JINI YAFI RUWA COMPLET BOOK BY D AUTA.doc

Author :  Hadiza D. Auta Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   34 / 69

99K to 102K   out of 206.5K words

ya kasa tsaye, hankalin shi yana Yola gani yake kamar Hashim na isa can Yola rungume Rooman zai yi shi yasa yayi ta kiranta yana mata kashedi da hannunka me sanda, karta sake wani abu ya had'a su, karta kuskura wani abu ya shiga tsakaninsu da Babangida, kai ko Darrah bai ta kanta kamar yadda ya damu da Rooman.

300? ... Insha Allah'

+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A'ichah

+22784506476

0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank

#Mai_Dambu

[11/19, 8:44 AM] Joindah Na: EWF*



JINI...!

? ? ?? ?Yafi Ruwa Kauri?

Mai_Dambu



BABI NA ARBA'IN DA?BAKWAI



_AYI HAKURI SAURA KAD'AN NA KAMMALA FREE PAGES INSHALLAH_



Duk iskancin da Darrah take wallahi bai tab'a damun shi ba, asalima sai yayi kwana biyu me kyau bai bi ta kanta ba, sabida yadda yake faffutikar niman abin da zuciyar shi take muradi. Ta kai karan shi ya kai sau uku wurin Khadi Adamu Moddibo, amma bai sa shi sauyawa ba, asalima sai dadda kunce mata yake sosai, yayi ta fada yana masifa kamar me.



? Karfi da yaji ya zama masifaffe, miskili mara son magana,? kwanakin biyar a tsakanin tafiyar Babangida ya fito zai tafi office ta lalle shi Wan itama ta shirya tafiyar zata yi ta ce mishi.



"Dr ya dai na ga kamar baka da walwala ne? Wani abu ya faru ne?" Banza yayi da ita yaki ma kulata domin a cike yake da kowa, burin shi ya shiga asibiti. Har zai fita ta ce mishi.

"Lokacin da nace bana son ganin Hashim ai laifina kuka gani, ashe kuma haka abin ya kasance, budurwar Hashim kake so? Toh ai kuwa zan ga yadda zasu dauke ta su baka bayan ga wanda ya dace a bawa, na share ka ne amma ai ko motsi kayi akan kunne na yake." Bai ce mata cikan ki ba, ya isa waje? tare da jan motar shi ya bar asibitin. Kai tsaye gidan Lamido ya nufa, suma sun gama shirin zasu tafi aikin. Yayi parking ran shi a bace yake amma kuma Wan ya gyara gama ya daidaita fuskar shi. Kallon Ummi yayi matar Lamido, ta riko hannun Yaranta.

*Lamido! Me yasa duk tattaunawar da muka yi da kai sai ka gayawa Matarka?" Shiru yayi? yana kuma kallon Dr Hayat, shima Hayat din kallon Dr Nu'aiym yake, jikin Ummi sai bari yake, domin tasan duk hiran da sika yi da mijinta akan Dr Hayat a kunnen Darrah..



? "Ban san me yasa nake kaunar Adam ba, kodan ya kasance mutum na kusa dani oho? Amma nayi imani akwai abin da ya sani ko uwar da ta haife shi bata taSa sani a kaina ba, amma kai da nake ganin kamar kafi kusa dani, muna sharing damuwar mu, ka gaya min naka na gaya maka nawa ban tab'a yin hiran ka da wani ba, Amma kai ko tusa in nayi sai ka gayawa Ummi, ita kuma munafuka zata gayawa Darrah.



? ?? Wallahi naji zafin haka, shin da kike gaya mata kin tab'a tunanin meye zata gaya Miki akan mijinki? Gwara ni na fito da damuwata ce fili shi kuma ki jira sakamakon abin da shirun shi zai haifar mara hankali ha mace har mace bata da sirrin kanta, sai ta duniya. Mahaukaciya kuma
Mahaukaciya kuma kika kuskura kika min magna sai na kira kawu sha Wari na gaya mishi jahilcin da kike min. Ki gaya mata da kyau aure zan yi idan tayi wasa igiyar Aurenki da nata yana lilo"



Daga haka ya juya tare da barin su a wurin, cikin zafin rai Lamido ya mika mata hannu.

"Phone Winki?"

