Chapter 11 Reading AJEEMAL Book 2 Hausa Novels By Khaleeseart Abdullahi Raeys.txt Arewa Novels

AJEEMAL Book 2 Hausa Novels By Khaleeseart Abdullahi Raeys.txt

Author :  Khaleeseart Abdullahi Raeys Category :  Hausa Novels 001

Chapter   11 / 24

30K to 33K   out of 70.1K words

din wayar dan ganin wanda ya uzura da kira haka shikuwa Ajmal ya ki kula wayar tana a jiye saman table daga karshe ma silent ya sanya wayar ganin an matsa da k'iran, Ajmal mikewa yayi gamida goge hannayenshi ya kamu kan Aheel ya sunbaci goshinsa yana fadi'n

" take care of yourself " bye yana fadi'n haka ya dauki phone d'insa tare da key din motarsa cikin hanzari ya fi ce daga parlourn Heelah har ya gama ficewa daga parlourn ya kurewa ganita binshi ta ke da kallo tana tab baki , shi kuwa Ajmal yana fitowa direct parking space ya nufa ya shiga mai gadi ya na ganin fitowar da rawar jiki ya tashi yabude masa gate haka Ajmal ya zo ya sa kai ya fice mai gadi sai daga masa gaisuwa ya ke

Guraren4 yamma wasu kyawawan mota guda biyar duka danno kai cikin gidan time din da mai gadi ya bude gate motar ga ba Daddy ne aciki sai kammala da ke driving dinsu sai yan rufa masu baya mota guda 3 suka karisa shigowa su kayi parking daidai parking space daga nan Daddy da Kamal suka fito daga bisani sauran security gidan suka shiga yayiwa Daddy sannu da isowa daga haka Kamal ya karbi dan madai daicin travel bag ya karisa shiga masa da shi ciki, yau gurinsu fareeda murna ba a magana Daddy ya dawo yau kowa na cikin farin ciki duk da tafiyar tashi ba wani jimawa yayi ba but kowa yayi kewarsa sosai kasan cewar Daddy mai yawan wasa da dariya wani sa'in harda tsokana.

a wannan rana Ammi ta kasa tsugul sai da ta zaiyyana wa Daddy duk wani abunda ya faru bayan ta fiyarshi wanda abun ba k'aramin mamaki yayi ba jin har suma Nisha ta yi ta kwanta rashin lapia tsabar girgiza da ta yi da lamarin ga kuma soyayyarsu da Kamal wanda basu san da shiba nan ya yanke shawaran neman Ajmal domin su zauna su tattauna a tsakaninsu ya ji ta ban garanshi kasan cewar abaya sun yanke hukunci ba tare da jin ta bakinsa ba duk da kasan cewar fatan Hajj mama kenan ba yi da ikon ja a kan duk wani maganarta hukunci ko k'udirinta but wannan karon ba zaiso a sa ke masa rashin adalci ba haka itama Nisha ba zaiso abunda zai sa ta shiga wani haliba ko a shiga hakkinta akan abunda ba ta da ra'ayi ba matukar ba ta son lamarin gwara Hajj mama tayi hakuri da lamarin a hakura babu cuta babu cutarwa matukar basuda ra'ayin junansu dan haka Daddy ya sa Ammi ta zauna da Nisha ta ji ta bakinta shima ta ban garansa zai zauna da d'an nasa.

Kamar yanda Daddy ya nemi zama da Ajmal haka a kayi da dare guraren 10 Ajmal dawowarsa kenan ko side dinshi bai nufa ba duk da kasan cewar dare yayi sosai kuma ya gaji yana bukatan hutu hakan bai hanashi zuwa katafaran parlourn Daddy ya sa me shi kamar yanda ya bukata ba, ban garansu Nisha harsunyi shirin kwanciya bacci Barka ta shigo domin isar da sakon Ammi ga Nisha ta na bukatar ganinta upstairs cikin bedroom d'in ta Nisha haka kawai taji kirjinta ya buga jin Ammi na naimanta cikin wannan lokacin jiki a sanyaye ta mike ta fice tana sanye cikin kyakykyawan kayan baccinta riga da wando masu laushi da taushi launin pink, ta na isa ta tura door ta shige bakinta dauke da sallama .

