ANA MALIK HAUSA NOVELS BY HUMAYRA BULAMA .doc

Author :  Humaira Bulama Category :  Top Hausa Novels 2025

Chapter   21 / 33

60K to 63K   out of 98.8K words

ura ta bari akan washegari ta yi mata.

Tunda Mallan yake bai tab a shiga tashin hankali irin wannan ba dan ya ji mutuwar nephew d in nasa gashi halin da ya ga d an uwa da Mahaifiyarsa sun shiga ya sake kid ima shi matuk a.

Kafin dare labari ya karad e unguwa ya zama topic of the day  Ma aah ya kashe wanda Dije zata aura, ba shi kad ai ba ma hatta Sagir saboda ya ga yana sinsinar Dijen ne shiyasa ya kashesa ashe.
Zuwa wannan lokacin kam kowa ya fahimci takurar Ma ah ga Dije ashe so ne, dan haka labarin sai ya yi sauk in fassaruwa aka dinga kasa shi a faranti dalla-dalla.
Yayinda babban tashin hankalin Inna a yanzu ya zamto  waye zai auri y arta? Dan ko ba d an unguwa bane ba tabbas ta san idan ya zo yin bincike akan Dije wannan shine abu na farko da za a fara fad a masa& ..duba da yadda a yanzu aka zuzuta abun a unguwar, ake ta shigowa ana jajantawa waenda bakinsu ba ya yin shiru ne suke fitowa su gaya mata halinda ake ciki yayinda waensu gulma da son sake gigitasu ne kawai yake kawo su.
Zazzab in da ya rufe Dije ya sanya dole sai da aka kirawo Sakina ta zo ta yi mata allurai itama tana yi tana tata gulmar& ..

Washegari da safe Ma ah ya nemi number Mallan ya kira shi a waya ya yi masa ta aziyyar rasuwar Yusufa! Wanda Mallan d in ya rasa ma bakin magana, daga haka ya sanar masa ya tafi Abuja ana ta shirye-shirye za su wuce England za a je a duba Mahaifiyarsa idan ya dawo zai zo ya same shi.
Daga nan ya kashe wayar ya bar Mallan da waya kare a kunnensa!
Tabbas idan zai mutu a yau to aurar da Dije will be the first thing to do in sha Allah a yau ba sai gobe ba.
Sai dai kuma a kaff garin babu wanda ya karb i shelar tayinsa dan ko an yarda idan aka ji ba asin rasuwar Yusufa wanda nan d in ma ya karad e garin sai a ce an fasa& .

Kwanan Mallan uku yana nemawa Dije Miji a garin Getso amma bai samo ba wanda hakan ya sake firgita shi matuk a.
Zuwa wannan lokacin kuma ya fahimci Kaka da Mahaifin Yusufa haushinsa suke ji ata dalilin rasuwar Yusufa saboda Dije wanda tun da aka yi rasuwar dama ya ga sun sauya masa to kuma tunda suka zo suka had u da Anty d in Kaka Iyya lami da Umma(Mahaifiyar Yusufa) abun nasu sai ya k ara tsanani. Yau kam k iri k iri Kaka ta ce masa  ya nemi wajen kwana d akin Baban Yusufa inda yake kwana ya cika taff da b akin kunya da suka zo gari ya gari dan haka ya nemi wani wajen ko kuma ya koma Kano kawai.

Shima dama abunda yake so d in kenan dan ya lura zama a tsakiyarsu a haka ka iya janyo matsala, dan haka ya tattaro ya sake yi musu gaisuwa da sallama wanda Iyya lami da uwargidan Yusufan suka k i amsawa sai amaryar tasa ce kawai ta amsa masa itama a kumbure. Su Kaka suma da kyar suke iya mayar masa da magana, shi dai ya yi musu duk wani abunda yake ganin ya dace daga haka ya wuto Kano da k udirin aurar da Dije kafin ma ya shiga cikin Gidansa.

BULAMA
'?
0806 402 1951
ANA MALIK!!
Book 01.
Page 18.

Humairah Bulama.
Mikiya writers Association.

Yana karyo kwanar layin gidan nasa ya ci karo da Mallan Manniru.
Ajiyar zuciya dattijon ya sauk e wanda yake kusan tsara d aya da Mallan d in sannan ya mik a masa hannu suka yi musabaha cikin jimami ya ce  Ashe haka ce ta faru kuma? Ya hak uri? .
Jinjina kai Mallan ya yi tukunna ya ce  Hak uri Alhamdulillah da godiya .
Fuskarsa na baiyyana rashin jin dad i ya ce
 Allah ya ji k ansa ya gafarta masa .
Mallan ya ce  Ameen
Dan gaba d aya jikinsa a sanyaye yake ga rashin lafiyar da take cinsa ba tare da kowa ya sani ba.

