Author : Khaleeseart Abdullahi Raeys Category : Hausa Novels 001
blanket ta rufo jikinta gaba daya har kanta ta shige ruf kirjinta sai bugun uku uku ya ke, .
Shikuwa Ajmal saman sofa ya nema ya zauna gamida rintsa idanu ya rasa mai ya ke da munsa yanzu because yanzu duk sanda suka kasance da yarinyar rasa nitsuwarsa ya ke duk da yanzu k'ark'ashinsa ta ke kuma mallakinsa but ba yaso alakarsu ta yi wani nisa saboda hankalinsa Sam ya kasa kwanciya da ita because duk sanda suka hada ido yanayin rashin gaskiya da tsoro ke fara baiyana kan fiskarta, ko abu ta ke cikin tsoro ta ke gabatar da shi kamar a ce mata shhhiiii ta gudu ,
wani zazzafan iska Ajmal ya furzar gamida kallon cup d'in coffee din da yasa ta kawo masa duk ya suma hucewa nan ya mike jiki ba kwari ya haye saman bed d'insa ya kwanta face d'insa na kallon celling daga bisani ya rungumo lallausan pillown baccinsa ya rungume gamida rintsa idanuwansa, face d'in Nisha ne ya sa ke baiyana masa yayinda ta ke zaro ido waje time din da ya matsa waist d'inta tsoro ya baiyana kan fiskarta ta yi ba ya har tana shirin tuntub'e Ajmal baisan sanda murmushi ya kwace masa ba ko ba komai wani lokaci tsoronta gareshi ya na bashi nishadi.
Bayan kwana biyu weekend guraren yamma wajan la'asar Nisha ta farka daga baccin da ta ke tun da azahar yau kusan ita kai ta wani because su Reeda su na can privet class inda Ammi ta kaisu wajan koyar dasu girke-girken zamani da na gargajiya , mike wa Nisha ta yi daga kwanciyar ta sakko ta nufi bathroom ta yi yo alwala ta fito ta gabatar da sallahn azahar idawarta kenan ta ninke sallayen ta ajiye sai ganin barka ta yi tashigo cikin bedroom din fiskarta dauke da fara'a
"Antashi daga baccin ne dazu Hajia ke ta da kokonki ai Ammi ta ce kina bacci da alamu yau kinyi kewar yan surutan na ki" Barka ta fad'i tana kallon Nisha ta na murmushi gamida ba ta amsa da cewa
"Dama yanzu na ke shirin fito wa na sa me ki ko da wani aikin da zan kama miki kar kewar ta min yauwa"
"Ke dai ba kya ra ba kanki da aikin wahala dama na zo na sanar da ke ne yanzu yayanku ya turo a kirawo ki shine na ce bari na duba ko kin ta shi daga baccin" haka kawai Nisha murmushin face d'inta ya kau k'irjinta ya shiga bugu yanzu kuma komai zai ce mata oho
"Ince dai lapia naga fiskarki ta sauya" Barka ta tambaya ganin yanda ta ke yanke fara'ar Nisha ta gushe
"Ah bakomai " Nisha ta fad'i a hankali
"To madallah maza hanzarta" Barka ta fad'i daga haka ta wuce ta fita daga bedroom din, Nisha sanye da hijab dinta wanda ta yi sallah ba ta samu Daman cireta ba ta fito ta bi bayan Barka da ga nan ta fice daga parlourn ta nufi side d'in Ajmal.
