Author : Khaleeseart Abdullahi Raeys Category : Hausa Novels 001
nakeson rayawa kinga kuma bamaija da sunnar annabi (s .a .w ), da ace tun farko kowa yasan tsakaninmu kuma nasan matsayin soyayyata a gareki dayanzu matsayin matata kike, dan haka banaso kisawa kanki wani damuwa kibarni zanji da komai , shiru Nisha tayi jikinta duk ya mutu sam bataji dadin hakan ba
'yanzu yanda Aunty Nabilah take cikin halin laulayin nan taya zaifara tinkaransu da wani zancen aure' jin shafo gefen face dinta da Kamal yayine yasa ta dawo daga duniyar tunanin da ta tafi ɗago kai tayi tana kallonshi yayinda yake tazuba mata murmushi,
"Am dama akwai wani tambaya da nakeson nami, but inkin bani dama kuma ban takurakiba, kan Neeshi kasa taɗan girgiza masa kai alamar bai takurataba , bude bakin Kamal keda wuya wajan kwararowa Neesha tambaya phone dishi datashiga yin rori yasa ya dakata da maganar yashiga zaro wayar cikin pocket din wandonsa ganin mekiran da kuma mahimmancin shi yasa yadauki kiran ya kara akunne , Nisha bataji mai ake faɗa daga cikin wayarba seji tayi Kamal yace
"I'm coming" daga haka yakatse wayar yakalli nisha daketa faman kallonshi yayinda yake wayar
"Excuse me bari naje nadawo so zamuyi magana back" daga haka Kamal yafice ahanzarce ya bar nisha tsaye tsakiyar dakin , daker ta tattaro nitsuwarta tasamu daman daga kafarta tabi bayanshi, Nisha naganin time din da Kamal yashiga motarshi ya mata key mai gadi yabude masa geat yafice, daga itama tasamu daman karisawa side din Ajmal, bata kaiga karisa shiga tsakiyar parlourn ba taci karo da Heelah dake sakkowa daga upstairs taci uwar ado tarayo mayafi gefe guda tareda back dinta se hararo Nisha take yayin da take sakkowan , kan Nisha kasa bata kuma dagowa takalli Heelah ba , itakuwa Heelah still harran Nisha take bata daina ba seda takariso gefe da ita tazuba uban tsaki tareda wani dugun kwafa takalli Nisha tana fadi'n
"mayya" kafin takuma hararnta tashige tayi ficewarta tabar Nisha agurin kai sunkuye , girgiza Kai Nisha tashiga yi ita tarasa wani kaddarace takawota gidan nan har takasan ce ak'ark'ashin bayan Allah nan gaskiya takaji da wannan wula kancin dan haka tana dab dayiwa tufkar hanci, kitchen din Nisha takarisa shiga tashiga hadawa Ajmal dinner kamar yanda ya bukata , tadau lokaci tana aikin kafin daga bisani tasamu daman kammalawa but har tagama bata ji motsin dawowar shiba gashi haryamma tayi amma shiru kakeji nan tasuma kokarin jira masa abincin bisa dining table kamar yanda tasaba tanemigu tazauna tana jiran shiguwarshi,
hankalinta ta mayar kan TV dayake kunne yana channel din boolywood ana gabatar dawani drama na larabci duk da bajin labcin takeba haka tazubawa TV ido tana kallon yanda aketa zuba soyayya ciki gwani burgewa da ban sha'awa Nisha tayi nisa cikin kallon soyayya , jidatayi anfadu saman cinyartane yasa cikin yanayin tsoro da firgici tashiga fida ido tana kallonshi cikin kayan uniform yanata washe mata bakin nan nashi daya yasaba ,
"Sorry Aunty nabaki tsoro ko ?"
