JINI YAFI RUWA COMPLET BOOK BY D AUTA.doc

Author :  Hadiza D. Auta Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   10 / 69

27K to 30K   out of 206.5K words

juyawa, ba dawakai bane mata ne tsirara, suke zuwa kuma ba zaka tab'a ganin kafar su ba.

? ? ? A hankali yake kallona.
"Tun d'azun nayi tsammanin zaki zo." Gyada kai nayi sannan, na sunkuyar da kaina. Domin matan suna zuwa suka shiga shafe mishi jikin shi. Yana kallon yadda na sunkuyar da kaina.

?? Tun da nake a rayuwata ban tab'a ganin yadda ake kwanciya da mace a zahiri ba, sai gashi nan a kan idanuna. Mutumin nan yana kwanciya da matan nan daya bayan daya, kuma idan ya gama zai sauka ya koma kan Waya.jikina ne ya dauki mugun rawa. Na firgice sakamakon tun karo ni da yayi.

?? Jikina yana rawa bakina ya gaza furta kome, haka tawo da mugun gudu ya dauke ni cak, tare da kai ni wani daki na daban a wani gida da yake sama zance ko haka yake ban sani ba, yana kai ni dakin ya dire ni.? A gaban madubi ya ajiye ni, tare da janye min kayan jikina, farin gashin da yake surke a jikin gashina ya bayyana, shafa shi yayi yana faWin.

"Haske na ne ya zuba a kan ki, shi yasa gashin kanki yayi fari tas. Haka nake son ki haifa min fararren Yara kyawawa irinki." Ya fada yana shafa kaina, na kasa furta kome, na kasa motsi duk yadda yayi dani haka nake bin shi.

? ? ? A hankali ya kai hannun shi zai tab'a jikina na ja da baya. Ina girgiza mishi kai.
"Waye kai?" Naji bakina ya furta haka,
"Me yasa ka shigo mafarkina, me yasa?"
"Ban sani ba! Ni dai ina sonki"
"Waye kai?" Na tambaye shi da karfi.
Kallon kofar dakin yayi sannan yace min.
"Zaki tarawa kanki mutane! Kuma bana fatan a fara miki kallon mahaukaciya"
"Me yasa zaka shigo rayuwata?" Na fada da ?arfi! Kai ne ka Wauke min sh..."

"Rooman tashi kiyi alola kin kwanta sai surutu kike ko?"? Naji muryan Innah, kafin nayi magana, ta shigo dakin tare da buga min matashin kaina, a hankali na bude idanuna, ina kallonta, ba ita nake kallo ba shi nake kallo da yake tsaye a bayanta.

? ? "Ina nayi mugun mafarki ne"? na fada ina mik'ewa daga kwanciyar. "Sai a kace karki yi addu'a? Wannan ai sakarcin ne? Maza tashi kiyi alola" ta faWa min tana barin d'akin, a hankali na kuma kallon wurin baya nan,. Kasala ce da kiwuya ya sauko min,? a hankali na nufi ban daki na shiga da addu'a nayi alola. Ina fitowa nazo na shimfid'a abin sallah. Sai da na gabatar da nafilla,.sannan na zauna tare da kallon window dakin da nake jin wucewar, abu da gudu.? Kamar wacce aka tura ni lallai sai na leka.

? ?? A hankali na isa jikin window zan bude shi naji an rike hannuna.
"Me zaki gani?" Yayi min tambayar kamar zai shige jikina.
"Hm"
"Koma ki kwanta" kamar wacce nake kiran umarnin shi haka na koma na kwanta, ban kuma sanin meye ya faru ba, sai da gari ya waye. Innah ta bude min so window,

? ? ?? A hankali na bude idanuna ina kallon agogon dakin.
"Subhanallahi! Yau ban yi sallah asuba ba, har bakwai" da gudu na isa ban daki nai wanka da alola tare da fitowa na gabatar da sallah, sannan na cigaba da azkar, har takwas saura na fito ina kallon Innah.
"Yau zaku wuce Yola!"
"Eh" na zauna a kujeran da Abdul Malik yake na dauke kofin kunun shi na sha.
"Matsalata dake kenan koda mutum yana marmarin ki da zaran ya ganki toh karshe dole" dole ki hau mishi kai gaskiya gwara ki koma Yola ko zamu maida kiba."

