Author : Khaleeseart Abdullahi Raeys Category : Hausa Novels 001
jin abunda Hajj mama tace yasa ba wani musu Nisha ta shiga d'aga k'afafuwanta gamida karisowa a hankali ta nemiguri kusa da su fadeelah ta zauna gamida kamewa tana zare yan idanu dan ko d'agawa Mom din Heelah gaisuwa ta kasayi dan ta san ba lallai ta amsa gaisuwanta ba yanda take ta faman wurginta da wani muguwar kallo.
Dan g'yara zama Hajia tayi tana kallon Heelah da Mom d'inta tana fadi'n
"To a takaice kun kawo k'orafine kan Nisha da aiyimata iyaka ko ince katanga daga zuwa side din Heelah?". Hajia ta tambaya tana kallonsu
"Kwarai kuwa tunda ita Heelah ba kuturwa bace ballai ace ko gazawa tayi wajan kula da mijinta da d'anta ballai ace har sai wata banza can daga gefe ta taimaka mata wajan kula da mijinta da muhallinta". Hajia jumana ta fad'i tana kallo Nisha cike da ta kaici.
"To ina so kusani ko shi Modibbo a yanzu bashida daman iya yakice Nisha daga tsaginsa saboda matsayin Raheelah da Nisha abu gudane ta ban garansa a yanzu".
"Kamar ya Hajia mai kike fad'a ne haka? Heelah fa matarsace kuma yar uwarsa ta jini ba suda alak'ha da wannan tsincecciyar magen". Hajia jumana ta fad'i cikin kasa fahimtar zantukan Hajia da inda suka dosa.
Wani k'ayataccen murmushi Hajia ta saki cikin rashin damuwa ta kuma kallon Hajia jumana tana fadi'n
"Hakane kamar yanda Raheelah ta kasance daya daga cikin y'ay'an gidan nan kuma babban sirika cikin gidan to Haka itama Nisha ta kasance a yanzu"
"What!!! ?".Heelah da KB suka fad'i a tare suna zare idanu kafin Heelah ta mike tsaye tana bin Hajj mama da kallon mamaki cikin maganganun ta .
Hajia jumana Heelah ta bi da kallo wacce ta mike tsaye cikin al'ajabi tana bin kakartasu da kallo kan Heelah gaba daya ya dau zafi.
Hajia jumana kallon ta tamayar kan Hajia cikin mamaki ta shiga tambayar ta.
"Kina nufin itama sirikan gidan nan ce ?". ta tambaya Tana zare idanu
"Kwarai kuwa sirikar gidan nan ce kuma matar Modibbo ce abokiyar zaman Heelah tun ba yanzu ba abunda ya dad'e yana rufene yau kuka bukaci sa ni dole sanar daku gamida yi muku bayani ina fatan kun fahimta?".
"Innalilahi wa'ina ilaihi raju'un yanzu wannan abunne kushiyar Heelah wacce zatayi shi da ita?"
"Kwarai kuwa kam ai ba ta fi karfin amata kishirya ba ko wannan da kike gani tafi Heelah sau dubu amfani". Hajia ta fad'i cikin alfahari tana kallon Nisha.
"Haba Hajia wannan karun kuma ta kan Heelah abun ya biyo abunda aka min shi aka kuma na na tawa akan y'ata? haba Hajia mai na tare muku a rayuwar nane fisabilillah kuma arasa da waza a hada kishi da Heelah sai wannan yar k'aramar alhakin mai zubin muna fukan matan tsintacciyar mage da bata mage".
"K'addarace ta zo da haka kuma kune silan faruwar hakan, kamar yanda kika amshi naki k'addaran haka itama zatayi hakuri ta amshi k'addaranta". Hajia ta fad'i tana mike k'afafuwanta cikin rashin damuwa na ko ajikinta, parlourn shiru yayi KB saki baki yayi yana kallon Hajj mama gefe kuma ya koma ya kalli Nisha wacce kanta ke sun kuye tana wasa da yatsun hannayenta dasuke ta faman bari daga ka ganta kasan a tsorace take kafin Kb ya kuma kai kallonsa ga Mom d'insu wacce ta ke cikin tsantsan bakin ciki da ta kaici zallah .