Zaune ta samu Ammi gaban dress mirror tana shafa kamsassun mayukanta da lamar wanka ta yi tana sanyi cikin duguwar rigar baccinta milk color bedroom d'in duk ya dau daddad'an kamshi,

"Kariso mana " Ammi ta fad'i time dinda ta mike tana kallon Nisha wacce ke tsaye daga bakin door jin maganar Ammi yasa ta shiga karisowa hankali yayinda Ammi ta jawo hanun ta ciki da murmushi suka zauna bisa sofan dakin

"Na sa antasoki ko? maybe ma harkin kwanta bacci " Ammi ta fad'i tana kallon Nisha still murmushin da ke kan face dinta bai goshai ba, itadai Nisha kanta sunkuye ba ta ce k'ala ba Ammi hanu tasa ta daura saman na Nisha ta tashiga fadi'n

"Daddy ku ne ya bukaci na kiraki mu zauna da ke Dan jin ta bakinki bisa batun auranku keda yayanku because na labarta masa halinda kika shiga da kuma tsakanku da kamal wanda ya sa shi cikin da muwa da tunanin kamar anshiga hakkin ki an yanke hukunci a ba tare da an shawarce ki ko jin ta bakinki Dan haka matukar ba kyason auran gwara a hakura da lamarin a hakura a raba auran because bayaso kishiga damuwa ko wani hali ya damu matuka akan sumar da kikayi bayaso a miki rashin adalci yace kuma ce na lallasheki na baki hakuri bisa wakanar wannan lamari kuma ki daina saka damuwa cikin ranki". nan Nisha ta fad'a cinyar Ammi ta saki kuka saka kasa abin tausayi tana fadi'n


Ajmal
Story and writing

By
Oum amreesh
"Please Ammi kudaina neman afuwa agareni matukar nima daya muke da su Reeda a gareku duk hukunci ko umarnin da zakuyi agaresu na dauka nima zata biyo ta kaina tunda nima tamakar ya'rda kuka haifa acikin ku haka kuka dauke ni to mai yasa zan butulcewa maganar ku , nasan iyaye su ne suke nemawa y'ay'ansu mazajen da su ka da ce wanda kuma kunsan zabin da kukayi a gareni ba zai cutar dani ba ko yayi sanadin shiga damuwata" daguwa Nisha tayi tana share hawayen face dinta kafin ta ci gaba da fadi'n

" Allah bai nufa ya Kamal shine alkhari agareni ba kuma Allah bai sa shi zai zaima abokin rayuwata ba duk da kasan cewar munyiwa kanmu fatan hakan Amma Allah bai nufa ba, please Ammi karku raba auran ba na yarda na zauna da shi cikin mutunci da mutuntawa tunda shi Allah ya zabamin a matsayin miji"

bakaramin jin dad'in maganganun Nisha Ammi ta yi ba ita tasan yarinyar ba zata basu kunya because ta san yarinyar akwai hankali da nitsuwa da kuma hangen nesa shiyasa ta ke da d'an shiga ranta ko da yaushe rungume ta tsam Ammi ta yi bisa jikinta hankalinta ba k'aramin kwanciya yayi da zantukan Nisha ba fatan ta Allah yasa dayan ban garan wajan Ajmal asamu rangwame yayi kawaici irin yanda yayi abaya na auran Heelah duk da ta San abune mai matukar wuya du ba da tun zuwanta gidan nan kowa ya karbeta hanu bibiyu but shikuma k'iri-k'iri ya ke gudun ta ra be shi saida zama yayi zama ya hakura. raba jikinsu Ammi ta yi cike da murmushin murna da jin dad'in ta ce

Allah dai ya mi ki albar kyakykyawan ya naji dad'i matukar da gaske na san dama ke yariyace mai biyayya ga iyayen ta kuma ina miki fatan kan wannan zabin da Allah ya miki insha allah shine farin ciki agareki yanzu kije ki kwanta karna shiga time din baccin ki , jinjina kai Nisha ta yi daga bisani ta mike ta fice daga bedroom din tareda yiwa Ammi sai da safe.v

