Chapter 4 Reading AJEEMAL Book 2 Hausa Novels By Khaleeseart Abdullahi Raeys.txt Arewa Novels

AJEEMAL Book 2 Hausa Novels By Khaleeseart Abdullahi Raeys.txt

Author :  Khaleeseart Abdullahi Raeys Category :  Hausa Novels 001

Chapter   4 / 24

9K to 12K   out of 70.1K words

masa dashi dazubane wani sabon girkin heelah tayi daban, kallon abincin yashigayi time din da take serving dinshi pepper soup din kazace da soyayyiyar doya da kwai girkin ko kamshi mai dadi baya bayarwa balle kasa ran zaimaka dadi abaki komawa yayi yajin gina da jikin sofa haryaji yunwar da yakejima tatafi, sam bai ji dadin canza masa girki data yiba kusa dashi Heelah tasamu tazauna tadaura hand dinta saman cinyarshi tasuma fadi'n,"

kayi shiru Dear meya samekane yau? tun bayanda muka dawo nadauko Aheel daga school mukazu muka taddaka kana bacci still har dare yayi sosai haka Aheel da mararin son farkawanka yayi bacci baka bude idoba nima naita yawo akanka shiru baka bude idoba ni harna tsoritama nace ko mutuwa kayi amma sena fahimci kana numfashi meyasameka kaketa wannan baccin haka kalau kake kuwa?"

I'm fine yabata amsa a takaice,

Alright kasamu kaci abincin ga gashashshiyar cheese burger with sausage pizza danayi mana order time din da muke dawowa nasan kanaso Heelah tafadi tana mai kai hanu tadauki plate din burger da pizza tamika masa ba musu ya gyara yamasa jin order tayi dan haka seya Kai hanu yadauki lallausan cheese burger yakai baki yasuma ci, barina hadu maka coffee daga haka Heelah tamike tafice bajimawa ta dawo dauke da cup din coffee tamika masa ya amsa ba tareda da wani jinkiriba ,
ataikace burger da pizza kadai ajmal ya iya ci papper soup din baiwuce tabi daya yayiba ya kauda plate din gefe ya Kai hanu yadauki phone din shi, 4 miss call yagani ankirashi koda yaduba yaga 2 miss call from staff and another miss call from Doctor fu'ad phone din nashi a silent take shiyasa ko karanta baijiba idonsa yarintsa ya kuma budewa time yakai idonsa ya duba 12 dan haka seya ajiye wayar baikira kodaya daga cikin suba because dare yayi sosai, mikewa yayi yanufi bed dinshi ya kwanta ya rintsa ido Heelah naganin haka itama tabishi tahaye saman bed din nashi takwanta ajmal yanajin motsinta agefenshi amma yaki bude idon shi harseda yaji takai hanu saman k'irjinsa ta rungimushi tashige jikinsa kamar mai komawa ciki yasa yabude manya manyan idonsa yana kallonta wacce itama shidin take kallo tana masa murmushi,

ahankali yadan zame jikinsa ya mirgina yajuya mata baya because kwata kwata baya son farkawanka ita kuma heelah takasa ganewa itade heelah har kullum mamaki ajmal kebata seyaita zille mata yana gudunta se yanzu take kokarin yarda da kalamun faruk nacewa mijinta bayida maraba da mace da yar uwarta mace take rayuwa gashide aido namiji har namiji but abu yake sekace mace anya kalau yake kuwa? ita tarasa gane wannan lamarin ace kullum ita ke nanike dashi yana zille mata se yaga dama tukun yake iya amincewa da ita gaskiya tagaji da abunda Ajmal yake mata na guje mata da yake

itade tasan ba kazama bace tana tsafta daide gwargwado to meye matsalar ne? wani kuka takawo tasake harda shashsheka cikin hanzari tamike daga bed din tafice daga bedroom din da gudu tana kuka,

