ANA MALIK HAUSA NOVELS BY HUMAYRA BULAMA .doc

Author :  Humaira Bulama Category :  Top Hausa Novels 2025

Chapter   27 / 33

78K to 81K   out of 98.8K words

baki kashesa ba fa ba fasawa zai yi ba kuma babu wanda zai iya tsayar da shi a kaff fad in duniyar nan.
Sosai kuwa maganar ta yi tasiri ta samu matsugunni a cikin zuciyarta.
Dan a take babban burinta alokacin ya zamana bai wuce ta ga ta aika Ma ah inda ya aika mata Ya Kamal d inta ba.
Zumbur!! Ta yi ta mik e tana fesar da wani irin hucin da yake baiyyana k unci da b acin ran da take a ciki& da ikon Allah tana waiwayowa ta hango wuk a an yanka lemon b awo an bar d aya ba a yanka ba.
K arasawa ta yi ta d auka ta zira ta cikin rigarta ta soke da skirt d in jikinta ta yi waje kamar wata mahaukaciya daga ita sai hula da d inkin atamfa fitted da skirt k afarta ko takalmi babu.

Bata san awanni nawa ta yi a sumar ta na farko da wanda tayi a d akin su Ya Aminu ba amma tabbas ta san ta dad e dan tun kafin 8 ne yanzu kuwa gashi har an shiga masallacin sallar Magrib ma.
Hakan ya taimaka mata ta k arasa k ofar gidan su Ma a (ba tare da an ganta ba) wanda har yanzun yake a hargitse dan d akinsa kawai aka kammala gyarawa amma cikin gidan da waje yana nan a k ok k one gashi ya yi fad a da Masu yi masa gyaran.
Tabbas ta san shi ta gani jiya! Dan yanzu kam ta na da tabbacin yana nan..kuma ta ji ana labarin yadda aka gyara masa d akin nasa har an kawo kayan kallo, d azu da sassafe.
Addu arta d aya kawai itace ta yi ido biyu da Ma ah, in sha Allahu ita kuma idan ta haifu sai ta kaisa lahira da hannunta.
Kamar wata wadda aka yiwa asiri gaba d aya lissafinta ya kwance ko hukuncinta a musulunci ma kamar an saka cleaner an goge mata shi sam bata ganinsa babban burinta a wannan lokacin kawai shine ta ga gawar Ma ah kwance a gabanta..


BULAMA
'?
0806 402 1951
ANA MALIK!!
Book 01.
Page 24.

Humairah Bulama.
Mikiya writers Association.

Sai da Dije ta d an jima da fita tukunna Inna ta farka da salati d auke a bakinta. Sakina dama tana kusa dan haka ta shiga dubata su Ramma suna gefe suna hawaye suna bata Baki.
Tabbas ita kanta Inna ta san ta dad e bata yi kuka sannan ta shiga tashin hankali kamar na yau ba!
Ji take yi inama sannan addu a ta ke kawai a samu wani d an albarkar ya tasheta daga wannan mafarkin tashin hankalin da take yi& tunda aka ce an tsinci gawar Ya Kamal a ruwan k asan gadar Kaduna (river Kaduna) gaba d aya ta ke jinta tana yawo a sama kamar leda, har aka shigo da gawar ta kasa gasgata hakan sosai take cikin rud ani da mad aukakin tashin hankali da fargabar amsar k addarar y artata wadda a yanzun ta fito muraran ba su Isa su ce zasu b oye ba.
Har da Mama ake zaune a d akin jigumm! Kowa yana cikin alhini dan ko ba komai Ya Kamal mutum ne mai kyauta da mutunci da sanin ya kamata duk fad ace-fad acen y an gidan nan ba a tab a jin hayaniyar sa da kowa ba shi ko Mahaifiyarsa.

Sai da Sakina ta tabbata Inna ta dawo dai-dai tukunna ta mik e ta ce  bari in je gida in shirya ina da night duty yau, idan ruwan ya k are ki k ok arta ko chemist ne ki je a sauya maki wani, dan Allah.
Daga haka ta sake
yi musu gaisuwa da addu a ta tafi zuciyarta a cunshe babu dad i.

Kaka tana ganin fitar Sakina ta taso ta zo bakin d akin ta tsaya ta kama k ugu ta ce  oya oya fito tunda kin farka, fito kema ki wuce da ke da y arki ku bi bayan Minu tun kafin farar k afar ku ta sake dandalo mana wata masifar.