"Na shiga uku na lalace! Hande kawai kununka kawai na kurb'a kake min jafa'i da masifa toh can da su gada"
Dariya kanena suke min, tare da goyan bayana, a hankali muke hira har Mama tazo nan na shiga wanka na barsu suna tattaunawa.

....
Karfe goma sha biyu muka bar garin Mubi zuwa Yola, mun isa gida da wuri dan haka muna isa muka fara abin ci, tare da hira
?? A hankali rayuwa yake tafiya cike da kalubale, musamman na rayuwa kuma jarabawa ta kowani fuska ina ganin shi abin da yake daure min kai iya ni ce nake fuskar ta haka, babu me fuskar abin da yake faruwa dani, babu me gane halin da nake ciki.

Na kan zauna nayi kuka nayi shiru, sai naga kamar rayuwar ba tawa bace,?? ganin Khamil yaki zuwa Alhaji Babba ya bani damar fito da wanda ya akace mishi ana gani na da shi a hotel. Wallahi ban tab'a zuwa hotel ba, amma sai gashi ana yawan gani na a can.

? ? Har Yola Daddy ya biyo ni yayi min fada, Innah ma tazo amma a banza. Zama nayi a gaban Mama ina kuka nace mata.
"Wallahi ban tab'a zuwa ko ina ba, ki yarda da ni."

?? Ganin yadda nake kuka yasa Baffa Chindo ya ce min.
"Tashi ki koma cikin gidan"

?? Wasu daga cikin dangin mu sun yarda wasu kuma kawai sun ji ne,dan sun ce ana son a rufa min asiri ne. Gefe guda Mehd yaki magana, nayi nayi ya fito amma bawan Allah nan yaki dan haka muka yi faWa dashi.

?? Muka rabu sabida bana jin tayi yadda nake tunanin shima muka nasan kofa magana tayi karfi, karshe suma tafiya zai yi ya barni da dakon kayan shi. Dan haka na watsar da su baki Waya.

Wani abin mamaki sai ba daina mugayen mafarkai da kuma ganin abin da nake gani, har nake murnan ko dai na samu lafiya ne, haka ba karamin dad'i ya sani ba.

? ? ? ?? **
Bayan shekara biyu.

? Ina wurin aiki, kaina yayi zafi aka ce nayi bako, na sha mamaki ganin Hammah Khamil da rakiyar Hammah yusef.
"Hmm! Ku ne? Sannun ku da zuwa" na juya tare da niman excuse. Basu hanani ba, kasancewar bana wasa da aikina.? Haka suka Barni muka nufi gida, duk da lokacin tashi aikina yayi haka nayi ta jin wani irin farin ciki yana ratsa ni.

? ? ? ?? "Manyan kunyi kudi kun boya?" Inji Hammah yusef,
"Hmm!" Kawai nace mishi, tare da kallon wayata.
"Yan mata baki tambaye ni yaushe na dawo ba?"
"Hmm!"

"Toh tun jiya nazo nace zan miki surprise"? murmushi nayi me sauti, kaina a sunkuye sannan nace mishi.
"Barka da hanya?"
"Yawwa"? ya ce min.
" Aiki?"
"Alhamdulillahi, ya naki aikin?"
"Alhamdulillahi! Yanzun gani nan na dawo saura kawai ayi bikin mu sai na tafi da takardun ki na fara nima miki aiki a can kafin ki? nan kin gama had'a kayan ki, sai ku biyo.."
"Kiiiiiii" Hamma Yusuf ya taka birki..
300? ... Insha Allah'
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A'ichah
+22784506476
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank
#Mai_Dambu
EXQUISITE WRITERS FORUM.
JINI..!
? ?Ya fi Ruwa Kauri?
? *Base on true life story*

*Sadaukarwa ga Family Hasssan Yero Family da Madakin Muri Family*

? ? ?? Mai_Dambu

BABI NA SHA BIYU

"Innalillahi wa'inna ilaihirrajiun! Lafiya?" Hamma Khamil ya tambaye shi, kallon titin yayi, dukkan mu har shi din, wata bakar saniya ce a tsakiyar titin. Tana huci, idan Hammah Yusuf ya motsa motar ta ja itama. Abin mamaki ka da baya yayi aikuwa ta rufi motar da gudu, tare da kai mishi wani irin duka da kawonta.

