JINI YAFI RUWA COMPLET BOOK BY D AUTA.doc

Author :  Hadiza D. Auta Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   2 / 69

3K to 6K   out of 206.5K words

nazarin maganar dan shi akan Umm-e-Rooman, akwai kamshin gaskiya a cikin wannan al'amarin, amma kuma taya zai gamsu da maganar shi bayan shi da kan shi har cikin gidan nan aka kawo mishi hoton videon, Umm-e-Rooman. Taya zai yarda da su baki daya sai dai idan Chindo yayi haka ne don ya rufawa yar dan Uwan shi asiri amma baki daya baya tunanin akwai wani hanyar da zasu kare kare kansu.

? ? Kallon matar shi yayi sannan yace mata.
"Ina cikin damuwa, maganar Umm-e-Rooman akwai wani abu da yake boye bayanta?" Yakura ta kalle shi kafin tace mishi.
"Toh me zance Alhaji duk abin da ka yanke ai daga ita har mu duk naka ne"

? ? ? ? Sauke ajiyar zuciya yayi yana kallon kasa.
Kafin yace.
"Allah ya kyauta"
**
Gab magarib muka shiga yola, kallona Baffa yayi sannan ya dauke kanshi ganin yadda nake rawan sanyi.
"Baki da lafiya ko?"
"Eh"
"Allah ya baki lafiya"
"Amin Ya Allah"
"Ka wuce damu Asibiti"? ya fadawa driven shi.
"An gama Yallabai"

Haka muka nufi asibitin, muna zuwa suka min allura domin asalin ciwon dukar da aka min ne, dan haka ba wani dogon jawabi bane, magani suka bani da allura muka nufi gida.

? ? ?? A hanya Baffa ya kalle ni cikin kulawa sannan yace min.
"Rooman!" D'ago kai nayi tare da amsawa.
"Tsakaninki da Allah, meke faruwa?" Sunkuyar da kai nayi sannan nace mishi.
"Wallahi tallahi ban san meke faruwa ba, wallahi ban tab'a zuwa club ba, ban san hanyar shi ba"
"Allah ya kyauta"
"Amin" na fada cikin shashekar kuka, domin shi daya ya rage min nayi bayan wanda nake yi kullum.
? ? Muna shiga cikin gidan, muka yi tozali da katon hoton Babangida, sanye da Kayan Lauyoyi yana murmushi, hawaye ne ya zubo min. Ban san lokacin da na isa gaban hoton ba, na tsaya ina shashekar kuka.
"Me ya sa? Me ya sa? Me ya sa baka gaya min zaka tafi ba? Me ya sa ka tafi ka barni? Me ya sa baka tsaya na zama mallakar ba ba? Ka gaya min meye nayi maka ne da ka guje ni? A ina kake?" Na shiga dukar hoton ina kuka da ihu.
"Toh me ya sa nima ban mutu ba? Meye amfanin bakin cikin da nake kunsa? Me ya sa baka tafi da Ni ba?"

? ?? Cikin wani irin rugugi hoton ya motsa, kallon shi nayi yana murmushi, tare da mika min hannun. Kai hannu nayi zan mika mishi naji an dafa kafadana.
Da sauri na juya tare da fashewa da kuka, Mama. Rungume ni tayi tana shafa bayana.
"Ashe abin da ya faru kenan? Ubangiji ya sauya miki da wanda ya fishi, kiyi hakuri kowani rayuwa akwai jarabtar naki jarabtar kenan"

? ?? Gyada mata kai nayi ta riko hannuna, muka wuce daki. Mama itace uwar gidan Baffa Chindo, kuma mahaifiyar Babangida, a hankali na juya baya ina kallon hoton. Har lokacin mika min hannu ya?e. Rintsa idanuna nayi na kuma juyawa, na ga hoton ya koma dai-dai. Hawaye ne ya zubo min.
Inda dakina yake ta kai ni.
"Kin bar su a can ko? Nasan zuwa an jima zasu shigo ko gobe da safe"

? ? ? ? Zama nayi a bakin gadon mu, na kalle ta sannan na ce mata.
"Amma me yasa sai ni?" Murmushi tayi sannan tace min,
"Haka Allah ya shirya miki baki da zab'i sai na amsar abin da ya ba?i"

?? "Mama ranar da Hamma Babangida" yadda ta kafe ni da idanu ya sani yin shiru ina kallonta. Murmushi tayi sannan tace min.
"Kiyi hakuri mana"
Kuka na fashe da shi ina jin babu dadi a raina. A hankali na mike tare da shiga ban daki nayi alola, sanan na fito na fara gabatar da sallah da yake kaina. Lokacin ta fita, sai karfe goma naji yan matan gidan mu sun shigo tare da? Amaryan Baffa Chindo.

