Chapter 20 Reading AJEEMAL Book 2 Hausa Novels By Khaleeseart Abdullahi Raeys.txt Arewa Novels

AJEEMAL Book 2 Hausa Novels By Khaleeseart Abdullahi Raeys.txt

Author :  Khaleeseart Abdullahi Raeys Category :  Hausa Novels 001

Chapter   20 / 24

57K to 60K   out of 70.1K words

saman bed din Ajmal oho to koma mai ya kawo shi nan din? Heelah ta shiga tambayar kanta tana kallon ribbon din.

Tana cikin wannan ya nayine Ajmal ya fito daga bathroom daure da towel bisa waist d'insa hanusa dauke da wani k'aramin towel din yana tsantsame ruwan jikinsa Heelah dai kallonsa ta ke har ya nemi duguwar jallabiyarsa ya sanya.

Heelah zamowa ta yi daga saman bed din gamida janyo yar rigarta ta sanya ta nufi Ajmal wanda ke gaban dreesing mirror yana g'yara suman kanshi.

"Honey wannan kuma fa mai yake saman bed din ka na wacece?". Heelah ta tambaya tana tsare shi da ido Ajmal kallo daya yayiwa ribbon din yasan na Nisha ne time din da ya cire mata bisa kanta.

"I don't know" . ya fad'i a takaice gamida zamewa daga gurin da ya ke ya nufi hanyar fita domin ta fiya masallaci ya bar Heelah tsaye baki bude ta bishi da rakiyar ido cikin ta kaici Heelah ta kuma bin ribbon da kallo abun da ta ke zargi bazai wuce ribbon din waccer sha shashar yarinyar bane Nisha because tasan ita kadai ke mata kutse cikin rayuwarta yau abin ya zu har saman bed cike da jan duguwar tsaki Heelah tayi wurgi da ribbon din gamida ficewa daga dakin gamida jan duguwar k'wafa,.

Guraren 7:30 Barka ne cikin kitchen tana tsaka da aikace aikacen kamar yanda ta saba tana yan wake waken ta Nisha ta shigo ta isketa cikin kitchen din wanda jin motsin shigowar ta yasa Barka jiyowa ta dago ta kalleta cike da fara'a gamida murmushi.

A hankali Nisha ta karisa shigowa cikin kitchen din tana sanye cikin kananun kaya riga t shirt mai dugun hannu white colour sai dugun wandon falazo mai fatsi fatsin black and white sai mayafin da ke dauri saman kanta tayi matukar kyau da ita kamar ka saceta ka gudu.

Tunda ta shigo Barka ta bude bakinta yana shan isa gurin kallon dressing gamida tsantsan kyau irin na Nisha.

"Kai Masha Allah tabarakallah irin wannan kyau kamar mai kokarin zuwa gurin gasar kyau ta duniya Kai koma ace nan zaki to ba mamaki ke zaki lashe kambun". Barka ta fad'i cikin gwad'a Nisha tana washe baki.

Cikin fara'a Nisha ta shiga d'agawa Barka gaisuwa tana murmushi Barka ta amsa gaisuwan na ta cikin yar tsokana tana zolayanta daga haka Nisha ta sanya mata hanu cikin aikace aikace nata suka cigaba da yi tare kamar yanda suka saba suna yar firansu.

"Yar nan nikam na ce na tambayeki ki mana?". Barka ta fad'i tana d'an duban Nisha yayinda suke aikin.

"Ina jikin ki Baba Barka".

"Wai nace ke yar wata kasa ce? amma dai mahaifinki ba yan Nigeria bane ko?". Barka ta jire mata tambaya

Cikin yar murmushin ya ke Nisha ta amsa mata da cewa

"Eh mahaifana yan asalin kasar Sudan ne neman kudi ya kawo mahaifina Nigeria suka haifeni cikin garin Adamawa".

"To amma ya akayi kuma kuka tsinci kanku cikin birnin kano tunda kince garin Adamawa kuke da Zama?". Barka ta kuma tambaya cikin mamaki.

"Bun kasan kasuwancin Abbana ne ya ya dawo damu garin kano". Nisha ta fad'i a takaice

"To shikenan mahaifin naki fa shima Allah ya masa rasuwane?". Barka ta kuma watso mata tambaya Nisha dai wannan karon shiru ta yi ta kasa bata amsan tambayarta gamida fadawa tunani time din har idanunta sun suma cikowa da k'walla.