Inna bata damu da haukar Kaka na  sai ta fita daga gidan ba maganarta da ta yi a
yanzun akan Minu ita ce ta jaa hankalinta ta kid imata dan haka ta d ago a gigice ta zubawa su Ramma idanu alamun tana buk atar k arin bayani.
Kawar da kai Ramma ta yi dan bata san ta ina zata fara yi mata bayani ba yayinda Mama ta k ok arta itama da kyar ta ce  muma ba mu san ya fita ba, lokacin ana ta kan alhini ba mu yi tunanin zai biye musu ya tafi ba. Sai d azu ne wannan Yaron d an biyun Kubra yake ce mana ya tafi fa kuma sun bishi har tashar mariri dan nan mai lemon bakin titi ya ji ya cewa napep d in da ya shiga. To kuma wai sun bincika an ce an ganshi sai dai unfortunately an gagara gano motar Ina ya shiga, ma aikatan tashar sun ce musu wai tunda ba a gani ba to bai bar garin ba kenan.
Amma ki kwantar da hankalinki sun bayar da har hotonsa, yana zuwa za a yi kiransu in sha Allahu.
Ya ce mana shi da Musa suna kan bin duk tashoshin garin nan za su bi sahunsa (ko ya tafin ko bai tafin ba) a hankali su lallab a shi ya dawo& ..

Wani irin dummmm! Inna ta ke ji ita ta ma kasa yin lissafi da kyar kwakwalwarta ta iya k iyasta mata  Minu ya bar gidan!!
To garin yaya hakan ta faru?
Ta yiwa kanta tambayar ba tare da ta san waye zai bata amsa ba.

Still har yanzu Kaka tana waje tana ta tujara tana cewa  Inna ta fito tun kafin ta shigo cikin d akin ta fito da ita.

A hankali Mama ta yi gyaran murya ganin dama ta samu, ta ce  kinga tunda matar nan ta fara haka to fa idan ba d ai-d aita miki kan y ay anki ta yi ba hankalinta ba zai
kwanta ba! Ga Minu yanzu dai ya tafi baki ma san inda ya je ba dan haka tun kafin ta tura miki
y arki budurwa inda baza ki sake ganinta ba, kawai ki kawota in kai miki ita aikatau Madina ko
England, yanzu haka akwai k anwata a chan nima na tab a yin aiki a chan babu wata matsala kuma ana samun alkhairi kwarai, sannan hatta kud in visa su waenda zata je yiwa aikin ne za su d auki nauyin komai& .
Tunda na fahimci ita Kakar tasu hankalinta ya fi tashi a kan Dije to tabbas zata hak ura idan Dijen ta tafi na san zata sarara muku su kansu mutane za su sarara mata(Dijen)&
Dan haka gara kawai ta yi tafiyarta ta huta kafin komai ya lafa, shi kansa wannan d an daban da na ji ana ta k ishin-k ishin d in shine ya kashe Kamal wallahi bai Isa ya yi mata komai ba idan ta tafi chaan d in..idan Allah ya bata Miji a chan ta yi aure tunda na ga y ar taki tubarkallah da ita, idan ma bata yi auren a chan ba to na rantse miki duk sanda zata tashi dawowa ta fi k arfin raini.
Ni kaina wata uku kacal
na yi a chan amma dana dawo sai da na sayi d an k aramin fili. Kuma wallahi wallahi kin ji dai na rantse miki babu harkar karuwanci a ciki dan inda nake saka ran zan kaita ma aikin reno ne gidan babu maza ma kuma mai gidan ba mai zama bane ba, kawai albashin su ne mai kyau kuma idan kina so ma zata iya had a aiki biyu a lokaci d aya. Kamar ita kam na san zata iya yiwa matar girki da raino, Yarinyar gidan da na yiwa aiki ce aka yi mata aure itama ta haihu balarabiya Mijin shima balarabe, sam bata da matsala wallahi. Takanas ta yi min message ta ce tana son Yarinya budurwa da zata taya ta raino, idan na samu biyu in had o da mai yi mata girki y ar Babba.
Za ki dinga waya da y arki da zarar kin ji ta gaya miki wata matsala ki ce a dawo miki da ita ballantana ma ni na san ba za a samu matsalar komai ba in sha Allah.
Tunda matar ta fara magana har ta dire aya Inna bata ko fahimci kalmar  A a cikin zantukanta nata ba sam!
Muryar Kaka da tunanin Inda Minu yake da kuma tashin hankalin da take a ciki sun Isa su hanata fahimtar wani sabon zance.

