JINI YAFI RUWA COMPLET BOOK BY D AUTA.doc

Author :  Hadiza D. Auta Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   22 / 69

63K to 66K   out of 206.5K words

yasa zai cigaba da ajiye wancan tsintaccen magen? Tunda babu gadon Ubanshi ya tafiya ya bar mana estate din mu?" Ta fada cike da kwarin gwiwa,

?? "Shi kenan?" Ya kuma tambayarta.
"Sai kuma ya gaya maka ina yaje har kwana biyu?" Kura mata ido yayi yana mamakin ta.
"Sai me?"
"Sai... Sai.... Sai.." shiru tayi kafin tace mishi.
"Babu sai yayi ta kula dani"
"Suke nan?"
"Eh suke nan"
Kallon sy Khadi Adamu Moddibo yayi sannan yace mishi.
"Kaji abin da take zarginka da shi?"
"Eh ya me shara'a" Dr Hayat ya amsa mishi.
"Shin akwai abin da take maka ne?" Ya tambayi Dr Hayat,
"A'a bata min kome!"
"Ka tabbatar?"
"Eh!"
"Meye yasa har yanzun baka sallame Hashim ba?" Kamar wanda aka mintsina ya gyara zaman shi sannan ya fara magana cikin tattausar lafazi.
"Dattijo,kai ma kasan bani da burin rike wannan abin tunda ba gadon shi nayi ba, sannan idan ka duba lokacin shi nake jira, domin an bani ne a bisa taimakawa wata baiwar Allah, ita kuma zata taimakawa wata.

? ? ? ? ? ? ?? Shi kuma Hashim ban san yadda zan gaya maka ba, amma matsalar shi ya manta kome ne, idan har zai dawo da tunanin shi Insha zan sallame shi, Dattijo matar da nake aure ta dauki hannun ta, ta mari wani namijin ina laifin ni ta mara ni?"

? Yayi maganar tare da tambaya, yana kallon kasa, shiru falon ya dauka.
"Anyi haka?"
"Eh anyi"
"Toh me yasa?" Khadi Adamu Moddibo ya tambaye ta,
"Fantsamamin kwata yayi jikin motata."

"Amma ai ya girme ki? Ko sa'an ki ne?"
B'ata rai tayi tare da dauke kai taki ma sauraron su, dan haka ganin zai daura mata rashin gaskiya, ta mike tare da fess rashin kunyarta son ranta, sannan ta fita daga cikin gidan. Shiru suka yi daga Khadi har Dr Hayat.

? "Yanzun meye labari?" Khadi ya tambaye shi.
"Eh Toh ina ganin na kusan rabuwa da wannan abin ne, domin na hadu da wata yarinya kuma ban sani ba, ko ita ce ba"

?? Gyara zama yayi sannan ya kuma kallon shi.
"Toh ka taimaka mata?"
"Ban iya mata kome ba, domin hatsari ne ya faru haduwar mu da ita, sau biyu."

? ? Shiru suka yi sannan khadi ya ce mishi.
"Toh matukar kuka kuma haduwa, Toh ka taimaka mata. Kana da rayuwa me kyau, harkan Aljanu ba karamin kasada bane domin suna tab'a zuri'a."

? ? "Insha Allah zan duba."
Ya faWa yana me jingina kan shi a jikin kujerar falon.
"Har Yanzun baka samu matar da kake so bane?"
Lumshe idanun shi yayi yana jin wani abu yana taso mishi kamar ana fama mishi ciwon da yake ran shi ne, dan haka ya kalli kakan sun, sannan ya ce mishi.

"A'a" ya fada tare da ware idanun shi,lumshe idanun shi yayi yana kuma hango yadda ta rintsa idanun ta, tare da k'amk'ame hannun ta, tana jiran saukar marin shi.
Tab'e baki yayi yana kara nazarin girman laluran ta, sun jima suna hira har kusan karfe goma, sannan yayi mishi sallama tare da leka dakin Nenneh tana barci barci kafarta na mata ciwo.