Tura door din ta yi ta shiga bakinta dauke sallama, kwance ta sa meshi ya mike saman duguwar sofa ya na sanye cikin riga t shirt da guntun wando iya ka gwaiwarsa kana iya ganin yanda kyawawan gashin kafarsa suka kwanta su ka yi luf da su gwanin sha'awa phone dinsa na bisa lallausan hanusa ya na dannawa .
daga gefe Nisha ta samu guri ta duka kanta kasa kamar yanda ta saba
"Sannu da hutawa" Nisha ta ce cikin sassanyar voice d'inta, lumshe idanu Ajmal yayi ya bude ba tare da ya amsa mata kafin ya ajiye phone dinsa gefe gamida kai kallonsa ga re ta wacce ta ke sanye cikin duguwar hijab ta k'udundune kanta kasa kauda kai yayi yana fadi'n
"So kike sai na daga murya? close to me" Nisha daguwa ta yi ta kalli Ajmal wanda ke hararo ta ya na magana , ba tare da musuba a hankali Nisha ta shiga matso dab da kujeran da ya ke sannan ta ajiye gwaiwowinta ta zauna kamar mai daukan karatu.
" Kin sani cikin tunani labarin da kika bani game da rayuwarki while na kasa gasgata labarun na ki but inaso naga wasu shaida da zaisa na gasgata ki na yarda da ke".
Dagowa Nisha ta yi ta kalle Ajmal time din da ya ke zance kamar mai wani rad'a
"Wa., wata shaida kenan ?"
Nisha ta tambaya cikin sarkewar murya
"Gidan ku da kuma Auntynki da kuma mahaifin naki tunda kince suna cikin garin nan" g'yada masa kai Nisha ta yi alamar eh kafin Ajmal ya jinjina kai yana fadi'n
I need to see them daga haka yamike ya na kuma fadi'n
Ba sai gobe ba yanzu dan haka kishirya ki sa me ni , ya na gama fadi'n haka ya juya ya nufi upstairs, wani farin ciki ne ya ziyarci zuciyar Nisha yau kam Mami ta shiga hanun magark'ama ko da tsiya tsiya sai taga mahaifinta yau Mami zata fad'i inda ta kai Abbanta da ta ke hanasu ganin da zarar sunje,
Da barin jiki Nisha ta fice ta nufi sashinsu sai murna ta ke tana shiga bedroom dinsu kaya kawai ta canza ta saka duguwar rigar atamfa ta daura mayafi bisa kanta dan ko dan kwali ba ta daura because ta san bazai zauna kanta ba kuma ita ba iya daura shi ta yi yanda zai zauna ba ko a gida time din da su ke tare da umma wani time din ita ke daura mata yau Nisha harda su lipstick da yar fauda gamida kwali abunda ta dad'e ba ta yi ba shape shape ta gama kimtsawa ta yi kyau da ita sai sanyen k'amshi ta ke a hanzarce ta fito parlour nan ta ci karo da Ammi wacce ta sakko daga upstairs ta na shirin nufan kitchen ganin Nisha cikin sauri ya sa ta ja ta tsaya ta na kallon ta, itama Nisha tsayuwar tayi ta kama sosa Kai irin na rashin gaskiya,.
"Ke fa ina zuwa na ga kina ta sauri haka" Ammi ta tambaya gamida fiskanto Nisha ta na kallonta
"Am,. dama fita zamuyi " Nisha ta fad'i ta na yan kame kame
Ah aiyo to na fahimta ke da yayan na kune kenan " Ammi ta tambaya tana washe baki gyada kai Nisha ta yi alamar eh sai sunnar da kai ta ke
"To maza kije karyaita jira adawo lapia," daga haka Nisha ta fice sumu sumu Ammi kuwa sai murmushi ta ke tana hamdalah da alama kansu ya suma haduwa gashi harfita zasuyi tare duk da ba ta san ina suka nufa ba.
Nisha na fitowa shima Ajmal time din ya fito daga side dinshi yana sanye cikin kananun kaya yayi kyau da shi, tsayawa yayi yana jiran karisowar Nisha time din da ya ga tafito Nisha ta fiya slowly kamar baza ta taka kasa ba duk da dama yasan al'ardata ne haka sam ba zata maka abu cikin sauri da kuzariba.
kallon daya ya mata time din da ta gama karisowa ya kauda kai ganin yanda ta ci uban lipstick kamar anyi barin mangyada sai shining ya ke yana kyalk'i , nan Ajmal ya kutsa kai ya shige motar driver ya maida kofar ya rufe yayinda itama driver ya bude mata murfin kofa gindan baya tashige sannan ya rufo kafar daga nan driver shima ya shiga because shine mai driving dinsu.
