Chapter 16 Reading AJEEMAL Book 2 Hausa Novels By Khaleeseart Abdullahi Raeys.txt Arewa Novels

AJEEMAL Book 2 Hausa Novels By Khaleeseart Abdullahi Raeys.txt

Author :  Khaleeseart Abdullahi Raeys Category :  Hausa Novels 001

Chapter   16 / 24

45K to 48K   out of 70.1K words

da jikin gari sai time din ta shiga kallon bangon bedroom din sannan ta ci karo da kyakykyawan agogo manne jikin bangon bedroom din.

a sukwane Nisha ta mike ta nufi bathroom ta dauro alwala daga bisani ta kai hanu ta janyo duguwar rigarta gamida mayafin ta fito kamar wani wanda akasa ta tsayawa kallon cikin bedroom din domin tsayawa ta yi musamman ta na karewa bedroom d'in kallo ta kalli nan ta kalli can bedroom din ya kwanto matuka komai na ciki blue and white gwanin sha'awa da burgewa komai fine Kai ka ce dama can da mutum wanda ke rayuwa ciki tsakiyar dakin ta koma ta shiga sauya kayanta daga rigar bacci izuwa duguwar rigarta gamida rufa mayafin jikinta kafin ta nemi sallaya ta shin fida ta shiga ta da sallah.

Bayan idarwarta ta shiga mika hannayenta sama gamida kwararo addu'oi ga ubangiji mahalicci sosai da sosai kafin ta mike ko sallayan ba ta tsaya ninkewa ba ta sa hanu ta fisge mayafin jikinta ta cillashi gefe, can saman bed ta nufa ta kwanta ta shiga yin sana'arta ta da ta saba na aikin kuka da ba ya mata wahala, sai da ta yi ya sheta harkanta ya suma yin ciyo kafin ta iya tsagaitawa har bacci yayi nasaran cinye idanunta because dama daran jiya ba ta yi wani baccin kirkiba.

Nisha ita ce ba ta samu farkawa ba sai guraren 10:30 wani azabeben yunwane ya ta data bawai baccin ba ne ya kare mata because rabonta da abincin tun lunch d'in jiya , da dare koma koda Ajmal ya ajiye mata abubuwan ta bawa kasa ci ta yi because ba ta yanayin da zata iya cin wani abu, jiki ba kwari ta sabulu daga saman bed din ta sakko.

Slowly ta ke jan kafafuwanta jikinta kamar wanda aka zarewa laka haka ta nufi gurin door d'in ta cire key d'in da ta sanya ta murd'a handle d'in gamida budewa ta sako kai waje ta na yar leke leke ko zata hango inuwar Ajmal sai dai ba kowa cikin parlourn shiru kakeji sai karan TV da ke aiki cikin parlourn.

Karisowa Nisha ta yi tsakiyar parlourn ledar da Ajmal ya ajiye mata jiya ta zo dubawa amma sai ta ga wayam ba komai gurin hakan yasa ta shiga yin mis mis da idanu ta na ya mutsa face kamar wata mai shirin yin kuka ta nemi guri ta zauna ta na shafa lallausan cikinta wanda ta ke ji tamkar ana gobara ciki , daga can bakin door din ta ji ana nocking wanda ya sa Nisha ta mike a zabure ta na shirin shigewa bedroom sai kuma ta ji wata kakkausan murya daga waje ana duka sallama wanda ya sa Nisha dakatawa tashiga kallon door din da sautin muryan da ake kwararo sallama cikin sassanyan murya Nisha ta shiga amsa sallamar wanda daga nanne a ka turo door akashigo.

Mai gadi ne ya shigo gamida rawar jiki ya na washe baki hannayenshi dauke da wata kyakykyawan ledar ya karisa shigowa tsakiyar parlourn daga gefe ya ajiye saman table daga bisani ya kai Kallonsa ga Nisha wacce taimasa zuro ta na binsa da idanuwa.

" Sannu hajjajo dama yallabo'i ne ya turo da wannan aikar akawo miki tundazo na keta zaryar sallama naji shiru ba amsa ba yasa na yi tsammanin bacci kike karna ta kuraki?"

