Author : Khaleeseart Abdullahi Raeys Category : Hausa Novels 001
ido dakowa batasonyi, amma daga kaga yanda eye lashes dinta kerawa zaka fahimci ba baccin takeba rufe ido kawai tayi dan murmushi Barka tasaki gamida kada kai tana fad'in, "
Megida bari naje nakarisa aiyukana se anjima allah ya inganta , kamal cikin farinciki ya amsa da "
amin mungode
daga haka Barka takama hanyar fita still de murmushi bai gushe daga face dintaba harta karisa ficewa tajanyu musu door din tarufe, kamal kallonsa yamayar kan nabilah yayinda yakuma jan dugun hancinta yanda fad'in, "
To yanzu kam semi samudaman bude idon iyayen kunya , waima kunyar mekikejine haka shigowar ammi dazu kigabi kika takura kanki sewani nuke nuke kikefa , bude ido tayi tana kallonshi daga bisani tatura baki tana fad'in"
Ni wallahi kunyar kowa nakeji yanzu ko hada ido dakowa banasonyi ,"
meye dalili ko saboda kintaho musu da tsaraban Canada kamal yafadi yana yar dariya, dan bugu takaiwa shouldern kamal tana fad'in, "
Kaikam bakajin komai ko ? "
To maizanji kuwa bayan nasan kokarin danayi tashi muyi breakfast dan yunwan nakeji kamal yafadi gamida tada nabilah zauna yashiga bude food flats din abincin, pepper soup din kifine da soyayyiyar irish tareda wani hadin salad nakayan itatuwa masu kara lafiya da kuzari se wani dan madaidaicin bowl wanda ke rufe da Yugo fruit salad ancika madara acikinsa, bawani tsayawa bata time kamal yashiga serving din su ,
yana gama zuba abincin a plate yashiga bawa nabilah abaki kamar karaman baby shima yanaci ba laifi komai tadan tabashi taji kuma jidadin abinci sosai especially hadin salad din tafi bashi ma himmanci dadin dadawa yanda kamal yayi tsayuwar kaida fata wajan ganin taci takoshi bakaramin dadi hakan tajiba koba komai yana kula da ita sosai but hankalita yaki kwanci ganin kamal da nisha Inuwa daya suke zaune suna haduwa dajuna wanda hakan baya mata dadi kokadan ,
*_IG AJEEMAL*_
Story and writing by
Oum amreesh
Nisha hanunta har rawa yake gurin kunna light din bedroom din aiko tana kunnawa haske maikyau da inganci yabaiyana cikin dakin , ahanzarce tajiyu tamaida hankalinta ga saman carpet , kwance yake ya dunk'ule guri guda kamar mejin sanyi still yana rungume da pillow tsam a chest dinshi yana sanye cikin kyakykyawan milk jallabiya gashin kansa duk sun hargitso face dinsa sun manne saboda zufanda suka tsatstsafo masa ,
idonsa arufe jin motsin mutum da kuma kuna light da akayi yasashi kokarin bude ido ahankali yasaukesu kan Nisha dake kokarin karisowa inda yake lips dinta se bari yake, idonsa yamayar yarintse wanda sukayi jawur dasu because haske yayiwa idonsa karfe "
Ya ilahi Nisha tafurta ahankali yayinda tagama karisawa gareshi gefe ta sunkuya kasa tana kallonshi"
meyasa sameka? are you okay? Nisha tashiga jera masa tambayoyi cikin rawar murya, jin shiru bai amsa mataba yasa takuma tambayan shi still shirun yakumayi ba amsa hakan yasa tayi tunanin tashi tabashiguri domin atunaninta maybe hanlin nasane na miskilanci yamotsa , amma ayanda taganshi yanzu kamar Wanda bashida cikakkiyar lapia saboda yanayinsa gaba kidaya yanuna hakan gashi yayi shiru baya magana balle tasan abinda ke damunshi, can gefe takalla inda wayansa keta faman ruri saman bed sekuma ta maida kallonta gareshi shiru bai motsa ba baikuma sake bude idoba se ajiyar zuciya dataji yana saukewa , gaba kidaya tagama tsorita anya papan aheel kalau yake kuwa ? gashi haryanzu kiran phone dinshi aketayi ba adenaba da alamar mekiran ya k'agu ,