Sai da ya d an numfasa tukunna ya ce  haka kurum ya janyowa Yarinya bak in jini! .

A hankali cikin sanyi Mallan ya d ago daga kallon k asan da yake yi ya kafesa da ido.
Wanda hakan da ya yi ya sanya Mallan Manniru gyara tsayuwarsa ya ce  Ko dai baka san abunda yake faruwa a layin ba kwana biyu?
Bai jira an bashi amsa ba ya ce  Ai yanzu bak in jinin Ma ah gaba d aya kan Dije ya komo, tunda suka fahimci yana k aunarta shikenan sai suka d auki karar tsana suka d aura mata kamar ma ta riga da ta zama matarsa ne.
A halin yanzu fa sun koreta daga makarantar islamiyya jiya Sumayya take gaya min, wai sun ce  saboda gudun kar a hukunta ta ko ta samu sab ani da wani ko wata shi kuma ya zo ya kashe kowa!
To d azu ma dai har ta tafi bokon kuma sai na ga nan ma d in ta dawo lokacin Ina shago kuma kamar ma kuka take yi, ta zo ta wuce gida alamun suma d in dai korota suka yi.

Wani irin yawu mai tauri da d aci Mallan ya had iye da kyar! A hankali ya sake zuba masa idanunsa waenda suka fara rinewa ya ce  Mallan Manniru za ka iya auren Dije?

Rasss!! Gabansa ya yanke ya fad i, sai kuma wani sanyi tare da fargaba suka rufe shi.

A hankali Mallan ya ce  D a na kowa ne Mallan Manniru, ka rufa mini asiri ka auri Yarinyar nan tun kafin fita ta gagareta, mutane sun yiwa abun hukunci da wuri wanda ba su da tabbacin Ma ah d in ne ya yi tunda ai bai ma san adreshin Yusufan ba ka ga kuma ba zai yiu ace ya nemo ya yi shiri ya je ya kashesa a cikin kwana d aya tak! Da ya ji labarin auren nata ba.
Jinjina kai Mallan Manniru ya yi, duk da cewa Dije ta kasance k awa, babbar k awa ma kuwa ga y ar sa
har ga Allah dama ya dad e yana harin Yarinyar.
Yanzu kuwa ga dama ta samu, dukda kuwa wanchan al amari da ya faru da Yusufa yana d an firgita shi amma sai ya tuna ai basu da tabbacin hakan ne, dan haka ya d ago ya kallesa ya ce  Na amince .

Jinjina kai Mallan ya yi cikin jin wani relief yana sauk ar masa ya bashi hannu suka sake gaisawa ya ce  na baka Khadijah, kar ka damu da duk wata bidi a sadakinta kawai za ka mik o a d aura muku aure yanzu. Bari in nemo shaidu sai a k arasa masallacin
Murmushi Mallan Manniru ya yi irin ta jin kunyar surukantakar nan, sannan ya d an sosa bayan kansa ya ce  da wuri haka Mallan&  .
A hankali gaban Mallan yana fad uwa dan so yake yi kawai ya ga ya d aurawa Dije aure ya ce
 In sha Allah .
Jinjina kai ya yi ya ce  to shikenan babu damuwa amma bari in je in sanarwa Mahaifiyata da iyalina in ya so daga nan ko bayan la asar ne sai a d aura .
Daga haka suka yi musabaha ya juya ya wuce zuciyarsa fes, tabbas ya san ya tsinci dami a kala! Mutane suna ta tunanin wani abu daban gashi shi zai Angonce kuma ya san in sha Allahu babu abunda zai same shi, shi fa dama tun lokacin da ya ji batun rasuwar Yusufa da aka ce Ma ah ne sam abun bai kwanta mas??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????a ba, dan ya yi kamar tatsuniya ko wasan Yara& .
Yana wannan tunanin ya k arasa gidansa, mai d auke da d akuna bakwai inda yake da Mata uku Y ay a ashirin da bakwai da Mahaifiyarsa duk a cikin gidan kuma da ikon Allah sana arsa  d an kantin ne ta inda yake sayar da kayan kanti, da shi yake ciyar da iyalinsa da taimakon mata da y ay ansa waenda suka kama sana a ba da wasa ba dan kaff cikin su babu mai zaman banza, hatta d an k aramin Yaronsa mai shekaru biyar yanzu haka yayunsa maza da suke d aki d aya sun fara tafiya wajen da suke fenti da shi yana kallo dan a samu ya koya da wuri.


