ANA MALIK HAUSA NOVELS BY HUMAYRA BULAMA .doc

Author :  Humaira Bulama Category :  Top Hausa Novels 2025

Chapter   18 / 33

51K to 54K   out of 98.8K words

ta san itace bangon su shiyasa yanzu da ta gaji ta kai mak ura kawai take so ta yi
musu kwab d aya dan ta
san idan ta kori Halima to kamar ta kore y ay an ne dan binta za su yi su je chan su shiga duniya, to amma kuma
gashi k iri-k iri ta yi falling flat akan face d inta dan hatta kawu Isa bataga alamun zai goya mata baya ba shi da ba wani shiri suke yi da Innar ba, kar ma matarsa ta ji labari.


Sosai kan Mallan ya d auki zafi kwana biyun nan, dan Kaka ta kunna masa wuta ba kad an ba.
Bai yi karatu ba ko ajin boko bai tab a shiga ba amma zai iya cewa shine ya sakawa Dije ak idar son karatu a cikin ranta tun tana y ar k ank anuwarta amma gashi yanzu k iri-k iri yana ji yana gani haka nan zai d auketa ya kaita k auye inda ya san in dai ta je to tabbas ta yi bye-bye da karatu kenan.
Dan ma dai Yusufa yana da addini kuma yana da k ok arin nema sannan Allah ya rufa asiri ya san ci da sha da sutura kam ba za ta rasa su ba in sha Allah.


An samu wani Babba a garin ya yiwa mutanen da abun ya shafa alkhairi sosai wanda rabin su duk k in karb ar uban kud ad en suka yi, dan washegarin ranar aka zo aka yi musu jaje aka rarraba musu kud ad e wai su gyara gidajensu, sanin da waensu suka yi kud in daga d aya daga cikin iyayen gidan Ma a d in ya fito dan a rufe musu Baki kuma ya gyara siyasarsa ya sanya suka k i karb a suka ce basa so sai an bi musu hakk insu yayinda ragowar suka amshe a cewarsu raba arne da makami ibada ne.

Suna ta zuba ido su ji an cafko su Ma ah da ikon Allah sai ga kira daga ofishin y an sanda.
Limamin layi (Mallan) da mai Unguwa sai wasu dattawa guda uku ne suka wakilci kiran.
Ko da suka je sai da suka kusan yin ihu tsabar takaici da bak in ciki da mamaki dan k iri-k iri ake so a yi musu tsakani kawai da su Ma a a barsu abinda suka yi ya tafi a banza, wai  ai shima an k ona masa gida kuma an kashe masa Aboki sannan yanzu haka Mahaifiyarsa tana kwance.
Kamar ma laifin akan samarin layin ake so a d aura wai  ai sune suka fara tayar da husuma Sannan aka ce wai  su Ma ah ba su kashe kowa ba wasu y an daba ne da ba a san daga ina suka zo ba (Yaran Scorpion) suka cinnawa gidajen wuta suka yi b arna&
Daga k arshe dai Mallan ne kawai ya iya tsayawa ya ji k arshen zancen ta inda aka yi musu gargard in  babu su babu shi kowa ya yi harkar sa dan ragowar mutanen duk fushi suka yi suka fita, saboda a ganinsu hakan straight up rainin wayo ne kawai! Duba da yadda ko d an Yaro mai tafiyar tatata idan ka tambaya a layin ya san waye Ma ah to su kuma y an sanda sun ce su kawo shedar wanda ya tab a kashewa za a d auki mataki sun kasa, dan wannan Yaron ma da ya yiwa juyin 360 da wuk a a ciki an ci sa a da Ikon Allah har yanzu yana icu kuma an ce ba shi bane ba Oscar ne ya yi aikin, wannan dalilin ya sanya kawai mutanen suka yi fushi suka fice daga ofishin y an sandan ransu a masifar b ace& & .

Kamar yadda aka yi musu haka shima Ma ah aka zaunar da shi aka yi masa tsakani da y an layin
daga nan magana ta mutu da ikon Allah kamar ba a yi komai ba.


Jikin Mama babu kyau sam! Dan ta kwanta mummunar jinya kwarai, yanzu haka shirye-shiryen fitar da ita waje ake yi dan jinyar ba zata yiu a nan ba, wanda iyayen gidan Ma a d in ne suka d auki nauyi..
He looks calm idan ka kallesa a ido amma fa shi kad ai ya san me yake going through deep down, da mugun kyar yake iya rik e kansa wanda yake jin kamar ba zai iya ci gaba da k ok arin holding kansa together ba dan tabbas jarumtarsa ta kusa k arewa gashi idan ya tuna shine musabbabin halin da take a ciki yanzun sai ya ji kamar ya binne kansa.