Ajmal najin fitan Heelah cikin yanayi kuka yasa ya mike daga kwanciyar da yayi yakoma ya jingina da jikiin bed , shiru yadanyi nawani lokaci yadau tsawan mintuna ahaka kafin yamike yasakko daga bed din yafito daga bedroom din shima , bedroom din aheel yanufa yana zuwa yatura door din yashiga, kwance yasamu Dan nasa yarungume wata big teddy bear yana ta baccinsa cikin kwanciyar hankali karisawa yayi yazauna gefen gadon yashafo gefen fiskan dan nasa yanajin sonsa da kwanarsa yana kara shiganshi, daga nan kuma yamike ya gyara masa rufowan blanket din daga bisani yarage masa hasken light din bedroom din yarufo masa door ɗin ,

bedroom din heelah ajmal ya nufa yana shiga yasameta tagama kukanta tahakura har bacci barawo yasaceta gaba daya jiyayi ba dadi tabashi tausayi , duk da bayajin karfi ajikinsa daniyar rarrashinta yazo ya kuma bata abunda tanema to ganin cewa tayi bacci yasa ya gyaleta yakashe musu light din dakin ya haye saman bed dinta ya kwanta tabayanta ya janyu musu blanket yarufe su daga haka yarintsa ido, bajimawa shima bacci yayi awungaba da shi,

tun bayanda Nisha tayi kiran ajmal a phone kusan sau 2 baiyi picking ba yasa ta hakura dasake kira takuma bedroom din su takwanta cikin yanayi na sanyin jiki da rashin jin dadi, dakuma kulla aniyar gobe da safe zataje taga yanayin jikin nasa
__________________________________
washe gari da safe 8:00 Nisha tayi wankanta tashirya cikin shirinta me kyau kananun kaya riga t shirt mai dogon hanu pink color mai laushi tana dauke da adon me alamar heart agaban rigar , se dogon skirt black se hulan dake kanta shima black tayi matukar kyau da ita
fitowa tayi daga bedroom din tabarsu fadeelah da reeda da suketa baccinsu kamar yanda suka saba because dama su basu cika tashin safe dawuriba inba school suke dashiba suna sallahn asuba suke komawa sukwanta bacci, direct side din shi tanufa seda suka gaisa da securityn dake tsaye wajan kamar yanda suka saba gaisuwa yabude mata door din tashiga,

koda tashigo parlourn azaune ta iske heelah bisa sofa da bowl din cornflakes tana sha gefe kuwa saman table plate ne dauke da kayan snacks tana ci tadaura daya kan daya tana kallon tv jin motsin shigowar Nisha yasa tamaida hankalinta gareta , gamida hararota yayinda take karisowa cikin parlourn,"

barka da safiya abunda Nisha tafad'i kenan kanta kasa tana kokarin karisawa da nufin tafiya kitchen,"

Hee uwar iyayi dakata! Heelah tafad'i tana wurgawa Nisha harara, Nisha tsayawa tayi tana kallonta ba tareda tace komai ba, mikewa heelah tayi tana kallon Nisha sama da kasa kafin ta tabe baki tana fadi'n,"

yau uban gidan naki baya bukatan komai already yayi breakfast dinshi yayi fitarsa but zaki iya shiga kitchen akwai wasu wanke wanken da ban iyayiba kihada da wadannan plate da bowl din kitafi dasu daga haka Heelah takuma watsawa Nisha wani hararan kafin tamatsa daga wajan tanufi upstairs tabar Nisha tsaye awajan tana binta da kallo tareda takaici umarni da take bata hala yar aikinta takeson maida ita ,

Nisha hartayi niyar barin parlourn sekuma tafasa takai hanu tadauki kayan tarkacen da Heelah tayi amfani dasu tanufi kitchen, tunda tashiga kitchen din take karewa gurin kallon ganin yanda akayi kaca kace dashi ga tarkacen wanke wanke da heelah ta tarashi agurin bata iya wankesuba har kullum Nisha mamakin Heelah take da irin lalacin da takedashi amatsayin ta na mace kwata kwata ba tsabtace muhalli ba karamin fama papan Aheel yake da Heelah, bawani bata time Nisha tashiga kimtsa kitchen duk wani abunda kitchen din dake bukata Nisha seda ta mishi ta gyara ta tsaftace, tana kammalawa Nisha tafito daga kitchen din tana yarfe zufar face dinta because ba karamin gajiya tayiba , daidai time din da aka turo door din a parlourn,

Ajmal ne yashigo tareda kamal Wanda suka dawo daga raka Daddy airport, suna tafe cike da nishadi kamal ganin Nisha cikin parlourn Ajmal se raba ido take ga zufa duk ya wanke mata face se yashiga mamakin ganinta ita nan suka karisa shigowa cikikn parlourn suka zauna bisa kujera still kamal se kallon Nisha take shikuwa Ajmal kamar baima san da tsayuwarta jikin parlourn ba Nisha matsowa tayi tashiga daga musu gaisuwa kamal yane ya amsa da ganan Nisha tashiga tambayan Ajmal ya jikinsa kansa sunkuye hankalinsa yana kan phone dinsa ya amsa mata da fadi'n,"