Mallan ya so ya b oyewa Inna dan yana jin tsoro kar ta hana, shi kuma har ga Allah shi kad ai ya san me yake hangowa a future d in Dije muddin ba su yiwa tufkar hanci da wuri ba, amma kawai sai ya zab i ya gaya mata.
Dan haka ya koma gefe bai bari ma ya shiga gidan ba ya kirata a waya ya shaida mata batun  auren Dije da Mallan Manniru wanda za a d aura a yau in sha Allah , daga nan ya d an bata haske akan dalilinsa na yin hakan.
Tabbas bata so had in ba dan ko babu komai Mallan Manniru Mahaifi ne ga k awarta kuma matayensa duk mutanen kirki ne ana shiri da su matuk a.
Amma fa Hausawa sun ce so so ne amma son kai ya fi!
Shiyasa Mallan d in yana gaya mata abunda yake hange da yadda ya rasa samawa Dijen Miji a Getso ma duk sai jikinta ya yi sanyi ta yi shiruuu kawai kafin
ta ce  Allah ya zab a duk abunda ya ke alkhairi& ..
Tana baro kitchen inda ta gama wayar ta nufi d aki.
Tana shiga d akin ta tarar da Dije da Sumayya baiwar Allah tana ta rarrashinta yayinda ita kuma ta kafe k unshin hannunta da kallo tana ta zubar da hawaye.

Tausayin su ne ya rufe Inna duk su biyun dan haka kawai sai ta juya ta bar musu d akin ta fito tsakar gida ta nemi waje ta zauna ta rafka uban tagumi..
Ba ta dad e da zama ba Iyya ta fito ta dinga rarrashinta tana bata baki& .da kyar Inna ta ke iya danne zuciyarta ta hana kanta yin kuka, abubuwan sun yi
mata yawa ne Astaghfirullah ga Ya Muhammad chan a kwance bai ma san Ina kansa yake ba, Likitoci sun ce a yi addu a kawai, ga kyarar da Kaka take yi mata dan Wallahi kawai pretending take yi amma abun yana masifar damunta, sannan ga Mallan wanda kwana biyun nan daga ya yi wannan idan ta kawar ta share sai ya sake yin wani, gaba d aya zaman nasu ya k i yin dad i ko wannensu a gigice, yanzu haka ma da ya kirata highlight kawai ya yi mata kuma da ta tambayesa ya dawo ne? Ko yanzu ya taho? Nan ma bai gaya mata ba, Mallan d in da a da ko kaya in zai saka to tare suke zab a amma yanzu ta lura kamar har da b oye-b oye ma ya fara shiga cikin lamarin nasu, ta yi masa uzuri tabbas saboda halin da yake ciki amma kuma abubuwan sun kasa fita daga kanta.
Tana cikin wannan tunanin ta ga an fito da Ramma tsakar gidan an shimfid a mata tabarma an kwantar da ita, hannun nan ya yi suntum! Ita kanta ta kumbura dan jiki take ji ba kad an ba!
Asabe itama hannun ya yi muni amma ba wani sosai ba dan tana ma iya yin komai dukda anata hanata saboda gaba amma ta k i ji idan ka ganta ras kamar ba mai jinya ba komai yi take yi dan bayan hannun ne ba ciki ba yayinda na Ramma ya munana sosai..D an koyo ne ya d aurata a gida ashe ba dai-dai ya d aura ta ba, dama tun a ranar Iyya take ta ce musu su kaita asibiti d aurin bai yi ba amma aka k i ko da yake saboda rashi ne da babu dan in aka je asibiti kud in kati ma ba lalle su iya biya ba. Sai d azu ne tukunna aka gane ashe d aurin bai yi ba to yanzu dai an kira wani kwararre zai zo ya gyara.
A gefenta y ay an suka zauna, sun saka ta a gaba wanda su kad ai suka san halinda suke ciki dan ba iyaka tashin hankali ba ko da yunwar cikinsu aka barsu ta ishe su, rabonsu da abinci tun jiya da safe wanda Iyya ta zuba musu. Ita Inna bata san basu da kayan abinci ba da zata basu ko da iyakacinsa kenan gareta dan kaff gidan ita da Iyya ne kawai basu da rowa.
Gashi su matan basu iya sana ar komai ba uwar kuma da take komai gata a kwance.

Usama ne ya kwanta a wajen yana ta faman murk ususu dan shi kam hak urinsa ya k are zuwa yanzu, Inna tana shirin yin magana Hajiya Uwani ta shigo cikin gidan a fusace Suwaiba a bayanta tana ruk ota tana cewa  ki tsaya mana. Kar ki yi haka dan Allah, tsaya ki ji
Ita kuma tana cewa  ki rabu da ni fa! Ki bar ni in jaa musu kunne ramin kura daga ita sai y ay anta wallahi bakin rijiya ba wajen wasan Makaho bane ba, ba zan zauna in nad e hannu a cuce ni ba!

