ya kakkarya ni! Mtswwww ta Yaya ma zan auri wannan tshohon, kuma d an daba
Allah ya Isa ma ni da ya ce yana so na, marar kunya ko a gidan wa aka ce masa mutum yana zuwa neman aure da kansa oho masa!!!!
Ta yi maganar duk ita kad ai a cikin ranta. A hankali kwakwalwarta ta shiga zoomo mata ranar nan ita da shi a asibiti!
 Ba zan tab a cutar da ke ba Khadijah!!
Maganarsa ta dawo mata tarr kamar yanzun yake fad a!
Da k arfi ta runtse idanunta sakamokon yadda ta ji ilahirin jikinta ya amsa.
A hankali ta shiga sauk e ajiyar zuciya sai kuma ta yi tsaki ta ce  cutarwa kuma ta nawa!!mugu kawai, har da had in guiwarka ne ya sanya za a yi min aure
Daga haka ta runtse idanunta ta shiga neman bacci afujajan tana mai sake danna tsana da kyamar Ma ah a cikin zuciyarta.
Tausayin Mama ne ya fad o mata dan ko d azu sai ta ji ana fad ar halin da take ciki, a hankali ta ce  Allah ya baki lafiya, Albasa ba ta yi halin ruwa ba.
Dan Mama tana da kirki kuma tana sonta, tun bata kai haka ba in dai suka had u ta gaisheta sai ta bata alawa ko kud i, tun ba ta karb a har ta zo ta fara karb a. Matar tana da kyauta ba ita kad ai ba hatta Yaran layin haka nan duk take yi musu alkhairi.


BULAMA
'?
0806 402 1951
ANA MALIK!!
Book 01.
Page 16.

Humairah Bulama.
Mikiya writers Association.

****************
A rikice sannan hankali a masifar tashe Gimbiya Sumayya ta shiga sashen Mahaifiyarta gudu-gudu sauri-sauri.
A babban parlournta inda ta saba zama ta amshi gaisuwar kowa ta tadda ita&
Yadda take tafiya kamar zata kifa jikinta yana wani irin masifar karkarwa ne ya sanya Mahaifiyar tata ta mik e tsaye tun kafin ta k araso ta ce  Gimbiya Sumayya kanki akwai motsi ne??? Kalli yadda kike tafiya kamar baki san matsayinki ba? .

A take duk bayin da suka rakota waenda suka sha gudu garin binta suka zube k asa suka sunkuyar da kawunansu k as, haka suma ragowar bayin da suka tadda a wajen (duk suka sussunkuyar da kawunansu k asa)&

Karkarwa take yi jikinta yana kyarma har yanzu ta gagara furta komai.
Da kyar ta iya cewa  Gimbiya Mariya..
Tana magana tana nuna waje da hannunta ba tare da ta kalli wajen ba, ta d aura da cewa  ta tara mutane a babban filin rabo wai za a jefe Gimbiya Sakina! .

Wani irin mahaukacin bugawa k irjin Gimbiya Mai Babban d aki ya yi wanda hakan har sai da ya sanya ta durk usa ta kai k asa tsabar yadda abun ya daketa.

A take duk bayin suka sake yin k asa da kawunansu yayinda hadimanta guda biyu makusantanta suka k arasa da sauri suka d agota.
D ayar ta fara k ak arin zaunar da ita yayinda d ayar ta shiga yi mata fifita tare da fad in maganganu masu sanyaya ruhi.
Mik ewa ta yi kawai ta wucesu ta zo ta wuce Sumayyar hankalinta a masifar tashe& . Tabbas yau kam sai dai a tsireta amma sai ta nunawa Mariya matsayinta! Yo hauka ake yi? Sakina fa y ar Sarki ce jikar Sarki gaba da baya da zata ce zata jefeta tana shaye-shaye ne?
Ta yaya ma zata zuba ido ta bari a jefe mata y arta kamar wata baiwa? Wanne irin sharri ne haka aka yi mata da har zai sanya wachchar mahaukaciyar ta yi yunk urin jefeta? & ..Tana waennan lissafe-lissafen ta zo ta wuce Sumayya fuuu kamar zata tashi sama.
A take bayinta suka mara mata baya ita kuma Sumayya wadda ta sulale a wajen nata suka durk usa suna kururuwa gashi basu da ikon tab ata.

A chaan babban filin rabo&
Tun kafin ta k arasa ta hango Gimbiya Sakina d aure jikin wata k atuwar bishiya jikinta babu komai sai doguwar shimi
har k asa fara tas dan hatta d ankwali babu a kanta sannan duk wani abun ado kama daga y an kunne zobuna suma duk babu gasunan ajjiye gefe guda tare da kayanta yashe a gefe alamun yanzun ne aka cire mata.

