Author : Khaleeseart Abdullahi Raeys Category : Hausa Novels 001
Ammi tana fadi'n
"Yau bai fi saura wata daya bikinsu fareeda da tariyar Nisha ba amma hankalina ya kasa kwanciya ta ban garan Modibbo ko mai zai ce a kan hakan karon farko da nashiga alhini kan lamari inaga kamar wannan karon nayi kuskure da rashin adalci tsakanin y'ay'an nan" Hajj mama ta fad'i cikin jimami kallon juna Daddy da Ammi su kayi kafin Ammi ta sauke wani nan nauyan ajiyar zuciya tana fadi'n
"Da ka fad'i mata yan da mukayi da y'ay'an nata ko itama hankalin nata zaifi kwanciya" Dan g'yara zama Daddy yayi gamida g'yaran murya still fara'arsa ba ta gushe ba ya kalli HAJIA kafin ya shiga fadi'n
"Hajia karki wani da mu kanki Ammi ta bani labarin bayan ta fiyana halinda yarinyar nan ta tsinci kanta aciki sai naga adalcin da zan iya musu shi a zauna dasu dan jin ta bakin kowannesu akan lamarin idan da yiyuwar wakan lamarin fanillahilhamdu idan kuma da yiyuwa hakura da auran baza su iya zauma da junansu ba to cikin sauki sai araba auran,"
"To alhamdulillah ta bangaran Modibbo a yanda muka yida shi bai wani nuna damuwarsa ga lamarin ba sai dai ya bukaci ya zauna shikadai yayi shawara da zuciyarsa a takaice dai nasan yaran basu ki bin maganar muba because suna da hankali baza su bamu kunya ba ta ban garan yarinyar ma ba wani tsaya wa dugun tunani ta amince ta zauna da shi matsayin abokin rayuwarta kamar yanda Ammi ta labarta min", wani hamdalah hajia tayi gamida godiya ga Allah alamura sun ta fi cikin sauki ta yanda ba tayi tsammanin ba
"Allah dai yayiwa yaran nan albarka ya sanya albarkarsa cikij lamarin" HAJIA ta fad'i cike da farin ciki da jin dad'i,
"Ameen " su Daddy suka amsa Time din da su Reeda da fadeelah su ka kariso dining din su ka zauna tareda dagawa iyayen nasu gaisuwa cikin girmama wa
"Yau har kun koshi da baccin kenan ko daukin dawowar Daddy ya sanya kuka tashi yau da wuri haka Dan nasan sai 10 ko fi " Hajj mama ta tambaya ta na kallonsu but ba su ce mata komai ba sai dariyar da su ke su na k'arawa nan su ma suka shiga daukan plate suka shiga serving din kansu breakfast yayinda barka ke ta kai kawo a tsakaninsu ta na dauko musu duk wani abinda suke so ko suke bukatarshi a gurin
" wai ina Nisha ne ita banganta:anan ba" Ammi ta tambaya ta na kallon su Reeda wanda su ke tsaka da breakfast, carab Barka ta karbi tambayar da cewa
"dazu muna tare da ita cikin kitchen din nan ta gama taya ni wasu ayyukan daga da bisani ta fice inaga side din yayansu ta nufa kamar yanda ta saba"
"Okay" Ammi ta ce gamida jinjina kai ta ci gaba da yin breakfast d'inta suna mai ci gaba da hira,
"Daddy ba ka kawo mana tsara ban komai bane" su Reeda suka tambaya suna kallon Daddy
"Sannu yan gidan tsaraba to ce muku a kayi ta fiyan jindadi yayi da kuke tunanin tsaraba" Ammi ta cafke maganar gamida basu amsa tana hararosu, dariya Hajj mama da Daddy su kayi kafin Daddy ya ce
