Chapter 18 Reading AJEEMAL Book 2 Hausa Novels By Khaleeseart Abdullahi Raeys.txt Arewa Novels

AJEEMAL Book 2 Hausa Novels By Khaleeseart Abdullahi Raeys.txt

Author :  Khaleeseart Abdullahi Raeys Category :  Hausa Novels 001

Chapter   18 / 24

51K to 54K   out of 70.1K words

komai ba ta na dan wasa da ya tsun hannayenta.

Reeda ne ta shigo cikin bedroom din yayinda hannayenta ke dauke da tray ta ajiyewa Salma gefe daga nan kuma ta suma fadi'n

"Bari mu koma gurin Hajia mu ba ku guri ku cigaba da tattaunawa ".

Reeda ta fad'i ta na kallonsu wanda daga ita har fadeelah suka mike suka fice daga bedroom din daya na bin daya .

Ganin fitarsu yasa Salma ta shiga g'yara zama gamida duban Nisha ta na fadi'n.

"Hankalina ya kwasa kwanciya tun bayan da Reeda ta sanar da ni abunda ke faru nashiga damuwa lamarin na jishi kamar walkiya daga sama bugu da kari bansa halinda zaki sanya kanki ciki ba jin kaddaran Aure da ya fad'a miki ba tare da kin shiryawa hakan ba".

"Shiyasa na daga hankali MB sai ya kawoni na ga halin da wannan kyakykyawan amaryan ke ciki, Allah sarki Kamal ashe ke ba rabonsa bace ". Salma ta fad'i cikin jimami tana kama haba.

Jin shirun Nisha ba ta tamka taba yasa salma zunguro Nisha tana fadi'n

"Wai ke kam kalaun ki kuwa inata magana kinyi shiru kina jina ko dai auranne ya nitsir da ke haka". tura baki Nisha ta yi ta na hararo Salma tana fadi'n

"To mai kikeso na ce "

"Labari zaki bani gameda sabowar rayuwar da kika fara da hadden angon naki kai gaskiya na miki murna ba kowa wacce mace bace ta yi sa'a da dace irin naki ba dace da babban mutum wanda duniya tasan da zamansa".

"Ina miki murna gaskiya ai wannan ba abunda za ki tsaya kina tunani da daga hankali bane kamata yayi kizoba ruwa akasa kisha ki gode Allah because ya riga ya daga matsayin ki fatana Allah yasa ya zama silar farin cikin ki arayuwa".

Wani kukane ya kwacewa Nisha wanda yasa ta fad'a cinyar Salma gamida rage sautin kukan na ta tana fadi'n.,

"Salma ba na tsammanin haka mutumin nan ya sakoni gaba daga shi har matarsa banajin akwai wanda zan iya rayuwa dashi cikin, wallahi sallama jinake kamar na gudu na bar gidanan".

"Subhanallah wai mai kike fad'i ne haka guduwa kuma because of what?". Salma ta fad'i tana dago Nisha wacce ta nake jikinta,.

"Tunda nazo gidan nan ya kyamace ni sam bai dauke ni yanda kowa na gidan ya dauke ni ba " .

Nan Nisha ta shiga zaiyanu mata yanda zaman ta ke tafiya cikin gidan da kuma yanda akayi ta rab'i Ajmal da kuma halinda ta tsinci kanta gamida halayensu shi da matarsa Heelah Nisha ba ta boye mata komai ba har fitansu da Ajmal izuwa gidan taje ta tadda sabanin tunanita har kawo yanzu da take bata labarin tana karishewa da zubar hawaye.

"Ikon Allah ashe ma har da wani love ya ke kokarin showing miki amma dai ke anyi yar k'auye ni harkin bani kunya ma ". Salma ta fad'i tana tab'e baki, Nisha kuwa sake turo baki gamida hade gira tana fadi'n

"Wanna ba soyayya bace"

"To menene ni duk cikin labarin da kika ban ni banga wani aibu cikin halayen shiba a fahimtar da nayi masa tun zuwana gidan nan na farko mutum ne mai tsare gida da baya son raini kuma irin mishkilin mutanan nan ne wanda ba su fiye son magana sosai ba but ke kuma a yanda na fahimta kina nuna tsoron ki fiye da kima wanda zaki iya sanya masa shakko bisa kanki har bukaci son jin labarin rayuwarki wanda su kansu yan gidan ba wanda ya yi tunani son ya jin labarin ki ko ya damu ya ji daga wani tushen kika fito ba ,but kinsa su kuma hukuma basa iya gani suyi shiru sai sun tantance mai kyau da bara gurbi cikin ahalinsu".

