Author : Khaleeseart Abdullahi Raeys Category : Hausa Novels 001
tashi haka kina tunanin ina suka shiga"
"Eh duk da haka but aiba ayi tariyar ba tukun sai ya bari sai ta tare kafin yayi ikonsa a kanta nidai gaskiya hankali ya kasa kwanciya yarinya mai rauni irin wannan"
"Yanzuma yana da iko akanta tunda matarsa ce halal d'insa kuma da igiyarsa uku bisa kanta to mai zai tsaya jira" Daddy ya fad'i cikin rashin damuwa da lamarin.
"Yanzu abunda yayi yayi daidai kenan kana goyon bayansa "Ammi ta tambaya ta na mai tsare Daddy da idanu
"please kibar wannan tunanin haka kikwanta zuwa gobe insha allah zai iya dawo da ita" Daddy ya bata amsa ya na kokarin g'yarawa ya kwanta
"Oh zaima iyane ba ya dawo da ita ba ?" Ammi ta fad'i ta na bin Daddy da kallo wanda ya ke ta dariyan kasa jin mitar da Ammi ke yi kamar k'aramar yarinya
"I think so ki kwanta kawai kijira tsammanin su gobe in Allah ya nuna mana"
Shiru Ammi kawai ta yi ba ta sa ke magana ba but hankalinta ya ka kwanciya sam wannan ranar bata iya irintsawa da kyau ba, bangaran Hajia kuwa zuciyarta fari k'al tunda ta tsinci labarin jin Ajmal da Nisha sun fita tare alamar cewa Allah ya suma hada kansu dan haka cikin farin ciki da walwala Hajia ta kwana yau.
Haka ta bangaran su Reeda duk sunyi shirin bacci sun kwanta but babu Nisha ba alamar ta da tunanin duniyar da su ka shiga su kwanta bacci su ma duk da sun san da yayan na su ka fice gashi ta bance phone d'in na ta agida da sun kira sunji lapiyar ta daga haka su ma baccin ya dauke su ma.
Guraren 11 na dare time din tuni ruwa ya tsagaita da sauka sai d'an yayyafi ka d'an da ke diga dis dis tare da kyakykyawan yanayi na ni'ima da daddad'an ya nayi da ke wanzowa ko ta ina .
Motar Ajmal ne ta danno kai cikin gidan yayinda mai gadi ya bude masa gate ya shigo yayi parking gamida fitowa ya bude door din gidan baya na motar ya janyo wasu kyawawan ledar guda biyu kafin ya rufo door din ya nufi ciki yana isa parlour ya ajiye ledar daya bisa table din parlourn kafin ya kunna kai bedroom din da ya jefa Nisha ciki.
Ko da ya bude door d'in dakin bedroom d'in duhu kake iya gani alamar light d'in bedroom d'in a kashe su ke karisa shiga ciki yayi gamida karisawa ya nufi light ya shafa ya kunna tar haske mai kyau ya wanzo cikin d'akin.