Dalilin da yasa Ajmal ya bukaci driver because ba ko ina ya sani cikin garin kano ba but shikuma driver ba lungu da sakon da bai sa ni ba, daga nan driver yayi wa motar key mai gadi ya bude musu gate suka fice, sai da suka dau hanya kafin driver ya d'an kalli Ajmal da ke danna phone dinsa cikin girmamawa ya ce
"Ranka shi dad"e ina muka nufa"
Ki sanar da shi gurin da zamu Nisha da ke tsili tsili da ido cikin mota ta jiyo muryan Ajmal na magana ba tare da bata lokaci ba Nisha ta shiga yiwa driver kwantace da kuma inda zaiyi tsaf kuwa driver ya gane kwatancen Nisha ya canza a kalan mota suka nufi cikin unguwar da Nisha tai masa kwatance .
Ba da daiwa hanya ta kawo su cikin anguwar Nisha sai mika wuya ta ke ta na leke zata iya cewa da ba dan tasan anguwar farin sa ni da zata iya cewa sunyi batan hanya ganin yanda anguwar ta canza cikin k'ank'anin lokaci anguwar sai ta koma kamar wata sabuwa because wasu ya na yi da zare tsare na tituna da aka shin fida a unguwar ga wasu gidan da ta ke gani rabi arushe titi ta bi ta kansu. Shidai har inda ta san gidan Mami ya ke sun shigu but sai ba gidan ba alamarsu yan hanjin cikin ta ne su Kai wani irin kadawa da zuciyarta da ke wani irin bugu idanunta kuwa kamar masu shirin bullukowa waje.
"Hajia daga nan kuma ina zamuyi" Nisha ta ji driver ya tambaya jin shirunta ya sa shi kanshi Ajmal ya dago kai gamida ajiyiye phone d'insa gefe ya juyo ya kalleta
" Ina magana kinyi shiru why" Ajmal gani yayi Nisha ta sanya hanu ta murd'a handle door din ta fice cikin sauri ko tsayawa ya g'yara parking ba tayi ba, gaba ki daya daga shi har driver bin Nisha sukayi da kallo wacce ta ke ta juye juye ta kalli nan ta kalli can gaba ki daya kanta ya juye anguwar gabaki daya ta sauya mata.
Ajmal face mask d'insa ya zaro ya sanya ya Zama idanuwansa kadai a ke iya ganin kasan cewar yau cikin gari ya shigo ba mamaki ya zama abin kallo daga nan ya fito daga cikin motar ya nufi inda Nisha ke tsaye tayi suman tsaye idanunta na kokarin kawo ruwan hawaye
"tsayuwar mai kike? Ina gidan mahaifin naki ya ke?" Ajmal ya shiga je ro mata tambayoyi ya na kallon ta. shiru Nisha ta yi ba ta kulashi ba sai kalle kalle da ta ke hawaye na gangarowa daga kyawawan fararan idanunta.
"I'm talking to you so what are silent? Ajmal ya kuma fad'i
Still shiru ba ta amsa shi ba ya sa Ajmal jan hanun Nisha but sai ya ga ta janye hannayenta gamida a zawa bisa kanta gamida Kiran sunan Abba saboda rudu da tashin hankali kanta harwani sarawa ya ke ya na juyawa ya ganin ba gidan ba alamarsa babu komai sai kwalta gaba daya ta firgita ta tsorata yanzu wata dunyar ta san Mami ta sa ke cilla mahaifin na ta .
Ajmal ganin kame kame da Nisha ke gamida waige waige ta ma rasa ma kama daya ballai ta amsa masa tambayoyinsa , kallon ta kawai Ajmal ke yi irin na tuhuma because da ma ya San za arina hakan karshe a zo ta shigayin kame kame irin na marasa gaskiya wani yayyafi mai karfine na ruwa sama ne ya su ma sauka kasan cewar gari yanayi na hadari nan da nan ruwa ya su ma saukkowa.
