ANA MALIK HAUSA NOVELS BY HUMAYRA BULAMA .doc

Author :  Humaira Bulama Category :  Top Hausa Novels 2025

Chapter   8 / 33

21K to 24K   out of 98.8K words

wani k ulli a hannunta ta ce  ungo, ki bi a hankali dai kar k aik ayi ya koma kan mashek iya, kin dai rik e yadda za ki yi ko?
 Eh Dije ta ce tana k ok arin bud ewa. Da sauri Sumayya ta rik e hannunta cikin zaro ido ta ce  rufa mana asiri, so kike ki saka mu rawar disko yau kenan, sai fa kin je kusa da shi tukunna, ko har kin manta yadda ake amfani da ita?.
 Tam Dije ta ce tana mai juyawa ta nemi wajen b oyo ta b oye tukunna ta kalleta ta ce  na gode, ya kike ya hanya?

Dariya Sumayya ta yi sannan ta ce  Sai yanzu kika ganni kenan, lafiya lau nake gida shima lafiya, bari in je in huta, yanzunnan fa muka dawo ko zama ban yi ba na taho kawo miki. Dan Allah Dije kar sunana ya fito.

Cike da assurance ta ce mata  Baki fa da matsala kar ki damu ai ba zan bari ma ya ganni ba.

 To Allah ya sa
Sumayya ta ce.
Sallama ta yi mata daga nan suka fito tare ta yi mata rakiya har bakin soron gidan, Sumayyan tana ta nanata mata cewa  dan Allah kar ta bari sunanta ya fito har sai da Dije ta danna mata ashar tukunna ta yi shiru.

Juyawa ta yi ta koma cikin gidan nasu ta wuce kitchen a zuciyarta tana ta adduar Allah ya kawo abinda zai sa a aiketa.

Aike bai taso ba sai wajajen k arfe hud u na yamma Inna ta aiketa ta je ta karb o mata kud in adashen ta a wajen Rabi dillaliya wadda ta kira wayar Innar ta sanar mata kud i sun had u.

BULAMA
'?
0806 402 1951
ANA MALIK!!
Book 01.
Page 06.

Humairah Bulama.
Mikiya writers Association.

Tun kafin Inna ta dire aya Dije ta mik e zunbur! Tana mai cewa Innar  to
Cikin d an fushi Inna ta ce  wai meye ne yake damunki tun safe sai kace mai tsutsu a d uwawu?
Sunkuyar da kanta ta yi tana d an sosa k eya tana murmushin yak e.
Inna ta jima tana k are mata kallo kafin chaan ta magantu ta ce
 Ki wuce ki tafi ki yi sauri sannan kar ki bi ta inda ya ke!
Dumm!! Gaban Dije ya yanke ya fad i dan ta fahimci wa Innar ta ke nufi gashi ita kuma shine ma babban dalilin da ya sanya take ta addu ar Allah ya sa a aiketan.
Tana shirin nufar wajen kayanta Inna ta ce  ta saka uniform d inta kawai ta yi alwalla ta d auki jakarta daga nan kawai ta wuce islamiyya dan ta san idan ta ce sai ta je ta dawo tukunna za ta shirya to za ta makara ne.
Jinjina kai ta yi ta ce  to
Daga nan ta hau shiri& .Allah ya bata sa a ta faki idon Inna ta d auko k ullin ta jefa a cikin jakar makarantar islamiyyarta ta ajjiye ta je ta yi alwalla ta dawo tukunna ta d auki jakar tana mai cewa  Inna na tafi
 Allah ya kiyaye ki lura sosai saura kuma ki bari a sace min kud i a makarantar .
Ita dai da  to kawai take ta bin Innaa har ta fice daga gidan zuciyarta fess.
Dayake ta san inda ta nufa ko hanyar gidan su Sumayya ba ta kalla ba ta wuce inda ta saka gaba.

Dukda ta kasance mace mai kazar-kazar amma sam idan tana tafiya ba ta iya sauri ba shiyasa ta ji gaba d aya ta k agu ta matsu ta k arasa filin ball d in da ta tasarma.
Addu arta d aya Allah dai ya sa suna wajen dan ta san lokuta da dama su kan je wajen tun kafin bayan la asar d in.

Tafiyar kusan mintuna bakwai ce ta kaita tafkeken filin ball d in& ..tun da ta tunkaro wajen ta hango Oscar shi da Scorpion suna zagaye wajen yayinda Ma a ya ke tsaye ya yi irin tsayuwarsa ta sojoji kamar kullum da whistle a bakinsa yana kallonsu.
Sai yanzu da ta iso wajen tukunna lissafinta ya bata  ta yaya za ta je ta hura masa kuma har ta juya ta gudu ba tare da an ganta ba? Dan sholl wajen yake babu kowa sai su uku kacal gashi wajen babba.