" Nagode" abun da Nisha ta fad'i kenan ta rakashi da idanu har yafice daga parlourn ya maida mata da kofar ya rufe, cikin hanzari Nisha ta isa gaban table gamida janyo ledar ta baje kasa ta shiga budewa tun kafin ta karisa bude ledar ta ke jin wani daddad'an k'amshi wanda ya sanya yawunta tsinkewa abubuwan ciye ciye dana tande tande gasu nan birjik Irish with plantain chips and crispy fried chicken gefe kayan itacuwane ingatattu ga snacks and drinks iri da kala ba tare da ba ta lokaci ba Nisha ta shiga sanyawa duk wani abunda ke cikin ledar albarka kafin ta yi hamdalah gamida sauke wani ajiyar zuciya jin cikinta ya dauka tam alhamdulillah daga nan ta shiga mikewa ta nemiguri saman sofa ta mike ta kwanta gamida kurawa kyakykyawan TV da ke kunne parlourn ya na aikin wanda Ajmal ya tafi ya bari a kunne ya na aiki.

Haka Nisha ta zauna ita kadai parlourn cikin kewa sai TV da ta sanya gaba tana kallo wanda kura masa ido kawai tayi but tunanin da hankalinta sam baya gurin kwallon ya na can wani guri daban haka ta na cikin wannan ya nayin bacci ya kuma awungaba da ita daga inda ta ke kwance...

Karan horn d'in mota daga waje ne yasa me gadi zaburuwa ya fito cikin hanzari ya shiga yayi gate wata bakar motar ta kunno kai cikin haraban gidan wannan karon Ajmal shi kadai ba kowa tare da shi ko parking bai tsaya g'yarawa ba ya fito cikin hanzari ya nufi ciki.

Koda ya shigo parlourn kwance ya tarar da Nisha ta yi d'aid'ai ta yi nisa cikin bacci gefe kuma kayan ciye ciye da ya kawo mata ne wanda ta gama cika musu aiki ta koma gefe ta yi kwanciyar ta, Ajmal hannayensa ya zura cikin pocket d'insa ya kafin ya shiga ta kowa a hankali ya har ya kariso tsakiyar parlourn ya tsaya.

Ajmal Nisha kawai ya zubawa manyan kyawawan fararen idanunsa ya na kallota tunda ga sirarun fararen kafafuwanta har izuwa kyakykyawan baby face d'inta yanda kasan mai k'wak'ulu mak'uran kyanta haka Ajmal ya zuba mata idanu ya na binta da su , time daya kuma Ajmal ya d'an waro idanu ganin wani wawan mik'a da Nisha ta yi gamida juyi da nufin g'yara kwanciya wanda ya sanya Ajmal cikin sauri ya shiga karisawa gaban sofan da ta ke wance ya sanya dugayen hannayensa ya taru ta ta fadu bisa jikinsa.

A razane Nisha ta bude lumsassun idanunta cikin ya nayi bacci ta ji ta fadu but kada ta bude idanunta da tar ta sauke face d'in Ajmal wanda ke tallafe da ita idanunsa ke kanta a hankali Nisha ta shiga zamiwa jikinsa ta mike tsaye gamida yin baya ta na kallon Ajmal wanda shima ya mike tsaye gamida cillo mata wani harara kafin ya wace ya nufi bedroom ya bar Nisha tsaye tsakiyar parlourn sai faman sosa kai ta ke, jinki a ma ce Nisha itama ta juya ta nufi dayan bedroom din ta mai da kofar ta rufe .

Zama bakin bed Nisha ta kumayi cikin damuwa ita tarasa zamar mai ta ke cikin wannan gidan gaba daya kadaici da kewa ya dameta sam gidan babu dadi cikin kwana daya har tayi miss yan uwanta su Reeda wanda suma suke cikin miss d'inta idanu ta shiga wulga jikin bangon dakin ta kalli agogo karfe 4 har ta wuce sam ba tayi tsammanin tayi bacci mai dugun zango hakaba dan hakan ya sa ta mike ta shiga cire duguwar rigarta tare da nemi towel ta daura daga nan ta nufi bathroom .