murmushi Nisha tayi tana sauke ajiyar zuciya tace,
"Aa akomai" daga ido tayi takalli bayanshi but bata ga kowaba jin motsin mutum tabayanta yasa tajuya bayan Ajmal ta kallah wanda tuni ya haura upstairs yana shirin nufa bedroom din shi, kallonta tamayar kan Aheel Wanda haryanzu washe mata baki yake cike da murna da farin ciki,
kaje sauya kayanka kadawo kaci abinci , Nisha tafad'i gamida Kai hanu tana kokarin karban lunchbox din shi takarisa dashi kitchen, but sai taga Aheel yanuke shoulder ashagwabe yake fadi'n,
"Aunty muje kitayani , like father like son shima komai se ammsa , dan karya wuya Nisha tayi tana fadi'n
Oya muje to nan takama hanun Aheel suka haura sama suka nufi bedroom din Aheel, sam Neesha bata gajiya da kallon gwanin sha'awa ga kyalekyale da akayiwa dakin Wanda zai nishaadan tar da yara ga teddy iri da kala kyan wasa bedroom din Aheel ba a magana Nisha seda tasa Aheel yayi wanka duk da bawai ya iya wankan sosai bane yadai dauraye jikin sane kwai yafito, Nisha tashiga kimtsa shi, ta tayashi ya sanya kyawawan kayanshi marasa nauyi Wanda bazai takuraba, daga nan ta janyo hanun shi suka nufo downstairs,
koda suka kariso Nisha bataga Ajmal cikin parlourn ba alamar cewa haryanzu bai fitoba kenan, dining table din takarsa da Aheel tazaunar dashi tashiga serving dinshi da daddadan delicious food dinta,
vegetables cuscus with liver soup and macaroni salad shine abinda Nisha tayiwa Aheel serving sedan wani madaidaicin bowl wanda ta zuba masa pepper soup chicken curry mai dadin gaske, duk da tasan Aheel bawai wani cin abinci yake sosaiba amma tanaso kowanne yazamu yasa masa albarka, gefe kuma tashiga tsiyaya masa sassanyan mango smoothie juice, ganin yanda Aheel yake bin abincin da kallo yasa Nisha tasake murmushi gamida shafo gefen face din shi tana fadi'n
"naba abakine, aikuwa kamar jira yake Aheel yashiga daga mata Kai alamar
" eh"
Nisha kujera taja tazauna tana facing dinshi tashiga dibo abincin cikin spoon tana kaiwa bakin Aheel yana ci, cikin matsuwa take bashi abincin yanaci yana mata surutan nan nashi daya yasaba,
"Aunty abincin nan akwai dadi sosai kece kika dafa?
" Eh mana saboda kaima nayi Nisha tabashi amsa tana murmushi, dan tabe baki Nisha taga Aheel yayi yana fadi'n
"Mommy na bata iya irin wannan abincin mai dadin ba but zaki koya mata? Aheel ya tambaya yana kallon Nisha,
" shiii !be quiet kaci abincin ka "
Nisha tafad'i gamida shafa bayansa, daga bisani Aheel yashiga kaɗa kai rin nayarinta yakai hanu ya dauki cinyar kaza yakai baki ya suma cin yana Santi, har wayaude zuwa yanzu shiru kakeji ba motsin Ajmal ba kuma alamar zai sakko har Aheel ya kammala nashi cin abincin papanshi bai sakkoba gashi har magarib ya gabato kai dan haka yasa Nisha taja hanun Aheel suka fice daga parlourn,
Nisha tana isa bedroom dinsu Reeda kaiɗai tagani cikin bedroom din alamar daya batacewa Fadeelah suntafi saloon din da Goggo rabi Reeda jin motsin shigowar su yasa tadago kai tana kallonsu gamida sakar musu murmushi yayinda suke karisowa ciki, da sauri Aheel yasake hanun Nisha yanufi sofa inda Reeda take zaune tana danna waya cikin hanzari Aheel yafada cinyar Reeda tareda fashe mata da kyakykyawan da riyanshi irinta yara
" My little yaron k'irk'i antaso daga school anzu acikamu dasu rutu koh? Reeda ta tambayi Aheel yayinda take sakar masa murmushi tana jan dan kyakykyawan dugon hancinsa, k'yelk'yale mata da dariya yayi gamida gyada mata Kai yana kallonta,
"Oh no ba dani ba wannan surutan naka sede Aunty Nisha kaga tafiyata ni alwalama zanje nayi oya ga phone dina kayiwa Angela wanka kayi feeding nata kafin nadawo Reeda tafad'i gamida zame jikinta daga na Aheel tamike masa phone dinta because tasan shi masoyin game ne especially game din Angela hanun Aheel har rawa yake wajan amsan wayar yana washe baki, Nisha de kallonsu take tana murmushi har fareeda tashige toilet danyin alwala itakuwa Nisha tamike tadawo kusa da Aheel tazaunar tana kallon yanda yake gudanar da wasan angelan nashi,,..