Ahankali Nisha ta isa ga bed din tasa hanu ta dauki wayar daga fiskar wayan taga maikiran sunan doctor fu'ad ya baiyana jikin screen phone din , nan Nisha ta fahimci yau ana duba file din ajmal that means bashida lapia kenan Nisha karisawa tayi tareda wayar inda ajmal take kwance taduka kusa dashi tana fadi'n,"
ga phone dinka anata kira , halwayude bai kumace mata kalaba idonsa arintse se red lip dinsa daketa faman bari yana motsi, "
Allah sarki maybe yanajin jiki sosaine da hartayi tunanin daga masa wayar tafadawa doctor fu'ad halinda ta iske ajmal aciki to amma wayakaita wannan karan banin dan haka seta ajiye wayar agefensa tana fadi'n,"
sannu bari naje nafadawa su hajia azo akaika asibiti Nisha na gama fadi'n haka tamike cikin hanzari, charab taji yariko kasan riganta cikin sauri Nisha tajuyo takalleshi still idonsa a rufe se bakinsa dayaketa kokarin motsawa yanaso yace wani abin , Nisha dawowa tayi kusa dashi tasunkuyu tana kallonshi,tana kuma kallon lips dinsa meyakeson fadi"
Help me! abunda taji yace kenan slowly araunace Nisha tashiga tambayanshi,"
wani abun kakesone kafin takomacewa wani abu sejitayi yace ,"
d'agani ! dan tsaro ido Nisha tayi tana kallonshi kafintace ,"
indagaka zuwa ina ? "
Bed kawai taji yakuma fadi yana mai sake rungume pillow jikinsa da alamar sanyi yakeji sosai , kallonshi Nisha tashigayi sama da kasa yanzu inba neman magana irin na papan aheel ba ina ita ina iya dagashi , gaba kidayanta in aka hadata guri guda bata wuce lumansa dayaba ga tsayi gajiki tasan ba karamin nauyi zaiyiba to amma yazatayi tunda ya nemi taimakonta dole ta taimaka mishi yaka karfinta , dab dashi taje takuma tsugunawa ta dan janye pillow dinda yarungume ita kanta pillow seda tayi dumi saboda zafin jikin ajmal, dan koda ta matso dab dashi numfashinda yake fitarwa shima dumine jikinsa yayi zafi sosai,
da ganan Nisha shiga taimaka mishi wajan tashin takamo hand dinshi tadaura saman shoulder dinta dakyar da sidin goshi tareda taimakonsa cikin karfin hali suka samu daman mikewa , sede koda suka tashi taku daya zuwa biyu suka shigayin tangal tangal da juna ajmal karfenshi ya gaza because jikinsa ba kwari sosai bayajin karfi ajikinsa jikinsa duk amace yake haka Nisha taji yasake mata ragaman jikinsa gaba daya duk yanda Nisha tayi kokarin tallafoshi amma se jikake luuu ajmal na kokarin faduwa aiko cikin sauri da fargaban faduwar tasa Nisha taja hanusa da karfi suka fada saman bed tare kamar kifan mazar k'waila haka suka kife ruf ajmal yarufe Nisha da faffadan k'irjinsa ko burbud'inta ba agani, wani dugun numfashi ajmal yashiga saukewa jinshi saman lallausan bed din shi zamu iyacewa gaba daya ajmal baya cikin sense dinshi Sam yamance yana kwance kan halittan da adam ,
itakuwa Nisha tunda suka kife takasa motsi se zazzare ido tashigayi face dintama ba agani balle hancinta yashaki numfashi taririn zafin jikin ajmal sebugunta yake gashi bayida niyar dagata hala ko suma yayi taji shiru bai dagataba bugun heart dinshi da yanayin yanda yake sauke ajiyar zuciya duk tana iyaji , shikuwa mutumin jin dumin jikin Nisha yabashi wani yanayi mai dadi da kozari ajikinsa yasa yashiga sake tattarota jikinsa yarungume kamar yanda yasaba rungume pillownsa jinwani wawan runguma da ajmal yamatane yasa idanunta suka fito waje tsabar tsoro dakidima Nisha tasaki wani kara tana fadi'n,"