"Yi hakuri yar nan na da meki da tambayoyi ko?". Barka ta fad'i

Dan girgiza kai Nisha tayi tana fadi'n

"Bakomai bari na je nayiwa papan Aheel breakfast kar time ya k'ure". Nisha ta fad'i gamida zame hannayenta daga aikin da take.

"Ayya to ba komai saikin dawo". Daga haka Nisha ta fice daga kitchen din cikin sauri Nisha Barka ta bi bayanta da rakiyar ido harta fice kafin ta jinjina Kai ta cigaba da aikin da yake gabanta...

Heelah ne ke ta faman zarya tsakanin kitchen da dining area tana ta faman shirya breakfast bisa dining table ta kai fari takai gauro tana cikin wannan yanayin Nisha ta sako kai cikin parlourn sai faman wul wulga idanu take hango Heelah da tayi can dining table tana ta faman shirya breakfast sai da taji gabanta ya fad'i but bata fasa takowa ta kariso tsakiyar parlourn ba.

Heelah tsayawa ta yi daga gurin tana hango Nisha wacce ke faman karisowa da nufin shiga kitchen, harde hanu tayi bisa saman k'irjinta tana jiran Nisha ta gama karisowa.

Nisha kanta tsaye ta suma kokarin shiga kitchen dan ko ta kan Heelah ba tayi ba direct ta nufi hanyar kitchen.

"Wait madam come back what are going for ".

Dan takatawa Nisha ta yi ta tsaya ba tare da ta dago ta kalli inda Heelah ta ke tsaye ba ta kowa Heelah ta yi har inda Nisha ta ke tsaye sai da ta mata kallon tsaf kafin ta tabe baki gamida ya motsa fiska tana fadi'n

"Ina kike kokarin shiga baki ga ina tsaka da hidimar mijina bane ince ko ba ki lura bane". Heelah ta fad'i tana nunawa Nisha dining table wanda ta jera breakfast kallo daya Nisha tayiwa gurin ta kauda kai Ajeemal


" I'm taking to you kunyi shiru kina kasa da kai sumu sumu kamar ta Allah, har wa yaude shirun Nisha tai mata ba ta kulata ba wanda yasa Heelah sake hasala ta dan ja da baya tana kallon Nisha cike da ta kaici tana fadi'n

"Na fahimci raini ya fara giftawa tsakaninmu to daga yau na sallameki daga ban garan mijina ko area side din nan karna Kara ganin kafafuwanki because na fahimci mad'en da kikewa mijina ya fara kaiki ga shimfidarsa".

Gaba daya kin sauya min tunanin miji Allah kadai yasan wani siddabaron kike kokarin yi masa Amma insha allah sai dai aniyarki ta biki daga ke har uwar ta ki ta daura ki kan layi ta tafi tabarki". Heelah ta fad'i tana ya mutsa fiska

Cikin ta kaici Nisha ta dago ta kalleta Heelah gamida ba ta amsa da cewa

"Ba ke nakewa hidima ko aiki ba wanda na ke zaune karka shinsa shi nake wa aiki, ba kuma matsayin yar aiki ko alfarma ba sai dan ya kasance hakki ne a gareni ko shi mai gidan na ki bai hanani saman aljannata wajan kula da shi tunda a hakkine a kaina na sarrafa na bashi ya ci ko ya sha matukar zai bukaci hakan daga gareni any way ko bai nema ba zanyi kodan ganin farin cikin sa but ke ba kida ikon dakatar da ni daga niman aljannata daga karkashin kafarsa" , Nisha ta fad'i cikin bacin rai tana fiskantan Heelah.

"Aljannarki ? a k'ark'ashin kafar mijin? shin kina haukane komai? haka kiga uwarki ta ke neman aljannata a karkashin kafar mijin wata ba nataba?". Heelah ta fad'i a fusace

Cikin ta kaici da rashin jin dad'in aunawa mahaifiyar ta zagi wacce take kwance cikin salama yasa Nisha jan wani guntun tsaki gamida kokarin barin gurin dan ba zata iya jure maganganun Heelah ba cikin hanzari Heelah ta sha gabanta ta tsaya ta na fad'in

"Where are going ? ai tsayawa zakiyi ki bani amsar tambayar da na miki idan ba haka ba yanzu zansa ki raina kanki".