Cike da murmushin Ammi ke bin Nisha da kallo zuciyarta na yi mata wani sanyi har Nisha ta gurewa ganinta, Nisha a fitowar ta kenan jiki asanyaye face d'inta yayi jawar da shi a hankali Nisha ta ke tafiya kamar wacce a ka zarewa laka a hankali ta ke sakkowa daga upstairs din sai motsi ta ji bayanta juyawar da zatayi sai ganin Ajmal tayi cikin hanzari ya nufo downstairs wanda yasa Nisha saurin kawar da faska tare da yayin gefe da sauri ta manne Ajmal ta matsa masa daga hanya kar ya banketa yanda ya dibo saurin nan. Ajmal har ya shige Nisha sai kuma ya ja ya tsaya tare da jiyowa ya Kai kallosa gareta yana mai cusa hannayenshi cikin picked d'insa ya na kallon Nisha sai da ya ya kalleta sama da kasa kafin ya ce

"Follow me," daga haka ya juya ya ci gaba da tafiya, rass kirjin Nisha ya wani irin bugu mai kuma zai ce mata yanzu Nisha ta ta shiga tambayar kanta ganin Ajmal har yafice daga parlourn ko waiwaye baiyi ba yasa ta bi bayanshi cikin hanzari kafin Nisha ta isa haraban gidan Ajmal har ya doshi side d'insa.

Zaune ta ke cikin kyakykyawan rigar baccinta ya'r siriruwar riga mai iya cinyarta tana zaune tana danna wayar ta Aheel na bisa cinyarta harya yi bacci ganin shigowar Ajmal be ya sa Heelah ta ajiye wayar hanunta gamida janye kan Aheel daga cinyarta ta mike tsaya tana lallausan murmushi ta shiga yimasa welcome gamida karisawa gabanshi ta rungume shi tana fadi'n

Honey sai yanzu tundazu naga isowar ka but ba kashigo nan ba kawoce side din su Daddy kabarmu da kewarka har Aheel yayi bacci, time din Nisha ta turo door ta sa ko kai a hankali kamar mara gaskiya tsayawa tayi turos lokacin da ta kalli Heelah na rungume da Ajmal , Ajmal zame jikinsa yayi daga nata ya kai kallonsa ga Nisha wacce tayi tsamu tsamu da ita kamar a ce mata shiii ta gudu, harara Heelah ta bi Nisha da shi ta nasanye cikin sleeping dress riga da wando sai bin shape d'inta yake to waima mai ya kawota side din nan ne a wannan time din kardai a ce fakon time din dawowarshi ta ke tana biyo shi

"What are you doing here? da daren ma sai kin biyoshi ko ce miki yayi yana bukatar wani abin" Heelah ta fad'i a zafafe but ga mamakinta sai gani tayi Ajmal ya juya ya nufi Nisha tare da jawo hand dinta fuuuu ya haura da ita upstairs wayaga idon Nisha kamar ana jijjiga bera abuta

Direct bedroom d'insa ya nufa da ita yayinda ya tura door da karfi ya janyo Nisha ya wurga ta ciki sai da ta shiga yin tangal tangal ta na naiman faduwa kafin ta sai ta tsayuwarta da kyau daga neman faduwar da ta ke kokari yi jikinta sai rayawa ya ke kamar mazari idonta tuni ya raina fata sun cicciko da hawaye tana neman yin kuka, kallon Ajmal ta yi wanda yayi mata k'uri da idanuwansa wanda su ka canza launi sai wani huci ya ke kamar wani tsohon zaki nan ta ga ya shiga ta kowa ya nu fo ta wanda yasa Nisha ta shigayin baya cikin sauri tsoro da firgici duk ya cika k'wanyarta gaba daya ta rasa inda zata shiga ganin yanda Ajmal ya nufota gadan gadan ta San ba lapia ba especially yanda ta ganshi cikin wani yanayin fusata.,

Nisha sai ja da baya ta ke har sai da ta zo karshin bedroom d'in ta kafin ta manne jikin bangon tare da hade hannayenta guri guda gamida rintsa idanu lips dinta sai bari ya ke ta na son cewa wani abu, time din da Ajmal ya kariso dab da ita har tana iya jiyo sautin zazzafan numfashinsa yanda ya ke fita, kallonta Ajmal yayi kafin iya bude baki ya na fadi'n