Can saman carpet ya hangi Nisha ta k'udundune sai rawar sanyi ta ke ko da ya kunna light baiga ta dago ko ta motsaba karisawa yayi kusa da ita nan ya ci karo da idanunta wanda su ke lumshe sai faman rawar sanyi ta ke tana sauke ajiyar zuciya Ajmal duguwar rigar jikinta ya bi da kallo wanda ya bi jikinta saboda damshin ruwan sama da ya ta bata ga kuma sanyen AC da ke ta faman aiki cikin bedroom d'in
Ajmal ledar hanunsa ya ajiye saman table d'in bedroom d'in kafin ya kai hanu ya dauki remote control ya kashe AC ya bar aiki cikin bedroom d'in daga bisani ya kuma kai kallonsa ga Nisha wacce ke kwance kasa abun tausayi, Ajmal duk'awa yayi kusa da face d'in ta ya na fadi'n
"open your eyes ki tashi ki zauna inason magana da ke"
Shiru Ajmal ya ji Nisha ta yi ba ta motsaba ballai ya sa ran zata amsa shi,
" Ba da ke nake magana bane?" Ajmal ya fad'i a tsawace gamida hade gira yana kallonta , Jiki ba kwari Nisha ta suma mikewa ta na k'yarman sanyi face d'inta duk ya kumburu idanunta sun kankance sun koma ciki sai da Ajmal ya mata kallon tsaf kafin ya mike tsaye ya kuma gurin table din bedroom din ya sanya hand d'insa cikin ledar da ya aje ya ciro wasu kyawawan kaya kafin ya kalli Nisha ya na fadi'n
" ki tashi ki sauya wadannan kayan jikin na ki " ya na gama fadin haka ya di re mata kayan saman sofa daga bisani ya juya harya nufi door ya bude ya na shirin fita sai kuma ya kuma juyowa ya kallo Nisha ya na fadi'n
"Kisame ni parlour idan kingama" daga haka ya sa kai ya fi ce , Nisha rintsa idanu ta kuma yi gamida rungomu jikinta duk ta takure jikinta guri guda , Jim kadan Nisha ta shiga mikewa tsaye gaba daya ji ta kinta a ma ce kafafuwanta sun mata nauyi kanta kuwa ji take kamar an a za mata kaya haka ta ta rarrafa ta nufi bathroom.
sai da ta cire kayan jikin na ta kafin ta shanya rigarta ta tare da mayafin na ta kafin ta shiga yin wanda da ruwa mai dumin gaske kasan cewar ta saba yin wanka finta kwanta kuma ta samu kuma ta samu kutsari sosai ba kamar da zufa sanyi da mutukar jiki duk ya kau.
Towel ta ne ma ta daura bisa jikinta daga bisani ta fito daga bathroom d'in slowly Nisha ta karisa gaban sofa inda Ajmal ya ajiye mata wadansu kayan nan ta shiga kallon kayan gamida dagawa ta tana dubawa .
Wata tsadaddiyar kyakykyawan duguwar riga ce a baya maroon cold tare da mafinsa rigar ta yi masifar kyau da k'ayatarwa Nisha gefe ta a jiye rigar kafin ta sa ke kai kallonta ga daya rigar ta dauka tana kalla.
Shi kuma y'ar rigar bacci ne mai taushi gamida sulb'i tare da wandonsa pink color rigar baccin shima yayi kyau sosai bugu da kari Nisha na sun abu pink color ya na mata kyau ya na kuma k'ayatarta da ita sai dai tayi mamakin ganin rigar baccin kenan kwana za tayi anan bazai maida ta gida ba Nisha ba waya hanunta ballai ta san ko yanzu time na wa ne wasu sabbin hawaye a ne suka shiga zubuwa kyakykyawan kumatun ta kafin ta dauki kayan ta suma sa wa.
Ajmal dake zaune parlour saman sofa ya mike kafafuwa ya daura daya kan daya yana shan zazzafan coffee yana kuma danna phone dinsa nan kuma ya a jiye wayar kafin ya gyara zama gamida a jiye cup din hand d'insa ya shiga jan wani gutun tsaki yana Kallon saitin door din da Nisha ke ciki canza kaya kawai shine ta jima haka ji yayi gaba daya ya ga ji da jira.
jim kadan sai ji yayi ta murd'a handle door gamida fitowa a hankali sumu sumu da ita ta kariso tsakiyar parlourn gefe ta ne ma saman carpet ta zauna kanta kasa ko hada ido dashi ta kasayi,
Ajmal Kallon Nisha ya ke sosai wacce ta sunnar da kai kasa kamar yanda ta saba da zaran sun hadu ko suna tare ,
"Close to me and have a seat"
Nisha abunda ta ji Ajmal ya fad'i kenan ya na kallota Shiru Nisha ta yi kamar ba ta ji abinda ya ce ba sai kuma ta dago kai ta kalleshi suka hada ido kafin ta maida kai kasa ta mike jiki a sanyaye ba musu ta karisa inda ya ke zaune ta shiga neman guri kasa ta zauna, nan ta ji Ajmal ya janyo ta da karfi wanda ya sa ta fadowa jikinsa bisa cinyarsa.