Dishi-dishi Gimbiya Mai Babban d aki ta fara gani tsabar mad aukakin tashin hankali da b acin ran da ya sake rufe ta!
 Wai yanzu y arta ce d aure jikin wannan k ask antacciyyar bishiyar a gaban bayi haka tsaye chak a kan k afafuwansu? Sannan on top of everything wai shirin jefeta ma ake yi!?
Tana cikin wannan tunanin ta k arasa inda Gimbiya Mariya take tsaye tana zuwa bata yi wata-wata ba ta sa hannu ta juyo da ita ta d auketa da wani irin mahaukacin Marin da ya sanya kowa durk usawa a wajen kawunansu a k asa suka shiga cewa  tuba take yi! Uwar sarki matar sarki a yi mata aikin gafara hannunta ne ya sub uce! .

A tsawace ta juyo ta ce  ku rufewa mutane Baki!
Sai kuma ta juya ta kalleta ta ce  Garr nake ganinta kuma ban tuba ba dan ubanki!
Rikicewa wajen ya yi yayinda wasu a cikin mutanen wajen suka fashe da kukan an zagi uwar sarki.

Cikin b acin rai ta ce  wasa ya wuce wasa amma ban da tsole idon uwar Miji da tab arya!
Dan ni duk haukan nan da kike yi tun daga ranar da aka nad a Yareema a matsayin Yareema har ya kawo Sarki wallahi a matsayin wasan Yara na d aukesa, dak ik iya wadda bata san inda yake yi mata ciwo ba!
A hankali wani Bafade ya k araso wajen shi da waensu sojoji guda biyu ya ce  Gimbiya Mai Babban d aki ki gafarceni, amma maganganunki sun yi tsauri ga Gimbiya Uw& .
Tass!! Ta d aukesa da Mari ta ce  ku kuke ganinta a matsayin Gimbiya Uwar Sarki ni har gobe a matsayin k ask antacciya y ar talakawa nake kallonta! .

D iff! Haka wajen ya yi ba ka jin komai sai sheshshek ar kuka, sai kuma suka ci gaba da cewa  Allah ya huci zuciyar Gimbiya Uwar kowa
Wata nannuyar ajiyar zuciya Gimbiya Mariya ta sauk e, tabbas sai ta gasa mata aya a tafin hannun da ya mareta, amma ba yanzu ba zata samu lokacin ta ne. Dan haka kawai sai ta juya ta kalli jama ar da ta tara a wajen ta ce  Bismillah, za ku iya fara aikin lada
Ta yi maganar ko kallon gimbiya Mai Babban d aki bata yi ba.
Dai-dai nan Nuraddeen ya k araso wajen yana wani bubbud awa&

Nufar bishiyar Gimbiya Uwar Marayu ta yi yunk urin yi amma Sojojin nan suka hanata shallake jan layin dake zagaye da bishiyar ballanta ta k arasa ga Sakina wadda duk dauriyarta zuwa yanzu ta fara kuka.

Cike da Isa da izza Nuradden ya k arasa inda take ya ce  kin kuwa san me ta yi? Ko dai bakinku d aya?
Ki rufawa kan ki asiri ki bar nan tun kafin a had a da ke!

Cikin fushi ta juyo za ta d aukesa da Mari shima amma sai ya yi saurin rik e hannuwan nata cikin b acin rai ya ce  kar ki kuskura tukunna ya yarfe hannun nata da k arfi dan har sai da ta tafi ta yi tangal-tangal kamar za ta fad i kafin ta d ago ta kafesa da idanu cike da tsananin mamaki da b acin rai tana masa kallon irin  kana hauka ne? D innan.
Shima d in ita ya tsare da dogayen idanuwansa cike da kwarin guiwa ba tare da wani d ar-d ar ba.
Ba ta shi take yi ba yanzun dan haka kawai sai ta zagayesa ta sake nufar wajen y artata, amma sai ya kalli tulin Sojoji da Dogaran da suke tsaye a wajen ya ce musu  ku d auketaa a nan! .

Ba su yi yadda ya ce ba sai da Gimbiya Mariya ta ce musu  ku d auketa aka ce!!!
Tukunna wasu Sojoji guda biyu mata na masarautar suka nufeta suna zuwa d ayar ta d urkusa ta shiga k ok arin d aukarta dan irin jibga-jibgan matan nan ne sojojin.

 Hattara daiiii
Muryar wani Dogari wanda suka taho tare da Wambai da Waziri ta karad e wajen
Tsayawa kowa ya yi yana kallonsu, hankali ya koma kansu& ..
Suna k arasowa wajen Wambai ya ce  kunce ta!

Jiki na rawa Dogarin nan ya nufi wajen amma sai matar (Gimbiya Mariya) ta daka masa tsawa  idan ka tsallake jan layin nan to ba zaka fito ba sai dai a fitar da gawarka dan tare za a jefe

19 / 33