**
Wani irin zama ake tsakanin Darrah da Dr Hayat, ta saka kanta a gaba, shima tun da ya dawo bai da lokacin kan shi sai ba inda zai samu mafita akan laluran Shi. Dan haka ya haWa dole da asibitin kwakwalwar wanda yake kasar Amurka a can,

Kafin su tafin ya dauki hutu tare da Waukar Darrah suka nufi Abuja, inda ya barta a gidan Uwarta.

Kamar wanda ya Kaita da ciwo, domin suna isa ya shiga ya gaida Hajiya Rushediyya, suka taba hira. Sannan ya gaya mata.
"Zan yi tafiya idan ta huta zata iya zuwa gidan Ummi ta zauna idan tana so, idan kuma bai mata ba ta zauna a nan."

"Insha Allah, zata je ta kwana biyu Insha Allah."
"Nagode"
Mikewa yayi zai fita ta biyo shi zuwa waje, a dan barandar wajen ya tsaya yana fuskarta waje. Tana fitowa ta rungume shi ta baya, tana me daura hancinta a saman bayan shi, tana goga mishi a bayan shi. A hankali ya juya tare da riko hannun ta, yana kallon fuskar ta.

Ya riko hannunta yana murza yatsun ta, tare da kallon su.
"Yatsun nan sun min kama da nayi ajiyar fa" gabanta ne ya fadi tare da kallon shi tana kakaro murmushin dole tana faWin.
"Kuma haka ne idan shi ne zan yi farin ciki"

"Well zan tafi ki kula da kanki like nayi dashe!" Ya fada yana sumbatar goshinta, taji dadi amma kuma bata yi maraba da cikin ba, domin tasan ba nasu ba ne, a kuntacce suka yi sallama ya tafi.

Duk yadda yaso ya kauda zancen cikin kar ya hana shi wasu abubuwan abin ya ci tura domin baya iya awa daya bai kira ta ba, sun ta waya kenan, yana tambayar ta labarin cikin, ita kuma Wan ta ga haka sai ta fara amfani da haka tana d'aga mishi hankali, tun yana daurewa har ya fara tura Aalim da yake Abuja yaje ya duba ta, babu laifi bata da lafiya. Amma bai kau yadda take gaya mishi zata mutu zata rasa ranta. Duk ta dagula mishi lissafi, har ya kwashi sati biyar a can sannan suka dawo domin yayi abin da yake gaban shi, sun mishi al?awarin aikin Insha Allah zai dawo dai-dai.

Haka suka dawo, ya dauke ta suka koma Gombe, tunda suka dawo baiwar Allah nan ta kuma saka shi a gaba da fitina da jaraba. Ga ayyukan da suka saka shi a gaba, da ya dawo ya samu sakon mutanen Mubi, kamar yayi tsuntsu ya isa musu, amma babu hali, dama Darrah ce take rage mishi aikin office din shi. Toh laulayi.

Wani abin da ya mugun tasiri akan shi da ita shine yana masifar son Yara, domin har imagine yadda zai dauki Yaron shi na kanshi yake ji, gashi baya iya mata fada ko wani abu domin lallabata yake da kuma cikin jikin ta, amma bata gani ba.

*
Yola.

Haka kawai na fara wani irin ciwo, domin zan kwana lafiya sai dai ban isa na wuni ba, domin kuwa wasu irin kuraje ne suka feso min ban isa na shiga rana ba, wallahi sai na fara kokarin cire kayan jikina, haka nayi ta zaryan asibiti ban samu sauki ba, sai da na had'a dana ISLAMIC shine na samu sauki sosai, har na fara amsar wasu ina sha.

Ana cikin wannan yanayin kanwar Mama na da take aure Jade tazo min da cewa nazo na bita mu tafi jade akwai me magani, kamar ba zan bita ba. Haka ta kira Innah tace mata ta min magana naki amsawa.