? ? ? Ban iya fitowa ba, sabida suma har yau kallo daya suke min, ina kwance Fanan ta shigo d'akin.
"Addah Rooman!"
"Na'am"
"Ya jikin ki?" Ta tambaye ni,
"Da sauki Fanan"
"Allah ya baki lafiya, ga wayar ki inji Khamil kin barshi tun a wurin Kamu" a hankali na mika hannu na amshi wayar. Kallona tayi sannan tace min..
"Wallahi na yarda da ke, ban tab'a miki kallon mara kamun kai ba." Hawaye ne ya zubo min. A hankali na share su. Sannan nace mata.
"Nagode"
A hankali abin da ya faru a cikin awa ashirin da hudu. A? babban zauren da aka tanadar? domin yin walima taro ko wani abu dai, duk a cikin gidan mu yake, muna hankalin mu yayi nisa, ina sanye da Kayan saki na fulani, kaina a sunkuye. Sako ya shigo min.
*Allah ya tabbatar da alkhairi*
Duba Number nayi, Khamil ya amshi wayar, yana murmushi.
"Hamma Khamil bani wayata"
"Daga jibi wayar da me wayar zasu dawo duk nawa"
"Hmm!" Nace mishi,.kasa kasa yace min.
"Ki shirya domin babu d'aga kafa, babu sassauci. Tuzurancina zan juye miki su kafa!"?
"Subhanallahi! Don Allah ka bar wannan maganar kar kunnen na yayi bindiga" daga daka cikin abokan shi ne ya matso wurin, ya Wan mishi magana a kasa kasa.
"Ina zuwa yan mata" ya fita daga dakin taron. Yana zuwa waje, wani dattijo ne ya mika musu takardan.
"Baba Lado ina wanda ya baka sakon?"
"Yallabai Khamil wallahi ya tafi" a hankali ya juya tare da nufar hanyar cikin gidan, ya fara bude sakon wata yar takarda ya gani.
*Ango da alamar dai kana daukin daren farkon ka ko? Toh gashi nan ayi shagalin biki lafiya!*
Kallon wasu hotuna yayi tare da ciro su, Rooman ce tsirara haihuwar uwarta da Ubanta, jikin shi yana rawa kamar zai fadi ya jingina da bango. A hankali yake kallon hotunar, bai san lokacin da ya daina gani ba, sai zuSewa yayi a wurin sumamme. Masu wucewa ne suka gan shi ga hotunar a kasa yashe. Shine aka fasa ihu tare da kwasar shi zuwa asibitin. Hotunan kuma kamar kyaftu da bismillah ya yadu sosai a cikin gidan. A can asibitin kuwa tsoro da tashin hankali ya sanya shi suma. Haka likitocin suka fada.

? Bayan awa biyu ya farka, sallamar shi suka yi tare da bashi shawara akan ya kula da lafiyar shi. A wurin Kamun kam ya watse domin kafin kace kwabo danginmu sun shigo dakin taron sun min cin mutuncin kamar ba jinin su bace ni.
? ? Sannan suka mika hotunar mutane suna gani, da gudu na fita a cikin dakin taron. Na nufi gidan mu, ina shiga Yadiko Salamatu ya kalle ni tana dariya,

? ? ? A can Falon Alhaji Babba kan muhawara ake, sai da aka yi musu sallama, Baba Lado ya mikawa Baffa Nura wani faffen video, suka karb'a.
"Inji waye?"
"Nima yanzun aka buga kofar gidan, na bude shine wani yaro yace wai na baku"

? ? ? A hankali suka amsa, tare da had'a kayan kallon falon Alhaji Babba, suka saka cd din, yana fara play sai ga Umm-e-Rooman tana rawa cikin yan iska, wannan ya dauke ta.
"Nura kashe haka!" Allah Sarki Mahaifinta kan shi ?asa, ya kasa d'ago kai ya kalli badakalar da yar shi take yi. Tashi Alhaji Babba yayi tare da cewa.
"Ku tawo min da Rooman gobe da karfe biyu," ya sallame su.