A hankali
ta mik e ta rik e ledar ruwanta a hannu ta yi waje.
Mik ewa matar ta yi zata ruk ota Ramma ta yi saurin rik eta da hannunta mai lafiya.
Dan haka har Innar ta fita babu wanda ya samu damar ce mata komai&
Mayar da ita ta yi ta zauna, ta share hawayenta ta fuskanceta tukunna ta ce.
 Ingila kika ce ko
Saudiyya?
Shiruuu matar ta yi tana lissafi kafin chaan ta ce  Duk wanda kika zab a, idan ma kina so za ku iya tafiya tare da y ar taki ki je ki ga inda take na san hankalinki zai fi kwanciya.
Rabonsu Ramma da su ga kwayar shinkafa ita da y ay anta tun washegarin ranar da ta karye, kullum sai dai a san musu idan an ga dama shima kuma bai fi sau d aya ba, gashi Iyya ta tafi Minna wadda ita ce k arfin ciyar da su d in, tabbas ta tab a jin labarin aikatau a Saudiyya amma bata san na Ingila ba, wata makwafciyarsu a inda ta baro bazawara ta tab a zuwa da ta dawo ta kud ance kuma an ce tabbas ba karuwanci ta yi ba albashin ne mai kyau.
Ita yanzu haka ma so take ta nemi ko gidan makwafta ne ta fara tura Usama yana yi musu y an share-share, Rakiya kuma wanke-wanke tunda babu yadda za su yi dan hannunta ya samu matsala sosai wanda ya zo ya sake gyara mata hannu (ya d aurata)
da kyar ya ce  ta tabbata sai ta warke garau bayan nan da kamar watanni uku tukunna ta fara aikace-aikace da shi& ..
 Kina so za ki kai Yarinyarki ne?
Mama ta yi mata tambaya tana tsattsareta da idanuwa.
 Eh, amma sai na sake bincike da tunani, Yara biyu ne ma ba d aya ba, y an mata.
Murmushi Mama ta yi kafin ta ce  ai na d auka y ar taki d aya ce Rakiya sai Usama ko?
 A a su biyu ne y an mata akwai Fiddausi wadda ta Baki ruwa jiya har kika aikesu ita da Abu (y ar Asabe) da Saddik arki (y ar Maman) ai itanma tawa ce, sai dai ita d in na ga kamar ta yi k ank anta shekarunta sha biyu, za su karb eta a haka?

 Da gudu ma kuwa, zata yi shara da wanke-wanke da wankin band aki ai, zasu karb a sai dai bai fi su bata dubu d ari ba a wata gaskiya.

Ramma bata san lokacin da ta damk i hannun Mama ba da mugun k arfi ta ce  Rakiya fa? Babbar ita nawa za su bata

 Eh to..
Idan aikin gida ne Ina ga dubu d ari uku haka, idan kuma har da raino to zai iya kaiwa dubu d ari biyar. Dan ko ni da nayi na had a biyu d ari hud u ake biyana ita kuma kinga da yarintarta da k arfinta.

Zaro Idanuwa waje Ramma ta yi tace  baiwar Allah kar ki saka mini rai fa.

Murmushi ta yi ta ce  ai baki ga komai ba, sai Allah ya sa ta samu masu kyauta idan ta tashi ta dawo
miki da uban alkhairi inaga sai kin kusan suma.
Shiruuu ta yi tana lissafi sai kuma ta ce  za mu yi magana.
Daga haka ta fara k ok arin mik ewa dan ta ji shigowar su Mai unguwa cikin gidan tun lokacin da Inna ta fita.
Mama ce ta taimaka mata ta tashi tana cewa  to shikenan
A ranta kuwa murna fall kamar ta zuba ruwa a k asa ta sha dukda kuwa Dije ta hara dan ta san idan ta kaiwa Nuraddeen ita watak il sai ya bata kyautar gida a k asar Khak il, dan sai ya more K uruciyarta kafin ya sakata aikin da suka shiryo idan ta gama su kasheta, to amma waennnan d in ma ba laifi ai da babu gara babu dad i sannan Dijen ma ba hak ura zata yi ba zata ci gaba da gwada sa ar ta.
Da wannan tunanin suka fita a tare Ramma ta tsaya a wajen ana tattaunawa Mama kuwa gaisawa kawai suka yi ta afka d akinta ta turo k ofar ta rufe ta d auko wata k asa a cikin wani abu mai fad i flat a k asan k atifarta ta bud e marfin ta rubuta sunayensu ta chachchake da allura jikinta har wani irin karkarwa yake yi. Sai da ta gama tukunna ta nutsu ta k urawa abun ido a ranta tace  naki wasa ne!! Sai in ga ta yadda za ki yi tunani da shawarar, ai in ba gani kika yi sun tafi aikatau ba hankalinki ba zai tab a kwantawa ba! Kin yi mai wuyar ai tunda har kika bari maganar ta shiga kanki .