"Rooman ki shirya ku tafi Allah ya baki lafiya matsalar rashin auren nan yana damuna." Cikin damuwa na ce mata.
"Innah haihuwa da mutuwa na Allah ne, bamu rike da kaddaran a hannun mu da ina da rike da ?addara ta, da tuni na san abin yi ni ba zan je ko ina ba gaskiya"

"Ki shirya ku tafi, bana son musu ai lafiyarki ake nima idan kuma zaman haka shine mafita zauna a wurin" babu yadda na iya domin naga ranta ya b'aci sosai, dan haka na tashi nace mata.
"Dole sai na dauki hutu a wurin aikina, domin zasu iya dakatar dani."

"Toh duk abin da yayi miki kiyi, ba zan kuma hana ki ko na saki ba, tunda lafiyar ki ma ba zaki iya tashi noman shi ba. Rumana ba zan boye Miki ba kina wasa ibadar ki domin nayi imani da Allah haka kawai ba zaki tsaya iya wannan lokacin ba, ina kika kai ilimin ki? Toh wallahi ki tashi daga barcin da kike" ta kashe wayar, naji babu dadi kawai Uwata ne babu yadda na iya da ita haka na ajiye mata wayar, na fita na bar Innah Aliyah, ina jin tana mita tare da kananun magana wai na mai da ita sakarya tana min magana akan lafiyata ina nuna mata ban damu ba.

Idanuna ne ya cika da kwalla kamar na rufe ta da duka, haka sai muka kwana washi gari na shirya cikin riga da zani atamfar bakar mace, asalin yar saudiya, na tafi aiki anan na samu hutun har Sabi'u yana ce min.
"Allah ya daura Miki laulayi, ki dage da maganin Hausa ko zaa dace!"

"Eh wallahi haka kowa yaje fada bana wata uku ban yi rashin lafiya ba, Insha Allah zan cigaba da niman na hausar" na fada ina tattara kayana,
"Ok kina da sikila ne?"
"A'a tun haihuwa ne nake haka, amma da sauki ai yanzun kawai zan cigaba da dai magani ne kawai."

Toh Allah yasa a dace!"
"Amin Ya Allah"
Haka na baro office din, na dawo gida ko hutawa ban yi ba wai take ce min.
"Sai mu wuce tasha!"
Kallon agogo nayi sannan nace mata.
"Bafa inda zani da wannan uwar ranar gobe mutafi kafin rana ya buWe?....
300? ... Insha Allah'
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A'ichah
+22784506476
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank
#Mai_Dambu
NEXQUISITE WRITERS FORUM.
JINI..!
? ?Ya fi Ruwa Kauri?
? *Base on true life story*

*Sadaukarwa ga Family Hasssan Yero Family da Madakin Muri Family*

? ? ?? Mai_Dambu

BABI NA TALATIN.

Cikin hasala da halina ta kura min ido, kafin tayi kwafa ta ce min.
"Allah ya kai mu tunda haka kika zab'a" shiru nayi ban tanka mata ba, kuma ban ce mata kome ba, haka yayi mugun hasalata har take gaya min ce wa.
"Da Uwar ki ce ba zaki barta ta zauna tana magana ita daya ba, amma dake idanunki ya bude da yawon bin maza kin min shiru kina jina, ban da uwarki ce ta nemi na kai ki ina zan fara zuwa daukar ki na kai ki niman wani abu da sunan magani, wawuya balagaza kawai"
??
Da wannan kalmar da ta gaya min da dukana tayi zai fin min sauki sama da sunan da ta kirani da sunayen da ta kirani, kallonta nayi kafin na dauke kaina ina share kwalla.?

? ?? Fita nayi daga dakin na fita can waje na je na zauna a lambu, na fara kuka, da gaske ina da rauni akan ibada ta? Shin me yasa haka yake faruwa dani. Haka nayi kuka har na godewa Allah, naki kuma shiga cikin gidan, ina zaune a wurin na jima a wurin har zuwa lokacin sallah yayi, a hankali na mike zan bar wurin na ji wurin yayi masifar sanyi, a hankali na koma na zauna ina lumshe idanun, kafin ba ji wani irin barci a wurin. Na kwanta.