? ?? Washi gari.
Khamil ya fita hayacin shi, domin yana mugun son ta, haka wajen karfe biyu na rana sun haWu, har da shi Win. Rarrafawa yayi gabanta yana faWin.
"Meye nai miki? Kin san yadda nake son ki kuwa?? Wallahi ina sonki haka bai sauya min sonki ba, wallahi na shirya aurenki"

?? "Ba zaka aure ta ba, ba zaka zauna da yarinyar da ta zab'i karuwanci ba, zuri'ar mu ta lalata mana, wallahi ko bayan raina ka auri Rooman Allah ya isa Ban yafe maka ba"

Inji Mahaifiyar shi, wacce ta kasance? Kanwar Baffana ce ita,babu wanda ya hanata magana sai Baban Khamil shi din Kawu nane, domin Dan Yayan Alhaji Babba ne.
"Ina ganin kuyi hakuri da wannan had'in tunda abin da ya faru kenan!" Inji Kakana wanda ya haifi Mahaifiyata. Alhaji Muhammad Madakin Muri ya faWa.
Alhaji Babba ya kasa cewa kome, sai dai kawai yana jin su,haka akayi ta fidda shaidun ina fito yawon dare, wallahi ban tab'a fita yawon dare ba, na rantse nayi kuka babu wanda ya yarda da ni, karshe watsa min hotunar suka yi, hannuna yana rawa na kalle tare da fashewa da kuka. Ina rantse musu.

?? Amma basu yarda ba, har Daddy ya rufe ni da duka, ina kallon Innah ta bar falon.

? ... Hawayen da ya jika min fuskana na goge, na tsani kowa haushin kowa nake ji, domin ina da yakinin bani da albarka ce yasa kome yake faruwa dani.
Haka na kwana ina kuka karshe da naga kukan bai da amfani na tashi tare da gabatar da sallah nafilla.? Na jima ina addu'o'in, sannan na kwanta.

? ? ? **
A hankali na bude idanuna, ina kallon dakin da nake, hayaniyar mutane nake ji, dan haka na fito tare da kallon waje.

? ?? Biki ake sosai tare da shagali, a hankali nake kallon mutanen wurin ban gane fuskar kowa ba.
"Rooman Barka da zuwa" na juya tare da kallon matar da tayi min magana.
"Yawwa ina ne nan?" Na tambaye ta.
"Hmm" ta min murmushi, kananun Yarana ne, suka zo da gudu tare da zage ni. Gasu nan tabarkallah, kallon su nayi na kasa magana domin bakina yayi min nauyi dan haka na kalle su da kyau. Ji nayi an riko hannuna, na d'ago kai, ban ga fuskar shi ba, amma kuma yadda ya rike hannuna har cikin tsakiyar kaina naji rokon shi. Dan haka ban san lokacin da na mike ba, sake ri?e hannuna aka yi na juya da sauri.
"Mehd!" Na ambaci sunan shi, murmushi yayi min.
"Karki bi shi zo mu tafi"
"Muje kina da rayuwar ki, babu gami da nasu."
Mutumin ya fisgo ni, yunkurowar da Mehd yayi, ai kuwa, mutumin ya daki kirjin Mehd, faduwa yayi tare da dungure.

? Bude idanun nayi tare da farkawa,tashi nayi zaune na kalli ko ina, sannan na tashi zaune. Lokacin ana kiran sallah farko, a hankali na sauka a gadon na nufi ban daki, alola nayi sannan na fito na gabatar da raka'atul fijr, ina idarwa na koma na zauna ina azkar. Wayata da take jikin Charger tayi haske, mik'ewa nayi tare da Waukar ta,.na duba.
"Mehd" na furta a hankali,.ina kallon wayar.
Duba sakon shi nayi naga abin da ya turo min.
*Ina sonki! Ina kewar ki! Allah ya mallaka min ke*
Takaici ya sani tura mishi da sakon cewa.
_karya kake domin da kana so na ba zaka ki gabatar da kanka ba, Mehd me yasa kike wasa da Rayuwata? Dan ka ga na damu da kai! Toh yanzun ma an fasa aure na idan har da gaske kake ka fito ina jiranka_

?? Na tura mishi daga haka na kashe wayar dan na san shi bai da hakuri Yanzun zai addabi rayuwata da sako, ko kuma zuwa an jima na gan shi domin ba kan gado ne dashi ba. Kuma bana tunanin akwai macen da yake tare da ita bayan ni. Shigar sallah yasa ni mik'ewa ma fara gabatar da sallah asuba, ina idarwa na zauna na cigaba da addu'a, har rana ta fara fitowa, kafin na koma na kwanta.