Kb da Hajia jumana tare suka kai kallonsu ga Heelah wacce tunda tamike tsaye ta kasa tsugul wani zazzafan huci ta dinga furzarwa zufa sai faman ke tu mata yake lips d'inta kuwa sai faman rawa yake tana su cewa wani abun Amma yanda zuciyarta ke faman ta farfasa saboda bakinciki ta kasa magana.
"Fadeelah ya kikaga sarakan kishi sai zufa ake kamar anyiwa sarki Karya?." Reeda ta fad'i k'asa k'asa.
"Aikuwa kalli yanda ta koma kamar anjika mage a ruwa". Fadeelah ta bata amsa cikin rad'a Nisha duk tana jinsu Saura kad'an Fadeelah da Reeda su tuntsire da dariya sai kowaccen ta tushe bakinta saboda kar sautin dariyarsu ya fito fili.
Wani ihun ta kaici Heelah tasake gamida zubewa kasa tayi zaman dirshen kamar ta b'abb'iya tana shure shure kamar yar bori, Nisha kamar ta sake fitsari gurin dan tsoro su kansu su Fadeelah sai da suka sha ruwan jikinsu ganin abinda Heelah keyi kamar wacce ta kune akai.
Haka Hajia bayan mamaki abun har tsoro ya bata ta shiga zazzare ido tana kallon ikon Allah , Hajia jumana ne ta matsa ta shiga d'agota tana fadi'n
"Innalilahi wa'ina ilaihi raju'un naga takaina ni jumana Yar nan ki kwantar da hankali ki karkije ki sawa kanki wani ciyon na rasa tudun dafawa taso mutafi kb taso ka tayani daga ta mukaita mota ". Mom ta fad'i cikin damuwa gamida bacin rai cikin hanzari Kb yasa hanu suka sun kuci Heelah sai faman fisge take tana fadi'n su kyaleta yau saita kashe Nisha .
Ganin yanda take borin bilhakhi da gaskiya ta na neman kwace musu yasa Kb ya tattaro karfinsa ya sun kuceta ya azata bisa shoulder d'insa ya fice da ita daga parlourn Heelah sai faman bugun bayansa take da karfinta kamar ta samu ganga shikuwa ko ajikinsa kamar an tsikari kakkausa.
Hajia jumana kuwa sai faman wai waiyansu Hajia da Nisha ta ke ta na kumbura baki daga nan itama ta bi bayansu ta fice ....
Karfe 8:30 familyn zaune suke Dining table suna gudanar da dinner d'insu kamar yanda suka saba suna yar firansu wannan karon harda Daddy a cikinsu kasamcewar yau dawowar wuri yayi, Hajj mama tas ta gama kwashe musu abunda ya furu dazu da yamma zuwansu Heelah da Mom d'inta da kuma kb abun dariya abun takaici su farida kuwa dariya kamar ba gobe suna mai da yanda akayi
"Ikon Allah abun mamaki basa k'arewa kodai almatsutsai gareta ba a saniba?". Daddy ya tambaya cikin mamaki
"Bawani shashanci ne kawai gamida kishi idanuta sun rufe karfi da yaji zata maida kanta bitacan akan kishi banza Allah dai ya kyauta". Ammi ta fad'i tana tab'e baki
"Amin ". gaba ki dayansu suka amsa gamida cigaba da gudanar da dinner d'insu suna hira banda Nisha da tayi shiru tana saurarensu yayinda suke hiran ta su jikinta duk a sanyaye Ammi kallon Nisha take afakaice cikin tausayawa tasan yanzu Nisha na cikin tsoron kasancewarta inuwa daya da Heelah tasan wannan ma kadai zai dinga sanya ta cikin tunani hankalinta yaki kwanciya.
Wani nan nauyan ajiyar zuciya Ammi ta sauki gamida ture plate din gabanta ta mikewa tsaye tashiga yi musu bakwana zata shiga bedroom din ta kwanta tasanar dasu cewa gobe tana da uzuri a office dawuri zata fita shiyasa takeso tayi bacci da wuri gudun makara kafin dagan tanufi upstairs tashige bedroom din ta.
Jim kadan shima Daddy ya mike gamida yi musu sallama ya bi bayan Ammi because ya lura da yanayinta da damuwa ta bargurin hakan yasa ya bi bayanta ya barsu Hajia gurin wanda suka cigaba da hiransu.