? ? ?? Bina ake da gudu, dakyar nake gudu domin kafaffuna duk sun dauje, dakyar na samu wani mafaka na boya, ina zubda kwalla.

? ?? "Ina take?"
"Ta gudu"
"Ku dauko min ita, ai tunda aka kawo min ita sai na cimma.."

? ?? Cikin azababben tsoro na rufe bakina tare da makalewa jinin dutsen, a guje suka nausa dajin ni kuma na tashi a hankali, na shiga niman hanyar da zata kai ni inda na fito, a hankali? nake tafiya ban san ina nake ba, amma idan nayi tafiya kad'an zan ji kamar ana bin bayana, har dai ba juya a firgice. Babu kome a wurin dan haka na shiga tafiya kamar wacce ake hankad'ani na isa wani gogo a cikin dutsen.

?? Babu kome a cikin shi sai zunzurutun kashin dabobbi, a hankali na kuma jin muryan mutanen suna fadin.
"Ku dubata ko ina"

?? Sake makalewa nayi a cikin kogon, tare da dauke numfashina, hka suka gama binciken su basu same ni ba, suka kuma kad'an kansu tai gaba.
?
? A hankali na sauke wani gauron ajiyar zuciya, ina kallon cikin kogon da nake jin motsi, a hankali idanuna ya sauka akan wani kore abu da yake tunkaro ni, tunda nake a lokacin na fara ganin idanun irin haka, sake bani nayi ina ja da baya, har abin ya fito fili, wani uban tsalle y buga sai gashi a gaba, wani irin ihu na saka wanda yayi matukar tasiri har a zahiri na, da gudu na farka dan ma Hisham yana kusa da ni ya shigo wurin yaji ina danna ihu, taimaka min yayi tare da kallona.
"Kinyi mugun mafarki,. a madadin kiyi addu'o'in, Addah Rooman zai kika buge da? ihu bayan akwai addu'o'in da Manzon Allah ya koyar mana, gaskiya kin bani kunya. Ina ilimin ki yake? Kin zauna kina ta ihu kamar wata karamar yarinya, sannan dubi inda kike fisabilillahi? Gaskiya ki sake lalle domin abin da kike ba wani abin arziki ba ne, addu'o'in ake idan aka yi mugun mafarki a yadda kuke zaune nan ina da yakinin ko sallah azhar baki yi ba, kin zo kina ihu a nan Please ki kula da kanki mana"

Wani irin azazzabben kunya ce ta kamani, tare da sunkuyar da kai na, na mike a hankali tare da cewa.
"Nagode Hisham"
"Babu kome" Haka na mike tare da nufar cikin gidan, na shige dakina nayi alola, koda na fito wallahi sai na manta me zanyi domin tun a wurin Alolan nake wasu wasi, dan haka na shiga niman me zanyi can kuma ba tuna sallah zan yi dan haka ba tashi na fara gabatar da sallah, ina idarwa na mike tare da fitowa falo na samu suna hira kitchen na shiga na debi abinci.

"Don Allah ban da lalacewar duniya taya mace kamar wannan ace babu mijin aure amma kiga ko a jikinta." Ta fada tare da bin bayana da ido,
"Allah ne bai kawo ba, idan ya kawo sai ayi bikin babu wani matsala."
"Hmm! Kun dai ?asa ganewa ne amma taya ?atuwar mace kamar wannan tana yawo a cikin gari a ce babu wani abin da zai dame ta? Indai ba bin wasu mazan take ba?"
"Amma Jamie kin bani mamaki yar Yar uwarki ce fa? Kike jifata da miyagun kalamai, dan kawai bata amince akan Kaita wurin magani ba, kuma kika gayawa Uwarta haka bai Miki ba kina niman mata kazafi! Idan na gayawa Alhaji Babba zai san yadda zai yi saku, amma ki ji kunya" ta fada mata lokacin ina fitowa, ban zauna a wurin ba domin duk wani karin ciwon kai ne na shige dakina na ci abinci.

