Chapter 13 Reading AJEEMAL Book 2 Hausa Novels By Khaleeseart Abdullahi Raeys.txt Arewa Novels

AJEEMAL Book 2 Hausa Novels By Khaleeseart Abdullahi Raeys.txt

Author :  Khaleeseart Abdullahi Raeys Category :  Hausa Novels 001

Chapter   13 / 24

36K to 39K   out of 70.1K words

dai ya canza yana amsa gaiyatarki yanda ya kamata domin na san abinyi, ko haryanzu ke ce mijin shine mata sai ana binshi ana lallabansa?" tabe baki Heelah ta yi tana fadi'n

Jiya I yau yanzu ba yadda da ni kwata kwata d'an da barun da na ke domin jawo tunaninsa yanzu abun ya fasskara hattakai yanzu baya yadda Dani wataran da fad'a muke karewa inna takura masa yamin k'eta ya fice ya barni da jinya ni duk na gaji da wannan halaiyan nasa", shiru Hajia Jummana ta yi tana jimami a kunyace ta kalli Heelah kafin ta ce

"Kuma lapia yarsa qalau kuwa? wannan lamarin nasa akwai abin dubawa ace abar mace haka bawani kulawa ki ce hoto kawai kike ko TV n kallonsa?"

"Mom TV ma ya fini ammfani tunda yana iya ya tsaya ya kalla na tsawon lokaci kuma karkiyi tunanin bayi da lapia qalau yake wallahi tunda harya iya jan waccen yarinyar turakarsa suna yiwa junansu mad'e"

"Aikuwa bazaki ci gaba da zama haka ba saboda ke ma jinini ajikinki ba ruwa ba sanya mayafinki bari nazo " Hajia Jummana wardrobe ta bude ta janyo mayafinta tare da daukan handbag dinta ta kalli Heelah wacce ta mike tana g'yara mayafinta kafin ta janyo handbag d'inta itama suka jera suka fice daya na bin daya kamar wasu kifin gwangwami,

A parlour suka iske Aunty Hafsatu ta na zaune tana cin y'ay'an ita ciya ta na kallon TV time ta kalli su Heelah da mom d'inta sun fito suna shirin ficewa daga Heelah har mom harara su ke bin Hafsatu da shi harsuka fice ita kuwa ko kallonsu ba ta kuma yi ba dan ta San ko adawo lapia tai musu sai sunje fe ta da maganar da bai mata dad'i ba shiyasama ta jira kanta da bakinta.

da dare misalin karfe 9 ta dan gauta Nisha na zaune bisa bed da Aheel da ke kwance yayi matashi da cinyarta yayi bacci wanda ya wuni kas gurin Nisha ya gama rigimar sa yayi bacci sai fadeelah da ke gefenta tana nuna mata kayatattun furnitures din da Daddy ya musu order daga Dubai wanda ta tura cikin wayar ta d'an ta tununawa Nisha kayan alherin da Daddy yai musu order na auransu su duka, Nisha kuwa sai kallo ta ke tana karawa because kayan sunyi matukar kyau da kwatuwa, Yayinda Reeda ke gefe zaune saman stool gaban dress mirror ta na danna wayanta kafin ta dago kai tana kallon Nisha gamida fadi'n

Salma ta kirani jiya na mance ban sanar da ke ba but na jita cikin ya nayin damuwa da ta shin hankali ta ce min ta yi waya da ke amma kinki ba ta hadin kai kuyi magana sai sautin kuka ta ke ji ta cikin waya ta tambayi dalilin kukan kin ki sanar da ita shine ta kirani domin ta tuntub'e ni gameda yanayin da ta jiki ciki ko Ina da masaniya akan halinda kike ciki

Ban boye mata komai ba na sanar da ita duk abunda ya ke faruwa but ta damu da halinda da kika shiga, Salma ta na so kuyi magana na san kuma ta damune ganin bikinta ya zo amma ko duriyarki ba ta jiba wanda ba ta ki iwar haka kuna tare ba because duk duniyar nan ke ce babbar kawa a gareta yar uwa kuma aminiyarta mai zai hana ki kwantar da hankalinki ko ita na ta hankalin zai kwanta a yi bikinta cikin salama farin ciki da kwanciyar hankali,.