"I don't have your time mijin ki zaki tambaya ba ni ba" . Nisha ta fad'i tana kokarin zamewa gefe ta shige ta yi ta fiyar ta amma cikin ta kaici Heelah ta janyo wuyar rigar Nisha ta baya gamida fisgota har tana neman faduwa

"Ni kike kallon tsabar idona kike min maganar banza son rainki?" . Nisha sai da ta dai ta tsayuwarta kafin ta kallo Heelah wacce take ta faman huci na tambayarta.

" Tunda ke ba kiyi tunani ki kama matunci ki kija girmanki ba ni kuma bazan cigaba da ta ya ki kamawa ba". Cikin taikaci gamida kunci Heelah ta nufi dining ta zaro wata yar karamar yan ka lemo ta nufi Nisha ta na tuna mata wukar tana fadi'n..

"Yau in ban kasheki kowa ya huta ba ba suna Raheelah ba". ganin yanda Heelah ta nufo ta da wukar gadan gadan yasa yan hanjin Nisha kadawa tashiga yin baya ta na tsare idanu da sauri Nisha takuma daukan hanya zata fice daga parlourn Heelah kamar wata mahaukaciya ta yun k'ura cikin hanzari ta janyo Nisha da karfi wanda ya sanya Nisha tangal tangal ta fad'i saman carpet ta shiga wuri wuri da idanu.

Ajmal dake kokarin sakkowa daga steps hango abunda ke faruwa tsakanin Nisha da Heelah ya sanya shi karisa sakkowa cikin hanzari har yana kokarin tuntub'e garin sauri ganin abunda Heelah ke kokarin ai katawa.

"Na tsane ki, kin kaini makura yau sai kin bakunci lahira kije kin tadda matsiyaciyar uwarki wata tayi asarar haihuwarki".

Nisha kare face d'inta ta yi da tafukan hannayenta gamida lumshe idanu saukan wukar kawai ta ke jira ta ji a wani sashe na jikinta but karisowa Ajmal gurin wanda ya riko hanun Heelah daga ita har wukar gaba daya yayi wurgi da su gefe sai ji kake tab Heelah ta yi tangal tangal ta fad'i saman sofa.

Jin sautin fad'uwan Heelah saman sofa yasa Nisha bude idanu ta kalli Ajmal tsaye cikin ta kai ci yana huci kamar tsohon zaki yana kallon Heelah tsabar ta kaici da bacin rai yama kasa bude bakin yin magana dan yau ya kara tabbatar wa da kanshi Heelah mahaukaciya ce ta gaske ba mamaki kwakwalwarta ya samu tabowa idanunta a rufe suke ba ta sanin mai take yi da ba dan Allah ya tun kud'oshi cikin wannan time din ba da ba wannan zancen a keyi ba yanzu.

Heelah kuma yun k'urawa tayi cikin rashin na dama gamida taurin kai ta na kokarin sake tin Karan Nisha.

Wani gigicecen maruka biyu Ajmal ya saukewa mata ne bisa kuncin face d'inta duka biyu wanda yasa ta ga giftawan wasu tauri da yasa ta d'urk'ushe gurin ta saki wani azabeben ihu ita kanta Nisha sai da ta tsorata da jin sautin marukan daga ji kasan cikin marukan ba wasa, Ajmal zaro belt din wandonsa ya shiga kokarin yi wanda cikin tsoro Heelah ta zabura ta mike tsaye gamida watsawa da gudu hartana tuntub'e ta haura upstairs da gudu kowai waye babu tana rike da kuma tunta biyu ta nufi bedroom d'inta ta da tse kofar tana ta faman kuka.

Cike da ta kaici Ajmal ya ciza lips d'insa idanunsa duk sun canza launi saboda bacin rai, a fisge ya waigo ya kallo Nisha wacce ta yi nare nare da ita idanunta duk sun fito waje sabida tsoro ganin yanda Ajmal ya kallota cikin fusata ya sa itama ta mike gamida afkawa da gudu ta bar parlourn dan ba tasan mai zai biyo baya ba.