karfe 9 na dare familyn an hadu cikin kata faren parlourn bayan kammala dinner suka shiga gudanar da fira a tsakaninsu gwanin sha'awa, Ammi Hajia Goggo rabi, tareda yan matan Ammi, gefe ga Kamal tareda muhaiseen Wanda Kamal ya daukoshi daga airport dazu ba Wanda yasan da zuwanshi hatta mom dinsa Goggo rabi batasan da zuwansa ba se ganin shi tayi shima Kamal din muhaiseen kirashin kawai yayi yace gashi ya sauka Kamal yaje ya daukoshi , Aheel dake zaune cinyar Ammi ya nata zuba hamma da alamar bacci cikin idanunsa because duk ya gama yin laushi,
" da alamufa yaron nan bacci yakeji naga se g'yan'gya dawa yake gaba kidaya bacci ya kama idonsa" Goggo rabi tafad'i tana kallon Aheel da idonsa sukayi ciki sun kankance, Ammi s hafo gefen face din Aheel tayi tana kallon shi daga bisani takalli Nisha wacce itama hankalinta yake kan Aheel
" ya kamata akai little ya kwanta because dare yayi sosai " aiko kafin Ammi tarufe baki Aheel yatashi sukuf dashi yanufi Nisha yasuma kokarin kama hanuta sutafi, bamusu Nisha tabishi suka fice daga parlourn su hajia se murmushi suke tareda cigaba da hiransu , Jim kadan Kamal da muhaiseen suka tashi sukafice daga parlourn suna dan k'usk'us atsakanin su
"kije ki gyara bedroom din da yayanku yasauka a shimfuda bedsheets , komai yazama clean" Ammi tafad'i cikin yayi na bada umurni tana kallon Reeda, ba bata lokaci Reeda tashiga fadi'n
"to"
daga haka tamike tafice , bajimawa suma suka shiga watsewa because sundau tsawon lokaci suna firan, koda Reeda ta isa bedroom din da ya muhaiseen yasauka baya ciki da alamar bai kariso bedroom din ba suna tareda Kamal, bedroom din a tsaftace yake komai fine because dama ba abarin ko ina da datti agidan ko dayaushe anasharewa a tsabtace shi agoge ko ina bedsheet dine kadai ba ashin fidawa se time din da bako ya ziyarci dakin ,
karisawa Reeda tayi ta bude wardrobe tadauko wani kyakykyawan bedsheet mai taushi tareda blanket tashiga shinfida bedsheet din saman bed daga bisani tadaura blanket saman bedsheet din , tana tsaka da gyaran muhaiseen ya turo door yashigo idonsa yasauka kan Reeda dake kimtsa masa bed nan yashiga sakar mata murmushi tareda karisowa ciki, itama Reeda murmushi tamayar masa tareda maida hankalinta ga abinda take but bata ankaraba seji tayi muhaiseen bisa bayanta yarungumu waist dinta gafi da sakalo face dinsa ta gefen wuyarta yana fadi'n,"
I miss you very much my pretty gaskiya nayi kewarki dayawa na kagu adaura auramu na daukeki natafi dake , nifa banki gobe ashafa mana fatiha nawuce dakeba , but Daddy yakaimu har 2 month wanda hakqn yamin nisa gaskiya ya muhaiseen yafad'i yayinda yake sake rungumar Reeda a jikinsa yanajin yanda sonta da kaunarta yake sake zama sabo fil cikin zuciyar shi, jin yanda ya muhaiseen ya rungumuta tamakar zai maidata jikinsa yasa gaba daya setaji wani irin yanayin da tunda take arayuwa bata taba jinsaba ga kamshin turarensa mai masifar dadi dayasa takasa janye jikinsa daga nata bata ki sutabbata hakaba har tsawon rayuwa ,
ba karamin kewarsa takeba itama ganinsa yayiwa idonta tsada se adau tsawon lokaci basuga junaba sede suyiwaya ko video call nan ma se inyana free because kullum cikin busy yake bugu dakari gari ba daya kuma baicika zama kasarba, jin shiru batayi maganaba ta tsaya kamar sak'aguwa yasa yajanye jikinsa tareda juyo da ita but seyaga ta lumshe ido murmushi ya muhaiseen yayi yana fadi'n
"Yadai " tareda shafo gefen face dinta, bude ido Reeda tayi dasaure gaba daya tafada duniyar tunani ta mance ida take nan tasuma yar kame kame
"Uhm am ba abunda kakeda bukata? Zan iya tafiya ?"