"Look at me "

Jin muryan Ajmal a fisge ya na magana yasa jikin Nisha cigaba da k'yarma kanta sunkuye ta kasa daguwa ta kalleshi kamar yanda ya umurce ta ba karamin tsoronsa ta ke jiba balle kuma hada ido da shi cikin wannan sigar da ya zo mata na rashin sanin dalili,

"Dan Allah kayi hakuri" Nisha ta fad'i cikin barin lebe tana jinjina hannayenta

"I say look me "

Nisha ta ji ya kuma fad'i karo na biyu a tsawace gamida dafa hand d'insa jikin bango ya kareta cikin hanzari Nisha ta dago kai ta kalli Ajmal wanda ya matso dab da ita tamkar zai shige jikinta daddad'an turarensa mai wuyar mancewa sai dukan hancinta ya ke, ido cikin ido haka Ajmal da Nisha suke kallon junansu ko kyafta ido ba maiyi cikin su rirarun hawayen da suka makale cikin kwarmin ido ta suka shiga yin zaryan gangaruwa saman lallausan kumatunta still ba ta iya kauda idonta daga kallon kyakykyawan face din Ajmal ba mai cike da sirrukan kyau da kwarjini, haka shima Ajmal gaba daya ya shagaltu da kallon tsantsan sirrin kyau irin na Nisha karon farko da ya zubawa yarinyar ido ba tare da ko kyaftawaba ko dauke idonsa daga kallonta ba surutan da ke cikin bakinsa duk ya kasa yinsu saboda shagaltuwa da kallonta wanda ya sa shi kasa furta komai , lokaci daya kamar wanda aka tsikareshi kuma ya dauke idanunsa daga kallon Nisha gamida ja baya kad'an daga bisani ya juya mata baya ya shiga tattaro nitsuwarsa ya rasa wani irin shagala yayi da kallon yarinyar haka,

Heelah ce ta turo door da karfi kamar wata za kanya yayinda idanuwanta su ka sauka kan Nisha wacce ta makale jikin bango ta rungume hannayenta jikinta sai hawaye ta ke shi kuwa Ajmal ya juya mata baya ya lumshe ido yana sauke ajiyar zuciya tare da sai ta nitsuwarsa, because ya rasa tunanin sa da nitsuwarsa time din da ya daura eyes d'insa bisa face d'inta gaba daya tunanisa ya juye, a zafafe Heelah ta karisa shigowa tsakiyar dakin tana cillawa Nisha wani banzan kallo tana fadi'n

"Amma dai ke anyi mayya wallahi tirr da halinki zo kiwuce kufita, ki fitarmin daga daki kafin nayi kasa kasa da ke muna fukar banza dama nasan sai kin sanya mijina ya fad'a cikin tarkon ki kamar yanda kikasa yan uwansa, na tsaneki banason ganinki sam ban san ina tunanin su HAJIA ya ta fi ba ta dauko wannan annobar ta kawota cikin familynmu wallahi sai na kasheki kowa ya huta inba haka ba bazaki bar zuciyata ta samu salamaba Heelah ta fad'i kamar zatayi kuka ta nufi Nisha tayi kanta tare da kai hanu da nufin shako wuyar Nisha but sai Ajmal ya sha gabanta yatsaya


"Please leave me yau sainayi ajalinta" Heelah ta fad'i cikin ta kaici

"Are you mad kinsa mai kike fad'i kishiga hankalinki kisan mai kikeyi" Ajmal ya fad'i a tsawace cikin taakaici da bacin rai

"Eh nafadi saina kasheta saidai nima akasheni bazan bar wannan yarinyar ba yau"