? Har yamma naki fitowa, ina zaune ta shigo dakin kallona ta nayi sannan na cigaba da aikina a kan laptop dina, ina yi ina satar kallonta, musamman yadda take wani cika da batsewa, wai sake wani fitinannin tsaki take, taSa kananun mita, tare da gasa min bakar magana, ko na d'aga kai na kalle ta domin bani da lokacin ta,

? ? "Idan muka je can ki nuna musu bani da kima da daraja a idanunki tunda baki ga Alkhairin da nake bibiyar ki dashi ba, mara fasali kawai."

? ? ?? Murmushi nayi tare da juya mata baya, ina wasa da biro na, har tayi barci ban sani ba, domin ina nawa uzurin. Kusan raba dare nayi ina jin zafin abin da ta min,sam zuciya ta, taki aminta da tafiyar kawai dan Innah ta saka baki ne, amma baki daya bana jin ina da ra'ayi akan tafiyar.

? ? ?? Washi gari.
Bayan nayi sallah Asuba ba shiga wanka akan lokaci. Na fito tare sa shiryawa na nufi kitchen na dafa abin ?aryawa ruwan zafin tea sai, dumamen tuwon da nayi mana. Na zuba na Innah Jamie na kai mata sannan na fito falon naci nawa, ina koshi na nufi dakin Mama na mata sallama, sannan na shiga na Aunty Binta na mata Baffa kan bai tashi ba, dan haka muka musu sallama muka fita, duk wani abin da za a kashe duk daga jikina ne da aljuhuna, haka muka bar garin Yola cikin rashin fahimtar juna.

? ?? Karfe hudu na yamma muka isa garin da take aure, daga isar mu bata barmu mun yi sallah ba wai nazo mu tafi.
"Kiyi hakuri sai nayi sallah" ganin haka ta zuba min ido nayi sallah. Ina idarwa bata yi tunanin abin da zamu ci ba, ta saka ni a gaba muka bar garin muka nufi wani kasungurmin kauye da mashin ake shigar shi, tun da naga yadda garin yake zuciya ta, yayi ta bugawa har muka isa wani gida can wajen garin domin yayi mugun fita daga cikin na mutane, ya ware kan shi can can. Muna zuwa na samu layin mutane,? muka zauna can ta mike tare da shiga.

? Aikuwa tana shiga aka ce na shiga cikin dakin, ina shiga na same su zaune suna magana, tana gani na suka yi shiru, can me ma ganin ya gama abin da zai yi sannan ya ce mata.
"Zaki iya tafiya domin aikin ta xan shiga yi daga Yanzun har zuwa gobe, ita kuma ta shiga wancan dakin da yake kallon mu."

?? Ya fada yana nuna min dakin da yake kallon mu, babu musu na shiga dakin na zauna, shi kuma ya sallami Innah, bayan tafiyar ta, ya cigaba da amsar mutane, har aka yi magabri, na mike tare da fitowa lokacin yana nan a wurin tare da mutane. Buga min tsawa yayi.
"Waye ya ce ki fito?"
"Sallah xan yi" na bashi amsa a sanyayye,
Bata gaya Miki ba a sallah a nan bane?" Ya tambaye ni,
"Aifa bata gaya min ba, amma kam xan yi sallah."
"Koma cikin sai na gama Miki aikin ki"
"Nan ne kuma ba zai yiwu ba" na fada ina barin dakin maganin, na fito babu kowa a gidan sai shi sai wasu masu jiran a gama da na ciki su shiga, dakyar na samu ruwa nayi alola, dakyar na samu alkbla na gabatar da sallah, sai na zama abin kallo a wurin ina idar da sallah magabri, nasan idan na shiga ba zai bar ni ba fito ba, na gabatar da sallah Isha.

? ?? Ina idarwa na daura da Shafa'i da witiri, ban san me ya bude min kaina ba, kawai sai gani ina addu'o'in niman tsari daga miyagun mutane da aljanu, ina gamawa na mike na kad'e dan kwallina, sannan na shiga. Dakin maganin, na tura kaina xan shiga cikin dakin da na zauna na ga me magani kan matar da yake gani, ikon Allah, basu san ma na shigo domin hake

22 / 69