Chapter 24 Reading AJEEMAL Book 2 Hausa Novels By Khaleeseart Abdullahi Raeys.txt Arewa Novels

AJEEMAL Book 2 Hausa Novels By Khaleeseart Abdullahi Raeys.txt

Author :  Khaleeseart Abdullahi Raeys Category :  Hausa Novels 001

Chapter   24 / 24

69K to 70.1K   out of 70.1K words

na wahala da tsoro idanunta duk sun shige ciki kanta kuwa kamar wanda aka daura mata wani abu bisa kai saboda yanda ya mata nauyi mikewa tayi ta sakko daga saman bed din ta nufi bathroom ta wanko face d'inta ta dawo bakin bed din tayi shiru tana karewa bedroom din kallo da tunanin shirun da taji Ajmal ba shigo ba duk ta takura a matukar tsorace take.

Phone din ta ta janyo 11 ma ta wuce idanunta ne ya ciko da k'wallah tab sai faman kallon door take tana jiran tsammanin shigowar shi but shiru kamar anshuka dusa hakan yasa ta g'yara mayafin saman kanta tamike asukwane ta fice daga bedroom din ta nufi parlourn.

Ko da tazo tsakiyar parlourn ba kowa shiru parlourn sai manyan ledar da ta gani an ajiye bisa saman table din hakan ya sa tayi tunanin Ajmal ya shigo da su

Upstairs din ta bi da kallo da tunanin ta Ajmal ya dawo but bai yi tunin ya dubata ko ya waiwaye ta ba sofa ta nema ta dan d'ofana ta k'urawa guri guda ido tana tunani ..

Allah yasa bawani babin wula kacin zai bude mata ba kasan cewar dawowar ta tsaginsa saboda a tunaninta ganin cewar ya tatare dakinsa but ba iya biyowa ta kanta ya duba ta ballai yasan mai take ciki, zare mayafin saman kanta tayi ta janyo ledar take kallah ta shiga dubawa , abubuwan da ake kawo duk wata amarya ce a ciki abubuwan ciye ciye barkate gasunan hanu ta sa ta ja goran yughourt ta bude ta kafa bakinta ba tare da wani ta raddadiba ta suma shaa because yunwa take ji sosai rabonta da abincin zata iya cewa tun safe shima cin sama sama ne.

Sai da ta sha ya kusa rabi kafin ta sauke tana ajiyar zuciya gamida komawa tayi lamo jikin sofa ta k'udundune jiki tana wulga yan idanu Nisha yanda taga rana haka ta ga dare sam ta kasa tsugul ta kasa nitsuwa ga tsoro da take ji ita kadai parlourn shiru ga kuma ta kaicin rashin k'arama wannan dare da Ajmal baiye ba yayi mata banza ko in kula kamar baisan da zaman taba ya kasa fitowa ya dubata halinda take ciki.

Haka Nisha ta dinga g'yang'yad'awa gurin tana farkawa a haka har bacci barawo ya sace ta gurin kwance, da suba k'iraye k'iraye sallah a kan kunne Ajmal ya sauka wanda ya sanya shi bude idanu gamida salatin annabi yana mika yana sauke duguwar hamma.

A kasalance Ajmal ya yaye blanket din da yake lullube ciki ya zaro santala santala kyakykyawan fararen k'afafuwansa ya zamo daga saman bed din ya nufi bathroom ya wanko bakinsa gamida yin alwala ya fito ya sanya fara jallabiyar sa yanufi hanyar fita .

Koda ya nufo downstairs ya iso tsakiyar parlourn sai Nisha ya kalla kwance saman sofa bacci yayi nisa tana sanye cikin adonta na amare ga mayafinta gefe yana lilo dan kallabin kantama ya bar saman kanta.

lumshe idanu Ajmal yayi jin wani abi da ya tsikare zuciyarsa gaba daya sai yaji ba dad'i ganinta haka shi kansa yasan bai mata adalci ba but ba yanda zayi because jiya ya tsinci kansa cikin gajiyar sosai da bai taba jin irin ta ba ta wannan ban garen .

Karisawa yayi har sofan da Nisha ke kwance yasa hanu ya sunkuce ta daga ita har mayafin nata wannan karon baccin Nisha yayi nisa don ko jin Ajmal ya daga ta ba tayi ba.

Cikin bedroom d'inta Ajmal ya mai Nisha ya nufi bed da ita ya suma k'okarin kwantar da ita but sai ji yayi tsam Nisha ta rike hanunsa bisa k'irjinta ta run gume

"Uhm please karka tafi kabarni, bana son kasake nisa dani na yi kewarka sosai". Nisha ta fad'i cikin muryan bacci tana sake shigewa jikinsa, Ajmal mamaki ya ishe sa yaushe daren ma yayi ba lallai gari yawaye ko mai take fad'i haka nan Ajmal ya sake janye jiki gamida jan hanunsa dan karfi yayi baya yana kallonta.

Ita kuwa jin yanda ya janye yasa ta dan bude idanu ta ware su bisa face d'in Ajmal wanda ke tsaye yana binta da wani kallo cikin mamaki duk da yasan ba cikin hankalinta take wannan sun batun ba sake waru idanu tayi ganin Ajmal tsaye bisa kanta yasa ta mike daga kwanciyar tana zare idanu gamida kallon d'akin da tunanin yanda tasamu kanta ciki tunda tasan dai ba anan ta kwanta ba but ganin Ajmal cikin bedroom din shi ya bata amsan tambayar ta.

Dan tura baki Nisha tayi gamida juya baya ba tare da sake kallon Ajmal wanda yake tsaye ba because haushinsa ne tab cikin zuciyarta saboda halin rashin ko in kula da ya nuna mata jiya time din da aka kawota ko lekata bai yi ba , yanzu harda dauko ta ya maido ta bedroom ko waya akesa oho Nisha sai tura baki take tana sumbatu.

Shi kuwa Ajmal ko takan yanayin da take bai bi ba sai sake kallon Nisha yayi wacce ta juya masa baya yana fadi'n

Asuba tayi ki kije kiyi alwala ki daura niyar yin sallah kafin Ajmal ya kai ga karisa maganar sai tsintar muryar Nisha yayi da cewa

"Bana yi " . yanda ta bashi amsa a fisgene ba tare da kuma ta jiyo ta kalleshi ba yasa Ajmal suma lalub'o face d'inta dan ya tabbatar da itace mai ba da amsar ko dai yar yanzu cikin yanayin baccin take .

"Mai kike nufi?". Ajmal ya tambaya yana hade gira ganin cewa cikin hankalinta take infact ma idanuta a bude suke , jin wata tambaya da ya kumayi yasa Nisha ta jiyu rigigine face d'inta na kallon celling tana fadi'n

"Eh fashi nake ina period". ta bashi amsa ba tare da takalli sun hada ido ba, Ajmal bai iya ce da ita komai ba jin yanda take bashi amsa tana wani ya mutsa gamida tura baki yasa yayi tunanin ba sense d'inta take ba shiyasa take bashi amsa gaba gid'i .

Ajmal yasa kai yayi yafi ce daga nan ya fito ya fice yanufi masallaci cikin hanzari because har yana shirin makara anshiga, ta ban garan Nisha ita kanta mamakin kanta ta karfin gwiwa wajan tsintan kanta dayi masa rashin kunya wanjan bashi amsa but Allah haushinsa ne fal cikin zuciyarta duk da tasan kad'anne daga halayensa bai kamata ta daurawa kanta damuwar hakan ba especially da tasan kallon jeka nayi ka yake wa auran.

24 / 24