"Kamar yanda ki kace kunje gida tare amma kin tarar da sab'anin tunaniki tun farko abun da na so sanar da ke kenan but baki bani hankalinki ba saboda yanayin da kike ciki".

"Nima da kike gani yanzu ba wannan anguwar tunda aikin gwamnati ya biyo ta kan gidanmu da wad'ansu gida jen dake anguwar muka ta shi muka koma can wani unguwar but bana son ki wani daga hankali ki nasan insha allah zaiyi binkice bazai bar lamarin haka ba fatana Allah yasa Abba ya nacikin koshin lapia". Salma ta fad'i gamida sauke wani gutuwar ajiyar ta na riko hannayen Nisha biyu .

Ameen Nisha ta fad'i a sanyaye gamida jingina kanta ga shouldern Salma ta na lumshe idanu

"Amma fa cikin jarabawan da Allah ya daura miki ya hadaki da mahaukaciya a matsayin kishirya ki , zama da irin wadan nan sai mutum ya shirya shiri na gaske sai kin busar da idanunki but ke kuma yanzu na ga gabaki daya ma kin susuce kinyi sanyi sosai kamar ba Nisha da nasani ba ".
"Kin barta ta na buga can da nan kamar wani ta muluta Harfa alwashi ta ke ci wai zata kasheki ". Salma ta fad'i ta na jan wani gutun k'wafa gamida kai hanu ta dauki sassanyan bottle water tashiga tsiyayawa cikin wani kyakykyawan glass cup ta kai baki.

Sai da ta sha ruwan sannan ta kuma kai hanu ta b'alli ayaba ta kuma kaiwa baki kafin ta cigaba da fadi'n

"Yanzu fa ba matsayin da ta sanki da bane duk da bawai ta sani bane but ya kamata ki busar da idanunki ki kwaci yan cikin tukan tafiya ta yi nisa karki zuba mata ido tana miki yadda ta ga dama kema matar shi ce kamar yadda ta ke matarsa, kamata yayi ki kashe ta a tsaye ko ba ta mutu ba tayi dugun jinya tunda ita iyayen kishine"

"Kamarya in kashe ta fa kika ce sam ni bazan iya kisa ba ". Nisha ta fad'i tana mak'e shoulder gamida ya mutsa fiska

"Kaji banza ninace kiyi kisane? ta shi ki zauna da kyau ke sam bakisan mai duniya ke ciki ba". Salma ta fad'i ta na mai ajiye b'awon ayabar hanunta saman tray gamida mai do da kallonta ga Nisha wacce ta g'yara zama ta fiskan to ta...

Follow the Oum Amreesh channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaDtGp2G3R3lkDkO9T3H

Ajeemal
Story and writing
By
Oum amreesh

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v

💪 JAJIRTATU WRITERS ASSOCIATION💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtatu ne kawai kan iya amfani da wannan k'asaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauki.✏️_

Book 2

Page 86&87
******************************
_____ Gaskiya na ji dad'in ganinki sosai Salma zuwan ki na kara ganin sauyi cikin face din kyakykyawan yata yau Nisha fara'a da nishadi abun ba acewa komai"

Ammi ta fad'i cikin farin cikin tana kallon Nisha da Salma wacce keta faman zuba murmushi kamar gonar auduga yayinda suke tsaka da yin kataccen dinner.

"Aiko dai ni da na ganta ma abun mamaki ya bani kwana uku da biki hankalinta bai kwanta ba sai da ta zu daga k'awarta wannan amintar ta ku ta gaske ne akwai amince sosai ku riketa da kyau Hajia ta fad'i cikin fara'a itama.

"Insha Allah Hajia".