K uruciya da k udirin d aukar fansar d aureta da kukan da ya saka ta ne suka tunzurata tare da bata amannar ta tunkare sa kawai komai ta fanjama fanjam!

Luckily, su Oscar gaba suke kallo suna ta gudu basu kai ga kaiwa angle d in da za su iya ganinta ba shi kuma dama ya juya baya su yake kallo.
Cikin sassarfa at the same time tana mai d auko k ullin dake a cikin jakarta, a haka ta k arasa inda yake dai dai ta gama zarowa ta ware da sauri ta d an durk usa ta hura masa a sangalalin k afafuwansa da yake kayan ball ne a jikinsa sai kuma ta mike ta hura masa a bayansa da wuyansa daga nan ta juya da niyyar d iba da gudu ta bar wajen ta ji gamm!! An ruk o hannunta da mugun k arfi!.

Yadda k irjinta ya buga ita kanta ta yi tunanin zuciyarta ta tsage ne. Da mugun sauri ta juyo dan a yadda yake bai ci a ce har ya juyo ya rik eta hakan ba.
Da mamaki take kallon sa tana kallon su Oscar waenda sam ba ta ma san lokacin da suka k araso wajen ba.
Suma su duka ukun ita suke kallo dan haka aka tsaya ana y ar kallon kallo.

Tunda Dije take ba ta tab a jin bakinta ya mutu murus ta rasa abin fad a ba sai yau, wani irin kallo ta ga Ma a yana yi mata wanda yake sanyata jin wani irin matsanancin tsoro dan bai saba yi mata irinsa ba.
Yunk urawa Oscar ya yi zai yi magana da sauri ya d aga masa yatsunsa biyu na tsakiya sai kuma ya yi masa alamar su tafi.
A take babu musu suka juya suka ci gaba da abinda suka baro ba tare da sun sake ko
da kallonsu ne ba.

Tsoro da firgici had e da dana sani ne suka lullub e Dije a take ta sake sunkuyar da kanta k asa ta ci gaba da k ok arin kwace hannunta wanda ita kanta ta san it s impossible dan wani irin rik o ya yi mata kamar zai karyata.

Kusan minti d aya tana abu d aya gashi a tsaye kamar wani dutse ko motsi bai fara ba ballantana rawar diskon da take tunanin zai yi, balle har ta samu ta gudu.
A hankali cikin raunin da ba d abi arta ba ta d ago kyawawan fararen idanuwanta da suka d an fara kad awa zuwa jaaa ta zuba masa da kyar ta aro jarumta ta furta  mallan ka cika mini hannu

Kallonta yake yi bai kuma cikatan ba kamar yadda ta so, a hankali ta ga jajajajaa yana maye gurbin farin cikin idanuwansa, sai kuma gumi ya fara tsattsafo masa a take.
Sai da ya lumshe idanuwansa tukunna ya bud e sannan ya juya ya kalli ledar da ta mak ale a k afar bencin da ke a gefensa iska tana kad ata tana shirin barin wajen, d an k urawa ledar ido ya yi wanda hakan ya sanya ita ma Dije ta kalli wajen, a take kuwa gabanta ya yanke ya fad i dan ta yi tunanin da ta gama hura masa ta yar tuntuni iska ta kwasa ta yi gaba da ita.

Dakewa ta yi ta sake aro jarumta ta ce masa  mallan na ce ka cika mini hannu ko???
Cike d an zafi.

Da mamaki ya d ago yana kallon Yarinyar kafin da kyar ya magantu kamar an fisgi maganar daga bakinsa ya ce  me na yi miki ki ka zuba mini karara??
Already jikinsa ya riga ya zama weak dauriya ce kawai yake yi amma masifaffiyar azabar k aik ayin da yake ji ba zai fad u ba! Gashi shi kansa by now so yake ya sakin mata hannu amma dukda hakan da kuma kokawar da take yi ta gagara kwace hannun nata.
Cike da tsiwa da fushi dan zuwa yanzu ya gama k ular da ita ta ce  hala kana da aljanu ko? B& 
Maganartata ce ta mak ale a take ta kasa k arasa abunda ta d ebo za ta fad a dan haka ta kawar da kanta tana guna guni, sosai ya tsareta da idanu gangar jikinsa tana karb ar azabar k aik ayin da bai tab a tunanin tana existing a duniya ba!
Mamakin audacity d in Yarinyar kawai yake yi dukda kuwa ya san tsiwa rashin tsoro da fad a d abi arta ce amma sam bai yi tunanin zata iya zuwa har nan ta d auki fansar abinda ya yi mata ba dan ba shi da tantama abunda ta yi masa yau d in yana da alak a da tare mata hanyar da ya yi kwanaki shidda da suka wuce!