Tun ranar da Mallan ya dawo daga asibiti ya fahimci Inna ta d au zafi, dan bai had u da ita ba sai ranar da ya sanar da d aurin auren Dije tun daga nan kuwa bai sake sakata (Inna) a idanunsa ba, dan ko jiya da ya shiga d akinta ma b uya ta yi a cikin bargo gaba d aya ta k i yarda su had u, ya san dai ya ci galaba a kanta tunda ya had ata da mai unguwa ya kirata a waya ya hanata tafiya amma fa fushin da take yi da shi sosai yake tab a shi& ..


Dukda cewa y an layin sun san baya nan hakan bai sa kowa ya hau masa sahun sallarsu ba a cikin mutane uku dattawa da suka riga su zuwa masallacin, kamar had in baki.
Ana cikin gabatar da sallar Magrib an kusa tafiya ruku un farko kenan kawai suka shigo shi da Scorpion da Oscar da wasu guda biyu daban waenda yanayinsu har ya ci uwar na su Oscarn.
Daidaita sahu suka yi suka kabbara sallah cikin nutsuwa kamar ba su ba.
Kafin a idar kuwa masallacin ya cika mak il, kowa idan ya shigo ya gansu sai ya shiga shock tukunna kafin ya yi sauri ya tayar da ik ama.

Ana idarwa aka fara kallon-kallo, da k us-k us& .waensu su ce a rufar musu wasu su ce a barsu kawai da Allah dan ko dawowa daga jimamin b arnar da suka yi ba ayi ba gashi y an sanda da kansu sun yi musu tsakani.

Farar shadda ce k all a jikinsa yau abunda mutane da yawa za su ce basu tab a ganinsa da shi ba wato manyan kaya, kamar ba shi ba ta baya idan bai juyo ba sai dai yana juyowa zaka fahimci waye shi d in gashi yau idanunsa sun yi wani irin dafewa alamun ransa a b ace yake kuma yana cikin damuwa sannan ya tamke fuska kamar wanda aka aikowa da sak on mutuwa.

Har addu a sai da suka yi tukunna ragowar biyun da suka zo da su suka mik e suka fita Ma ah shi kuma shi da Scorpion da Oscar suka k arasa wajen da Mallan yake.

Diriricewa Mallan ya yi da farko, yayinda Kawu Isa ya tsaya kallon ikon Allah dan shi mamaki ma suka bashi!
Saboda fatar jikinsu kad ai abun kallo da al ajabi ce sakamokon yaddda take kacha-kacha abun kyankyami!
Ko ba a fad a masa ba ya san waennnan sune su Ma a d in da suka tashi kusan rabin Unguwa Uku kwanaki uku da suka wuce.


BULAMA
'?
0806 402 1951

ANA MALIK!!
Book 01.
Page 15.

Humairah Bulama.
Mikiya writers Association.

Sai da ya yi iyaka bakin k ok arinsa ya nutsu sosai tukunna ya ce  Barka da dare Baba
Wani yawu muk ut!! Mallan ya had iye yana jin fad uwar gaba matuk a dan bai san me ke tafe da su ba. Da kyar ya tattaro kalaman ya samu harshensa ya furta  Barkanmu dai Ma aruf, ya jikin Mahaifiyarka? .
A hankali ya lumshe idanuwansa ya bud e, k irjinsa yana yi masa wani irin zafi, da kyar ya iya cewa  Alhamdulillah .
Shiruu Mallan ya yi yana jira ya ji ko shi za su yi masa gaisuwa amma sai ya ji shiru.
Yana cikin wannan tunanin ya ji Ma a ya fara magana cike da kwarin guiwa sannan babu wani kwana-kwana& ..
 Na san ka riga ka sanni ka san iyayena, na san a musulunce idan mutum ya ga Yarinya yana so to iyayenta ya kamata ya fara zuwa ya nemi izini a wajensu kafin ita, hakan ita ce kamala.
To ni ba ma izinin fara zance da ita ko wani abu makamancin hakan na zo nema kad ai ba!
Na zo ne in gabatar maka da kaina a matsayin wanda yake neman auren y arka Khadijah kuma Mijinta har a aljannah in sha Allah.

Har ga Allah tsabar yadda Mallan ya shiga mad aukakin tashin hankali da rud ani wallahi shi manta ma  wacece Khadijar ya yi! Sai da ya dedeta kanshi da taimakon addu o i tukunna da mugun kyar ya samu ya iya had a 1+1.
Wani Irin gumi ne ya shiga tsattsafo masa ta koina, da ya bud e Baki zai fara magana sai bakin ya hau karkarwa ya ji ya gagara furta komai!
D agowa ya yi ya d an kallesu ya ga Ma ah ya kafesa da rikitattun rinannun idanunsa babu alamar annuri rahama ko sassauchi a kan fuskarsa.
Da sauri ya kawar da kansa gefe yana mai jin yadda zuciyarsa take wani irin hantsilawa kamar za ta fashe ne.