An kai ruwa rana da Kaka kafin ta bi maganar mai unguwa da ya ce  ta bari Mallan ya dawo daga Minna tukunna sai a san abun yi. Sannan at least ta bari alhinin rasuwar Kamal ya saki mutane. & ..dan har sai da ya fara jiyo k amshin anya kuwa bata da wata b oyayyiyar agenda apart from kasancewar zaman Dije hatsari ga y an unguwa tukunna suka farga ita da Asabe, Asaben ta yi saurin janta d aki suka tattauna, kafin ta (Asabe) fito ta ce  shikenan ba komai Kaka ta yarda, Allah ya dawo da Mallan d in lafiya.

Da  Ameen kawai ya amsa tukunna ya juya ya fita daga gidan bayan ya sake yiwa Inna gaisuwa, tausayinta fal ransa.


Tafiya take tana had a hanya tana adduar  Allah ya sa ta tarar da Ma ah a gidan
A haka ta k arasa k ofar gidan wanda marabarsa da kango kad an ne, sai dai an saka sabuwar k ofa mai kyau kuma da alamu gyara ake yi har ta ciki, dan ga kayan aiki nan su yashi suminti da su bulo
jibge a k ofar gidan wanda ko da wasa duk son Yaran layin da wasan yashi basu ko je kusa da shi ba.

K irjinta yana dukan uku-uku ta taka dakalin gidan ta hau ta k arasa bakin k ofar gidan tana jin yadda bugun zuciyarta ya k aru.
A hankali ta d aura hannunta a kan k ofar gidan ta ga ta yi motsi dan haka ta ji wani sassauchi sakamokon
k amshin kusantowar cikar burinta da ta fara jiyowa.
Cikin sand a ta tura ta shiga. Sai kuma ta d an jaa ta yi turuss!! A ranta ta shiga aiyyana yadda zata yi da zaratan maza har uku, dan warin kayan mayen da ta ji yana fitowa daga cikin d akin soron wanda take da tabbacin nan ne d akinsa kad ai ya Isa ya sanar mata yana nan kuma ba shi kad ai bane ba dan akasari wannan shaye-shayen su Scorpion ne suke yinsa shi bai cika yi ba.
A take lissafinta ya Bata dole fa sai ta had a da wayo! Dan haka ta d an nutsu tukunna ta juya ta mayar da k ofar gidan ta rufe dai-dai a kan idanun Mallan Idi wanda yake wasar y ar b uya da Ma ah d in.

A hankali ta k arasa bakin k ofar d akin, wani sanyi ta ji a cikin ranta sakamokon k arar waya da ta ji wanda hakan yake sake bata tabbacin yana nan fa kuma burinta ya kusan cika dan idonta idon Ma ah yau ko ita ko shi!.

Har ta d aga hannunta zata yi
musu knocking sai kuma ta chanja shawara ta tsaya a dai-dai bakin k ofar tana mai toshe hancinta dan warin ya fara damunta sosai har kanta yana sarawa& ta shiga jero sallama.

Mafarkinta yake yi wai an zo an tara mutane za a d aura musu aure amma k iri-k iri ta ce  ita fa bata son shi
Kawai kamar a sama muryarta ta farkar da shi.
Tsaki ya yi ya yarfe hannuwansa dai-dai saitin fuskarsa kamar mai kad e k uda ko sauro sannan ya juya zai ci gaba da baccinsa ya sake jin sauk ar zazzak ar muryarta cikin kunne zuciya ruhi da gangar jikinsa.
Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauk e sannan ya juyo kwanciyar rigingine fuskarsa ta na kallon sama kafin ya shiga k ok arin bud e idanunsa a hankali a hankali.
Dai-dai bai ma kai ga fara ganin dai-dai ba ta sake sakin wata sallamar a karo na uku zuciyarta tana mai aiyyana mata ta lek a kawai maybe ma sun bugu ne bacci suke yi ta yadda zata k addamar da shirinta cikin sauk i.

A hankali ya mik e zaune a kan gadon yana mai runtse idanuwansa sakamokon yadda kansa ya shiga sara masa sannan ga baccin da yake shirin sake wanchakalar da shi a nan kan gadon.
 Assalam alaikom
Ya sake jin muryarta daf da daf wanda hakan ya sanya tsigar jikinsa zubawa dan a buge yake gashi ita d in daban take a cikin ransa.
Dishi-dishi yake ganin komai kafin a hankali ya fara gani sosai amma still kansa ya yi wani Irin nauyi.
Zuwa yanzu ya gama gasgata ita d in ce dan haka ya mik e daga kan gadon wanda sai da ya dafe kansa da k arfi sanda ya mik e d in
saboda yadda ya sara, tukunna ya d an nutsu ya nufi k ofar gadan-gadan daga shi sai gajeran wandon da bai ida

27 / 33