A razane Nisha ta dago kai ta kalle shi gamida kokarin zamewa daga jikin nasa but sai ta ji yarike ta gam ya na binta da wani kallo, nan ta ga Ajmal ya matso da face dinsa sosai har numfashin su na gauraya da na juna kafin taga Ajmal ya matso da lips d'insa dab kusa da nata kamar mai Shirin mata kiss wanda ya sa Nisha rintsa idanu gam duk tsoro ya cikata gashi ya mata kyakykyawan riko ba halin kwacewa, nan kuma ta ji ya kusa kai gefen suman kanta ya na shinshinar gefen wuyarta wanda ya sanya Nisha sa ke idanu da karfi ji ta yi kamar ta sake fitsari .
A hankali Ajmal ya kai labb'ansa saitin kunnenta kamar mayin rad'a
"I can't believe you! kin sanya ni cikin tunanin na kasa gasgata ala'amuranki wata zuciyar ta na son yarda da ke but wasu halayenki na sa nakasa yarda da ke ".
"But tall me ya zan fara yarada da ke da kuma gasgata ki gameda rayuwar ki? " Ajmal ya tambaya yayinda Nisha ta jiya kai dayan hand d'insa yana mata ta fiyar tsutsa saman lallausan rigar baccinta zaro idanu waje Nisha ta yi cikin tsoro da firgici da rashin sanin mai Ajmal ke kokarin yi haka wanda ko a mafarki baza ta taba tunanin haka ba wantsilwa ta yi da sauri ta bar jikinsa tayi baya da sauri ta na kallonsa k'irjinta sai bugun uku uku ya ke sabida tsoro.
"Please kayar da dani wallahi babu karya cikin lamarina ko dan gane da labarin rayuwarta but idan ba kayarda bani ba na amince nayi nesa da ku nabar cikin rayuwarku na kuma tawa rayuwar inda na fito na zanje na ne mi mahaifina da kaina kuma nayi alkwarin gabatar dashi gare domin gasgata ni Amma ni ba makaryaciya ba ce koma kadaina kallona haka" Nisha ta fad'i cikin kuka tana hawaye
Ajmal kansa sunkuye ya rintsa idanu Ajmal ya na sarrafa tunani da nitsuwar sa jikinsa duk ya suma mutuwa shiyarasa mai yake shirin faruwa tsakanisa ga yarinyar duk da wani abun ya kanyi ne dan ya ga wannan tsoro da firgici na ta bawai dan wani abuba but zuciyarsa da tunanin sa da ke d'arsa masa wani yanayin dangane ga yarinyar ya ke kasa control din kasan wanda watarn zai iya wuce gona da iri wanda kuwa baya fatan hakan because zai da de yana da na sa nin hakan, daga nan ya mike tsaye wanda yasa Nisha sa ke zaro idanu ta na neman gurin shiga sai kuma ta ga ya suma kokarin barin parlourn.
Sai kuma ta ga ya d'an tsagaita daga tafiyar da ya ke ba tare da ya juyo ya kalleta ba
"Ga wadannan a bubuwan na saman table ki dauka ki ci "
yana ga ma fadi'n haka ya juya ya nufi daya daga cikin bedroom d'in parlourn, wani nan nauyan ajiyar zuciya Nisha ta sa ki gamida lumshe idanu ta na jin yanda zuciyarta ke mata wani rin zafi komawa tsakiyar parlourn ta yi har time din zuciyarta ta ba ta daina bugu ba haka zalika tsoro da firgici bai bar jikinta ba. zubewa saman carpet ta yi gamida hade kai da gwaiwa ko ta kan ledar da Ajmal ya ajiye saman table din ba ta yi ba ta shiga riro kuka kasa kasa ta tabbata nan zata cigaba da zama maybe ma nan zata karishe rayuwarta sai randa ya ji ya gamsu da ita tunda ya kawota nan ya ajiyeta .