Ajmal komawa yayi ya zauna saman sofa yana kuci cikin bacin rai, gaba daya tunanisa yanda Heelah ta zame masa da gaba daya ya rasa yanda zaiyi da ita because ta zame masa problem sosai tana bashi ciyon Kai, a jima kad'an ya tashi fuuu ya mike ya fice daga parlourn yanufi haraban gidan ya shiga daya daga cikin motocinsa mai gadi ya bude masa gate ya fice daga gidan.

Ba jimawa da fitan Ajmal Heelah ta biyo bayanshi sanyi cikin wani shiri na duguwar rigar atamfa da d'an k'aramin mayafi bisa kanta hannunta dauke da handbag d'inta gamida key din motarta fitowa tayi ta yi tanufi motarta ta shiga sai faman matsar k'walla take zuciyarta kamar zata faso k'irjinta ta fito tsabar takaici da bakin ciki tunaninta tunda yarinyar nan tasa kafa ta shigo cikin rayuwarsu ya juya mata baya fiye da daaa sam baya ganinta da wani daraja face d'inta kuma ya koma tamkar ganga abun bugu da zaran tayi yun k'urin taba Nisha sai idanunsa su rufe , motarta tayiwa key daga nan tasa kai ta fice itama.

Nisha direct part d'insu ta nufa koda ta karisa parlourn can dining area ta tadda su Hajia tare da su Reeda har sun suma yin breakfast d'insu ganin haka yasa Nisha ta shiga karisawa garesu sai zare idanu take ya yinda zuciyarta ta kuma keta faman bugu.

Nisha sai da ta d'agawa Hajia gaisuwa Hajia ta amsa cikin nishadi gamida fara'a kafin Nisha ta samu daman jan kujera ta zauna, hankali Nisha Sam baya jikinta domin tunda ta zauna ta kasa ta ba komai sai idanunta da ta kafar dasu guri guda ta fad'a duniyar tunanin yau abunda Heelah tai mata ya tsorata ta matuka lallai kishi ya fara haukatar da ita ba ta banbance fari da baki.

"Ince ko lapia naga kintusa table a gaba mai makon kisuma yin serving abinda kikeso kici sai kuma kika zauna shiru ko wani abinne?". Hajia ta shiga jero tambayoyi tana kallon Nisha wacce tayi sauran dawowa tunanin jin maganar Hajia, girgiza kai Nisha ta shigayi cikin sanyin jiki tana fadi'n

"Bakomai".

daga nan tashiga serving din kanta ga abinda takeso, tun shigowar ta Hajia ta ke lura da yanayin Nisha tunda ta shigo ta zauna suke ta faman hira dasu Fadeelah but ita kuma ba ta sanya baki gaba daya jikinta a mace yake ba kamar yanda ta saba ganinta ko yaushe ba duk ta nacin abinci ta lura gaba daya ba ta tunanin ta ballai tasan firan da suke.

gaba daya yinin yau Nisha tayi shine cikin rashin walwala tsoro da kuma fargaban mai zaije ya dawo yana daya daga cikin abunda yasa takewa k'addaranta kuka shigowar Heelah cikin k'addaran rayuwarta, gaskiyar salma ne fadi'n ta na cewa zama da mahaukaci sai anshirya ballai hauka irin na Heelah kishi da ya zamto mata tamkar haukar dole sai ta nuna mata salon ta haukan maybe ta iya komawa cikin sense d'inta.......

Guraren 4 Nisha tsaye bisa saman sallaya tana gudanar da sallahn la'asar wanda tun dazu take ta faman shan bacci sai yanzu farkawanta ta shiga gabatar da sallahn da ke kanta yauma ita kadai bisa bedroom din duk da kusan tare suka kwanta baccin da su Reeda but su sun rigata tashi sun gabatar da nasu sallan sunyi nasu waje kasance cewar kanta na ciyo tasha maganin shiyasa baccin nata yayi nauyi.

Nisha na idarwa ta mike gamida ninke darduman gamida cire hijab din jikinta ta dauki dan k'aramin mayafin ta tamai dashi saman kanta daga nan takai hanu ta janyo phone di'nta nan ta cikaro da shigowar sako cikin wayar wanda yasa Nisha g'yara Zama gefen bed.