A b angaren Dije kuwa bayan tsoron Inna da Kunyar Ya Muhammad da shakkar Mallan ba ta tab a jin wani abu makamancin hakan ba ga wani d an Adam sai a yau! Dan sosai Ma a yake bata mamaki da kuma tsoro ita kam a ranta har ma ta fara tunanin anya kuwa ba al jani bane ba! Saboda kararar k auyen su Sumayya daban take, duk ranar da ta je k auye ta taho da ita wallahi ko waye idan suka zubawa sai ya kwana yana hauka amma gashi da ikon Allah ko
motsi Ma a bai yi ba sai dai fa daga ganin yanayinsa ta san yana kan karb ar azaba& ..


Wani mahaukacin k aik ayi da ya mintsine shi ne ya sanya bai san lokacin da ya damk e mata hannu more than ruk on da ya yi mata da farko ba.

Zabura ta yi ta sake k aimi wajen k ok arin kwacewa a lokacin guda kuma ta na jin wani irin tuk uk in bak in ciki yana taso mata ga zafin da take ji, ba ta san lokacin da ta doka wani uban tsaki ba ta ce  mugu d an daba kawai!
Da sauri ya d ago ya kalleta cikin wani irin yanayin da ta gagara fassarawa.
A hankali ta ji ya sakin mata hannu ya juya mata baya ba tare da ya sake cewa uffan ba.
Shiruu ta yi kamar kuma wadda ta tuna wani abun sai ta juya da sauri ta bar wajen cikin sassarfa& & &


Har ta je gidan Rabi a ta karb a kud i daga nan ta k arasa makaranta zuciyarta fal sak e-sak e, ganin tunanin abun da ya faru yana neman damalmala mata lissafi ne ya sanya ta kawar da duk wani abun da ya shafe sa ta shiga sabgogin gabanta, alk awari d aya ta yiwa kanta shine ba zata sake tunkarar Ma a ba, hannunta da ya rik e take tunanin sake musguna masa shima ta barshi kawai Allah ya Isar mata, dan ta lura al amarin sa ya fi k arfinta sai yanzu ta ga gaskiyar su Inna da suke ta cewa ta guje masa shi d in ba tsaran yinta bane ba.

Ko da Sumayya ta tambayeta  ya ake ciki? Bata ce mata komai ba kawai sai ta sako wani zancen, fahimtar da Summayar ta yi Dijen ba ta son yin maganar ne ya sanya itama ba ta sake cewa komai ba.

& & ..

A bakin k ofar gidansu ta tarar da Ya Muhammad a tsaye yana jiranta! Haka kurum tana ganinsa dama ta ji gabanta ya yanke ya fad i. Da sauri ya taso daga kan d an dakalin sokaway d in da ya ke kai ya k araso inda ta ke yana zuwa ya kama hannunta ya jaa suka wuce gidan sai da suka kai bayan layinsu tukunna ya cikata. Daga yanayin yadda ta ji jikinsa yana karkarwa tun lokacin da ya ruk o ta dama ta san a rina! Ai kuwa yana fara magana ta fahimci yanayin da yake a ciki. Cikin inda inda ya ce  Dije mai yasa bbaa kkya ji neeee?
Sai kuma ya yi shiruu ya dafe goshinsa bakinsa ya shiga karkarwa.
Kuka ta fashe da shi a take dan wannan yanayi na Ya Muhammad shine abunda take matuk ar jin tsoro da gudu.
 Shhhhhh ya ce da ita kamar zai yi magana sai kuma ya yi shiru sakamokon mak alewar da ya ji maganar ta yi. A hankali da kyar kamar an fisgi maganar daga cikin bakinsa ya ce  kar ki shiga gida yanzu
Har ya juya kamar zai tafi sai kuma ya dawo da sauri ya damk i hannuwanta duka biyu da sauri sannan da k arfi ya ce  Dddjee mai yyyasa ba kya ji ne?
Fashewa ta yi da kuka sosai ta ce  dan Allah Ya Muhammad ka yi hak uri& 
 Shhhh ya sake cewa da ita cikin katseta sannan ya ce  ya zaki je wajen Ma a da kanki??
Sosai gabanta ya yanke ya fad i tana shirin yin magana ta ga ya fara karkarwa sai kuma ya fara kai mata duka, da sauri ta matsa Allah ya taimaketa bai sameta ba ya samu bango, cikin k ank anin lokaci kafin ta juyo ya zube a wajen sumamme.
Zuwa lokacin dama hankalin mutane ya d an karkato zuwa garesu dan haka aka nufesu& & .