wanka ta yi gamida alwala sannan ta fito ta nufi saman sofa ta janyo wannan duguwar rigar abaya wanda Ajmal ya kawo mata Nisha gaban mirror ta nufa gamida manna duguwar rigar jikinta ta na karewa rigar kallo ta jikin mirror abayar tayi matuk'ar kyau sosai dagani kuma kaga tsadaddiya gashi mannawa kawai ta yi jikinta ta ga yanda rigar ya haskota sosai, murd'a handle d'in da a kayine gamida turo door kai tsaye yasa Nisha juyawa ta kai kallonta gareshi lokacin da Ajmal ya kunno kai cikin bedroom din gamida mai da door din ya rufe face d'insa ba alamar wasa ciki rigar da ke rike hanunta tana kokarin sawa ba ta san sanda ya zame ya zubuce daga hanunta ba kamar wani wanda ta ga mala'ikan mutuwa haka Nisha ta shiga zare idanu ta na yar kame kame ganin daga ita sai d'an towel wanda ko gwaiwarta bai karis isaba.

Kallo kawai Ajmal ke bin ta da shi ya na daga tsaye ya na kallonta yanda ta ke ta muzurai ta na zare idanu kamar ta yiwa sarki karya gamida sitirta jikinta da hannayenta biyu , Nisha direct bathroom ta nufa zata koma sai kuma ta tsinkayi maganar Ajmal cikin kakkausan murya ,

"stay here "

jiki na rawa gamida k'yarman Nisha ta tsa cak daga inda ta ke jitayi kamar ta tuna rami kasa ta shige kanta kasa sai faman mammatse idanu ta ke gaba daya kirjinta ta sai wani irin bugu ya ke ya fahimci yanzu bayan tsoronsa da take ta koyi salon guje masa , cikin natsuwa Ajmal ya shiga ta kowa ya na kallonta daga sama har izuwa kasa sai da ya zo dab da ita sannan ya tsaya .

Nisha ja da baya ta danyi ganin yanda Ajmal ya matso ta very close kamar mai shirin rungumarta carab ya riko hand d'in Nisha ya fisgota jikinsa gamida bin sirarun fararen kyawawan hannayen Nisha da kallo wanda take ta faman kankame jiki gamida rungume jikinta da hannayen na ta.

Ajmal hanu ya kai bisa nata hannayen kafin ya sauke duk hannayen na ta kasa gamida bin duk ilahirin lallausan jikinta da kallo, nanfa jikin Nisha ya suma bari tamkar mai jin sanyi ko daga idanu ta kalleshi ta kasa yi dayan hand d'insa ya kuma sawa ya azashi kasan haban Nisha gamida dago habarta face d'inta na faskantar ta sa still de Nisha ta kasa daga idanuwa sai pink lips d'inta da keta faman rawa.v

"Look at me"

Ajmal ya fad'i cikin wata raunanniyar voice Amma mai makon Nisha ta sanya idanunta bisa nashi ta kallishi kamar yanda ya fad'i but sai gani yayi ta lumshe idanu tana shako daddad'an k'amshin turarensa mai dad'in gaske bisa hancinta zuciyarta sai wani bugu take da karfi kamar a mafarki ba tare da ta yi tunani ko tsammanin ba sai tsintar lallausan harshe Ajmal cikin bakin ta wanda ya Kai mata wani kyakykyawan sumbata mai wuryar mancewa yayinda ya kama lallausan lips d'in Nisha yana mata wani sucking cikin wani irin salo .

Shi kanshi Ajmal baiyi tsammanin haka daga gareshi ba kawai ya tsinci kansane cikin wannan ya nayin ya kuma kasa dakatar da kasan daga aikin da yake.

Nisha waro idanu waje ta yi kamar zasu fado kasa yayinda ta shiga fizgo numfashinta da ke kokarin nemansa ta rasa gaba daya jikinta ne yayi wani irin sanyi kamar kankara ya mutu murus kafafuwanta da sukayi raune cak suka tsaya daga rawar da suke nan Nisha ta sakewa Ajmal jikinta gaba daya because jitayi kamar anzare mata lakan jiki gaba daya .

