Chapter 17 Reading AJEEMAL Book 2 Hausa Novels By Khaleeseart Abdullahi Raeys.txt Arewa Novels

AJEEMAL Book 2 Hausa Novels By Khaleeseart Abdullahi Raeys.txt

Author :  Khaleeseart Abdullahi Raeys Category :  Hausa Novels 001

Chapter   17 / 24

48K to 51K   out of 70.1K words

ya ke ta gefen ido yawani hade gira gamida bata fuska kamar wani hadari nan ya figi motar suka d'aga suka bar compound din gidan.

*******************************

"Aunty Nabilah anya ba twins zaki haifa mana ba kuwa only three months kalli yanda ya fito see it" .

Reeda ta fad'i tana haga gira cikin tsokana yayinda take nunawa fadeelah dan k'aramin cikin Nabilah da ke kunshe cikin duguwar rigar ta har ya fara turowa gaba daga fadeelah har Reeda dariya suka kwashe dashi gamida kallon Nabilah wacce ta keta faman musu murmushi ta na girgiza kai ta na kuma sun kuyar da kai but bata iya ce dasu komai ba ta naji suna ta tsokanarta suna dariya.

"Oh ni Allah ya ranan sam ba kuda kunya Nabilah fa ba matsayin da kuka santa da bane yanzu matsayin matar yayanku take ba abokiyar wasan kuba da ku ka wani sanya ta gaba kuna tsokana ".
Ammi ta fad'i ta na hararo su fadeelah da Reeda wanda suka sanya Nabilah tsakiya suna mata surutai

"Ah to kya fa d'a musu dai mijin na mune yaimusu nisa shiyasa daga dawowar ku kuntar muna d'an firanmu cikin hankali da nitsuwa kunzo kun ka tsaimu da shashanci idan ta haifo muku yan biyun zuwa zakuyi ku tayata rainone ? Hajia ta amshi zancen ta na kallonsu gamida tambayar su

"Eh dama inta haifa muzamuyi rainon koya". Reeda ta kuma fad'i tana kallon fadeelah wacce ta yi saurin g'yada mata kai suna mai cigaba da darin ta su.

Jim kadan Nabilah ta mike gamida yi musu sallama ta wuce part d'insu kasan cewar magarib ya gabato kai ta tafi tabarsu Hajia zaune suna yar hiransu sama sama daidai time d'in Nisha t ta sako kai cikin parlourn sumu sumu kamar ba kuwar kaza wanda tun kafin ta kaiga karisowa parlourn take jin muryoyinsu daga waje tun kan ta kaiga karisowa tsakiyar parlourn fadeelah da Reeda su tasu daga zaunen da suke sukayiyo kanta gamida rungume ta dukansu suna fadi'n sunyi kewarta kai kace shkekara sukayi basu sanyata idansu ba.

Hannun Nisha suka ja cikin hanzari da daukin ganinta da nufin karisawa su zauna wanda yasa Nisha rintsa idanu saboda radadin da kafarta keyi ba ta iya wani tafiya cikin kuzari ita ta na tunanin ma kamar kafarta ta dargadewa yayi yanda take
jin zogi cikin kafarta sai mis mis take da idanu tana cizon lips d'in ta cikin dauriya ta bi bayansu fuu suka karisa cikin parlourn suka zauna .

Koda suka zauna bakin Nisha yayi nauyi ta kasa magana ko kyakykyawan d'aga kai bata iya yi sai su fadeelah ne da suka tusa ta gaba da tambayoyi ina sukaje akabarsu da kewanta ita dai Nisha ba ta samu daman basu amsan tambayoyin da suke ta faman yi mata ba.

Daga Ammi har Hajia tun shigowar Nisha bakunansu ya kasa rufuwa jikinsu duk yayi sanyi kamar anjefi kaza da gishiri ganin yanayin da suka kalli Nisha time din da su Reeda suka jawota ciki sai wani mammatse idanu take ta na jan kafafu gamida cizon lips kamar wanda ta samu rauni kafafuwanta.