" That's means ke bakiyi missing dina ba" muhaiseen ya fadi'n tareda yin baya ya zauna bisa sofa dakin yana kallonta, girgiza Kai Reeda tayi tana fadin
"Aa ya muhaiseen meyasa zakace haka?"
"gashi kuwa kina fadi'n zaki tafi kibarni cikin kewarki maimakon kizauna kitayani fira har wayewar gari , fito da ido waje Reeda tayi tana fadi'n,"
" wayewar gari fa kace ?
"Eh mana bawani matsala ai Dan munraya dare kina min firan soyayya mai dadi" muhaiseen ya amsa yana mata k'ayataccen murmushi, dariya kawai Reeda tayi gamida tabe baki tana fadi'n
" Muk'wana lapia " tana fadi'n haka tajuya zata fice ,
"ba ki jiba " jin muryan muhaiseen na magana yasa Reeda dakatawa daga fitan da take kokarin yi tajiyo tana kallon shi Wanda ya mike yanufi inda take , kallon kallo sukashiga yiwa juna kafin muhaiseen yadan numfasa ya Kai hanu ya janyo hand din reeda sannan ya sanya dayan hand dinshi bisa pocket dinshi ya zaro wani box dan karami gwani sha'awa wanda ke dauke da kyakykyawan rings na gold mai haske da kyalkyali zoben ya zaro daga box din yasaita yatsar Reeda natsakiya ya sanya mata akwai ya zauna mata damas gwani kyau rings din ba karamin sake fito da kyakykyawan hand dinta tayiba,
"I'm sorry pretty wannan karamin kyautace daga gareni but zoben nan yayiwa hand dinki kyau ko mace hand din ki yayiwa rings din kyau, muhaiseen yafad'i gamida murmushi yana kallon Reeda wacce tasake baki ta zaro ido waje yayinda take kallon hand dinta tana juyashi gamida karewa zoben kallon,
" wow ! wow!! Ya mu muhaiseen gaskiya rings din nan ya yayi kyau sosai ya burgeni matuka thanks you so much gami da sunbatan zuben tana murmushi farin ciki,
" but wannan kyakykyawan sumbatar niyakama ta ayiwa ba zoben ba , dagowa Reeda tayi takalli muhaiseen wanda ya miko mata face dinsa gamida rintsa ido yana mata alamar nuni da yatsansa ta sunbaci kumatunsa aikuwa ba tsammani yaji saukan k'ayataccen kiss bisa kuncinsa saide kafin yabude ido tuni tajuya baya tabude door tafice da saurin, lumshe ido yayi tareda shafa kumatunsa inda ta sumbace shi sauke ajiyar zuciya yayi kafin ya tattaro nitsuwarsa ya shiga cire kayan jikinsa ya sanya towel yanufi toilet wanka yayi sosai daga bisani ya fito ya sanya white jallabiyar sa yanemi saman bed ya kwanata yadau lokaci yana dan tunane tunane face dinsa yana kallon sama sannu ahankali bacci b'arawo ya saceshi,
itama Reeda koda takarisa bedroom dinsu tasamu Fadeelah tayi d'aid'ai tana bacci da alamar baccin ta yayi nisa sosai ga wayarta dake gefe saman bedside table yanata kawo hasske alamar Kira but phone din ta sanyashi silent shiyasa baza aji karantaba dan leka phone din reeda tayi domin ganin mai uzurawa da wannan Kiran ganin boyayyiyar number ne wato ( private number) yasa ta share tashiga neman Nisha cikin bedroom din but ba ita ba alamarta ,.
'bade tunda takai Aheel side din su bata dawo ba' Reeda ta tambayi kanta ganin cewa bata da amsa tambayar ta yasa ta d'an tabe baki daga bisani tashiga yin Shirin bacci kafin ta kwanta tareda rungumu hand dinta tana kallon d'an ya tsanta wanda ke sanye da kyakykyawan zoben gold da hubbynta ya yasanya mata yaude da mutukar murna gamida annashuwa cike da tunanin gwarzon masoyin nata bacci yayi awungaba da ita,..........
'haba Nisha ashe duniya zata iya rudanki ki mance da mahaifinki ? asha akwai rayuwa cikin daula da jin dadi zai iya mantar dake tushenki , Nisha Ina alkhari da kikayimin akan kasance wa da mahaifinki atare dake? ashe zakiya mancewa da abbanki cikin sauki haka? shin kinsan wani irin hali yake ayanzu ?