Wayyo Allah wayyo ummana zaikashenii.., tar ajmal yabude ido jin muryan Nisha datake sumbatu, cikin zafin nama dakarfin hali ajmal ya kauce gefe cikin sauri yasa hand yadafe goshinsa face dinsa yana kallon sama yarintsa idonshi, Nisha najin kaucewan ajmal tayi hanzarin zamowa daga bed din tana sauke ajiyar zuciya tareda tattaro numfashin ta dake kokarin tsayawa hanu takai tadauki mayafinta dake saman bed din Wanda yafice daga kanta tamaidashi mazauninsa , sidi sidi tasuma kokarin barin bedroom din kanta asunkuye hartazo bakin door tajiyu takai kallonta gareshi, lokacin harya yasan gyara kwanciyarshi yakai hannu yaja blanket yarufo jikinshi , Nisha juyawa tayi tafice daga bedroom din ajmal yabi bayanta da kallo akunyace yarasa wani irin zazzabine yarufeshi haka da har yakasa control kanshi har seda yanemi taimako,
rintse ido yakumayi gashide yarufe jikinsa da blanket but baisamu irin relief dinda yasamu dazu da yarungume Nisha ba amatsayin pillow shine mai wannan dumi me dadinba dan mintunan daya samu yayi ajikinta har yafara jin saukin abunda ke damunshi, gaba daya ji yayi ransa yadagule masa yarasa meke masa dadi , Nisha kuwa tana fitowa daga bedroom din tanufo downstairs gudu gudu sauri sauri haka take sakkowa idonta duk sun fito waje tsabar o, tana gama sakkowa taja ta tsaya ganin doctor fu'ad zaune bisa kujeran parlourn yanata faman Kiran line din ajmal,
ganin sakkowan Nisha arikece yasa hankalin doctor fu'ad dawowaa gareta wanda yasashi mikewa yashiga yimata murmushi, itama murmushin tashiga kirkirowa tana shafa gefen wuyanta daga nan tashiga dagawa doctor fu'ad gaisuwa, cikin fara'a ya amsa da mamakin yanda yariyar ta canza kyanta yagara baiyana dan da ace baisan tabama ba lallai yace yataba ganin taba ,"
mutuminfa nakirashi bai daukaba doctor fu'ad ya tambaya,"
yana bedroom din shi Nisha ta bashi amsa asanyaye,"
Alright barinaje naduashi doctor fu'ad na gama fadi'n haka yanufi upstairs tareda akwatin agajinsa yana kuma waiwayen kallon Nisha yarinyar akwai kyau da kwarjini ba amagana gurin yarinyar ga hankalin da nitsuwa ga kuma shiga zuci, yana isa bakin door din yatura door din yakarisa shiga bakinsa dauke da sallama yanda Nisha tafita tabarshi haka doctor fu'ad yazo ya taddashi idonsa arintse kamar mai bacci, ajmal jin bude door anshigo yasashi bude ido ahankali ganin doctor fu'ad tsaye kansa yasashi kara bude idon dakyau yana kokarin gyara zama doctor fu'ad dakanshi ya taimaka masa wajan gyara masa zamar ganin cewa yau abokin nashi jikin ba kwari sosai, "
sannu boss yajikin ?doctor fu'ad yafad'i tareda duba yanayin zafin jikinshi , "
tunyaushe kake fama da zazzabin maizafi haka? doctor fu'ad yakuma tambaya, Dan numfasawa ajmal yayi cikin cool voice yake fadi'n "
Problem din da kasanine ya tasomin after that bayan sallahn asuba zazzabi yabiyo baya , "
meye amfanin pills in problem din yatasu meyasa kakeson wasa da lapian kane ? "
I'm tired ajmal yafad'i yana Dan ya mutsa face, Dan murmushi doctor fu'ad yasaki yana kallon abokin nasa wanda ya hade gira yabata fiska "
Hmm naji tunda ka gaji dashan pills se ka sauke miskilanci dake kanka kafahimci rayuwar aure kadinga sauke hakkin dake kanka kabar cutar da kanka da bokiyar zamarka duk da nasan matsalar ka da ita amma hakan bazai hana katauyewa kanka hakkiba, so gaskiya inde zaka cigaba da cutar dakanka haka zanyiwa Daddy da ammi bayani Dan bazan tsaya insa maka ido kana kokarin cutar da lapiyar kaba , kana daya daga cikin maza masu bukata over so kama tayi katafiyar da lapiyar ka yanda yakama karka tsaya cutar da kanka because wannan problem din bakaramin effect garetaba lokaci daya zaiyi affecting naka ba tareda ka ankara ko kashirya masaba so you have to be very careful with that issue