Ammi da Hajia kallon juna sukayi daga bisani kowa ya kauda kai gamida sake kai kallonsu ga Nisha wacce tayi zuru da ita nan suka ga ta dago musu gaisuwa ta na sunsun da kai cikin fara da sakin fiska suka amsa daga bisani suka ci gaba da yar hiransu ta su da suke kai but hankali su gaba daya yanaga Nisha

Kiran sallah na magarib ne yasa Hajia mikewa ta fice daga bisani Ammi itama Ammi ta mike gamida kallon su Reeda da suka sake baki kamar fanfon kasuwa suna zuba suna suna ta surutan nan nasu da basa gajiya ta umurce su da suje suyi sallah time yayi haka gaba daya yansu suka mike ba da wani jinkiriba suka nufi bedroom dinsu Ammi sai kallon Nisha ta ke wacce ta ke taman nuke nuken kafa, jiinjina kai kawai Ammi ta yi daga bisani Ammi ta haura upstairs ta nufi bedroom din ta itama.

Bayan su fadeelah sun idar da sallah Nisha ne karshen ta na zaune bisa sallaya tana lazumi gamida addu'oi kafin ta mike tsaye ta ninke sallayen ta shiga warware mayafin kanta

"Sis wai mai yasamin kafar ta kine kam tunda kika dawo kike ta jan kafar kamar dawani problem"

Reeda da ke gefe ta cillo mata tambaya tana mai tsare ta da idanu fadeelah ma tsuri tai tana jiran ta ji amsa don dama ta su mata wannan tambayar Reeda ta rigata because abin ya damesu ganin dingishin da Nisha ke yi , dan kallato murmushi Nisha tayi gamida ba ta amsa da cewa.

"Faduwa nayi" Nisha ta ce cikin sanyin murya gamida samun guri kusa da fadeelah daga bakin bed itama ta zauna, kallon juna fadeelah da Reeda su kayi kafin faddei ta kalli Nisha tana fadi'n

"Omg 😱 garin ya ya ince dai ba targade bane buguwa ce " g'yada kai Nisha kawai ta yi alamar "Eh " tana mai mike kafafuwa , nan suka shiga yimata sannu kafin nan Ammi ta sako kai cikin bedroom din bakin ta dauke da sallama.

Sai suka amsa mata kowannesu ya zuba mata ido suna kallon karisowarta, Ammi sai da ta kallesu daya bayan daya kafin ta tsaida idanunta ga su Reeda ta na fad'i

"Kutashi ku bani guri but ina fatan kunyi sallah ba surutu ku ka tsaya yiba"

Gyada mata kai su fadeelah sukayi alamar "Eh" daga bisani suka mike suka fice daga bedroom din a sukwane, Ammi zama tayi inda fadeelah ta tashi kusa da Nisha kafin ta kallo Nisha wacce tayi zuru da idanu kamar tayiwa sarki karya suna fiskantar juna.

"Kyakykyawar y'ata ta ce dai ko lapia na ga kundawo but kafar taki kamar ba kalau wani abinne ya sa mi kafar?".

Ammi tamabya Nisha cikin na tsuwa da kulawa, cike da sauke ajiyar zuciya Nisha ta ce

"Tuntub'e na yi na fad'i " .

ta bata amsa voice d'inta har na shakewa" .

"Tuntub'e kuma yar nan garin ya ya ?".

Shiru Nisha ta yi tama rasa wani amsa zata ba ta kuma garin gudun ne ta ci tuntub'e ta fad'i za ta ce mata koyaya? Daga Nisha har Ammi shiru sukayi ba mai magana Ammi ta gefen ido kawai ta ke kallon Nisha wacce ta sunnar da kai kasa tana wasa da d'an ya tsun hanunta.

Sam ta kasa yadda da zantukan Nisha duk da ta san dawuya Nisha taimata karya tunda tasan ba d'a bi'anta bane but tunanin ta akwani abin da Nisha ke buyawa maybe ko kunyarta ta keji dan ta san ba yanda za ayi Modibbo ya dauki yarinyar ya sutafi can wani gurin su wuni su hantse ace ba abinda ya gifta zakaninsu tunda shi namiji ne ita kuma macce maccen ma wacce take halalinsa.

Ita da farko ma tayi tsammanin d'an wani shakatawan zasu fita yi dan yawo shopping da sauransu but batayi tsammanin abun zai kaisu ga kwana ba.