Ajmal ne ya turo sakko yana umartarta da shiga sides dinshi ta g'yara masa bedroom d'insa idan ba shi takeso ya dawo ya g'yara da kansa ba cikin sakon harda alamar emoji na bacin rai alamar fad'a, Nisha gefe ta cillar da phone din gamida tura baki

' shi wannan papan Aheel din ya cika fitina a wannan halinda ake cikine zata yi katub'aran komawa side d'insa ta san mai zata tarar idan wannan mahau kaciyar matar tasa na nan dama ace yana nanne zata iya zuwa koba komai wani abin ya tasu zai iya tare mata but yanzu da baya nan sai dai aje a tadda dan buzunta dan bilhakhi da gaskiya ta ke tsoron haukar Heelah' Nisha ke maganan zuci, mikewa Nisha tayi a sukwane ta nufi door ta bude ta nufo parlour koda ta zo parlour bata iske kowa ciki ba dan haka sai tunanin ta ya bata suna can sashin Hajia dan haka daga nan ta fito haraban gida ta nufi side din Hajia........

" Ni Sam nakasa gane wannan alamar ansamu cikin duhu g'wara a fito da mu haske a fad'a mana matsayin yarinyar nan a cikin gidanan because zagewanta yayi yawa bazai yiyu na cigaba da zuba ido ana cutarmin da ya cikin gidan nan ba yarinyar ta zama kamar gangan church dan Allah ka duba fa kaga yanda yarinyar nan gaba ki daya ta zare ta fita haiyyacinta" Hajia Jummana ta fad'i tana huci gamida kallon KB wanda g'yara zama cikin na tsuwa kamar na Allah yana fadi'n.

"Gaskiya dai kam Hajia ya kamata aduba lamarin gaba daya zuwan yarinyar nan ta canza mana alkibilan family yanzu kuma tana shirin shiga tsakanin ma'aurata da gani wannan yarinyar ba yar arziki bane" KB ya fad'i yana wani markwad'e baki irin na bugagun mutane

"Kai da Allah can rufewa mutane baki kai yaushe ma kasan kan kance ballai ka iya banbance mai kyau da mara kyau kafara yiwa kanka fad'a kafin kayiwa wani dan haka karna sake jin bakinka anan kafita idona" Hajia ta fad'i cikin fad'a tana kallon KB wanda ya sake baki jin warning d'insa da Hajia ta yi jinjina kai KB yayi gamida komawa jikin sofa ya jingina yana ta faman cizon lips yana kallonsu, su Reeda kuwa idanunsa kamar zai fad'u kasa don harara su kalli KB su kalli Heelah wacce itama take ta faman jefo musu harara a fakaice tana wani langwab'ewa jikin mom d'inta

Ajeemal
Story and writing
By
Oum amreesh

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=159698751105534&mibexti=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

Book 2

Page 91

_______Baki Hajia jumana ta bude da nufin yin magana jin turo door da akayi ana kokarin shigowa yasa gaba ki dayansu suka shiga zubawa door din idanu don ganin mai shigowa.

Nisha bakinta dauke da sallama ta turo door da nufin shigowa amma sai tsayawa tayi cak kamar wanda ruwa ya shanye sallamar bakintama sai cikin zuciyarta ta iya karishewa wani abune taji ya tushe mata mak'oshi wanda da k'yar ta iya hadiye miyun bakinta Nisha dai tsayawa tayi ita bata shiga ba haka zalika bata komaba k'afafuwanta sun mata nauyi ko k'wak'waran motsi bata iyawa idanunta da ke hango mata KB wanda ya mata wani k'uri yana binta da wani shu'umin kallo ya kasa dauki ido gefe kuma ga Heelah da mom d'inta wacce take ta faman hararo ta kamar idanunta zasu fice.

Heelah tun shigowar Nisha take tawani kafura tana muzurai gamida huci cikin ta kaici da tsanar Nisha cikin zuciyarta jitake kamar tayi wani kukan kura tayi kan Nisha ta kai mata suraa .

"Yar nan ya kika tsaya daga bakin kofa shigo kariso ciki mana".

Hajia ta fad'i cikin fara'a tana kallon Nisha da tayi zuri da ita kamar ace da ita shiii ta gudu

20 / 24