Ajmal tunda ya shiga bedroom ya suma cire kayan jikinsa ya nufi bathroom, wanka yayi sosai kafin ya fito ya nemi duguwar jallabiyar sa ya zire ya nufi bed ya kwanta gamida janyo blanket ya rufo jikinsa, lumshe idanu Ajmal yayi gamida tunanin zantukan Nisha ta na shashsheka kuka mai tsuma rai da zuciya bacci ya kasa daukarsa sam sai juye ya kai shi kadai bisa gadon da kyar ya samu baccin ya ci karfin idanunsa.
Da asuba jikin Ajmal duk a ma ce gashi ko wani baccin kirki bai iya yiba pillow da ya rungume jikinsa ya kawar gefe gamida sakalo dugayen kafafuwansa kasa ya sakko daga saman bed din a daddafe ya nufi bathroom ya yiyo alwala cikin bedroom din ya fito yayi sallah dan ko masallaci bai iya tunanin fita yanzu , bayan idar warsa ya dad'e zaune kan sallayan ya dan lazimi wanda daga bisani ya mike ko sallayan bai ninke ba ya koma bed ya kwanta gamida lumshe idanu, k'aran wayarsa da ya jine alamar kira ya sashi bude batare da ya motsa daga inda ya ke ba ya kai hanu ya janyo phone din ya saita face dinsa Dan ganin wake kira da asu ban nan ganin Ammi ce ke ta faman rangwada masa kira duk ta damu rashin ganin Nisha cikin gidan kuma hankalinta ya kasa kwanci duk kasan cewar ta a tare da Ajmal.
Mikewa Ajmal yayi daga kwanciyar da yayi yana ganin har kiran wayar ta katse bai samu daman dagawa ba yarasa wani irin damuwa family dinsa su kayi da yarinyar gaba daya hankali Ammi ya kasa kwanciya tun jiya ta ke kiranshi da magarib wanda daga karshe ma kashe wayar yayi gashi yanzuma ta kuma kira da asuba d'in nan duk da baisan damuwarta a kan hakan ba tunda shi dai ya kasance miji a gareta mai kula da ita da duk wani halinda zata tsinci kanta ciki so bai ga abunda damuwa ko daga hankali ba.
Ajmal gaba daya kuma sakkowa yayi daga bed din ya nufi parlour ko da zuwan sa tsakiyar parlourn ya cikaro da Nisha kwance saman carpet ta ruf da ciki gamida k'udundune wa face d'inta na kallon gefe gashin kanta duk ya har gitso ya rufe face d'in na kirif , gefe kuwa saman table d'in yanda ya bar ledar haka ya zo ya tarar da shi ko ta bawa ba tayi ba cikin na tsuwa Ajmal ya ta ku inda ta ke kwance ya tsaya gamida dukawa kusa da face d'in na ta ya sanya hand ya janye lallausan gashin nata wanda yake baki wuluk da shi shining ya ke nan ya matsar da shi gefe ya shiga karewa kyakykyawan face din ta kallo yana ganin yanda naman saman idanunta suka kumbura saboda kuka ba k'aramin tausayi ta bashi ba sam abin kuka baya mata kadan shi ya na gama kamar kukan dad'i ya ke mata shiyasa abu kad'an zai iya tsokano hawayenta.
Ajmal hanu ya kai da niyar dagota daga kwanciyar da ta ke saman carpet izuwa cikin bedroom but Nisha kamar wacce ta ke ankare ko take jira a taba ta tar ta bude idanu ta shiga zareso time din da ta kalli Ajmal d'urk'ushe gaban ta ya kai hanu ya na neman dagota aikuwa cikin zafin na ma Nisha ta mirgina ta mike tsaye gamida yayin baya ta na kallonsa sai sose sosen Kai ta ke ta na ya mutsa fiska ta na neman yin kuka shikuwa Ajmal baki ya saki ya na kallota ya rasa tsoron uwar mai ta ke daga bude ido ta ganshi sai kawai ta kama gudu kamar ta ga wani dodon .