?? A hankali barci me nauyi ya dauke ni, mafarkin dai da na saba shekaru goma baya, wato wani farin doki yake bina tare da wasu karannuka manya da kananu, bina suke? nayi gudun nayi gudun har na gaji. Bakina sai ambaton Allah yake, saura kadan dokin nan ya cimma ni,.naji an riko hannuna. Tare da fisgo ni sama. Da sauri na ja wani numfashi domin ina jin rikon har yanzun kallon dakin nayi, kafin na kuma lumshe idanuna. Sai dai me gurnanin da nake ji a saman kaina ya sani, bude ido na. Ina me rasa abin da zan furta dangane da addu'a ko niman kariya. Wata bakar halitta kamar mace kamar ba mace ba, gashi ya rufe kanta, hawaye ne ya shiga zuba min ina kuka tare da damke zanin gadon sai gunjin kika nake.

?? Kamar wacce aka buge ta da wani abu ta b'ace, a hankali ya tako tare da hura min iska, tuni barci yayi gaba dani. Ban kuma farkawa ba dai karfe sha biyu na rana, a hankali ya bude idanun. Ina kallon dakin. Kafin na sauka a gadon ina son tuna abin da ya faru amma ina na manta kome kamar shafe min shi akayi a ?wa?walwata...
300? ... Insha Allah.
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A'ichah
+22784506476
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank
#Mai_Dambu
EXQUISITE WRITERS FORUM.
JINI..!
? ?Ya fi Ruwa Kauri?
? *Base on true life story*

*Sadaukarwa ga Family Hasssan Yero Family da Madakin Muri Family*

? ? ?? Mai_Dambu
BABI NA UKU.

Mika nayi ina me zaro manyan idanuna waje, tare da sake wata siririyar tsaki domin na gaji sosai. Kallon lallen hannuna nayi ina kara jin damuwa a raina, a hankali na nufi ban daki ina jin kamar nayi ta kurma ihu. Ban dakin da na shiga haka kawai na ji ba zan iya kome ba, domin wata irin kasala ce ta saukar min sakamakon rashin addu'ar shiga ban daki da ban yi ba, na kai awa daya a cikin ban dakin. Ina nazarin abin da ban san ni ba.

?? Kamar ba zan yi kome ba, a daddafe nayi wanka tare da gyara jikina, na dauro alola sakamakon jin ana kiraye kirayen sallah, a hankali na fito. Na shimfid'a abin sallah. Jakata na bude tare da ciro doguwar jallabiyar sallah ta, na saka da casbi na fara gabatar da sallah. Ina idarwa na zauna a gurin ina addu'o'in, barci me nauyi da kasala ya sani mik'ewa a saman abin sallah, ina ambaton Allah, daga nan barci ya dauke ni.

? ? ?? Gudu nake sosai a bakin dajin nan, dakyar na fita cikin surkukin dajin, kafin na isa bakin wani ruwa, ina son shiga ina jin takun shanun da suna biyo ni, juyawa nayi naga wata mata da nake yawan mafarki da ita fuskarta a rufe yake da mayafi. Ta kawo min hannu zata cafko ni, na ji an cire ni sama, a firgice na bude idanuna, ina kallon yadda d'akina yayi wani irin sanyi, har ina rawan sanyi. A hankali na tashi daga sallayar na koma bakin gado, naja bargo.

? ?? Shashekar kuka nake sakamakon jin abin da ake da gangan jikina, a da can baya mafarki nake, amma a yanzun a zahiri nake ganin ana? shirin having sex dani, sai dai a duk lokacin da haka ta faru ba tab'a yin Sex dani ba, sai dai za ayi ta jagwalgwalani.