Karkiso kiga yanda hanlalinta ya tashi jinki cikin wannan ya nayin ta damu da damuwarki hak'ik'a Salma kawace ta gari kuma ta na sonki sosai, Reeda ta suwa ta yi daga inda ta ke zaune ta dawo kusa da su ta zauna gamida kallon Nisha tana fadi'n

"Please and please ki kwantar da hankalinki ki daina damun kan ki haka , na lura da ke tunda kika tsinci wakanar wannan lamarin kika ragewa kan ki farin ciki fara'a da annashuwa sometimes cikin kuka da tunani da kike ban san mai kike tunani gamida auran ba but rokona a gareki Ki ra ge damuwa ki rungumi kaddaran da Allah ya daura miki fatan hakan ya zamo alkhari a gareki, ya Ajmal da ya Kamal duk kusan abu guda ne sai d'an hali da yasha banban ya. Ajmal bamai wasa ba ne Kamal ya Kamal ba zaki ta ba gani kyakykyawan halinsa da ga fiska ba sai kin zauna kin fahimce shi da kyau zaki fahimci yana da saukin kai fiye da tunaninki duk da wani sa'in idan ya juye bazaki ta ba ga ne shi ta dad'i ba ina fatan ya zama farin ciki a gareki ki kuma sauya shi ta yadda kikeso".

Shiru Reeda tana murmushi kafin ta cigaba da fadi'n

"Allah dai ya kawomin time din da Heelah zata tsinci ke abokiyar zaman ta ce kamar daga sama ranar sai na zuba ruwa a kasa nasha," tintsirewa da dariya fadeelah ta yi tana fadi'n

"Amin fa uwar yan kishi zanga yanda idanunta zasuyi" ita kuwa Nisha fargaban ta kenan wannan ranar duk ranar da Heelah ta fahimci hakan ba tasan mai za ta mata ba dan tun yanzuma ta fara mata ikirarin zata kashe ta ita dai Allah ya sa ma kafin lokacin a nemeta a rasa ta gudu dan yanzu burinta zai cika da zaran ta fara zuwa school zata gudu domin komawa gurin Abbanta ta san halinda ya ke ciki dan ba ta san ta ya zata fara rayuwa da wadannan fusatattun mutanen ba . Ta wani ban gare kuma ta na ganin kamar inta gudu batayi adalci ba ta yi butulci fatan ta dai Allah ya kawo mata mafita cikin lamuranta.

" To yanzu ya ake ciki da batun zuwa bikin Salma ko haka zamu zuba ido har ayi bikin a kare bawanda ya je cikin mu? Idan mukayi haka kamar bamu kyauta ba" fadeelah ta fad'i tana kallonsu.

" Gaskiya dai kam a duba lamarin" Reeda tafad'i tana kallon Nisha duk su biyun idanunsu ya koma kan Nisha, ita Nisha kallon nasu ta yi tana fadi'n

"To ya zamuyi ni kunsan da aure bisa kaina i mala'iku tsine min zasuyi idan na fita ba da izini ba"

"Why not ki tambaye shi zaki auran kawarki " fadeelah ta bata amsa

" Tab di ke ma kinsan halin ya Ajmal abunda ba zai yiyu bane muma da yaya muke fita ballai ita da ta ke k'ark'ashinsa yanzu, dama da a sace zamuje mudawo ba tare da ya sani ba tunda ba wuni ya ke gidan ba balle ya san tafiyar mu da dowar mu but ita kuma bazai yiyuba mala'iku zasu tsine mata" ita dai Nisha jinsu ta ke koma ace zai barta bazata tambaye shi ba because ta san abun magana ba ya masa kad'an.