Ajmal cike da ta kai ci ya mike shima gamida hararo Nisha wacce ta manne jikin bangon parlourn ta na muzurai, Ta kowa Ajmal ya kuma yi gadan gadan ya nufota cikin hanzari Nisha wuf ta zame ta shige bedroom cikin sauri ta maida kofar ta da tse,
Ajmal tsayawa kawai yayi yana jinjina kai harwa yau mamakin tsoro irin na yarinyar ya ke ko mai ta kewa gudun oho, tunanisa randa a ka waye gari ta shiga ma komarsa ba halin guduwa ya kenan ranan kam ya naga sai dai ta hadiye ranta , wani k'ayataccen murmushi Ajmal ya saki wanda bai shiryawa yinsaba wanda daga bisani ya juya ya koma ya nufi cikin bedroom, koda ya shiga direct bathroom ya nufa wanka ya kumayi kafin ya fito ya kimtsa tare da shiryawa cikin ingantaccen shiri kafin ya dauki phone d'insa ya nufo parlour ya nemiguri saman duguwar sofa ya zauna.
Hanu ya kai ya dauki remote ya kunna TV nan ta ke ta suma aiki daidai channel din BBC hausa shiru Ajmal yayi ya kurawa TV idanu wanda daga bisani ya mike kafafuwa gamida kwantar da kai ya maida kansa na kallon sama idanunsa na kallon celling shiru yayi kamar mai nazarin wani abu jim kadan kuma ya kuma g'yara zama gamida furzar da wani sassanyar isa cikin bakinsa wanda daidai time din ne phone dinsa ya shiga rori alamar kira daga zaune inda ya ke ya wurga manyan idanuwansa sa jikin screen d'in wayar ya hango sunan mai kiran kafin mike ba tare da ya amsa kiran ba Ajmal ya janyo phone d'insa ya wurgata cikin pocket d'insa.
Ledar saman kan table din da ya ajiye tun jiya saboda Nisha Amma ba ta kulashiba bare ta bi ta kanshi ya dauka daga nan ya kama hanyar fita daga parlourn sai da ya zo har daidai bakin gate ya samu daman tsayawa mai gadi ya ta su cikin rawar jiki ya shiga rangwada masa gaisuwa gamida dukawa kamar zai masa sujjada cike da girmama wa,.
Sai da Ajmal ya amsa kafin ya mikewa mai gadi ledar hanunsa mai gadi ya amsa sai faman sambad'a godiya ya ke ya na washe baki kafin Ajmal ya umarcesa da ya bude masa door zai fice cikin rawar jiki da hanzari mai gadi ganin mai gidan nasa na kokarin fita a kafa ya sa mai gadi tunani ko wani aikan zashi
"Ah ya lallabo'i wani abun kake da bukata daga wajene yanzu aje akawo?"
" No! Don't worry just open the door for me" jiki na bari mai gadi ya bude masa gate koda budewa sai hango wata kyakykyawar motar white color dalleliya gwanin sha'awa da burgewa da alamar motar tana fakene ta na jiran isuwar Ajmal sai dai ko wanda ke cikin motar ba ayi hangowa ballai kasheda wanene because glass din motar baki wuluk take .
Ajmal ya na isa gaban motar ya bude kofar motar ya shiga daga nan akayiwa motar key motar ta d'aga suka bar area gurin, bangaran Nisha kuwa tunda ta shiga bedroom ta rufe ta nemiguri gefen bed ta zauna ta na zare idanu gamida maida ajiyar zuciya kirjinta sai wani irin bugu ya ke da karfi karfi, ta dau tsawon lokaci zaune haka ta yi shiru ita kadai bisa dakin ta na karanta wasikar jaki ita sam ba tasan asuba ta yi bama har gari ya suma wa yewa gashi ita ba waya ba haka zalika ko kiran sallah ba ta jiba ballai ta san time din sallah yayi because guest house d'in Ajmal yayi nisa