"Kyalesu na kawo musu tsaraba babbama kuwa kuma na san zasuji dadinta" Daddy ya fad'i gamida murmushi yasanya hanu cikin picked din jallabiyar sa , fadeelah da Reeda sai tsili tsilli da ido su ke sunyi k'uri da ido dan ganin mai Daddy zai ciro cikin aljihu, nan suka ga ya zaro phone d'insa ya dan daddanna kafin ya mika musu har rige rigen karba su ke
"Kuyi dai ahankali karku mini ta adi Daddy ya fad'i ya na kallon su fadeelah da suke ta fada kowa so ya ke phone din ya zama a hanunta akarshe Reeda ne ta damke wayar tana fadi'n
"Ke dallah ki tsaya mugani a nitse" fadeelah sai hararanta ta ke tana cizon lips daga bisani suka shiga kallon wayar don ganin mai Daddy ya keson nuna musu, kayan furnitures ne kala kala masu ke tsadaddu Daddy ya musu order daga Dubai kafin zuwan bikinsu komai da amare suke bukata anta na daishi masu kyau gwanin sha'awa da burgewa su Reeda murna kamar ba gobe cike da murna su ka shiga nunawa su HAJIA da Ammi, Ammi dai mamaki da kallon y'ay'an nata ta ke yanda suka wani zage sai murna da farin ciki su ke bawani kunya atare da su oh yarinta kenan,
Yau Nisha cikin fargaba da tsoro ta kammala komai ta g'yara ko ina fes Aheel na biye da ita duk inda tayi to ya na biye da ita ya na mata surutan nasa da ya sa ba da baya gajiya ita kuwa sai biye masa ta ke badan tana cikin ya nayi mai dad'i ba ,ta na tsaka da jera breakfast din bisa dining table kamar yanda ta saba sai wul wulga ido ta ke ta na sauraran sakkowan daya daga cikinsu aikuwa sai Ajmal ta gani cike da nitsuwa ya na sakkowa daga upstairs ya na sanye cikin black jallabiyar sa gwanin sha'awa, sau daya suka hada ido Nisha ta kauda kai gefe ta cigaba da abunda ta ke yayinda Aheel na ganin papanshi ya ruga aguje ya he ya rungomesa kamar yanda ya sa ba suka kariso dining table din suka zauna a dan su kwane Nisha ta shiga daga masa gaisuwa ganin ya zauna.
"Ina kwana antashi lpy, daga mata kai kawai yayi ba tare da ya kalle taba ko bude baki ya amsa mata ba cikin damuwa da sanyin jiki Nisha ta shiga yin serving din Ajmal kamar yanda ta ke yi kullum daga nan shima Aheel Nisha ta yi serving d'insa da duk a bunda tasan yanaso kafin Nisha ta dan saci kallon Ajmal wanda ya ke breakfast ya na kuma danna waya hankalinsa ma baya kanta haka yasa ta tayi ba ya ta haura upstairs ta nufi bed din Ajmal domin ta gyara masa gudun karya kuma yi mata magana a kan hakan , Nisha sai da ta fara g'yara toilet ta wanke ta tsaftace kafin ta dawo bedroom ta suma g'yarawa shima a hanzarce ta ke yin aikin yau because ta kosa tabar sashin Ajmal.
Tana tsaka da g'yaran Ajmal ya turo door ya shigo cikin bedroom din Wanda ya sa Nisha dagowa time din da ta ke tsaka da gyara masa bed, Ajmal kamar baisan da zaman Nisha cikin bedroom din ba yazo yawuce yanufi bathroom ya wanko bakinsa gamida hannyensa kafin ya fito because dama already yayi wanka kaya yake bukatan sawa, Nisha ta na ganin Ajmal ya fito hankali kwance ya nufi wardrobe domin duba kayan da zai sanya but duk wani motsinta ya hankale da ita , Nisha kama hanyar fita ta yi because ta kammala aikin da ya kawota .