? ? ?? "Ya waduddu Ya Zul'arshin Azim, Ya fa'ali limayuri?" Bakina ne yayi nauyi sabida yadda ake min wani irin abu kamar ana dukana yasani fara ayatul kursiyu, har karshen ta, kafin nayi dama dama, duk abin da yake faruwa idanuna a rufe, domin duk yadda naso bude idona bana iyawa, a hankali nayi idanun sun bude, kallon gefena nayi. Kafin na lumshe shi zan mike naji na ?asa tashi..
"Hmmm!hmmm!hmmm!" A mugun tsora ce ba d'ago kaina ina kallon sama, wani ajiyar zuciya na sauke tare da kafewa da kallon matar me gashi buzu buzu? har fuskarta bana ganin kome.
"Rooman! Waye zai cire ki daga kundin ukubar mu? Waye zai yayye miki mayafin azabbar da muka shirya miki, Lallai muna bukatar ki a cikin mu, dan haka ke tamu ce har abada ba zaki tab'a subuce mana ba"
? ??
? ? ?? Ta kai hannu zata tab'a, ina kallonta. Tare da kokarin motsawa amma babu hali,shigowar Mama zata min magana na bude wayata, taga na kafe ina kallon sama kamar na suma, tayi maza ta kira. Shahid dasu Fanan, suka rufa? a kaina,? jijjiga ni Fanan tayi tana faWin.
"Wayyo mafarki ne ko gaske? Gashi ta kafe fa?"

? ? ? Da sauri Shahid ya tallafi kaina tare da d'ago ni.? Jan numfashi nayi, sannan na fashe da kuka, na fada jikin shi ina kuka.
"Don Allah,ka b'oye ni zasu zo"
"Addah Rooman! Meye ya faru?" Ya tambaye ni,
"Wata mata ne," kafewa bakina yayi tare da kasa magana, tana takowa tare da cewa.
"Ba zaki fada ba, Bama son su tuna da wani abu da zai taimaki rayuwar ki, ke tamu ce. Tun daga lokacin da na ganki na fara sonki, dan haka dole kiyi shiru dan bama son a tuna da wani abu da zai mana iyaka dake."

"Wayyo Allah na, don Allah ka b'oye ni karka bari ta tab'a ni, don Allah karka bari ta tab'a ni" aikuwa na sake wata irin kara sakamakon tab'a ni da tayi, na koma jikin shi kamar an sake danyen nama. D'ago kai na yayi, yana Kallon Mahaifiyar shi.
??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????"Ta suma fa!"
"Me zamu mata?"
" A saka mata ruwa mana" da sauri Fanan ta fita can sai gata da? ruwan, tazo suka saka min.? Bude idanun nayi ina jan wani ajiyar zuciya, kallon su nayi da sauri na tashi a jikin shi,ina hararan shi tare da cewa.
"Ban son Iskanci, meye haka?" Dama bamu cika shiri da shi ba,
"Toh tsigai, baki da lafiya ne kuma kina ta ihu shine muka taimaka miki!"
"Mama wai bani da lafiya? Ya ban ji haka ba a jikina? Ni fa lafiya na lau" na fada mata ina kallon su. Mamaki ne ya kama su.
"Yanzun kika ce a boye ki zata kama ki"? Inji Fanan,

? "Ni din?? Lafiya ta lau, kun fara gane gane ne?" Na tambaye su,
"Amma!"
"A'a!" Mama ta dakatar da Hisham da dama tunda aka fara abun yana kallon mu.
"Babu abin da ya faru, dama wayarki ce a kashe Mariyah tana son magana dake" gyada mata kai nayi, sannan na gyara zamana a tsakiyar gadon ina kallon su, kowa ya fita a sanyayye.
? ? ? ? Jikin Mama yayi masifar sanyi, suna fita.
"Mama amma bata da lafiya fa" inji Hisham,
"Eh mana, toh babu abin da za a mata ne?" Inji Fanan,
Riko hannun su tai sannan tace musu.
"A'a fa! Kar na kuma jin wanin ku yayi yunkurin shiga rayuwar ta, Allah yana gani kuma yana ji, ba zai barta haka ba, kuskuren da Babangida yayi kenan, shine sai labarin shi babu shi babu dalilin shi."

? ? ? ? ?? Ta faWa kwalla na zubo mata, kallonta suka yi bayan sun shiga d'akinta, tare da tambayar ta meye ya faru.
Kallon su tayi kafin tace musu.
"Babu kome"
"Mama kina boye mana wani abu" inji Shahid.
"Ban boye muku kome ba, don Allah

2 / 69