Ita dai bata isa ta hanashi fita da matarsa duk inda ya keso ba sai dai sam bazataso wani alaka ya suma shiga tsakaninsu tun yanzu ba tunda bawai ta tare bane sansamu ya jira har time din da aka dibar musu ta isa ga dakinta na sunna cikin mutunci kwata kwata bai wuce only three weeks bane ayi abun kowa ya huta.

But tun yanzu ya tusu yarinya gaba tansan yarinyar da zurfin ciki ballai tai mata bayanin da zai gamshe ta ba duk da itama basai ta wahalar da kanta wajan tambaya ba, a sukwane Ammi ta mike tsaye ta na fad'i

"Allah ya kiyaye na gaba ki dinga kula sosai " .

Gyada kai Nisha ta yi alamar gamsuwa kafin Ammi ta kuma fadi'n.

"Ta so muje muyi dinner the food is ready" .

"Bayan nan aikwai wani manzafin da zan baki sai ki shafa a kafafun naki insha Allah zuwa safiya zakiji kamar ta ki da d'an dama".

Ammi ta kuma fad'i

"To " .

Nisha ta ce tana g'yada kai , daga nan. Ammi ta tuso Nisha gaba suka nufi parlour dan gabatar dinner kamar yanda ya ke a tsari...

Washe gari Nisha kamar yanda ta saba ta na yin sallah zata nufo kitchen ta kamawa Barka wasu aikace aikacen duk kasan cewar yau ta d'an makara zuwa ba kamar ko yaushe ba Nisha kafin ta kaiga kitchen d'in Ammi ta hango bisa dining table suna kaiwa da kawo ita da Barka suna tsaka da aiki Ammi na hango Nisha ta shiga yin fara gamida da sake kyakykyawan murmushi tana kallon karisowar Nisha.

Nisha na karisowa dining d'in cikin nitsuwa tashiga dagawa Ammi gaisuwa wacce ke ta faman shirya abincin bisa dining kasan cewar in Daddy nan da kanta take shiga kitchen ta sarrafa masa abunda zaiyi kumallo dashi kuma dake shi yana rigata fita.

Cike da fara'a Ammi ta amsa gaisuwan gamida tambayar Nisha ya saukin kafarta ta amsa da

"Alhamdulillah"

Daga Nisha ta juya ta na kokarin barin gurin wanda cikin hanzari Ammi ta daga tar da ita gamida fad'i

"Please yau dai kam kije ki kwanta ki huta yar nan, nida kaina zan kai Modibbo breakfast am na gama kafar ta ki wahalar da kanki" .

Wani irin sanyi Nisha ta ji cikin zuciyarta kamar ana zuba mata kankara dama sam yau ba ta jin haduwa da shi gaba daya ya sanya mata fargaban haduwa da shi ba musu Nisha ta g'yada kai gamida sakai ta koma ciki zuciyar ta fari tas

__
Zaune ya ke saman stool gaban drees mirror yana sanye cikin tattausan duguwar bathrobe ( rigar wanka) white color yayinda hand d'insa ke rike da hair dryer yana ta faman busar da duguwar suman kanshi cike da nitsuwa.

Heelah ce ta turo door din ta shigo gamida tura door din ta maida ta rufe face d'inta cike da fara'a yayinda take kokarin karisowa tsakiyar d'akin direct gurin Ajmal ta nufa sai faman zubu masa murmushi take tana kallonsa ta jikin mirror wanda ko ta kanta bai bi ba lallai ya san tanayi .

Heelah hannayenta biyu ta sanya saman shouldernsa gamida kutso face d'inta gafen wuyarsa tana mai lumshe idanu.

"Good morning dear" .

Heelah ta fad'i gamida manna masa kiss jikin wuyarsa , shiru yayi mata dan ko daman amsa mata bai samuyi ba sai faman g'yara suman kansa yake, Heelah za ga yo wa gabansa ta yi gamida hayewa saman cinyarsa tashiga garban hair dryer hanunsa ta na fad'i

"Let me help".

But sai ji tayi ya rike gam yaki sake mata sai ma wani banzan kallo da ya ke wurginta da shi wanda yasa ta zame hannuta daga shishshigin da take kokarin yi masa gamida sakin murmushi cikin rashin zuciya Heelah ta shige jikinsa saman kirjinta ta kwantar da kanta ta na fad'i

"Honey! am na mance ba sanar da Kai time din da muka fita daga Aheel can na baroshi gun Mommy I think can zai kare hutun school d'insa dafatan ba matsala?"