? ? ?? "Innalillahi wa'inna ilaihirrajiun!" Na fada da karfi, kamar almara haka saniyar nan tayi ta dukar motar mu. Sosai fa ta haukace mana, dakyar Allah ya kwace mu, sakamakon zuwan wani dattijo zai wuce, ya daka mata tsawa, shine ta shiga daji da gudu, shi kuma ya tsayar da mu tare da leka motar, sannan yace mana.

"Waye zai aure a cikin su?"
"Ni ne Baba" inji Hammah Khamil,
"Toh ka shirya da kyau" ya fadi haka tare da juyawa ya dauki keken shi ya shiga dajin.

?? Kallon juna suka yi, sannan Hammah Yusuf ya ja motar muka bar gurin, koda muka isa gida, kamar wanda aka shafe mana tunani mun manta.

? ? **
Ganin Hammah Khamil ya dawo aka saka bikin a kurkusa, tare da shirin ba zata.

Ana saura sati biyu bikin, Khamil ya tafi lagos,. Bayan ya gama abin da zai yi ya nufi masaukin shi, zai shiga hotel din ya hango Rooman, tsaye da wasu maza biyu,? daya yana dafe da k'ugunta suna masha'a, hango shi da suka yi ne, suka bar wurin, dan haka yana shiga dakin shi ya fara kokwanto, sai ya gwada kiranta.

Yana kiranta yaji muryanta tana barci.
"Kina ina?"
"Ina Yola mana" ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa.
"Mu kwana lafiya"

? ? Da zai kwanta yayi wanka da alola, sannan ya zauna sai da yayi azkar da ya saba tare da karatun Alqur'ani, sannan ta rufe ya kwanta,. Koda suka zo kan shi gaza cutar da shi suka yi tare da kallon shi da bakin ciki suka juya abin su,? haka yayi barcin shi a tsanake.

? ?? **
Bayan wayar shi na juya na cigaba da barci na,? sai dai ban yi nisa ba, naji kamar ana tashi na, ina bude ido naga wata mace sanye da jajajjyen kaya, d'ago ni tayi tare da kai ni gaban madubi, fuskarta a rufe da bakin gashin kanta, tana taje min gashin kai na.
"Mun hanaki kula kowa! Amma baki ji ba, mun tsorata ki baki ji ba" jan gashina tayi tare da nad'e min wuyana, ta matse sosai. Kakari nake tana faWin.
"Ki gaya mishi ya tafi ko nayi ta azabtar dake har karshen rayuwar ki, daga yau na fara saka ki kuka duk lokacin da kika kawo yarimarki ba zamu fasa koran shi ba" ta shake min wuyar. Yadda nake tari da kakari yasa su Mama da Fanan suna tawo dakin sai dai suna shigowa suka same ni ina ?o?arin kwace kaina daga kwanciyar da nake, hannuna a wuyata, ina ?o?arin cire gashin.

"Babu wanda ya isa ya cire ki a ukubar nan sai ni, dan haka zan kuma gargadinki da babban murya kika kuma barin wani ya zo da niman auren ki sai na kashe shi"

? ? ? Tamke wuyar matar tayi sosai, har na daina kokarin kwace kaina, a hankali jikina ta fara sakewa, da sauri Mama ta d'ago ni, hawayen jini ne ya zubo min. Har lokacin bata fasa shake ni ba, dai da wannan farin hasken ya kuma bayyana, gashin gaban goshina yayi fari tass har da haske,. Kawai ya wurgi matar sai da ta bugu da bango lokacin na suma.?
"Shahid" Mama ta kwala mishi kira, daga shi har Baffa Chindo suka tawo,? dole aka nufi asibiti dani, hankalin su yayi mugun tashi domin koda ka kawo ni bana ko motsi balle numfashi.