Salma ta fad'i ta na kallo Nisha ta gefen ido wacce ke ta faman juya spoon cikin plate ta na juya wani tunani cikin ranta, kasan cewar wajan cin abincin ga kujeran Nisha ga ta Salma yasa Salma zunguran Nisha da ido ta mata alamar ta bar tunani ta ci abinci wanda yasa Nisha g'yada mata kai ba tare da kowa ya ankara da suba, nan su kaci gaba da cin suna yar firansu wanda annane Salma ta sake godiya gasu Hajia da abubuwan arzikin da su fadeelah da suka kai mata ranar bikinta nan suka nuna mata bakomai ta cancanci hakanne.

Phone din Salma ce tayi kara nan ta ja wayar tashiga dubawa ganin angonta ne ke kira yasa Salma jan tissue paper tana share bakinta da hannayenta gamida mikewa ta na sanar da su mijinta ya zo daukarta , daga nan Ammi ta mike ta haura upstairs ta nufi bedroom jim kad'an ta dawo hannunta dauke da kyakykyawan ledar ta zo ta mikawa Salma tana fadi'n.

"Gashi ba yawa mungode sosai da ziyara".

Salma ta amsa gamida surfa godiya daga haka Reeda dauko mata handbag d'inta cikin bedroom ta dawo ta mika mata daga nan ta musu sallama su Nisha suka rufa mata baya dan yi mata rakiya.

MB jingine da jikin motarsa wanda yayi parking d'inta compound din gidan Kamal na gefe tsaye suna yar firansu sama sama yayin da suke jiran fitowar Salma, hango su da sukayi suna ta howanne yasa kamal sake idanunsa kan Nisha wacce hannayensu cikin na juna da Salma suna ta fe suna fira.

"Allah sarki wato akcewaba mutum abu ba rabunsa bane sai dai kallo da hakuri" .

Mb ya fad'i yana kallon Kamal wanda ya shagala da kallon Nisha but jin abunda abokin na sa ke fad'i yasa Kamal kalloshi gamida hararoshi ya na kauda Kai.

"Gaskiya kayi na mijin kokarin da saurin karaya koda ya ke fad'an da ya fi karfin mutum ai sai yamai da shi wasa".

Shidai Kamal ko k'ala bai tufa masa ba yana jinsa yanata tsokanar shi duk da abun yana masa ba dadi but inya biyeshi zasu iya diban yan kallo.

Nisha tundaga nisa da tangi mb da Kamal tsaye sai da ya sanya k'irjinta buguwa gaba daya nauyin haduwa da Kamal ta ke duk da kwana biyu ya bacewa ganinta kamar baya duniyar.

"Afuwan mun barku kuna ta jira sallamar ce ta ki karewa jinayima kamar na kwana kawai abina".

Salma ta fad'i tana ta fa hannaye gamida kallon angon nata da yake mata wani kallon wanda yasa ta tuntsirewa da dariya ta na mai kauda Kai.

"Ah kidaiyi hakuri karkisa wannan angon naki mai rawar kai yaita mana zariya cikin dare ya hanamu bacci".

Kamal ya fad'i cikin tsokana.

"Ai batama isaba ai sai asanya ta cikin duniyar alajabi".

Mb ya fad'i wanda ya sanya su kwashewa da dariya duk kansu daga nan mb suka shiga gaisawa da su Reeda gamida yiwa Nisha fatan alkhari gamida batun auranta daga nan suka shige mota gamida yi musu sallama motarsu ta d'aga tabar harabar gidan.

Daga nan su Fadeelah suka suma kokarin juyawa su koma ciki Kamal kiran sunan Nisha wanda ya sanya duk kansu su ka juyo harsu Reeda.

"Da ita kadai nake but kunwani juyo sai kace sunanayen ku na kira".

Kamal ya fad'i yana hararo su Fadeelah.

"Kuyi tafiyar ku da ita kadai na keson yin magana".

Kamal ya kuma fad'i wanda yasa su Reeda suka bargurin suna dariya gamida waiwayansu suna yar gulma.

Kamal kallon Nisha yayi wacce kanta ke kasa tana wasa da yan ya tsunta gamida tunanin abunda zaice.

"Come here please follow me".

Kamal ya fad'i gamida yin gaba alamar ta biyoshi baya, ba tare da wani musu ba Nisha ta bi bayansa suka karisa cikin kyakykyawan garden da kullum ta ke tunanin shigarsa because ba ta taba kai kanta gurin ba kuma tana da sha'awar shiga ta ji irin ni'imar da gurin ke da shi tare da shuke shukensa masu kyau da daukar hankali dake ba da wani sassanyan ni'ima mai dad'in gaske.