Jin yanda Nisha ta sake jiki wanda ya sa suka kusa kifewa kasa because shima Ajmal ya gama sake jiki ya fada can wata dunyar cikin yanayin na mutuwar jiki slowly Ajmal ya shiga zare lips d'insa daga na Nisha ya zuba mata irinanun idanunsa wanyanda suka canza launi duk ya gama fita hayyacinsa ganin yanda Nisha ta sake jiki ta lumshe idanu kamar wacce ta yi sumar tsaye yasa Ajmal g'yara tsayuwa da kyau ya sanya hannayensa biyu ya sunkuci Nisha ya karisa da ita izuwa bed ya kwantar da ita .

Ajmal bin Nisha ya yi da idanu wacce ke kwance lamo shiru ko motsawa ba ta yi sai zallar sauke ajiyar zuciya da ta ke ta faman jerowa shima Ajmal d'in ajiyar zuciya ya sauke kafin ya dire idanusa saman santala santal fararan cinyoyinta da su keta faman shining yana kallo a hankali har izuwa saman kanta nan ma ya bi dugon suman gashin kanta da ke baje saman bed baki wuluk da shi daga nan kuma ya garzaya kyakykyawan face d'inta ya zuba mata idanu ya na kallon dan k'aramin tsukekken pink lips d'inta, Ajmal hanu ya kuma kaiwa saman lallausan lips d'in Nisha gamida jan leben kasan a hankali ya na jijjiga shi yana fadi'n

"He! Open your eyes 👀"

Amma sai jinta shiru yayi bata motsa ba bata kuma bude idanunta ba sai eyelashes d'inta da ya ke ganin yana ta faman motsawa yana rawa ta na son bude idanu but ta kasa because jima tayi gaba daya idanunta sun mata nauyin da bazata iya bude su ta daura su bisa face d'in Ajmal ba da ke zaune gefe wanda ya sanya ta cikin hannayensa ya rank'wafo Kai da jikinsa ya mata runfa.

Numfashi su yana gaureye da na juna ko wannensu ya najin yanda zuciyar d'an uwansa ke buguwa especially Nisha yanda zuciyarta ke ta faman bugu kamar zai faso k'irjinta, Ajmal ganin shi bata da alamar bude idanu ta kalleshi kamar yanda ya fad'i ya sa ya zare hanusa daga saman lips d'in ta ya kai saman k'irjinta daidai madaurin towel d'inta ya suma kokarin kwancewa .

Azabure Nisha ta bude idanu tar gamida kai hanun ta saman na Ajmal ta danne hannyensa da nata tana kokarin hanshi abunda ya ke kokarin yi Sam ba tayi tsammanin abun zai kaisu ga haka ba aikuwa nan Nisha ta shiga kokarin zamewa ta na so ta mike ta tashi but sai dai babu halin hakan.

" Plea., Please! kayi hakuri dan., dan Allah" . Nisha ta fad'i tana girgiza masa kai duk ta wani langwabe ta rikice sai zare idanu ta ke saura kiris ta fashe da kuka time d'in har zufa ya suma keto mata.

"Meyasa zanyi hakuri ?wani abin na ce zan miki?" .Ajmal ya tambaya ya na hade rai, girgiza kai Nisha ta yi gamida sunkuyar da kai ganin wani harara da ya cillo mata nan taga Ajmal ya zame hanusa daga jikinta gamida yin baya wanda ya sa Nisha ta samu kuzarin zamowa daga bed din cikin hanzari ta na g'yara madaurin towel d'inta da ya suma suncewa.

Ajmal raka Nisha yayi da ido wacce ke ta ke faman rawar jiki da hanzari kafafuwanta sai gauraya suke da na juna kankance mai sai sautin faduwa tim kakeji Nisha Taci tuntub'e kafarta daya yashigewa daya garin sauri ta fad'i kan gwaiwowinta Nisha ba k'aramin zafi ta jiba but ganin Ajmal ya mike tsaye ya sa cikin hanzari ta karisa shiga bathroom d'in da rarrafe ta maida kofar ta datse i Ajmal wani guntun ajiyar zuciya ya sauke gamida rintsa idanu ya kuma budewa sam mamakin yarinyar da tsoro over irin nata baya kare masa jibi wani irin sauri da hanzari da take har da su tuntub'e inda zataje ta jiwa kanta wani raunin.