"wakeup! wakeup !!mana yanzu dan fitowar nan da mukayi daga gida harkin kiyi bacci, Fadeelah ke magana yayinda take tashin Nisha daga d'an gajeren baccin da tayi, nan Nisha tashiga zazzare idanu tana kallonsu se zuba ke tsatstsafo mata idonta yayi jawur dashi yayinda zuciyar ta kuma keta maimaita sunan umma because mafarkin datayi da ita yanzu bisa tuhumar da take mata akan abbanta na nauyin da ta daura mata ,
" Lapia kike kuwa? yanaga kamar arazane kike ko mafarki kikayine? girgiza Kai Nisha tayi tana fadi'n
"Aa"
"kode bakijin dadine because tunsafe nake ganinki so silent " Reeda tajefo mata tambaya, gyada Kai Nisha tayi tana fadi'n
"kaima ked'an ciyo" Nisha ta bawa fareeda amsa cikin kosawa da magana,
"Sorry kijira mu a motar bari muje muyi shopping din mudawo but bari na sauke miki glass din motar saboda iska yadinga shigo miki" gyada Kai Nisha takuma yimusu daga nan Reeda ta sauke mata glass din motar because dama itace ke driving dinsu daga suka fice daga motar suka nufi cikin babban plazan suka bar Nisha cikin morta wacce take ta faman sauke ajiyar zuciya idanunta suncika tab da k'walla karo na farko da tayi mafarkin umma wanda ya bata tsoro yakuma farkar da ita daga shagalan da tayi dan haka takudiri aniyar fita daga motar tagudu tashiga duniya neman mahaifinta, fitowa tayi daga motar tareda handbag dinta da phone din ta tasuma tafiya,
harta danyi nesa da plaza sekuma taja ta tsaya ganin wani mutum dake tin karota yana gudu yana haki, yana sanye cikin manyan kaya riga da wando but sede kayan sunci ubansu da dotti shikanshi mutumin yayi kura yayi futu futu dashi fiskarshi tayi baki sosai gashin kanshima tayi kura gakuma tacika akansa cunkus ga gemanya gaba daya de kallon daya zaka masa yuwa kaga tsohon mahaukaci , nanfa Nisha cikin tsoro tafarayin baya jikinta har rawa take nan tashaga waige waige da neman inda zatayi tunda da alamar gurin wannan mahaukacin yake yiyuwa, harta juya da gudu zata koma gun motarsu saitaji sautin wannan mutumin yana ihun neman agaji
"taimako! taimako jama'!! dan Allah a taimakamu suna bina zasu kamani sucutar dani dan Allah a taimakeni, cak Nisha tatsaya daga kokarin guduwan da take tamaida hankalinta ga mutum dan ganin ina yanufa still gurinta yanufu gadan gadan hakan yasa tarintsa ido gam jiki se bari yake, jin shiru yasa tabude ido bata ganshiba nan tashiga waige waige seda tajuyo bayanta tanganshi ya dukunkune face kanshi da hand dinshi jikinsa se kyarma yake nan tamaida kallonta daga hanyar dataga yafito nan made bakowa bakuma wanda yake binnashi 'to taimakon mai yake nema' jiyuwa tayi takalleshi tashiga tambayan shi,"
" malam suwaye ke binka bacin banga kowa dake biye dakai ba "?
"gasu can suna kuma biyoni" mutumin yabata amsa ba tareda ya dago face dinshiba sake duba hanyar tayi da kyau still de ba k'yallin kowa dan haka Nisha tasauke ajiyar zuciya takalli mutumin ciki da murmushi tace,
dago fiskarka ka kalli bakowa dake binka duba kagani, jin abunda tafad'i yasa mutumin cire hand din shiga face dinshi yashiga kyalla ido yana dube dube kafin ya sauke ajiyar zuciya yana dariya yana fadi'n,"
" Alhamdulillah wallahi natsira sundaina biyoni kasan cewan yanayin gari da hadari sosai nan take ruwa mai karfi ya sakko ganin haka yasa gaba kidayansu suka shiga neman mafaka nan taga mutumin ya watsa da gudu yanufi wata runfa ya shige domin fakewa Nisha itama cikin sauri tabi bayanshi tashige tana rawan sanyi tsayawa tayi