Alhamdulillaha! ba tareda ya kalli inda takeba dan tabe baki Nisha da mamakin kamar ba ita yanemi taimako gurin taba har numfashi fashinta yaso tsayawa sobada shi amma yanzu tana tab bayarshi yajiki kamar bazai amsaba balle ya dago ya kalli inda tak yanzu da lapia tasamu za acigaba da halin Nisha sid'i sid'i Nisha tasamu tafice daga parlourn kamal se waiwayanta yake harta fice, "

Bro meyasameka? Kamal ya tambayi y'ay'an nasu cikin nuna kulawa da damuwa, dagowa ajmal yayi ya kalli kanin nasa tareda sakar masa murmushi yana fadi'n,

"Nothing wani dan zazzabi nayi but now I'm okay, cikin sanyin murya tareda sauke ajiyar zuciya Kamal yace ,"

Masha Allah , Allah yakara lpy bro "

Amin!

Ajmal ya amsa fiskarsa dauke da murmushi ,"

yaushe zaka koma office kaci gaba da aiki ko baka gama hutawaba ? Ajmal ya tambaya yana kallon Kamal, dan shafo gefen wuyansa Kamal yayi yana yar murmushi yace ,"

am da yau nakeda niyar komawa but nabari se zuwa gobe because akwai dan Shirin da nake kamal yabashi amsa cikin girmamawa ,"

That's good daga haka Ajmal yamaida hankalinsa ga phone din shi but ya lura da yanda kamal yaketa muzurai kamar bakinsa yana bukatan cewa wani abun se wani nuke nuke yake ,"

Eheem ina jinka kace kanaso muyi wata magana but kayi shiru kuma what happened? Ajmal ya kuma tambayan Kamal yayinda ya ajiye phone din shi saman table din parlourn yana kallon Kamal tareda sauraron shi, Kamal bude baki yayi daniyar magana but jin rurin karan wayan Ajmal yasashi dakatawa daga abunda yakeson fadi'n, Ajmal hanu yakai yadauki wayan nashi ba tareda ya daga Kiran ba ya kalli Kamal yana fadi'n,"

I'm very sorry zan fita office yanzu but zan nemeka any time , "

Okay bro

kamal yafad'i because dama maganar dayazo dashi nauyin fadawa yayan nasa yake dan haka Kamal yayiwa Ajmal sallama yafice daga parlourn, Ajmal yana ganin fitar Kamal shima ya mike yanufi upstairs bedroom din shi yashiga daga nan yashiga cire kayan jikinsa yanemi towel yadaura a waist dinshi yanufi toilet wanka yayi yafito yasuma shiryawa cikin shiga maikyau black suit yayi kyau matuka yasanya black glass da takalmi se wani agogon gold ta hanu daya sanya kyau kan kyau abun ba amagana, fitowa yayi daga bedroom din shi yanufi downstairs daga bisani yafice izuwa haraban gidan parking space yanufa yashiga daya daga cikin motocinsa white color tsadaddiyar hadaddiya abun kallo da ban sha'awa me gadi yana ganin fitowan Ajmal cikin barin jiki ya bude masa geat Ajmal yayiwa motarsa key yasa kai yafiice,

Karfe 11:30 Hajia da Goggo rabi dasu Reeda suna zaune parlour wanda tun bayan kammala breakfast dinsu suka yada zango gurin suna dan taba hirarsu da suka saba ,"


yaude yakamata naje saloon din nan da shopping kafin tafiyata gobe Hajia karama (Fadeelah) fatan zakimin rakiya , Goggo rabi ta tambaya tana kallon Fadeelah dake washe baki gami da faɗi'n,"

Eh Goggo rabi zan miki rakiya Fadeelah tafad'i tana kallon Reeda gamida yimata g'walo Banda Nisha datayi sunkui da kai tana murmushi , Fadeelah da Reeda suna kaunar fita yawo because basu cika fitaba daga gida se makarnta barin ma yanzu dasuke hutu ba zuwa school duk se zaman gidan ya ishe "