"Wait "Ajmal ya fad'i gamida jiyuwa yana kallonta, ras k'irjn Nisha ya buga, kafin ta tsaya kyam kanta kasa ta rasa mai Ajmal ya ke nemanta da shi kullum ba arasashi da abun fad'i ko korafi
"Samu guri kizauna "
Ajmal ya kuma fad'i still idonsa na kanta harta kuma tsakiyar dakin ta nemigu saman carpet ta duka da tunani iri da kala a ranta, shikuwa Ajmal bakin bed ya nema ya zauna gamida kai kallonsa ga Nisha wacce tayi ladab da ita dad'in sa da yarinyar akwai respect din mutum baisan tsantsan kwarjinin da ya ke matane yasa ba ta iya hada ido dashi
"Look at me carefully magana nakeso muyi da ke but feel free banaso kina wannan rawar jikin da kike kuma ki bude baki kiyi min bayani sa'in da na tambayeki"
Nisha shiru ta yi gamida sake k'ank'an da kai tana sauraren abunda zai tambaya ye ta , d'an gyara zama Ajmal yayi gamida kallonta da kyau kafin ya ce
"Am tunda kikazo gidanan nan ba wanda ya nemi karin bayani akan ta rihin rayuwarki ko jin wani labari da ya shafi rayuwarki sai dai ayanzu ta bangarena kin kunna min sha'awar sun jin labarin rayuwarki da ta rihinki kasan cewar ina da right na san wacce ke sunan ki da kuma ta rihin iyayenki go ahead I'm hearing you " shiru Nisha ta yi idonuwanta sun cuko da kwallah ta na neman kuka ta na sonyin magana but kuka yana neman kwace mata
Nasan mahaifiyarki ta rasu shine dalilin da yasa hajia tausaya miki ta dauko ki ta kawo ki cikin gidan but ina sauran yan uwanki da mahaifin ko shima ya rasune? Ajmal ya kuma tambaya Amma gamamakin sa abun ta kaici kuka ta shiga jira masa tana shashsheka wanda yasa Ajmal ransa ya suma baci duk tambayoyin da yake mata cikin sigan nitsuwa da kwanciyar hankali mai makon ta nitsu ta bashi amsa ta shiga yi masa kuka Ajmal tsabar takaici ya suma kokarin mikewa but sai ji yayi ta bashi amsa cikin cool voice
Mahaifina bai rasuba Nisha ta fad'i tana share hawayen face d'inta gamida jan hanci
Ajeemal
Story and writing
By
Oum amreesh
Book 2
Page 74
_____cike da mamaki Ajmal ya kuma ya gyara zama jin tana da mahaifi but ta zauna a nan tsawon lokaci tana rayuwa ba tare da sanar da kowa ko ta nemi mahaifin na taba duk da baisan dalilin ta akan hakan ba Ajmal g'yara zama ya kumayi da kyau kafin ya kalli Nisha cikin tsare gida ya ce
I'm hearing you continue your talk,
"Ni sunana Aisha Hashim yarima friends dina suna kirana da Nisha an haifeni a garin adamawa maihaifana yan asalin kasar Sudan ne fatauci ya kawoshi Nigeria, ni ba yar kowa ba ce amma Allah ya rufawa mahaifina asiri kuma Allah ya bun kasa masa samunsa ta hanyar kasuwancinsa wanda yayi sana diyar dawowarmu nan cikin garin kano da zama, ni kadai Allah ya mallakawa Abbana a matsayin y'arsa daya tilo ya kuma nuna min gata sosai kamar yanda a ke nunawa y'ay'aye mafi soyuwa wajan iyayensu sun kuma bani tarbiya daidai gwargwadon iyawarsu sun kuma sanyani makaranta mai inganci amma duk da haka hankalin Abbana bai kwanta ba ganin ni dayace jininsa banda yaya ko k'ani hakan yana damunsa kwarai da gaske, kasan cewar Abbana mutum ne mai sun yara da kuma son tara zuri'a, amma umma ta ba ta sa ke samun wani karuwa ba bayan ni hakan yasa ya kara wani auran, ya auro aunty faty wacce na ke kira da Mami wacce itace silan rugujewan farin ciki rayuwata da ta mahaifiya ta.,