? ? Har gari ya waye babu wani kyakyawan sakamakon da zai tabbatar musu na farfaWo, haka Baffa Chindo ya kira Daddy ya gaya mishi, babu shiri ya zo dan sai yamma ya shigo, koda ya ga halin da nake ciki, kasa hakuri yayi yace.
"Ina ganin mu mai da ita gida ayi na gargajiya ko za a dace"
"Amma mu bari nan da kwana biyu mana"
"Inji Mama" haka ya hakura babu yadda ya iya, amma ya gayawa Innar mu, aikuwa bata tashi zuwa ba sai da magani, lokacin da tazo ana na asibiti, ana na gidan,? babu wani Cigaban haka nayi sati Daya aka mai dani gida, can mubi.

?? Muna komawa gida, aka fasa auren domin dai bani da lafiya, nan ma aka shiga kananun magana,. Ban san iya adadin wahalar da Innah tasha ba,. Mutane dayawa zasu dauki abin kamar wasa amma wallahi matsalar da nake ciki gaske ce, haka tayi ta yawon gidan magani dani, na kare lalace.

? ? ? ? ?? Haka dai muka samu wani me magani da ya taimaka min da magani amma ya gaya min gaskiya.
"Kuyi hakuri! Matsalar ta akwai hannu a cikin shi bayan laluran ta akwai wasu masu hannun a cikin shi, zan bata magani ne domin hannun wadancan ya fita a jikinta, amma bani nake da maganin ta ba, tun kafin a haife ta, Allah ya samar mata da mai maganinta, har yanzun ba a dace bane amma tabbas zai shigo kuma ba tare da ta nime haka ba, waraka na Allah ce"

? ? Haka ya gaya mana, har zamu tafi ya ce min.
"Kiyi hakuri! Kuma ku zuba runshin wuta a cikin jikon Insha Allah zaki koma bakin aikin ki"

?? Ya fada min haka, godiya muka mishi tare da barin kauyen, na sha bakar wahala rayuwata, domin kuwa, karfi da yaji aka shiga jifana da kalmar Yar iska,. Tun ina daurewa har na gaza hakuri, na zama kamar mahaukaciya a cikin dangin mu, yawan mutane basu yarda da abin da zan fara ba, asalima kallon makaryacinya suke min.

? ?? Bayan na gama jinya na koma bakin aikina, kuma dake sun fahimci wacece ni basu tab'a fushi da halin da nake ciki ba, haka na cigaba da rayuwa har tsawon shekaru biyar.

A lokacin na cire rai da maganar aure,? sai ga Mehd Moin Indimi, muka kuma dinkewa,. Domin lokacin na koma makaranta, yin masters, anan dai muka kuma dinkewa kamar bamu ba, har yake gaya min yayi aure matar shi da yara biyu,. Ban wani damu ba domin dawowar shi da karfin shi ya dawo. Kwana biyu muna cikin haka ban san me ya faru ba, sai shafawa nayi na ji labarin baya kasar, wannan abin yayi min ciwo.? Gashi lokacin an kusan bikin Hamdiya da Shkuriyah,. Haka nayi ta kuka ina gayawa Innar mu, murmushi tayi sannan tace min.
"Karki damu Insha Allah Ubangiji yana sane dake, baya barci baya gyangyandi, idan ya tashi koma waye sai Allah ya tabbatar da ikon shi. Wallhi lokaci ne da saura."

? ? ? ? Haka tayi ta kwantar min da hankali, koda bikin su Hamdiya ta taso dakyar nazo, haka suka yi ta min gori, idan na zauna a daki bana fitowa sai naga kamar nice abun kallon su.

? ? ?? Sau dayawa mutane idan suka ganni sai suta tambayana.
"Yaushe zaki yi aure? Har yanzun baki yi aure ba? Zaman me kike haka batu yi aure ba?" Wadannan tambayoyin yasa ko cikin gidan bana shiga, bana magana da kowa abin da ya kawo ni nake yi, ban cika son magana ba.

Idan naga zaka dame ni da magana ma kyale ka nake, nayi ta zaman kad'aici. Haka suka gama bikin Wallahi ban san me aka yi ba, ranar da aka kai Amare nasan da ni aka ji gidan Hamdiya aka fita, muka kai Shkuriyah, kuma na dawo na samu Innah tana dakin Daddy, na shiga ban daki ina wanka, naji ana buga min kofar ban daki, da sauri na fito.