ajmal shiru yayi yana sauraron zantukan doctor fu'ad duk da ba yau yasaba jinsuba yasaba tunatar dashi duk lokacin da suka kasance tare shima duk yarasa meke damunshi , idan yace baya bukatan mace yayi karya to amma feelings akan matarshine Sam bayida ita kwata kwata bayajinta aransa balle yaji shaawar neman wani abu daga gareta , some times itake bibiyanshi tana shishshige masa wani lokacin yabiye mata wani time dinkuma inta dameshi haka zaizame yafice yabata guri ,
duk da wani lokacin yakanso yiwa kansa fada Dan yasan ba karamin cutar da ita yakeba baya bata kulawar da tadace , to amma ya zaiyi rayuwarsace tazu da haka amma yana fatan canzawa , sauke ajiyar zuciya yayi yana kallon doctor fu'ad wanda ya mike tsaye yabude akwatin agajinsa ya zaro allura seda yayi arranging din alluran kafin ya kalli abokin nasa yana fadi'n,"
Allura zan maka wanda zazzabin zai sauka daga haka yanufoshi ba musu ya gara yamasa alluran daga bisani yakuma dauko daya alluran yakalli ajmal yace wannan kuma alluran baccine zan maka because kanada bukatan kahuta sosai nasan jiya baka iya bacciba , shide ajmal binsa yake da ido bayacewa komai harya gama alluransa ya kuma ya tsaya yana fadi'n,"
Zuwa anjima bacci zai iya daukanka kafin doctor fu'ad yagama ida zancensa seji sukayi anturo door anshigo Nisha ne tafe bakinta dauke da sallama tashigo hanunta dauke da try din abinci tanufi table din tsakiyar dakin ta ajiye daga bisani takai hanu tadauki cup din dake bisa saman try din Wanda ta hadowa ajmal hot coffee din daya saba sha yakeso especially yau datake tunanin baisa komai acikinsaba saboda rashin lapiyan da yatashi, dashi , gabaki daya zuba mata ido sukayi barinma ace doctor fu'ad yakalleta yakalli ajmal wanda ya zuba mata namujiya yana kallonta gaba daya itama Nisha setaji wani irin nauyin ganin irin kallon da suke mata , "
am dama coffee na hadu maka kokanada bukata Nisha tafadi muryarta harsakewa yake harta suma kokarin kasa kasa da hannuta ganin bai karba cikin sauri doctor fu'ad ya amsa yana fadi'n,"
sannu da kokari sister kamar kinda abunda yake da bukata kenan doctor fu'ad yafad'i yana mata kataccen murmushi, itama dan murmushin tayi jiki asanyaye takalli ajmal wanda yasuma lumlumshi ido allura yasuma ratsashi daga bisani tamaida kallonta ga doctor fu'ad wanda keta zuba murmushi kamar gonar auduga kafin tajuya tafice tabasu gari , doctor fu'ad naganin fitanta yajiyu yakalli ajmal wanda ya lumshe ido bacci ya fara cinye idonshi doctor fu'ad cup din coffee ya mayar ya ajiye bisa table ya kai hanu yadauki akwatin agajinsa daga nan yasuma kokarin ficewa ganin mutumin nasa yasamu bacci seda yarage masa hasken dakin kafin doctor fu'ad yasamu daman ficewa daga bedroom din yajanyo masa door din yarufe , yana fitowa daga side ajmal yashiga motarshi mai gadi yabude masa geat yafice yaso yashiga sugaisa dasu hajia but saurin dayake bazai bari yakarisa cikin gidan ba yabari sewani lokacin da ya ware na musamman,
yaumade kamar kullum bayan sun kammala dinner dinsu suka koma parlour akashiga taba hira kamar yanda kasaba gabaki daya family da kakalli fiskokinso zaka fahimci suna cikin nishadi da jin dadi , daya yasanar dasu gobe Daddy zaiyi tafiya kamar yanda yafad'i musu abaya , kuma sanar dasu cewa sun zauna da dan uwansa sun tattauna tsakaninsu yakuma sheda musu yanda sukayi sun tsayar da bikinsu fareeda da fadeelah zuwa 2 month masu zuwa inshallah, su hajia ba karamin dadi sukajiba da wannan kyakykyawan labarin ,"
Masha Allah to allah de yakaimu yasa albarka cikin lamarin , hajia tafadi cikin murna da farin ciki goggo rabi Daddy da ammi sukashiga fadi'n,"