"Ya Lamido!" Ya kira sunan shi a tsora ce, sake tamke fuska yayi ya mika mata hannu, babu musu ta ciro ta bashi.

"Cire min a key"

A hankali ta kuma dauka ta cire a key, sannan ya bashi ya shiga Whatsp dinta, yaga Dr Darrah, bude sakon ta yayi ya fara hango duk jiran da suke da ita ta kwashe ta gayawa Darrah, kallonta yayi shi yana can yana alfaharin yafi karfin gidan shi, da shine da auren Darrah da tuni ya sake yar banza kome za ayi? sai ayi.

? "Abokina tun na yaranta, muke raba damuwar mu, yau kinnja yana gaya min da ya kuma gaya min sirrin shi gwara ya gayawa Yaron da bai kai ni kusanci da shi ba? Meye nayi miki kika raba min zumuntatta? Meye na tsare Miki da kika rabani da Abokina tun na yaranta? Daga nan kar na ga kafarki a cikin gidan gidan Moddibo ko gidan Anneh wallahi ki bar estate din nan kafin fushina ya ta'azzara akan ki jahilar banza jahilar wofi munafuka, wallahi kika sake na juyo gidan nan kina nan, sai na miki iyaka da ni har abada."



Ya mata tas har za tafi ya kwace dan shi a hannunta domin Babbar Yar tana gidan su.



"Wallahi kar ki kuskura naji kin je gidan mu domin sai na sake ki. Munafuka me fuska biyu." Kasa magana tayi tana kallon shi, har ya saka kai zai fita. Ya kuma juyowa yayi mata gargad'i sannan ya fita, bai tsaya ko ina ba sai kofar gidan su Adamu.



Kiran layin Umma Hani yayi, can sai gata. Jikinta a sanyayye ta isa wurin shi.

"Abban Affan ina kwana?"

"Shigo"

Ya fada a sanyayye, babu musu ta zaga tare da shiga.

"Lafiya! Me yasa kika ki daukar Wayata?"

Idanunta ne ya cika da kwalla, a hankali ta d'ago kai tare da cewa.

"Amma ban ga fa'idar haka bane, idan aka san akwai wani abu a tsakanin mu zan iya shiga tashin hankali, please mu tsayar da abin haka..."



Bata kai aya ba, ya matsa sosai kusa da ita. Tare da janyo fuskarta, ya had'e bakin su wuri guda, wani irin tsoro ne ya kama ta, bata san lokacin fa ta ture shi ba, kuka ta sake mishi tare da kifa kanta a kan gwiwar ta, tana kuka sosai.

Shafa bayanta yayi tare da cewa.

"Ba nufina na Miki haka ba, wallahi na haukace akan ki. Ina sonki please"



? ? "Meemah" Affan ya fada a hankali,

"Yawwa ga shi nan ki rike shi nasan aikin dare kike dashi anjima da yamma zan zo daukar shi!"

"Toh" ta fada tare da? fita ta dauki yaron suka nufi cikin gidan.

Bai san lokacin da ya fada soyayyar yarinyar ba, daga Dr Hayat sai Adam suka san yana son Hanih amma bayan su babu wanda ya sani, shi yasa duk abin da zai yi ko aiki ne tare suke shiga, baya tab'a shiga sai da ita. Babu wanda ya fahimci haka, domin daga Board yasaka sunanta, Lamido irin mazan nan ne masu mugun karfin sha'awa, shi yasa Matar shi ma a office din shi take, Indai suka hadu toh sai ayi da gaske domin yayi ta jagwalgwalata ke.



? ? ? ? Lokacin da ya fara son jin wani abu akan Umma Hani yayi mugun kame kanshi dan kar ta dauka sha'awarta yake, da tazo ta fahimci yana sonta toh ba karamin rigima suke sha ba, domin matse musu nonuwar yar mutane yake. Dr Hayat ya tab'a ganin shi sau daya shi ya mishi magana akan yana da Ya kuma yana da Mata, itama Yar wani ce, idan ya lalata mata rayuwa kan shi ya cuta, shine ya daina itama kuma bata son abin da yake mata, daurewa take kawai, amma wani lokacin kuka take mata. Babu abin da yake fisgar shi kamar dirin kugunta da yan madaidaiciya nonuwarta, wanda basu cika girma ba, basu cika kankanta ba.