Garden din ya k'awatu matuka fiye da tunaninta ga wanin haske tar wal mai kyau da inganci kai kace ranane ba dare ba, karisawa su kayi suka zauna saman wani k'ayataccen guri da aka killace dubin zama d'an nishadi babba table ne tsakiyar gurin gamida zagaye shi da akayi da kujero yan ma daidaita gurin sai wani ba da ni'ima mai dadi ya ke.

Bayan da suka zauna kamal ya kallo Nisha wacce itama ke kallon shi wanda suka shiga kurawa juna idanu daga bisani kowannesu ya kauda Kai yanajin kewar wani gurbi cikin zuciyarsa.

Sisy kinsan meye? Kamal ya tambaya gamida d'agowa yana kallon Nisha girgiza masa kai tayi kafin ya jinjina Kai ya cigaba da fadi'n

"Wato fa abu in a kace ba rabonka bane tofa duk yanda ka kaiga k'wallafa rai ga abu ballai kasamu ba"

"Bantaba kawo rai na bazan sameki matsayin mata ba sai gashi kin kasance babba Aunty a gareni".

But bana bakin ciki da hakan because ni da shi kusan abu gudane sai hali da ya babanta kasan cewar wasu halayensa sunfi nawa tsafta because ni sabon tubane shiyayi kokarin daurani bisa hanya ina alfahari da shi .

Shiyasa bana bakin ciki kasan cewarki abokiyar rayuwarsa but...

"banasu wadannan zantukan please ". Nisha ta fad'i cikin damuwa na rashin son jin abun da ya riga ya wuce.

"Alright my Aunty wadanne zantuka kike son ji to ?".
Kamal ya tambaya gamida gyara zama yana tallafo kuncisa da tafin hannusa ya na kallonta, dagowa itama Nisha ta yi tana kallon na shi kafin ta ce

"Labarin kwallon kafa". ta fad'i gamida sakin murmushi ta na sunnar da kai , wani dariya Kamal ya tuntsire da shi ya na fadi'n

"Ke kuma maiye abunso ji a labarin k'wallo ke da mace ba na miji ba ". Ya tambaya yana dubanta.

"To waya fad'a maka maza ne kad'ai wasan kafa ge burgersu ? Akwai wasu matan ciki kuma har da ni ".
Nisha ta fad'i

"Uhm to hakane but mafi akasari maza dai sunfi yawa akan mata".

"To Amma dai labarin k'wallo ba aba da shi sai dai a kallah because idan labari zan baki bazai miki har mashi ba kamar kallo , dan haka ki zuba ido akwai wani wasa da zamu gabatar cikin satin nan dan haka sai ki saka TV gaba wajan kallo b".

"Hmm to shikenan". Nisha ta fad'i , sun dau lokaci suna yar firansu cikin wasa gamida nishadi suna dariya Nisha ta sake sai zance ta ke daga nan Kamal ya mike ya na fadi'n

"Bari na je na dakko Nabilah daga gida na ga dare ya suma rufawa". G'yada masa kai tayi gamida mikewa itama suka fito daga garden din tare daga nan yi masa sai ya dawo ya mata sallama ya wuce haraban gidan ya shiga motar shi mai gadi ya bude masa gate ya fice Nisha tana tsaye wajan harya kurewa ganinta kafin ta juya ta nufi part d'insu

Ba jimawa motar Ajmal ta kuma kunno Kai wanda ya sanya mai gadi sake yayi gate shima ya kutso motar shi cikin haraban gidan daidai parking space yayi parking yau Ajmal yayi dawowan wuri.

ya nayin parking ya fito daga motar ya nufi cikin side d'insa, Nisha ko da tashigo parlourn bakowa duk sun watse kowa ya nufi turakarsa, hakan yasa direct ta nufi bedroom din su time din da ta karisa shiga ta samu duk sunyi shirin bacci sun kwanta.