Nan Nisha ta shiga baiwa Ajmal labarin rayuwarta da ki da ki ba tare da ta boye masa komai ba da ya shafi rayuwarta da ta iyayenta, da b'acewar Abbanta wanda har yau har gobe ba ta sa ke sashi idonta ba duk da bata cire tsammanin sa ke tuzali da Abban na ta ba kuma bakin cikin ganin nasa ne ta ke tunanin yayi silar rasa mahaifiyata saboda damuwa da rashin sanin halinda ya ke ciki ya kuma kasa zuwa inda suke, haka Nisha ta cigaba da bawa Ajmal labarin yanda ta ka sance a rayuwarta cikin kuka mai tsuma rai da ban tausayi sai dai kuma cikin labarin na ta tayi hide wani ban gare da ya shafi haduwar ta da Kamal, kamar yanda tayi tunani kar garin g'yaran gira arasa ido saboda tsonrata da bara zanar kb da yayi mata na cewa,
' duk ranar da Ajmal ya fahimci itace silan ilatasu kwanakin baya to fa k'oneta zayi da ranta ko ya daure ta sai igiya taisaura, da sauran uk'uban da ya dinga lissafo mata wanda Ajmal zaiyi mata duk randa dubunta ya cika, duk da ta su ta fada masa but tunanin ta ba ta san ta wani fiska zai dauki al amarin ba, maybe ma kafin ta gama sanar da shi zata tsinci harsashi cikin kwakwalwar kanta
Nisha sai da ta kai karshen labarin karfin ta diga aya cikin kuka ta na jan hanci gamida goge hawayen face d'inta abun tausayi face d'inta yayi jawur dashi idanunta duk sun kunburu saboda kuka, parlourn ne ya dau shiru kai kace ba halittun mutane ciki, Nisha jin shirun da tayi kamar ba mutum a wajan ya sa ta d'an dago kai ta sato kallonshi carab idanunsu suka hade cikin na junansu Ajmal ya mata kuri ya na kallonta kamar wata tv tunda ta fara magana ya jingina jikin sofa yana sauraronta kamar wani radio ya naso ya gasgata labarun nata but bayi da tabbacinin abunda ta ke fad'i gaskiya ne ballai ya dauka ya sanya cikin mind d'insa,amma in har da labarain ta gaskiya ne akwai abun tausayi da rikita hankali, wani goron numfashi Ajmal ya sauke gamida duk'o da kai ya sanya hannayensa duka biyu kasan habansa kafin ya kuma duban Nisha da kyau yana fadi'n
"You can go but but karki fita da wannan hawayen face din nakin, so Go and wash your face in side the bathroom Ajmal ya fad'i cikin cool voice na shi mai kamar rad'a wanda ya sanya Nisha sa ke marairaucewa ta na matse ido kafin ta mike ta nufi toilet kamar yanda Ajmal ya fad'i
Nisha wanko face d'inta tayi sosai kafin ta fito tana goge ruwan face d'in na ta da gefen d'ankwalin ta wanda tuni yabar saman kanta dama bai cika zama ba saboda laushi da sulb'in gashin na ta, Nisha dai tv ta komawa Ajmal because sai kallo ya ke bin ta da shi ya na k'arawa da tunani iri da kala cikin ransa ita kuwa kanta kasa duk ta tsargo da kallon da Ajmal ya ke bin ta da shi to ko bai gamsu da labarun na ta bane oho because ta sanshi bai dasaurin yadda da mutum Sam, Nisha dai haka ta fito ta bar Ajmal na binta da ra kiyar idanu,
A cci ta na jin mom din na ta tana magana but ta kasa amsa mata saboda bakin cikin da ke kwallace cikin zuciyarta.