Cikin magagin buguwa Oscar wanda suma duk sun zuba masa idanune ya ce  Baba ya na ga ka shiga trembling ne?
Mu fa nan da ka ganmu ko a yanzu a shirye muke da sadakin mu a hannu, idan kuma kana buk atar preparation to sai a saka sati d aya ko biyu, saboda Mai gida za su tafi k asar turawa ne jinyar Mama kuma da ita yake so ya tafi& 

Cikin bayarda umarni Scorpion ya ce  ka yanke komai mu gama magana yanzu, kawai dai ka tabbatar ka yi abunda mukeso, dan ko baka yi ba ranka ne zai b aci amma dole za a d aura da izinin Allah, saboda Oga shine Mijinta har a gidan Aljannah
A tare duk suka ce  in shaa Allah .

 Ikon Allah, Allah shine mai aljannar amma Astaghfirullah yanzu suma waennan ashe suna saka ran shiga aljannah??
Kawu Isah ya yiwa kansa tambayar a cikin zuciyarsa ba tare da ya san mai bashi amsa ba.

Sunkuyar da kai Mallan ya sake yi a karo na babu adadi!
Bai riga da ya d aura auren Dije da Ma aruf ba kuma ya san kansa a gabas ba zai tab a d aurawa ba amma the fact that  wai Ma aruf d an daba wanda yake yiwa kallon the most useless human being a duniya a idanunsa! Wai yau shine ya zo yana neman auren y arsa hakan ya sanya wasu hawayen bak in ciki da tashin hankali suka zubo masa& shi musulmi ne kuma mutum ne mai addini ya san cewa kyamatar d an uwa musulmi bai dace ba amma tabbas a yadda yake jin kyamar Ma aruf wallah idan aka ce yau ya auri Khadija to sai ya had iyi zuciya ya mutu har lahira!.

D agowa ya yi suka had a ido da Ma ah wanda har yanzun shi yake kallo ba ya ko k yafta idanu.

Ganin yana ta faman dibi-dibi akan abunda ko hauka suke yi ba za su tab a k ullawa ba ya sanya Kawu Isa ya kalli Ma ah ya ce  Mallan Ma aruf ko? Bai jira ya bashi amsa ba ya ce  asalin gaskiya shine gobe iwar haka ma Dije tana a matsayin matar wani idan Allah ya yar.

 To ai da sauk i! Tunda gobe ka ce ba yanzu ko jiya ba, kawai yanzu abunda zai faru shi ne..a d aura musu auren ma yanzu tunda ga abunda na ji kun fara cewa saboda gudun samun matsala, dan a zauna lafiya.
Scorpion ya zaiyyane musu hakan cikin katse shi fuskarsa tana mai chanjawa zuwa wani yanayi na daban.

 Ina ga kamar baka fahimce ni ba& .mun riga mun bayar da ita ga d ana d an uwanta, kuma na san ka san cewa neman aure cikin aure haramun ne ko?

Cikin tarar numfashinsa Oscar ya ce  mun fahimci abunda kake nufi mana kwarai! Abunda muma muke so ku fahimta shine ku chanja tsari a bawa wanchan hak uri a mayar masa da kud insa dan mu bamu san mu ce muna son abu a ce mana A a ba!
Kune iyayenta kune magabatanta dan haka chanja hakan a wajenku na tabbata abu ne mai sauk i& ..

Shi dai Mallan bai ce komai ba Ma ah kawai ya tsurawa ido wanda ya kawar da kansa gefe guda! Ya lura hatta naman kumatunsa wani irin karkarwa yake yi alamun bala i yana cin sa.
Oscar yana dire aya Ma a ya mik e tsaye kawai!
A hankali ya ce  Baba a duba lamarin nan saboda Allah.
Daga haka ya wuce ba tare da ya k ara ce musu komai ba& ..
Sai da su Oscar suka gama treatning su Mallan kamar ba surukan da suke saka ran auren y arsu ba! Tukunna suka mik e suka fita Scorpion yana ta bala i kamar zai ari harshe& & & & & ..