Shi tunda ya dawo jiya baya cikin yanayin mai dadi zai iya cewa ji kwata bai ya ganewa jikinsa ba shiyasa ma ko ta kansu bai bi ba amma sam bai yi tsammanin Aheel baya cikin gidan ba, Sanin kanta ne Ajmal ba yason abunda zaisa yayi nesa da shi indan ba ya kasance dole ba ta ban garanshi ballai ma yasan Aheel ta kura zai because bawani sabawa yayi da can d'in sosai ba tunda ba taba kaishi da nufin ya dau tsawo lokaciba ba.

Dan hade gira Ajmal yayi ba tare da ya bata amsa ba ya shiga zameta jikinsa ya mikewa tsaye gamida tufke suman kanshi guri guda daga nan ya zame jikin ya nufi wardrobe domin duba kayan da zai sanyawa jikinsa, d'an tab'e baki Heelah ta yi gamida g'yara zama gurin ta jifansa da wani kallo wanda bazakace gashi na mainene ba.

Nocking din door da ake daga waje ne ya tattaro hankulansu daga Heelah har Ajmal su ka tsurawa door din ido, bugu daya zuwa biyu Heelah ta saki wani guntun tsaki gamida mikewa tsaye ta nufi gurin door din ba tare da ta bude ta ga kowa ye bane ta shiga magana cikin tsawa.

"Madam bugun k'ofar ya isa haka idan wani uzurin muke fa kinwani ishi mutane da nocking sassafen Allah kin di bowa mutane jiki" . Heelah ta fad'i cikin fad'a tana huci a tunaninta Nisha ne kamar yanda ta yi tsammani but sai kuma ta ji an cigaba da yin nocking wanda ya sanya Ajmal dakatawa daga abunda ya ke ya suma kokarin karisowa gurin door din cikin hanzari Heelah ta sa hanu ta murda handle d'in door din bakin ta na fadi'n

"Amma daike wannan anyi may.." sit Heelah ta kama bakinta ta tsuke ba tare da ta karisa abunda take son cewa ba ganin Ammi tsaye bakin door din time d'in da ta karisa budewa

Zuru sukayi dagav ita har Ajmal d'in da ya biyo bayanta yana kokarin bude door din Heelah ta rigashi .

"I'm sorry na yi zaton waccer shashashar yarinyar ce" Heelah ta fad'i ta na kasa da kai kamar wata ta Allah.

"Ba sha shashar bace uwarta ce bani guri na shige" . Ammi ta fad'i cikin bacin rai tana hararo Heelah wacce take sanye cikin wata yar fingilar wando ko alamar ta ji kunyar ganinta haka ba tayiba.

Heelah kai sunkuye ta zame jiki ta bar bedroom din sai faman tab'e baki ta ke kasa kasa ta na kallon Ammi ta gefen ido , ganinta dauke da tray d'in abinci hanunta, harta karisa ficewa Ammi kallon Heelah take tana jinjina Kai gamida mamaki.

"Amma dai wannan anyi sakara, duk yanda akayi wannan yarinyar kanta ba daya ba" . Ammi ta fad'i cikin jimami tana kallon Ajmal wanda ya sauke wata ajiyar zuciya ganin shigowar Ammi sab'anin tunanisa.

Karisowa tsakiyar d'akin Ammi ta yi gamida ajiye tray d'in bisa table din tsakiyar d'akin kafin ta dubi Ajmal wanda ya zauna bakin bed yana kallonta shima gamida dago mata gaisuwa.

"Good morning ".

"Morning ya wayewar garin?". Ammi ta tambaya cikin yanayin fara'a

"Fine". Ajmal ya amsa a takaice ya na kallon Ammi

"Breakfast na kawo maka but nazo na tadda kana tsaka da shiryawa incedaiba sauri kakeba?" . Ammi ta tambaya, girgiza kai kawai Ajmal yayi gamida cillowa Ammi tambaya.

"But where is she".

"Wai Nisha naga tun daworku jiya na fahimci bata jin dad'i shine nace na hutar da ita yau kam ni da kaina na hada maka kyakykyawan delicious wanda na san zakaso ".