Koda ya isa bedroom din Ammi zaune ya hangeta bakin bed ta rafka uban ta gumi tana tunani , karisawa Daddy yayi ya zauna kusa da ita cikin natsuwa ya kalleta gamida tambayar ta.
"Lapia kuwa hajjajo", Daddy ya tambaya cikin kulawa
"Uhm sam na kasa farin cikin kasamcewar wannan lamarin tsakanin Nisha da alh k'arami sam banso wannan k'addaran auran ya fad'a kan yarinyar nan ba". Ammi ta fad'i cikin damuwa.
"Kash haba hajjajo mai yasa zaki fad'i haka kuma mai abun rashin jin dad'in acikin wannan Lamarin Allah ne fa ya had'a abinsa ".
"Bawai ina ja da hakan bane kawai ina tausayin yarinyar ne ganin halinda ta tsinci kanta tsakanin mutane biyu duk da nasan Modibbo ba son Nisha ya keba kawai yayi biyayya ne ga maganar mu but nasan zai zauna da ita cikin aminci kamar yanda ya zauna da Heelah ba tare da k'yara ko hantara ba.
"To amma duwana shine ina tsoron Heelah da mahaifiyarta ina tsoron abunda zaije ya dawo ina tsoron su saka yarinyar nan a gaba bana son abinda zai cutar da ita ko yasata cikin damuwa kasan Nisha ba mai son haya niya ko fitana bane kuma gata da tsoro ballai ace zatayi hobb'asan karbawa kanta yanci a zaman takewan su ita kuma Heelah rigimarta ma ya fi karfinta ranar ba kaji abunda take fad'i akan Nisha bane time din da nake nocking door d'insu a tunaninta Nisha,".
Dan g'yara zama Ammi tayi gamida kallon Daddy da kyau ta cigaba da fad'in.
" Ni son samu ne ma idan abun zai zo da fitana gamida tashin hankali araba musu gida kawai ita Nisha abar mana ita nan ita kuma Heelah ya maida ita can sabon gidanshi ta zauna acan suyi nisa da juna.." .
"Shiii ya isa haka please insha allah ma ba abunda zai faru , muna nan zamu saka idanu akansu ba lallai rabe muhalli shine ma fitaba ganin motsawansu kan idanumu shi zaisa mudinga ankara da halinda suke ciki". Daddy fad'i cikin nusar da ita yanda zata fahmita.,
Shiru Ammi tayi tana sauraren maganganunsa cike da gamsuwa Ammi ta jinjina Kai tana fadi'n
"Gaskiya ne zancen ka yana kan hanya yallabo'i to Allah ubangiji ya hade kawunansu".
"Amin". Daddy ya amsa gamida mikewa tsaye yana fad'i
" Bari naje nadan watsa ruwa because zafi nakeji sosai". Gyada masa kai Ammi ta yi harya mike da nufin fita sai kuma ya koma ya zauna yana fadi'n
"Au na mance ban sanar dake ba gobe za akawo kudin auran hajia k'arama ya kamata a shiryawa zuwansu da yaune but ban samu dawowa da wuri bane saboda uzurirruka".
"But insha allah guraren 4 na yamma zamu samu halartarsu zuwa cikin gidan nan ".
"Masha Allah insha Allah Allah bari na sanarwa da Barka tun yanzu idan da akwai abin da babu a tanada duk da gobe fitana office zai kasance dawuri but zan dawo dawuri saboda ayi komai da ni". Ammi ta fad'i cikin farin ciki tana washe baki.
"To shikenan ya kamata" . daga haka suka Mike a tare Ammi na biye da shi suka fito tare Daddy ya nufi bedroom d'insa ita kuma Ammi ta nufo downstairs.
Koda Ammi ta sakko ba ta tadda kowa ba duk sun watse sun nufi makwancinsu bayan da suka gama Shan firansu hakan yasa direct Ammi ta nufi bedroom din Barka time din har Barka ta suma shirin kwanciya jin nocking bakin door d'inta yasa ta mike ta bude ganin Ammi tsaye bakin door din ta shiga washe baki
"Sorry hala kinsuma bacci na katseki".