? ? Tare da kallon Innah, kafin nayi wata magana ta kifa min mari,
"Innah!" Sake marina tayi, tare da rufe ni da duka, sosai fa duka na take tana kuka, narasa me nayi. Sai da Daddy ya kwace ni. Sannan Tace min.
"Tir da halinki, ba zan miki baki ba, Amma wallahi kin." Shiru tayi domin tana tsoron kalmar da zata fada min kar ya tarwatsa min rayuwa yasa tayi shiru tana share kwallar da yake zuba mata.

? ? ? Fita tayi daga d'akin, ta shiga d'akinta ina takure jikin gadona na lullube jikina da zanin gadon, domin dukar da ta min dai da towel din ya sunce, wani irin tsoro ne ya kama ni, ina kuka tare da jin kamar bani duniyar shigowa Shamsudeen yayi ya zauna tare da kallona.
"Addah Rooman! Me yasa kika zab'i haka a matsayin adalci? Zina da babu kyau"

Ware idanu nayi akan shi tare da fashewa da kuka, na durkusa kamar bani ce gaba da shi ba, na shiga rantse mishi ina gaya mishi ban tab'a aikata zina ba.
"Wallahi na rantse maka da Allah, ban tab'a zina ba, na rantse da Allah, wallahi babu wanda ya tab'a rike hannuna."

Shi kan shi ya rud'e, kuma yana tayani kuka.
Abun da ya faru kuwa, Alhaji Babba shi da Madakin Muri sun fito wani gaisuwa da suka gangara kasan su, kadan na rasuwa da aka yi basu samu zuwa ba, shine suka yanke shawarar zuwa a daren, aikuwa suna Dawowa, suka tsaya a kofar gidan Alhaji Muhammad Madakin Muri, suke tattaunawa, bayan sun gama. Suka nufi gidajen su, a hankali ya sako kai tare da sallama a zauren. Hango Rooman yayi da wani mutum suna masha'a, da sauri ya dawo da baya, haka mutumin ya fito yayi tafiyar shi, ita kuma ta juya tare da shigewa cikin gidan.

? ? Yana shiga ya samu Yawuro yace ta kira mishi yakub, aikuwa ko minti goma basu yi ba, sai gasu tare nan ya gaya mishi. Amma ya nime ya bar maganar a rufa asiri ba sai duniya taji ba, lokacin da ya dawo yake gayawa Innah shamsudeen yana wurin, bakin cikin haka yasa Innah rufe ta da duka.

?? Shine abin da ya faru, kuma wallahi bani bace amma babu wanda zai yarda bani bace,? haka washi gari da sassafe na bar Mubi. Ina kuka har isa Yola.

? ?? Tun bayan Khamil babu namijin da ya kuma zuwa niman aurena kai ko a cikin Familyn mu, kowa cewa yake nafi karfin shi. Naso ba fara bin malamai ko zasu taimaka min, na gayawa Mama fada ta min tare da cewa, ban godewa Allah ba kenan dan ya jarabce ni, haka yasa ni hakura na zuba ido akan kome.

?? Ban kuma waiwayar al'amarin rayuwata ba, sai da na samu good ten year rabona da kwanciyar hankali, bayan b'atar Babangida, da samun matsalolina.

? ? A cikin wannan?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? shekarun na girma,kannen na sun haihu da yaran su, kuma har yau ba a fasa gaya min magana ba, idan aka ga na zo Mubi sai an tambaye ni,.dama baki yi aure ba? Lallai duniya ta miki dad'i. k'iyayyar da Yadiko Salamatu take min yasa aka fara zargin ko tana da hannu a cikin abin da yake faruwa dani.

Shima zargi ne bai zama dole. ya kasance gaskiya ba, abin tausayi. Kowa ya juya min baya, kamar basu damu da halin da nake ciki ba, tun da uwar da ta haife ni da juya min baya na Fahimci yanayin da nake ciki ya ta'azzara.

Mama da Shamsudeen, kai Yaron nan Allah yayi mishi albarka, domin kuwa babu inda baya zuwa domin nimo min magani, shi akan shi ya fahimci cewa lalura ce dani, amma sauran jama'a basu yarda ba, wani kauye aka mishi kwatancen har Kamaru, yaron nan yaje.

Ya amso min maganin turare da hayaki, ya kawo min na fara, kwatsam sai ga

10 / 69