Yau dai Mallan ya shirya tunkarar Inna a yita ta k are dan tabbas shirunta ya fara yi masa illah! Ya shirya zai shiga d akin ya rutsata idan za su shekara ba zai fita ba har sai ta kula shi.
Sai da ya kira Usama ya bashi tofin da ake bawa Kubra (wadda take neman haukace musu a gidan, dan har ta fi Mahaifiyar Sagir d in gigicewa) ya ce a mik a mata Yaron ya karb a ya shiga d akin da sallama, tukunna shima ya yi sallama kafin ya tura k ofar d akin na su Dije ya shiga.

Suna zaune tana cikin yiwa Dije nasiha Mallan d in ya shigo.
A hankali cikin nutsuwa Dije ta gaida shi ya amsa idanunsa a kan Inna.
Waje ya nema ya zauna a gefensu still yana kallonta ita kam ko inda yake bata kalla ba.
Ba dan tana so ba sai dan ba zata iya ba ya sanya ta ce masa  Ina wuni
Still ba ta kallesa ba.

A hankali ya sauk e numfashi idanunsa a kanta ya ce  Alhamdulillah, ya jiki da gida?.

 Da sauk i kawai ta ce, daga haka d akin ya kasance shiruu..
Mik ewa Dije ta yi za ta fita ya ce  dawo ki zauna
Cikin kasala da mutuwar jiki ta koma ta zauna kanta a k asa tana mai k ok arin danne kukan da yake ta faman taso mata.

Gaba d aya tunda aka ce za a aurar da ita yau kwana uku kenan bayan fitar uzuri sau uku kawai ta fita daga d akin nasu, na farko zuwa asibiti emergency na biyu duba Ya Muhammad
sai na uku d azu da rana da ta fita ta tuk a musu tuwo amma ko girki Inna ce take yi y an gidan kansu ta yi musu yaji sun daina ganinta!
Ita ganin abun ma take yi kamar a mafarki wai ita Dije za a aurar auren ma na dole duk a ta sanadiyyar Kaka! Gashi abun ya had e musu da alhini dan haka k uncin sai ya assasa.
Tabbas tsakanin shekaran jiya da yau Kaka ta sha zagi da tsinuwa tare da Allah ya Isa a wajen Dije ya fi cikin kwando!
Ba ta tab a jin takaicin rashin dangin da Innarsu ta tsinci kanta a ciiki ba sai a yau! Dan wallahi da gidan d aya a ciki za ta gudu ta b oye sai an manta an hak ura da maganar tukunna za ta dawo& &

 Dije,
Ba ni da niyyar yi miki dole, ba ni da niyyar aurar da ke yanzu sannan ban so na kai ki ki yi rayuwa a k auye ba amma an fi k arfina ta koina ba ni da yadda zan yi ne shiyasa& .
Tun ba yau ba saboda Ma aruf na so a ce mun bar Unguwar nan duba da yadda ya tasoki a gaba amma Kaka ta k i aminta da hakan! Kina da hakk i a kaina haka zalika itakuma nata matsayin mafi girmane, duk yadda zan fasalta miki mafi k ololuwar darajar da ake so ka kamanta wajen mu amalantar iyayenka da hakan ya yi kad an!
Amma duk da hakan na san kuna ganin yadda nake iyaka bakin k ok arina wajen kareku a duk lokacin da aka wuce layi duk da kuwa ko musayar yawu ba a so ka dinga yi da iyaye!.

Ina so ki san cewa tun kafin ki kai haka kawunki Isa yake nema wa d ansa Yusufa aurenki.
Bayan ku da Kaka da Isa su kad ai gareni a kaff fad in duniyar nan sai ko iya lami.
Kaka tana ik irarin tsinemin shi kuma ya zo min da wannan maganar wadda ita ce mafitar dukkannin matsalata ya kike so in yi?
Duk da haka ban so kaina ba dan inda ace ba dan kariyarki ba to da ba zan fake a bayan inuwarki in ceci kaina ba!
Dije baki ya yi yawa a kanki, Kaka Asabe y an gidan nan duk sun sakoki a gaba wanda ban san dalilinsu na yin hakan ba kowa so yake yi ya ga bayanki. Harshe yana da kaifi su kuma a ko da yaushe idan suka bud u Baki basu da abun fad e na alkhairi a kanki sai sharri!
Wanda Allah kad ai ya san kalar tashin hankalin da nakan shiga a duk lokacin da na ji Irin haka.

Abu na biyu shine
Ina so ki san cewa idan Allah ya k addara Yusufa ba Mijinki bane ba to babu ta yadda za a yi ki auresa ko da kuwa abunda yake a tsakanin ku da d aurin auren naku bai rage girman kwayar zarrah ba!
Haka zalika idan Allah ya k addara Mijinki ne shi to ko da ace babu mu kuma ba ku san juna ba babu wata dangantaka a tsakaninku ke kina China shi yana Getso Dije sai kin auresa!

18 / 33