Wani kallo Ajmal ya wurgawa Nisha gamida matsawa dab da ita ya finciko hand dinta da karfi da nufin komawa su shiga mota su ta fi amma Nisha kyam ta kafe ta ci je da kokarin kwace hand dinta ta yi ba ya cikin kuka ta ke fad'in
"Please ni dai ku ta fi ku barni anan ba inda zani na bar Abbana bansan halinda ya ke ciki ba please and please leave me alone" Nisha tafad'i cikin kuka harda shashsheka ta na yin baya gamida hade hannayenta guri guda alamar roko.
Wani guntun tsaki Ajmal ya ja gamida sake fisgo hannayenta yarike gam ya na fadi'n
"Let's go" nan fa Nisha ta shiga kiciniyar kwace hand dinta but ta ji ya ri ke gam daga nan ta shiga kokarin zamewa kasa ta na kiran sunan Abba ta na shirin ta ra musu jama'a duk da kasan cewar unguwar ba hayaniya sosai kuma ba yawan giftawan mutane gashi ruwa har ya su ma jikasu.
Ajmal duk yanda ya su jan Nisha abun ya ci tura kamar akuyar daure ganin haka cike da ta kaici Ajmal ya sun kuci Nisha saman shouldernsa kamar wata yar tsana ya nufi mota da ita haka ta dinga wuntsila kafafu ta na buri , nan Ajmal ya bude motar gidan baya ya azata ciki but da mamakinsa ga rigimar yarinyar sai kiciniyar kokarin fituwa ta ke ganin haka ya sa shima ya shige ya zauna gamida rikota kam jikinsa da hannyensa biyu ganin irin salon rikicin da Nisha ke yi ta na kuka ita ala dole sai dai su ta fi su barta a gurin Ajmal duk yanda ya so ya nitsar da ita ta koma haiyacinta abun ya gagara gaba daya ta rikice masa.
Ajmal Kallon driver yayi wanda yayi tsuri ya na kallon ikon Allah kafin ya sanar dashi ba gida zai mai da su ba ya wuce da su guest house d'insa kai tsaye cike da girmama umarninsa driver ya dauki hanya ba bata lokaci sam Nisha ba ta cikin tunanin ta ballai ta san abunda Ajmal ke fadi'.
Luf ta labe jikin Ajmal gamida rintsa idanu tamkar mai bacci ta saduda because ba yanda ta iya but da ta na da yanda za ta yi da ko door d'in motar ne sai ta balla ta fi ce inyaso ko wani motar ne ta bi ta kanta ta mutum kowa ya huta , ko itama ta huta da wannan kaddaran rayuwar.
Wani irin sauke ajiyar zuciya kawai Nisha ke yi cikin sauri sauri gaba daya hankali da nitsuwar ta ba ya tare da ita tunaninta naga rashin sanin wace duniyar Abba ya dosa ya na tare da waccer azzalumar matarsa wacce ba ta san wani hali ta sanya shi ba , sanadinta ya ba ce tsawon lokaci ya kasa ne mansu sai su ke ta yawon ne mansa.
Time din da su ka kariso ruwan sama sai dad'a karfi ya ke nan da nan driver ya shiga danna horn sai da mai gadi ya leko kai dan ganin waye cikin hanzari ya koma ciki gamida ya yaye musu gate d'in gidan kafin driver ya kunno motar ta sako kai haraban gidan ya nufi parking space yayi parking.
Ajmal zame jikinsa yayi daga na Nisha face d'insa babu alamar wasa time d'in Nisha ta bude idanunta wandan da su ka kumbura su ka k'ank'ance saboda kuka ta shiga wulga idanu a tunaninta gida suka dawo but sai ta ga sa b'anin haka , k'irjinta ne ya cigaba da bugawa sauri sauri ina ne nan kuma da su ka zo.