"Ah rankiyadad'e bawani bacci shiri dai nake yanzu wani abin kike bukatane ?". Barka ta tambaya tana washe baki.
"Am Barka dama gobe muna da bak'i cikin gidan nan so inason list din abunda kitchen dimu yake da bukata zuwa gobe da safe kafin na fita office".
"To shikenan Hajia ba matsala insha allah kuwa". Barka ta fad'i cikin girmamawa, daga haka Ammi ta juya tanufi upstairs ta koma bedroom d'inta.
Guraren 10 motar Ajmal ta kunno kai haraban gidan wanda mai gadi ya bude masa gate ya shigo yayi parking daidai parking space daga nan ya fito daga motar cikin ta fiyar k'asaita gamida kamewa ya nufi side d'insa..
Ajmal
Story and writing
By
Oum amreesh
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/ ?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Book 2
Page 93
______ Koda ya karisa shigowa komai fine kamar yanda ya zata parlourn sai wani sassanyan k'amshi ke tashi na air freshener, Cikin natsuwa Ajmal ya suma haurawa upstairs ya nufi bedroom d'insa yana isa bedroom d'insa ya tura door ya shiga ya maida motar ya rufo.
Lumshe idanu Ajmal yayi jin wani laune k'amshi dake wanzuwa na musamman cikin bedroom din wanda yasashi karisawa a hankali ya karisa tsakiyar d'akin a kasalance sai wani lumlumshe idanu ya ke kamar mai jin bacci da alamun gajiya sosai a tare da shi.
Daidai bakin bed d'insa ya karisa zauna ya na wani sake ajiyar zuciya a hankali daga nan ya kai hanu yasuma zare tie din dake mak'ale jikin wuyarsa yana daga zaune ya ra ba kansa da kayan dake jikinsa da yake jin sun ishesa sunyiwa jikinsa nauyi ya rage daga shi sai short cikin yanayin kasala da k'iwa Ajmal ya mike bisa lallausan bed d'insa face d'insa na kallon celling ya rintsa idanu.
Jin motsin bude door din bathroom yasa Ajmal ya dan waro idanu ya kai kallonsa ga gurin nan idanun shi sukaci karo da na Nisha wacce ta bud'o door din cikin hanzari tana shirin fitowa wanda ganin Ajmal kwance saman bedroom yasa ta danyi jim tana wutsi wutsi da idanu duk saurinta kenan kar Ajmal ya dawo ya taddata sai yanzu take masa gyaran bedroom d'insa wanda tun ido na ganin ido ya sanya ta but ita kuma tuni ta manta da batunsa domin kuwa har tayi shirin bacci ta kwanta ta tuna da aikin da ke gabanta but wunin yau da hankali ta baya jikinta yasa ta mance shalaf.
Shima tunani Ajmal kenan bata tashi masa gyara ba sai yanzu da tayi ra'ayi Ajmal dauke idanu yayi daga kallonta ya maida idanun ya rintsasu cikin rashin damuwa da lamarinta .
Wanda yasa Nisha ta hadiye miyu mai daci kafin ta fitowa ta shiga karisowa tsakiyar d'akin tana kasa da kai ganin yanayin da Ajmal ke ciki da gashi sai short ya wani mike ko ajikinsa bare kuma ya damu.
D'an tsaya ta yi daga gefe dashi cikin ladab ta dan lankwashe gwaiwowinta kamar mai shirin dukawa ta shiga fadi'n
"San sannu da dawowa", muryanta harna sarkewa, amma bai amsa mata sannunta ba ya bude manyan idanuwansa ya shiga kari mata kallo da ita da yar night gown d'inta wanda ko gwaiwowinta bai isa ba mai tsantsi da taushi ita kanta sai faman ta kure kanta take saboda tsarguwan da kallon da Ajmal ke jifanta da shi.