"Is not your work please kidaina wahalar da kanki" Ajmal ya fad'i cikin face d'in damuwa.

"Don't worry just iya yaune but nasan kana matuk'ar son abinda na girka da hanuna nasan kuma kayi kewar hakan while indan kanaso ma har abiki saina iya baka na tuna maka yatintar ka because na sanka da son jiki idan ba ka canza yanzu ba? " . Ammi ta fad'i cikin tsokana tana yar dariya

Shi kanshi Ajmal baisan sanda murmushi ta kwace masa ba harsai da kyakykyawan hushiryarsa ta bayana gamida lotsawan dimple d'insa ya na kallon Ammi wacce ta mike tsaye cikin annashuwa

"Bari naje na baka guri kar na dameka da surutu, zanturo Barka ta zo ta kimtsa muku muhallin na ku idan da bukatan hakan" . Ammi ta fad'i harta juya zata fice sai kuma ta juyo ta dan kallo shi kad'an tana fadi'n.

"Am nace ba tunda an tsaida ranar bikin adan jinkirta fita yawo da kwana wani guri sai zuwa bayan biki tunda ba ayi tariya ba tukun kaga kai babban mutum ne ba kowa yasan da batun auran ba" . Zuru Ajmal ya bi bayan Ammi da kallo wacce ta fice tana murmushi ta janyo masa door din tarufe .

Shi dai ya kasa gane maiye tunaninta gameda shiba tunda suka fita da yarinyar hankalinta ya kasa kwanciya har kawo yanzu da take kokarin k'wab'ansa ga abunda ya ke k'ark'ashinsa, d'an jinjina Kai Ajmal yayi gamida mikewa ya shiga sunce madaurin rigar kafin ya cire ya shiga sanya kyawawan tufafinsa.

*******************************
Nisha

Karfe 4 dawasu yan mintuna yamma lis Nisha ta farka daga baccin da take ta faman yi tun bayan azahar, ita kadai bisa cikin bedroom din ta nasanye cikin riga t shirt mai dogon hanu white color gamida high waist skirt black colour, direct bathroom ta nufa ta gabato alwala ta fito ta shinfida darduma gamida sanya dugun hijab tashiga gabatar da sallahn la'asar.

bayan idar da sallah ne ta shiga yin addu'oi daga bisani ta mike ta cire hijab din ta koma ta kwantar ruf da ciki ta rungumo pillow gamida janyo wayarta tana dubawa.

Door din aka turo akashigo cikin bedroom din ita dai taji motsin shigowa but ba tasamu daman g'yarawa ta ga ko waye bane ta yi tunanin su Reeda ne yasa ta ci gaba danne dannen wayarta , dukan da taji ankaiwa gadon bayan ta ne yasa ta mike azabure ta waigo gamida zaro ido waje.

Salma ta gani tsaye kamar amafarki ta ci ado sosai ta yi kyau da ita lullube cikin wata kyakykyawan sari yayi mata kyau kwarai.

"Surprised" .Salma ta fad'i gamida lankwashe jiki tana juya idanuwa".

"Salma!" Nisha ta fad'i cikin mamakin ganinta cikin wannan time din yau kwana uku dayin bikinta ta ganta anan to koma dai gizo tai mata ga idanunta gaba daya Nisha ta sake baki tana binta da kallo daga samma har kasa.

"Please rufe bakin mana kin bude shi yana shan iska" . Fadeelah ta fad'i wanda suka shigo tare da salma , Nisha gimtse baki tayi tana bin Salma da kallo wacce ta zauna gefenta sai faman zuba kamshi take.

"Kinyi mamakin ganine ? Na gaza hakurin ganin ki shiyasa nazo sam hankalina yaki kwanciya". cikin hanzari Nisha ta fad'a cikin Salma ta rungume ta gamida sake kukan farin cikin ganinta.

lumshe idanu Salma ta yi gamida saukar da ajiyar zuciya ganin aminiyarta wanda ta ke jinta tamkar ciki daya suka fito , d'an zame jiki Salma tayi gamida kallon Nisha wacce ta keta faman goge hawayen farin cikin.

" Godiya nazo na miki na musamman". Salma ta fad'i tana dan hararo Nisha wacce ta sunnar da kai a kunyace ba tare da ta ce

17 / 24