Reeda hartayi bacci Fadeelah ne kawai ta rage idanunta biyu tana daga kwance tana chat tana murmushi da alamar tana nishadantuwa da chat din, bathroom Nisha ta nufa wanka tayi wanka gamida tsaftace jikin ta kafin ta fito ta nufi gaban drees mirror tashiga shafa kamsasun mayukan da ke wajan daga bisani ta koma wardrobe ta shiga neman seeping drees don ta sanyawa jikinta .

wata yar half vest ne milk colour sai d'an wando mai laushi da taushi iya ka gwaiwa launin blue daga nan ta haye saman bed ta nemiguri ta kwanta gamida janyo wayarta ta shiga lazawa itama, guraren 10:30 Nisha ta suma g'yang'yad'awa phone din harta su b'uce hanunta Fadeelah itama tuni ta kashe datar wayar tajuya ta yi kwanciyar ta sai bacci.

Phone din Nisha ne yashiga rori alamar kira wanda ya sa firgit ta bude ido because baccin na ta bai riga da yayi nisa ba phone din da ya tsulale hannunta ta shiga lalub'owa ta shiga duba jikin screen din wayar time din har kiran ya katse,.

Daga saman bed din ta mike ta zaune ta na murza idanu ganin Kiran ogan na ta cikin wannan time din ko mai ya ke bukata kuma ? dan ta san wannan kiran da ya mata ya na bukatar ganinta ne . jim kad'an ta danyi na wani lokaci kafin ta mike ta bude wardrobe ta dauko wata zungureriyar hijab ta sanya bisa jikinta kafin ta fito ta nufi hayar fita.........

Zaune yake cikin kata faran parlourn sa saman duguwar sofa ya mike kafafuwa ya daura daya kan daya yana karkad'asu a hankali cikin na tsuwa ya na sanye cikin wani riga t shirt mai guntun hannu gamida dogon wando dark blue yana ta aikin danna phone dinsa.

Turo door da akayi aka shigo baisa ya dauke kansa daga abinda ya keba, cikin sanyin murya Nisha ta kutso kai cikin parlourn gamida sallama ta na mai karisowa cikin tsakiyar parlourn.

Cikin zuciyarsa Ajmal ya amsawa Nisha sallamar ta but bai iya dago da kansa ba, can gefe Nisha ta duka saman carpet kanta kasa ta shiga fadi'n.

" Sannu da hutawa andawo lapia?".

"Fine ". kwai Ajmal ya ce kafin ya shiga nuna mata ledar da ke ajiye saman table ta dauka ta shiga cikin ta sanyo cikin plate ta kawo masa, ba musu Nisha ta nufi ledar gamida dauka ta nufi kitchen da shi.

Tunda ta mike Ajmal ke binta da kallo daga ita har hijab din da ta sanya da yake ta faman sharan k'asa, ita kanta sai faman tattareshi take kar ya kayar da ita, kauda kai Ajmal yayi ya cigaba da abunda ya sanya gaba aikin danna phone dinsa.

Nisha ko da ta shiga kitchen ta shiga bude ledar kayan snacks ne nau'ika da ban da ban da wanda baya gajiya da cinsu da kuma ka kasa sabawa cikinsa da abu mai nauyi irin na gargajiya, gefe kuma kayan marmari suma nau'ika da ban da ban .

Plate ta dauko ta sanya wasu kayan snacks din ciki gefe ta kuma dauko wani kyakykyawan bowl tashiga hada masa k'ayataccen yoghur fruit da wadannan kayan itaciyar daga bisani ta dauki sauran raguwar kayan ledar ta sanya su cikin fridge ta dauki kyakykyawan tray din data shirya abubuwan ciki ta nufo parlour.

Koda ta dawo parlour babu Ajmal ba alamar shi cikin parlourn hakan ya sa ta karisa cikin parlourn ta ajiye tray din bisa table ta samu guri daga gefe ta zauna tana jiran sakkowan shi maybe wani uzurin ya shigayi.

Ta dau tsawon lokaci tana zaune gurin ta ga alamun bayi da niyar sakko gashi dare na dad'e yi yasa ta mike ta dauki tray din ta shiga haurawa upstairs.

A hankali ta ke taka steps din zuciyarta na wani irin bugu jita yima kamar ta koma ta ajiye masa ta yi tafiyar ta but wani zuciya kuma

18 / 24