Goggo rabi dukansu uku taso suyi fitan tare zaifi armashi but ganin cewa Nisha da igiya uku akanta baikamata sufitaba ba tareda sanin mijin taba , to gwara sutafi da Fadeelah Reeda ta Taya Nisha debe kewa kar abarta shiru ita kadai, itama taban garan Nisha da Goggo rabi cewa tayi tare zasuje amma ganin cewa tacanza zabi se bata damuba , Hajia itama tasan dalilin dayasa Goggo rabi tayi hakan amma da tare duk yakamata sufita tunda dukansu suna shaawar fitan, "

Allah sarki yarinyar batasan nauyin da ya rataya wuyan taba wannan duk ninayi sanadin hakan amma nan ba da jimawaba zata San nauyin dake kanta duk da batasan ya Nisha zata kalli lamarin takuma karbeshi batareda wani damuwaba duk da tasan hankali da nitsuwa irin na yarinyar, Hajia ke maganan zuci yayinda take kallon Nisha cikin tausayawa da hukuncin da tayanke ba tareda tayi la akari da wani abunda zaije ya dawoba , tana matukar kaunar yarinyar tana kuma jinta sosai cikin zuciyar ta bazataso tayi wani abunda zaicutar da itaba,
sunyi firansu sosai gabatuwan sallahn azahar ne yasa duk suka Mike suka nufi muhalinsu domin gabatar da sallah , Goggo rabi da Hajia suka nufi sashinsu sukuma yan matan suka nufi bedroom dinsu'

bayan sun idar da sallansu suka daura aniyar zuwa side din Kamal gurin Auntyn su Nabilah yar uwa kuma kawarsu suna jin dadin kasan cewa da ita ba kaman Heelah ba da ko kallon side din ta basayi balle suji sha' awan zuwa duk da ita din yar uwarsuce tajini but halinta yasha ban ban da nasu because Heelah akwai bakin hali da rashin kunya shiyasa basa shiri balle suje inda take "

Ke bazaki biyomu muje firan bane gurin Aunty Nabilah, su Reeda ke tambayan Nisha wacce take zaune bisa bakin bed tana kallonsu,"

A'a ni bacci nakeji kuje kawai, Nisha ta basu amsa , basu takura mataba because sunsan kwanan zancen dan haka suka fice daga bedroom din cikin rawar jiki sukabar Nisha wacce ta gyara kwanciyar ta bisa saman bed din , nanfa tafara g'yan'gya dawa bacci yanason cinye idonta Karan shigowar message ne yasa tabude ido da kamar bazata duba wayarba sekuma ta janyota tashiga dubawa , tsulum tamike tazauna ganin message din Ajmal ne Wanda yake bata umarni tashirya masa lunch hulan kanta tazara da sauri Wanda yafice daga saman kanta tamai dashi mazauninsa, dan turo baki tayi ita batasun komawa side din shi ta tarar da wacce masi faffiyar matar tashi tunda matarshi tana nan mai zai hana ta mishi lunch din kamar yanda tamasa breakfast ,

mikewa tasomayi daniyar tafita daga bedroom din ganin shigowar Kamal yasa taja ta tsaya tana kallonshi da mamakin me yakawoshi ,"

yade wannan kallonfa? Kamal ya tambaya yayinda yake karisowa yanemi sofa ya zauna , still de Nisha kallonshi take ba tareda ta motsaba kotace wani abinba ,"

sisy kizauna mana wata magana nazo muyi Kamal yafad'i yana kallon Nisha wacce tadaga kafa ahankali takoma tazauna bakin bed tana kallonshi, murmushi Kamal ya sake yana kuma fadi'n,"

Ko kina wani uzurinne nazo nakatseki , murmushin itama ta kwakwalo tana faɗi'n,"

A'a bakomai, "

Alright barinaje kan batun da yakawone ba tareda bata lokaciba, "

yarda da amincewarki nakeda bukata, dan zaro ido waje Nisha tayi tana faɗi'n,"

Amincewata akan me ya Kamal,? dan gyara zama Kamal yayi hankali kwance yana mata murmushin kashe zuci yace,"

tunbayan da nabada labari abaya gaban Nabilah friends da sisters dina yanda sonki da kaunar ki yadinga d'a wainiya dani har kawo yanzu damuke gida daya dake but ta ban garanki bansan ya kika dauki soyayya taba inaso naji daga gareki ya matsayin kaunata agareki ? yakike feeling soyayya ta cikin heart dinki? shin kina sona kamar yada nabai yana miki ko aa? inason sani wannan shine tambayoyin da Kamal yajerowa Nisha Wanda yasatayin shiru tana kallon kasa kamar mai nazarin wani abu, "

sisy what are you silent kamata yayi ki amsamin tambayoyina ,"