" Yanzu mun hakura kenan?" fadeelah ta tambaya

" Aa mudai zamuje muwakilce ta sai muje tare da ya Kamal tunda mijin na ta abokinsa ne, kinga ko ba komai zatayi farin ciki inta ganmu fareeda ta fad'i

" Nima nayi farin ciki sosai Allah ya bar zumunci" Nisha ta ce gamida murmushin jin dad'i

"Amin " suka amsa daga haka su ka ci gaba da firansu wanda daga bisani suka kwanta bacci sannu ahankali bacci b'arawo ya sacesu but ita kuma Nisha bacci ya kasa na sara a akanta daga ta rufe idanu zata hango kyakykyawan face din Ajmal tare da kyawawan fararan idanun Ajmal masu kamar madara time din da su ka k'urawa junansu idanu kowa ya kasa dauke ido daga kallon kyawun da Allah yayiwa dan uwansa.

Lumshe idanu tayi ta bude kafin ta mike daga kwanciyar da tayi ta na kallon Aheel wanda ke ta bacci hadda minshari tsoronta daya kar ya tashi mata cikin dare ya na rigimar nan ta sa yace a kaishi gun papansa gashi side dinsu ba kowa ciki da Heelah har papan nasa ba wanda ya dawo cikinsu.

Sakkowa tayi daga saman bed din ta nufi window gamida yaye labule tana sauke ajiyar zuciya gamida jin kyakykyawan ni'ima ta na kallon kyawawan bishiyoyi masu fitar da sassanyan mashi na musamman guri yayi shiru alamar dare ya ja gida ko ta ina ya dau haske kai kace ranane ba dare ba dan ba abunda baka iya gani tarwal, .

Jingina kai Nisha ta yi jikin window ta na dan tunane tunane ta dau tsawon lokaci tana tsaye a gurin kafin ta hango mai gadi ya na kiciniyar bude gate saboda hon din da ake ta yi daga waje koda mai gadi ya bude gate motar Ajmal ne ta danno kai cikin compound din gidan daidai parking space yayi parking daga bisani ya fito ya suma nufan side d'insa cikin tafiyar ka sai ta irin na manyan mutanen nan .

Nisha zuba masa idanu ta yi tana kallonsa wanda duk dama ya riga ya sanya ido akansa to zaiyi wuya yayi saurin janyewa, Ajmal haka kawai jikinsa ya basa ya dago ya kallo sama karab idanunsa suka sauka kanta duk da bawai ya gama kare mata kallo bane ballai ya samu tabbacin wanda ya gani Nisha tayi saurin sake labule ta yi baya da sauri ta haye saman bed ta kwanta Ajmal sauke Kai yayi gamida karisa shiga side din na sa.

Nisha ta na ganin yanda Aheel ya ke ta juyi yana neman farkawa wanda tun bayan mangariba ya kwanta bacci har zuwa yanzu kusan 10:30 nan ta kuma ganin Aheel ya bude idanu tar yana wulwulga idanu wanda ya sanya Nisha saurin rintsa ido kamar mai bacci ko hakan zai sa ya koma bacci because dare yayi sosai bazata iya da wainiyar kaishi side dinsu ba Amma gamamakin ta sai ji tayi ya kwanto jikinta cikin muriyar bacci ya shiga kiran sunanta ya na tashinta ya na fadi'n zaije papansa because Aheel ya saba inba jikin papansa ba baya iya bacci mai kyau saboda ya wanci a jikinsa ya ke kwana ya ke ta shi.

"Aunty ki kai ni gurin papana" Aheel ke ta fad'i ya na mai mai tawa ya neman kuka bude idanu Nisha ta yi ta zauna gamida kallon Aheel tana faskantansa sannan ta ce

"Please kakoma ka kwanta ba ka ga dare yayi ba ne sosai kabari gobe da safe sai na kai ka gurinsa " Nisha ta fad'i but sai ganin Aheel ta yi ya langwabe kai gamida ma ke shoulder alamar ba zai yadda ba yanda ya marairaice mata ya na neman kuka ya sa dole ta sakko da shi ta dauki mayafi ta ya fa bisa kanta daga nan ta sunkuci Aheel ta daga shi bisa hanun ta suka fice.