Amin Banda su reeda da suka shiga kallon junasu suna muzurai farin ciki ba amma magana Nanda dan wasu lokaci suma zasu zama matan aure gurin mazajensu , sede ita hajia karama( fadeelah) ta dan damu because gashide ana maganan tsaida ranar bikinsu but ko saudaya basu zauna da mutumin nata sun tattauna tsakaninsu balle kowannensu yabada labarin yanda yake feeling dan uwansa to amma de tazubawa sarauta Allah ido taga yanda lamarin zai kasance, "
Alakullihalin tunda alamaru suntafi yanda yakamata nimade zuwa jibi jirgina zai daga zan koma gida nima, "
Au wai tafiyar zakiyi baza kitsaya ayi bikin da keba seki koma gaba daya naga month din bayawa Daddy yafad'i cikin zolaya yana kallon goggo rabi wacce tafiddo ido waje ,"
wani ! rufamin asiri gida yayi kewata nafa jima anan tun bikin kamal yau kusan wata daya kenan gashi har ansamu rabo inanan ina zaune ai gwara natafi daga baya nakuma dawowa ga baki daya family dariya sukashigayi jin batun goggo rabi sunsa ba karamin miss dinta zasuyiba zayi miss barkwancinta , sun raba dare suna hira har guraren 10 daga bisani sukashiga yiwa juna sallama kowa yanufi makwancinsa ,
gari yayi shiru gida yayi tsit su nisha duk sunyi shirin bacci sun kwanta , reedane kawai take zaune bisa sofa tana waya da habibinta Wanda take sanar da ita zaizo seda suka kammala wayan tadawo bed takwanta zuciyar ta fari tas farin ciki da annashiwa ba a magana , aka har bacci ya dauketa , Nisha kuwa lumshe ido kawai tayi but bacci yakasa daukanta ta juyanan ta juya can bacci yaki , nan tunanin ta yashiga tuna mata yanayin da suka kasance dazu da ajmal, yanda tayiyo zafin jikin ajmal bisa jikinta time din dasuka fad'i bed dakuma time dinda yarungumota Wanda yasanya tsikar jikinta tashi , mikewa tayi zaune tazauna ,"
oh Allah koya jikin nasa yanzu ?
Phone din ta tadauka ta sakko daga bed din tanufi parlour shiru parlourn ba kowa harta doshi hanyar fita se kuma taja ta tsaya ganin dare yayi sosai gashi tasan wannan uwar tsiwar Heelah tanan batasan ya zasu kareba but tamatsu taga ya yanayin jikin nasa yanzu, haka tanemi guri tazauna tana ta sakawa da kuncewa mafita dayane yazo mata Kiran line din Ajmal kamar yanda yace zata iya kiranshi taji koyanada wani bukatan duk da ba kowani lokaci yake daga kiranba balle yanzu dayake cikin halin rashin lapia, ba wani tsayawa bata time tashiga kiranshi kamar yanda tunanin ta ya bata,
Ajmal wanda tashinsa kenan tun bayan da Doctor fu'ad ya masa allura bai farkaba se yanzu 11 cikin yanayin kasala da rashin karfin jiki Ajmal ya yaye blanket din jikinsa saboda zufanda yasuma tsatstsafo masa alamar cewa zazzabin ya sauka adafe yanufi toilet wanka yayi sosai tareda alwala ya fito, sam bai lura da Heelah wacce take kwance saman sofa tamike bacci yayi awungaba da ita se yanzu daya fito idonsa yasauka kanta, kauda kanshi yayi yashiga zaro wata jallabiyar yasanya sannan yashin fida sallayan yashiga jera sallolinda suka biyoshi,
seda yamika sallonshi duka sannan ya sallame ya ninke sallayan yadawo saman sofa ya zauna abincin da Nisha takawo masa dazu yashiga budewa because yunwa ya tashi dashi acikinsa, Heelah jin buruntun bude food flakes yasata motsawa tabude ido tana kallonshi,"
Dear wani irin bacci kayine yau din nan? Heelah tashiga tambayan Ajmal cikin muryan bacci shiru yayi mata yana kallon try din abincin da Heelah tajera a table din Heelah mikewa tayi ta taso tamatsu gareshi tana fadi'n,"
bari nayi serving dinka nan tashiga kokarin serving dinshi ya tsaya kawai baice mata komaiba gaba daya jiyayi ransa yadagule masa ganin ba abincin da Nisha tashigo