" magana fa na keyi shiru kinajina yau ina aikin kika taho sassafe inama kika baro Aheel idin ince dai ammusu hutun school suma" gamamakin ta maimakon Heelah ta tashi ta amsa ma ta tambayoyin ta but sai kuka Heelah ta fashi da shi cikin kuka ta ke fad'i
"Mom yarinyar nan za ta sa zuciyata ta fashe saboda bakin ciki, ta rabani da kowa bawanda ya ke ganin da wani kima ko farin jini yanzu sunfi daukarta da mahimmanci fiye dani," zaman dirshen Heelah ta mike ta yi bisa gadon ta na ci gaba da fadi'n
"Mom yarinyar nan ta rabani da farin cikin rayuwata d'ana Aheel mijina duk ta rabani dasu ke kadai na ke dashi yanzu" Heelah ta fad'i gamida fadawa jikin mom d'inta ta cigaba da jero koke koken nata, shiru Hajia Jummana ta yi tana tunani na rashin fahimtar zantuttukan Heelah inda suka dosa to wacce yarinyar da Heelah ke magana akaine because hajia Jummana ta ma mance da wata Nisha da ke rayuwa cikin gidan Daddy.
"Kinga barwannan kukan ki tashi kimin bayani yanda zan fahimta kinsani aduhu kintayar min da hankali wai wace yarinyar da kike magana akai ne?"
"Nisha ta ke ko nishii ita ce ta ke kokarin shiga min hanci da k'udunduni ta rabani da farin ciki na akanta ya Ajmal ya fara wulakanta har dukana ya ke kamar jaka a kanta kowa na gidan ya juyamin baya kamar ba susan da ni cikin gidan ba haka shima ya Ajmal matukar yana ganinta tana wulgawa komai ita ta ke yi masa kamar matarsa ni dai nazama yar kallo jiya da dare har side d'insa ta biyu shi shiko ya ja hanunta suka shige bedroom d'insa suka rufe shine da na shigo na ta da masifa ya rufeni da duka ya fitar dani mom Aheel ma ta kwaceshi daga gareni idan ya ganta jikinsa har bari ya ke idan ya ganta mancewa ya ke Dani kamar banice na haifeshi ba " Heelah ta karisa zancen cikin kuka.
"Tab d'i lallai fa tsincecciyar magi ba ta mage akuyar sunce ta samu sake yanzu haka al amura suka cab'e daga zuwar wannan yarinyar cikin gidan shine suka hadu suka juya miki baya harta fiki kima da mutunci aidanunsu to wallahi bazai taba sab'uwa ba bindiga a ruwa dole su gayamin matsayin yarinyar nan agidan saboda zagewar yayi yawa wato har makwanci mijinki ta ke shiga idan kika hana akai miki duka?" Mom ta tambaya tana kama haba tana kallon Heelah.
"Eh harda min warning hakan ta wai ko kallon banza karya sa ke shiga tsakanina da ita gaba daya ma fa kamar sonta ya ke sai kin gani" Heelah ta fad'i tana cizon lips " mom inban kashe yarinyar nan ba bazan hutaba Allah sai dai nima a kasheni"
"Kul karna sa ke jin haka idan kika kasheta ke kuma aka kasheki inyi yaye kenan? ke kwata kwata ma bazaki ci moriyar zaman duniya ba wayace miki ta haka ake huce ta kaici sawa zakiyi ta gwammaci kida da karatu, duk dama wani ban garan hadda sakaci irin na ki da kika bata kofa ta rab'i mijinki gaba ki daya kin lalace kin susuce sai na rasa uwar mai kike a gidan ince daga kwanciya sai bacci ba aikin fari bare na baki duk yan aikin da ake kawo miki sai kin koresu kuma ke ba abunda kika iya sai zuwa office"
"To duk ba ke kika sangartamu ba ko tsinkefa bana dauka a gidan time din da na ke nan hajjo da Nabilah ne keyi sai waccen Aunty amaryan gashi na tashi a tutar babu harwata na so ta kwacemin miji saboda tsabta da iya girki wallahi koni mace sai da na sarawa iya girkinta shiya sama na ke zagewa na ci nima" Heelah ta fad'i tana tura baki
"Eh lallai kice kema aikin ta ya fara ta siri a kanki kenan ke wato nine ma na san gartaki na hana kikoyi abubuwan rayuwa? gatan da nanu miki saboda karki sha wahala shine sangarci to yayi kyau kin kyauta amma dai bazan bar wannan lamari ya ci gaba da ta fiya haka ba
"To amma ya batun wancen complain din ince