Idan ba ta mance ba nan suka taba zuwa dashi ya shiga ganawa da d'an su mutane da ta tambaye shi ya ce gidan yankan kai har ya na mata ikirarin gidan da zai sai da ita ne .
gwalalo idanu Nisha ta yi ta nabin Ajmal da shi fitowa yayi daga motar kafin ya rank'wafo Kai ya kallo Nisha wacce ta makale cikin mota sai muzurai ta ke ba ta da niyar fitowa Ajmal cikin hade gira ga ruwan sama da ke ta faman jikashi ya hararo Nisha gamida fadi'n
" Come out" but sam ta nuke ta ki fitowa dama ya san sai tayi masa musu gashi duk ya gama jikewa da ruwa sharkaf dan haka bai sa ke yin magana ba ya jawota yafito da ita ya sun kuce ta bisa hand d'insa ya nufi ciki da ita.
Direct bedroom ya nufa da ita ya di re ta saman lallausan gadon kafin ya fito cikin sauri ya mai da door din ya rufe yanda ba za ta ayi fitowa ba, ya nufi dayan bedroom din ya je ya sauya kayan jikinsa kasan cewar wadan can sun jik'e daga nan ya dauki umbrella ya fito hara ban gidan ya koma ciki motar daga nan suka sa ke ficewa daga gidan.
Nisha jikinta sai rawa ya ke ya yana k'yarma yayin da ta ke bugun door d'in ta na kuka ta na rokonsa da ya bude ta tsoro da firgici duk ya cika kwanyarta Nisha cikin sauri ta nufi window inda ta ke jin kiciniyar bude gate yayinda ta ga motar Ajmal ya fice daga haraban gidan, wajan ta tsuguna ta shiga rero kukanta ta na shashsheka sai da ta yi kukan ya ishe ta wanda harsaida ta su ma jin ciwon kai kafin ta koma gaban bed saman carpet ta k'udundune jikinta duk ya dausanyi sai bari ta ke sanyi AC ga kuma kayan jikinta da ya jike haka ta takure gamida hada kai da gwaiwa ta na kukan zuci.
'Why ? ya kawota nan ya rufe yayi ta fiyarshi ko yayi matsayin ma karyaciya ce ita wacce ta bashi labarin karya a karshe suspect d'insa ya tabbata a kanta ta zama makarya ciya a idanusa ta kasa gasgata labirin ta ga re shi , duk da dama shi already ya gama tsanarta ya kuma kasa daukarta yanda halinsa su ka dauke ta '
'Why ? tun farko zuwan ta gidan nan ta kasa musu bayanin family din ta da rayuwarta maybe ma da andad'e da samun mafita yanzu gashi alamura sun cabe mata ta rasa tsammanin Abba then makaryaciya'
Zane Ammi ta ke bakin bed sanye cikin rigar baccinta ta rabka uban ta gumi ta na tunani Daddy ne ya shigo cikin bedroom din ya na sanye cikin duguwar jallabiyarsa black color fiskarsa dauke da fa'ara ya karisa shigowa but ganin Ammi cikin hali na ta gumi ta na jimami yiwa amma ta rasu ya sa Daddy karisa ya zauna bisa bakin bed din shima gefe da ita ya na kallonta.
"Ince dai lapia naga kin rafaka wannan ta gumi haka mai kike tunani" cike da damuwa Ammi ta kalli Daddy gamida fadi'n
"Kamar yanda na fad'i tun guraren yamma Ajmal su ka fita da Nisha but haryanzu ba ko kwalkiyan daya daga cikinsu har dare yayi kowa na shirin kwanciya na kira wayarsa a kashe ita kuma Nisha already ma ga wayarta ta mance shi gida" murmushinsu irin na dattawa Daddy ya sa ki gamida jinjina kai yana fadi'n
"To inbanda abunke wannan ne abun tunani da d'aga hankali ince dai yarinyar da mijinta su ka fita ba da wani ba da har hankalinki zai