Tsaye Kaka take a tsakar gidan hannunta d aure da bandeji an sak ala mata ta wuya ga Asabe a gefenta Ya Aminu a kusa da Inna yana huci sai Mallan shima a tsaye a gefen Kaka ta d ayan b angaren.
Ragowar mutanen gidan kuwa kowa ta turo k ofa ammafa da za a yi rashin sa a wani ya tura k ofar d akin d aya daga cikinsu to da tsaff zai yi tafiyar ruwa da duk ahalin d akin saboda yadda suka kafa kunne suka mammanne a jikin k ofofin d akunan nasu suna d aukar rahota.

Cike da d acin zuciya Ya Aminu ya ce  har ga Allah abunda ake yi mana a gidan nan ya Isa haka! Hak urina ya fara k arewa za fa a yita babu kyau wallah!
Ya k arashe maganar cikin d aga murya.
Da sauri Mallan ya daka masa tsawa ya ce  wa kake d agawa murya? Sa ar ka ce ita

Wani Irin murmushin takaici Minu ya yi kafin ya ce  ni iyaka d aga murya kawai na yi amma gashi ka ji haushi! Shin ni kuma ba ka ji abunda ta gayawa tawa uwar ba?
Cikin zafin nama Mallan ya d aukesa da mari mai tsananin sauti&
Kafin ya yi magana Kaka ta rigashi ta hanyar cewa  ai ka ga irinta nan! Shiyasa na ce waennan Yaran ba jinina bane ba ba y ay anka bane su tun wuri ta je ta nemo ubansu kafin su kaimu lahira.
A mugun fusace Aminu ya yi kanta kamar zai rufeta da duka! Kuma da gaske da niyyar shak etan ya nufeta Allah ya taimaka Mallan ya shiga tsakani.
Fashewa da kuka Kaka ta yi ta ce  wallahi na gama zama gida d aya da shegun y ay an nan, ka duba ka gani yanzu fa inda ace baka nan da rufeni fa zai yi da duka! Ace Yara daga mahaukaci sai marar mutunci sai y ar iska sannan a haka a ce wai jininka ne su?? Wallahi da sake.
Da sauri Mallan wanda ya gama dakawa Minu tsawa akan ya nutsu ya juyo ya ce  Kaka ba fa Halima kad ai kike aibantawa a nan ba har da ni tunda y ay anane, kuma maganar jini ma ba ta taso ba dan na riga na san nawa ne su d in dan haka ki ma daina wannan maganar dan Allah..Dije kuma babu inda za ta je, na hukuntata tun a ranar sannan yanzu ma zan sake hukuntata amma ba zan kori y a ta mace budurwa daga gidana ba ki yi hak uri dan Allah kar ki kaini wuta hakkine a kaina in kula in saka ido a kanta in bata ingantacciyar tarbiyya, yanzu idan na koreta Ina za ta je??

Dai dai nan aka shigo da Ya Muhammad hankali a tashe Dije a bayansu tana wani irin kuka kamar ranta zai fita.

**************
D aki ne Babba sosai wanda a k alla fad insa zai kai taku 40 tsayinsa shima haka.
Kallo d aya za ka yiwa d akin ka fahimci na y an Sarauta ne sakamokon adon da pop da bangon d akin har ma da k ofofin da windunan d akin suka sha na asalin gold da azurfa abun har abun tsoro dan kamar ba a san darajar abun da aka yi adon da shi ba.
Kujeru ne na asalin Royal waenda suka amsa sunansu Royal da wata tafkekiyar tv a ajjiye gefe guda. Sai wani tangamemen gado (king size) da wardrobe d insa da madubi da drawer da side drawers suma a gefe guda.
Hatta standing acn dake a d akin itama adon ta tsarin yanayin d akin ne& ..

Dogo ne fari tass wanda kallo d aya za ka yi masa ka san cewa shi d in kyakkyawa ne ajin farko, sumar kanshi ba lallausa bace ba yanayin ta irinta Hausawanmu ce, bai cika k iba ba sannan ba siriri bane ba. Yana sanye da wata fara k all d in alkyabba da dogon wando shima fari, k irjin akyabbar a bud e kuma babu komai a ciki wanda hakan ya bawa faffad an k irjinsa damar baiyyana wanda kana ganin
yanayin jikin nasa za ka san ya saba ziyartar gym.
A kwance yake (kwanciyar rigingine) a kan gadon yayinda sangalalin k afufuwansa suke a kan

8 / 33