"What do you want". Ajmal ya tambaya murya can ciki yana wani hade gira ganin ta k'ikam ta masa tsaye bisa kansa , dugun hijab d'inta da Ajmal ya kwanta kai da bai san da zamansa ba Nisha taimasa nuni tana so ta dauka sai time din Ajmal ya mike da ga kwanciyar da yayi jiki ba kwari yana ya motsa fiska kafin ya kai kallonsa ga duguwar hijab din Wanda sam bai lura da shi ba kauda kai Ajmal yayi gamida da hade hannayensa ya shiga yin wata duguwar mika kafin ya mike tsaye cikin zafin nama wanda sai da ya sanya yan hanjin cikin Nisha suka kad'a tayi baya kad'an cikin tsoro ganin yun k'urin da Ajmal yayi wajan mikewa kamar mai shirin kawo hari shikuwa Ajmal dama da gangan yayi hakan Dan kawai ya tsukano tsoronta dan ya san abu kan ya ke tsoratata gashi yanzu ma hardayin wani baya da sauri na zare yan idanu,
Wani harara da Ajmal ya watsa mata kai kace mace ne sannan ya juya abunsa ya nufi bathroom don wanke jikinsa, Nisha tunda ya bar gurin ta kasa dauke idanu akansa ta bishi da kallo tana sauke ajiyar zuciya gamida karewa zubin halittar jikinsa kallo
' masha Allah darirren namiji tsayayye san kowa kin wanda ya rasa wanda ko wacce mace ke fatan samu matsayin madubi a bin haskaka rayuwa gaskiyar salma ne da tace ta godiyawa Allah samun Ajmal matsayin a bokin rayuwa komai ya had'a a abunda ya rasa sai mishkilanci '
"Wai tunanin mai nake hakane ?". Nisha ta fad'i afili ta d'an bugi goshinta kad'an ta sauka kan layi sai faman zantukan zuci take hanu ta Kai ta janyo duguwar hijab d'inta tasanya ta yi ta fice daga bedroom din.
Ajmal wanka yayi sosai ya sakarwa kansa ruwa mai dumi ya shiga tsaftace jikinsa kafin ya fito cikin bathrobe hanusa rike da wani k'aramin towel yana tsantsame ruwan dake bisa suman kanshi ko da ya fito bai tadda Nisha cikin bedroom din ba kamar yanda yayi tsammanin , mai mai sanyin k'amshi Ajmal ya nema ya shafa bisa jikinsa kafin ya nemi duguwar jallabiyarsa fari k'al ya sanya kafin ya fito daga bedroom din ya nufi downstairs domin hadu coffee kamar yanda ya saba ya zamar masa jiki sai yasha kafin kwanciyar sa.
Koda ya nufo parlour ya karisa dining table nan ya lura da abubuwan da Nisha ta jere su gurin ta koma gefe tayi tsaye tana jiran sakkowan sa , Ajmal table din ya bi da kallo yana karewa abubuwan da Nisha ta shirya masa saman table din gwanin sha'awa, shi sam baya jin yuwa already cikinsa ma a ciki je ya ke ba space din saka wani abin kuma .
But bayaso yayi miss special food na ta because yasan yarinyar akwai zakin hanu wajan girki bugu da kari yanda ta iya sarrafa abubuwa kala kala wanda yake so yake iya ci idan yana diban girginta har rasa tunanisa yake da yasan da hidimar data ta nadar masa da ba abunda zaisa ya cika cikinsa duk da yana jin a yanzu ba wani gurbi da wani abu zai iya samun g uri amma bazai gwalewa bajintar ta ba d'an haka ya sanya hanu ya jaa kujera ya zauna .
Yashiga bude kyakykyawan bowl mai dauke da vegetables beef potato soup sai k'amshi kakeji ya nata faman tashi sai oat milk daga gefe cikin cup sai v plate d'in snack shima a gefe ,vegetables soup din nan da yake jin k'amshin sa na faman tsokano hancinsa ya suma da shi .
taikace komai na gurin sai da Ajmal ya taba Nisha duk tana daga gefe tana sato kallonshi ta gefen ido ganin yanda ya zage yanata sanyawa abubuwan albarka, Ajmal yaso shanye oat milk din nan because ya masa dadi sosai but yakasa yanda yake jin cikinsa yayi bala'in cika yaukam yanaga harda koshin haramun yayi don baijin ko k'wak'waran motsi zai iyayi ballai ya mike .
Shiru yayi yana shafo cikinsa wanda yayi masa nauyi kafin ya dago yan idanunsa ya kallo Nisha wacce suka hada ido tana kallonshi itama idanu su haka gameda na juna da hanu ya mata almar kira kafin ya dafa table ya mike tsaye.
Nisha jan kafa tayi k'irjinta