Firfitowa na cikin d akin suka fara yi, kafin ka ce kwabo tsakar gidan ya cika tap! Hatta su Sumayya wadda suke d aki tare da Dije.

Tunda Uwani ta shigo dama
Inna ta sunkuyar da kanta k asa dan ta san labari ya iske mata kenan.

Idanun matar yana sauk a a kan Inna ta ce  muguwa azzaluma!! Butulu! Makira& .
Da kika san duk wanda ya ko kalli y arki kamar ya yanki tikitin mutuwa ne ai sai ku hak ura da aurar da ita ko kuma ku bashi shi d in ya aura kawai, amma shine tsabar muguwar zuciya irin taku za ku mak alawa Mijinmu?
Mai ya sa ba kwa jin tsoron Allah ne??

Rass!! Gaban Sumayya ya yanke ya fad i k irjinta ya fara bugawa, a hankali ta zamiye hannunta daga cikin na Dije ta k arasa inda Mahaifiyar tata take tsaye ta ce  me ya faru? Wanne Baban ne zai auri Dije?

Cikin b acin rai wanda yake had e da firgici da tsoro ta ce  Baba ubanki mana! Ina da wani Mijin sama da shi ne? Shi ne dan tsabar nemawa Kai aka bashi wannan masifar ta yi maganar tana nuna Dije, sannan ta d aura da cewa  shi kuma ya amsa, wai anjima bayan sallar la asar za a aura masa ita.

Da k arfi Inna ta runtse idanuwanta tana dad a danne zuciyar da take tasowa take yunk uro mata, dan sosai ta kawo iya wuya (mai hali a duk halin da yake ciki halinsa halinsa ne).

Juyawa Sumayya ta yi suka had a idanu da Dije, a hankali Dijen tana hawaye ta shiga girgiza mata kai alamun ita babu ruwanta, kafin da kyar ta matsa kusa da ita ta samu ta iya furta  Wallahi ban san ma me yake faruwa ba, muna d akin nan tare da ke mun fi kwana uku kina tare da ni.
Kuma Ina so ki saka a ranki maganar nan ba tabbatacciya bace ba dan ba zan tab a yarda in auri Baba ba.

 Zancen banza ma kenan!! Abunda an riga an bashi ya karb a kuma me ya rage? Sunanki da nashi ya riga ya had u dan haka kin gama gamawa da mu!
Allah ya Isa tsakani na da ke in har wani abun ya samu Mijina wallahi Allah sai na baku mamaki da ke da mugayen iyayenki
Ta fad i hakan tana mai rushewa da kuka.

Hak uri jama ar gidan suka lullub eta suna bata yayinda idanun Dije suke cikin na Sumayya tana hango b acin rai yana maye gurbin tausayinta d in da take gani a cikin idanun nata, hannunta da yake a cikin na Dijen ta sake damk ewa ta ce  Sumayya ki yarda da n& 
Tass!! Ta d auketa da mari sai kuma kawai ta fashe da kuka a take ta juya ta fice dan sai da ta yi Marin sai kuma ta ga rashin dacewar hakan tunda ba laifinta bane ba sannan kuma ga bak in cikin abunda yake shirin faruwa d in tabbas ya ci ta rufe Dijen da duka ma! Dan haka duk sai ta sake rikicewa ta sake gigicewa ga kukan Mahaifiyarta da take jinsa har tsakar zuciyarta.

Ko bayan fitar Sumayya haka nan Uwani ta ci gaba da tsinewa Dije tana kuka tana aibantata ana ta bata hak uri amma ta k i hak ura.
Sai tsine mata take yi tana kiranta da masifa!!.

A fusace Inna ta mik e ta ce  Malama ya ishe ki! Y a ta ba masifa bace ba .
Kusan a tare ita da Maman Sagir suka ce  Wallahi Masifa ce!
Sai kuma uwani ta d aura da cewa  ki rubuta ki ajjiye ke kam kin gama yawo dan kin haifi ajalin ki ne.

A fusace Inna ta yi kanta kamar za ta dake ta tana cewa  ni kuma na ce ki rubuta ki ajjiye sai kin ji kunyar abunnan da kika fad a in sha Allah y a ta alkhairi ce kuma sai na shiga aljannah a ta sanadiyyar ta!
Gud a ta rangad a ta ce  ai Yarinyar da aka aurar ta kai mutuncinta gidan Mijinta ita ce ake saka rai da hakan sab anin ita da kowa ya san karuwar d an daba ce wanne mutunci za ta kai? Ki yi addu ar neman gafara dan sam baku kula da amanar da Allah ya baku ba wallahi.
Hakan kuwa da ta fad a ya taimaka wajen sake fusata Inna dan haka ta hau ta fara ita ma Uwani da Maman Sagir d in suna yi a take tsakar gidan ya

21 / 33