Heelah ta fad'i cikin kunar rai gamida yin gefe tana shirin damko Nisha nan madai ya kuma tareta gamida ri ke ta yana kokarin hanata nanfa Heelah ta rike ce musu ita ala dole sai ta kashe Nisha, Nisha ganin Ajmal na rike da Heelah yana kokarin hanata abunda ta keson yi ya sa ta rabe ta gefensa ta fice da gudu ta bar bedroom din, ta kaici duk ya ishi Ajmal ganin haukar da Heelah ke yi tana kokarin bin bayan Nisha cikin bacin rai Ajmal ya dauke ta da mari sai da ta ga wasu taurare daga bisani ya cillata saman bed, sam baiso abun ta kai ga mariba but yaga sai ya kai hanu ta ke iya nitsuwa ta fiskanci yaren kuka sosai wuiwui Heelah ke yi tana birgima saman bed kamar wata karamar yarinya gefe Ajmal ya zauna bisa sofa yana kallonta yanda ta ke kurma ihu tana kuka tamkar wacce ta zauce Ajmal sai huci ya ke yana furzar da zazzafan iska cikin bakinsa cikin ta kaici Ajmal ya jawo hand din Heelah ya turata waje kafin ya tura door d'insa ya rufe, hanunta na kan face d'inta ta ruga da gudu ta yi bedroom d'inta ta kwanta saman bed d'inta ta ci gaba da kuka,

Ajmal zama ya dawo ya kumayi yayinda ya dafe goshinsa da hand d'insa biyu Heelah ba k'aramin caza masa kwakwalwa ta ke ba gaba daya al'amuranta babu tunani da lissafi Sam ya rasa mai ke damunta duk da wasu dabi'un nata zuwan Nisha ne ta farayunsu wai ita kishi ta wani gefen kuma tunani ya ke wacce wannan yarinyar da ta saye zuciyoyin ahalinsa da harsukayi tunani daura masa aure da ita ba tare da wani tunani ko shakkan yin hakan ba ko dan sunga yayi shiru ya zuba musu ido da fari shiyasa suka sake yin wani iko kansa ba tare da tun tubarsa ko jin ta bakinsa ba to wai shin wacce wannan yarinyar kuma suwaye familynta inane tushenta duk ba su ta ba wannan tunaniba ta shi daya suka k'ak'aba masa ita babu wani shakku ko bincike, lumshe idanu yayi gamida jan wani goron numfashi kafin ya mike ya cire kayan jikinsa ya daura towel ya nufi bathroom,

Sai da yayi wanka ya fito ko tsayawa wani shafa mai baiyi ba ya zira jallabiyar sa ya fito ya nufi downstairs tsabar saurin da yake na kiran Daddy d'an shopping d'in da yayima ya mance shi cikin mota gashi dare ma yayi sosai coffee kawai ya zauna ya shaa yana dan tunane tunane har ya gama ya mike ya nufi inda Aheel ke kwance saman sofa gefensa saman table kayan ciye ciye wanda suka gama kodumo da mom d'insa saman shoulder d'insa Ajmal ya daura Aheel ya nufi dashi upstairs daga nan ya wuce da shi bedroom d'insa ya kwantar da shi kafin shima ya kwanta gamia rage musu light daga nan ya lumshe idanu mai makon bacci ya dauke shi but sai face din Nisha ya ke hango wa da d'an k'aramin pink llips d'inta da ke motsawa a hankali bude ido Ajmal ya kuma yi da sauri yana zazzare idanu wai mai ya sa meshine yanzu da ya kasa bacci ya ke tunanin mara amfani irin haka, ya juya nan ya juya can haka Ajmal ya dinga yi har ya samu bacci b'arawo ya saceshi,.

Bangaran Nisha tunda ta samu ta fice tashige part dinsu tanufi bedroom d'insu time din harsu Fadeelah sunyi nisa da bacci haka itama ta nemiguri ta kwanta gamida dunk'ulewa guri guda gaba daya duk a tsorace ta ke fatan ta Allah ya kawo mata dauki gamaida Heelah da Ajmal because zasu kasheta kwananta bai kareba especially Heelah da ke ikirarin zata kashe ta yanda ta fahimci zafin mahaukacin kishi irin na ta ko shakka babu zata iya aiwatar da abunda ta ke fad'i.

Washe gari karfe 9 dawasu yan mintuna Daddy da Ammi ne zaune bisa dining table gefe Hajj mama suna zaune suna breakfast suna yar hiransu yayinda Hajj mama ta kalli Daddy da

11 / 24