Ko da su ka fito gari yayi shiru sai kukan halittu kakeji security da ke gefe shima tuni ya kishingid'e yayi bacci haka Nisha ta tura door din a hankali ta shage parlourn da Aheel a hanunta da idanunsa su ka cicciko yana zaresu.

Nisha maimakon ta kaishi gurin papan nasa sai ta wuce dashi bedroom din sa a hankali ta na sanduwa kamar mara gaskiya.

Kwantar da shi tayi bisa lallausan be din nasa ta g'yara masa kwanciya ta rufe shi da blanket Aheel sai binta da kallo ya ke ganin ba ta kaishi gurin papan nasa ba ta kwantar da shi anan shikuma papan nasa ya ke son gani , Nisha ganin kallon da Aheel ke mata duk ya wani marairaice yasa ta sakar masa murmushi gamida shafo saman goshinsa ta na fadi'n

"I'm here" nan Aheel ya ga ta kwanto gefensa gamida da daura hanuta bisa bayan shi ta na shafosa ta na dan bubbuga bayan nashi kamar wani jinjiri dan dai ta samu yayi baccin aikuwa harwani sauke ajiyar zuciya ta ji ya nayi daga nan Nisha ta rintsa ido kamar ta yi bacci daga nan shima Aheel ya kulle ido kankance mai ya koma baccin sa sai sauke ajiyar zuciya ya ke.

Slowly Nisha ta zame jikinta ta sakko daga bed din gamida rage masa light ta fito ta janyo masa door din a hankali ta rufe, tajuya ta suma ta fiya cikin sanda tana jan ka farta dai dai time din da Ajmal ya budo door ya fito daga bedroom din sa daga shi sai towel da ke bisa waist d'insa sai wani dan k'aramin towel da ke hanunsa ya na goge suman kansa da shi da alamar daga wanka ke ya fito ya na shirin nufa downstairs kamar wanda aka ce ya kallo gefe idanunsa suka yi tuzali da Nisha wacce tayi tsayuwan cak ta kasa gaba ko baya tana sanye cikin duguwar rigar baccin mai laushi da santsi sam ba ta so haduwarsu da Ajmal ba but duk yanda ta so kaucewa masa sai da su ka hadu, .

Kauda kai Ajmal yayi irin na ko in kula kafin ya tsaida abunda ya ke na goge suman kansa da ya ke ya sa ke dubanta still ko motsawa Nisha ba ta yi ba daga in da ta ke shiya rasa wani irin tsoronsa ta ke because duk sanda suka hadu ko yanai mata magana tsoro da rawar jiki ke fara bai yana ga yanayinta, Ajmal hanu yayi wa Nisha alamar ta kariso kusa kafin ta shiga karisowa da rawar jiki kamar yanda yayi tsammani kanta kasa ko kallonsa ta kasa yi ganin yanayin da ya ke ciki shikuma Ajmal ko ajikinsa har Nisha ta kariso gabansa ta tsaya,

"What are you doing here " Aheel kawai ya iya jin ya fito daga bakin Nisha dan sai faman kame kame ta ke Ajmal kallonsa ya kai ga door din Aheel kafin ya sa ke kai kallonsa ga Nisha Wanda ya ka sa juran jiran abunda ta ke fad'i ya dai fahimci mai ta ke son cewa nan ya hade gira yana fadi'n

"Kawomin coffee" dan dama abinda ya fito da shi kenan yana fadi'n haka ya juya ya koma bedroom d'insa tura baki Nisha ta yi tana sun ba tu kafin ta nufi downstairs jim kadan ta dawo dauke da cup din coffee bisa hununta ta nufo upstairs gamida karisawa bedroom din Ajmal ta tura door din ta shiga.

kwance ta kalle shi syan bed ya kishingid'e yana sanyi cikin kyakykyawan rigar baccin sa yana danna laptop d'insa jin motsin shigowar Nisha ya sa ya dakata gamida kulle laptop din ya shiga kura mata idanu time din da ta ke karisowa, Nisha a hankali ta ke karisowa sai jan kafar ta ke kamar wani wanda ya mata nauyi kanta sun kuye ko kallonsa ba ta yi ,

daga gefe Nisha ta tsaya kafin ta shiga mika masa cup din coffee din ba tare da ta ce komai ba shi kuwa Ajmal bai amsa cup din coffee din ba time din da ta ke mika masa sai mata nuni yayi da ta ajiye shi gefe saman table.