Ya Kamal tambayarka bata da amsa Nisha tafad'i ba tareda tadago sun hada idoba,

"means bak'ya sona? nikaɗai nake ta dakon soyayya? shiru Nisha tayi batace kalaba bata kuma ɗago kai takalleshi ba , shima Kamal shirun yayi tareda sunnar da Kai kasa tsawon wasu mintuna kafin ya ɗago kai yakuma kallonta idonsa duk yayi jawar kamar mai Shirin yin kuka , mikewa yayi jiki ba kwari yasuma tafiya asukwane kamar wanda aka zarewa lakan jiki, wani dariya da Nisha tafashe dashine yasa Kamal dakatawa daga tafiyar dayake yajuyo ahankali yana kallonta,

ganin yanda Kamal yajiyo yana kallontane yasa ta kai hanu takulle bakinta tana me cigaba da dariyan kasa kasa tareda mikewa daga zaunen da take tashiga karisowa inda yake tsaye seda tawurga masa wani murmushi kafin tace,

"tafiya zakayi ba tareda kaji mai zan faɗi' ba"
"mekikeson na tsaya naji bayan kince ba k'yasona , still kin ɓige dayimin dariya like kinga wani mahaukacin" Kamal yabata amsa tareda hararota yana mai kauda kai gefe, murmushi Nisha takuma yi tana fadi'n

"ya Kamal yaushe kaji nace bana sonka?" Nisha takuma tambaya still ta tsareshi da ido , rintsa ido Kamal yayi ya bude tareda sauke ajiyar zuciya ahankali kafin ya jiyo da face dinsa suna facing juna yace

"I'm hearing you talk me kinasona kamar yanda nakesonki ko a'a ?" Kamal yakuma tambayan Nisha yaname tsareta da ido , dan juya mishi baya Nisha tayi kafin tashiga fadi'n,

" Ya Kamal wata macece zaka mata tayin soyayya taki amsa , tun ranar da muka soma haduwa nayabawa hankalinka duba da yanda ka durkusa kana bamu hakuri bisa rashin hankali da dan uwanka yamana duk da ba laifin ka bane haka kuma baka sareba kabimu har lnda muke kaci gaba da bamu hakuri, juyowa tayi takalli Kamal wanda ya tsura mata ido yana kallonta yayinda take maganar kafin taci gaba da faɗin
" Ya Kamal baka da girman Kai zuciyar ka kyakykyawa ce kuma kana da tausayi duk da ilartar da kai danayi cikin rashin sani sana diyar zalunci irin na dan uwanka hakan bai hana nazo da damuwata gareka ka kasa kashare min hawayeba a lokacin da narasa me taimakona ,amm tunani na.......

"shiiiii Kamal ya katsare ta daga surutan da take tafaman kwararo masa

" har yanzu banji amsar da nakeson jiba daga gareki do you love me or not" Kamal yasake jefo mata tambaya, dukar dakai kasa Nisha tayi kafin tace

"Ina sonka ya Kamal but Aunty Nabilah.., cikin hanzari Kamal ya dakatar da ita daga maganar da takeson yi yashiga fadi'n,

"karkisa wani tunani game da ita kibar komai hanuna , kwai abunda zan gaya miki shine bana tsayawa buye abunda nakeso dan haka zan sanar dasu Ammi cewa muna soyayya kuma aure zamuyi banason bata time, dan zaro ido Nisha tayi tana faɗin,

" da sauri haka ? Ya Kamal yaushe ma akayi auren naku gaskiya idan akayiwa Aunty Nabilah haka ba amata adalciba maganar aure tsakanina dakai yayi sauri gaskiya please ajin kirta,

" I'm sorry bazan bari ina kallon muna rayuwa gida daya ace nakasa mallakankiba , bazan iya jiran dugun time ba , karki mantafa nina mijine , mijin mata 4 kuma Allah ne ya bani wannan daman to me Zan tsaya jira nifa ko daga yau zuwa gobe nace ina bukatan Karin aure ba mecemin a'a ko ayi kokarin dakatar dani because sunnace

4 / 24