A sukwane Ajmal ya mike gamida ficewa daga bedroom din ya nufi dayan bedroom din zama Ajmal yayi saman sofa ya mike kafafuwa jikinsa duk a mace duk wani motsi idan yayi tunani abunda ya faru tsakaninsa ga yarinyar nan ne ke dawo masa ya rasa ya akayi ya sauka layi ya kama wata hanyar da ban wanda ko kusa ko alama baiyi tunanin hakan zata iya kasancewa ba but ya je yana kokarin kunnowa kansa wata wutar lallai ya zama wajibi ya tattari yarinyar nan su koma gida if not zai iya kirawo kansa ruwanda bazai iya dakatar da shiba because ke b'an cewarsu tare da yarinyar zuciyarsa na d'arsa masa abubuwa dan gane ga yarinyar za iya samun mishkila bugu da kari kuma yanda Ammi ta sa shi gaba da rangwada masa kira gaba daya hankali ta ya kasa kwanciya tunda ya tafi da yarinyar.

Ajmal ya jima zaune gurin yana sakawa da kuncewa kafin ya kai hanu ya dauki
phone d'insa ya shiga duba time 5 saura kafin ya zura wayar cikin pocket d'insa gamida daukan key d'in motarsa ya kuma dawowa parlour.

Nisha sai da ta kuma wani alwalar kafin ta fito still har yanzu jikin ta bai daina rawa ba a hankali Nisha ta dingiso kafarta saboda buguwar da tayi har cikin jikinta ta ke jin zafin buguwar direct door ta nufa ta tsaya gamida murda key kafin ta kuma juyowa ta nufi duguwar rigarta wanda ke ya she kasa ta dauka cikin hanzari ta zura jikinta gamida nannad'e mayafin bisa kanta ta fito fes d'as da ita kamar wata balarabiyar Saudia daga nan ta hau saman sallaya ta shiga ta da sallah sai da tamika duka sallolinda ke kanta kafin ta g'yara zama bisa gurin ta ci gaba da lazimi da yan yatsun hanunta.

Ta dad'e tana zaune gurin ta na lazumi ta na jin yanda zuciyarta ke wani irin sanyi kamar ana yayyafa mata ruwan sanyi har wani lumshe idanu ta yi ta na bada himma , tana cikin wannan ya nayin a zaune ta jiyo nocking daga can bakin door wanda ya haddasa mata faduwar gaba da tsoro .

Nisha ji tayi kamar karta tashi ta bude haka ta zauna ta na kallon door din ta kasa ta shi ta bude , Ajmal dake tsaye bakin door yana nocking amma shiru ba ta bude ba kuma ta na jin nocking din da ya ke gaba daya ransa ya suma baci ya gama hasala har Ajmal ya juya da nufin barin gurin sai kuma ya ji alamun budewarta wanda yasashi dawowa ya tsaya.

Nisha murda handle d'in door din ta yi ta bude gamida fitowa ta tsaya daga bakin kofar kanta sunkuye.

"Bakyaji ana nocking ne da kika kasa ta sowa ki bude?". Ajmal ya tambaya cikin fad'a ya na hararo Nisha wacce ta hade cikin kyakykyawan duguwar rigar abaya da ya kawo mata.

"I'm sorry 😔 ? " .

Nisha ta ce cikin sanyin murya.

"Let's go" .

abunda Ajmal ya ce kenan ya sa kai ya fice daga parlourn , Nisha bayanshi ta bi da kallo gamida mamaki ina kuma zasu Nisha komawa ta yi ta zura talkami bisa kafarta kafin ta kuma fitowa ta bi bayan Ajmal.

Ajmal tuni ya shige mota ya mata key gamida canza ak'alar motar ya na shirin fita mai gadi tuni ya bude masa gate Nisha kawai ya ke jira ta shigo motar su dauki hanya Amma sai hangota yayi ta jikin mirror safaman jan kafa take kamar wacce kafafuwanta suka samu matsalan shanyewa.

A hankali Nisha ta kariso jikin motar gamida bude kofar motar ta shige a sukwane Ajmal sai faman hararota

16 / 24