A hankali Nisha ta juya saman table ta ajiye cup din kamar yanda ya fad'i , juyowar da zatayi sai gani ta yi Ajmal ya mike tsaye hannayenshi na shafa gefen suman kansa ya shiga ta kowa gurin table d'in inda Nisha ke tsaye ta ajiye masa cup din coffee din kenan ta juyo suka hada ido kauda kai Nisha ta yi gamida zamewa gurin ta na kokarin barin wajan, cike da tsoro da mamaki sai gani ta yi Ajmal ya tsare mata hanya ya sha gabanta ya tsaya dam k'irjinta ya buga , shiru Nisha ta yi ba ta iya ko motsiba ganin ya na tsaye gabanta bai kauce ba haka ya sa Nisha kauce masa saboda a tunaninsa ko ita ta tsaya masa bisa hanya but sai gani ta yi ya sa ke ta kowa ya kuma tsayawa gabanta, a tsorace Nisha ta dago ta kalli Ajmal time din zufa ya suma tsatstsafowa goshinta gani ta yi idanun Ajmal na kanta ya tsareta da ido ya na jifarta da wani irin kallo wanda ta kasa fassarashi ko na mai ne ne koma bai iya ce da ita k'ala ba.

Karo na uku Nisha ta sa ke yin gefe cikin hanzari tana kokarin barin gurin Ajmal kafarsa ya sanya cikin na Nisha Wanda ya sanya Nisha ta fiya luuu ta na naiman fad'uwa cikin sauri kuma Ajmal ya rikota gamida fisgota ta fado jikinsa, nan fa Nisha ta shiga yin wuri wuri da idanuwa , Ajmal yana jin yanda zuciyar Nisha ke bugu da cikin sauri kuma da karfi ta kumq kankameshi da karfi ta rike shi saboda tsorita da tayi jim kadan kuma ta shiga zame jikinta tare da tunanin mai yasa ya sanya mata kafa ya na neman yar da ita because ita dai ta San ba tuntub'e ta yi ba .

But sai ji ta yi Ajmal ya kuma riko ta da kyau daga kokarin barin jikinsa da ta ke, rankwafo da kai Ajmal yayi daidai face d'inta numfashinsu ya na gamewa da na juna suna kuma kallon juna Nisha sai zare masa ido ta ke ta na kallon jin rokon da ya mata ya ki sa kinta.

Nisha ba ta ankaraba sai jin Ajmal ta yi ya kai hand d'insa daya kan waist d'inta gamida da matsa waist d'in na ta da karfi wanda ya kuma sa Nisha zabura da sauri ta zame jikinta cikin hanzari ta yi baya gamida g'yara mayafin ta da ya zame ya bar saman kanta numfashin ta sai fisga ya ke aikin tsoro sai fiddu idanu waje ta ke ta na k'yarma kamar wata maijin sanyi.

"Gudun mai kike? akwai wani abinda na yi da ba daidai bane?"

Ajmal ya fad'i time din da ya ke karisawa ga re ta ganin haka ya sa cikin hanzari Nisha ta naimi hanyar fita ta fice a guje cike da tsoro da firgici duba da ya nayinda ta ga Ajmal ya koma ciki , duk da kasan cewar dare tayi sosai gari yayi tsit hakan bai hana Nisha fitowa daga side din Ajmal kamar wata mota ba fuuuu ta nufi sashinsu ta na isa bedroom d'insu ta nemiguri ta kwanta tayi lamo ta na sauke ajiyar zuciya cikin rawar jiki Nisha ta ja

13 / 24