?? Jan motar shi yayi tare da barin kofar gidan, gidan Kakan su ya nufa, anan ya samu Ummi tana kuka tare da rokon a bashi hakuri. Zama yayi bayan ya gaida Moddibo. Sannan yace mishi.

"Moddibo don Allah ka samu malam Idi akan yar rikon Addah Jebu, Umma Hanih ina sonta zan aure ta." Dafe kirji Ummi tayi tare da zaro idanu tace.

Na shiga uku na lalace!"

"Toh zan mishi magana amma Meye ua had'a da Khairi!"

Gyara xama yayi ya kwashe tas abin da ya gani har da shaida, s
Gyara xama yayi ya kwashe tas abin da ya gani har da shaida, sannan ya kuma gaya mishi cewa.

"Dattijo bawai dan mun samu sab'ani bane zan yi aure, a'a dama ina da niyyata, kuma ina son na maka magana. Toh Allah ne bai nufa ba"

"Toh Allah ya idda nufi, ita kuma kayi hakuri ka mai da ita, a ba zata kuma ba, insha Allah"

"Shi kenan" ya fada tare da mikewa.

"Wallahi ba zan yarda da auren wannan munafukar yarinyar ba, wato shi yasa baka tab'a shiga tiyata sai da rakiyarta, kome zaka yi da ita kake ni gani mahaukaciya ban san wainar da ake toyawa ba"



"Ai Yanxun kin sani?? Dan haka idan kin ka kuskura kika mata wani shirme na rantse da Allah dai na sake ki, Dattijo ka zama sheda na" ya fada cikin kwarin gwiwa.

"Ina ka kai min Yarona" fita yayi yana gaya mata kome ba, hakq tayinta kuka, ita me cika baki sai gashi ita ce take jin labarin za a tafi niman auren mijinta, fita tayi da gudu tare da nufar gidan Darrah. Kamar mahaukaciya haka ta shiga gidan tana ihu. Tana me zubewa akan kafet.



"Lafiya?"

"Lamido aure zai yi!" Ta fada cikin kuka, da hargagi.



"Yar gidan Uban waye zai aura?"

"Yar rikon Addah Jebu"

"Bura uban can, taso muje"

"Yo ko ni da Rooman tana Gombe dan Ubanta ba sai na b'atar da shegiya ba." Ta fada tare da jan motar ta, suka fita.



Gidan Addah Jebu suka nufa, tare da shiga cikin gidan, ai kuwa taji muryan Danta.

"Affan!" Ta fada a haukace.

"Meema!" Sauke shi Ummu hani tayi jikinta yana rawa.

"Shegiya karuwa, iskancin da kuke kenan? Ya dauko Miki dan mutane kin amsa gobe ma idan ya zo koran shi zaki yi" Darrah tayi kanta da itaccen da ta gani a wajen ta shiga zuba mata.

Da sauri Addah Jebu ta fito tare da ture ta.

"Ke wacce..".kifawa Addah Jebu mari tayi, ganin haka Ummu hani ta shiga dakin tare da kiran Dr Nu'aiym, tana kuka domin tana jin hannun ta kamar ya samu matsala.

"Dr kazo Maman Affan da Auntyn Darrah sun zo suna dukar mu."



?? Kashe wayar yayi ta leko tare da ganin Yadda Darrah take marin Addah Jebu. Bata gusa a wurin ba, ita kuma matar Dr Nu'aiym tana farfasa musu kayan su.



? ? Lokacin da Ummu hani ta kira shi suna tare da Dr Hayat da Adamu. Yadda ya amsa tare da cewa.

"Darrah da Ummi suna dukar Addah Jebu?" Tsakanin Adam da Hayat ba a san waye ya riga wani fita, domin dukkansu mota daya suka shiga, a fusace Dr Hayat yake tuki. Har kofar gidan. Bai kashe motar ba, ya shiga daidai lokacin da Darrah ta shake wuyar Addah Jebu tana faWin.

" Ba zaki fito ba, dan Ubanki sai na kashe banxa."? Zare belt din wandon shi yayi tare da kwashe ta, ta zube a kasa, ya shiga kwallo da ita..adam ya nufi wuri mahaifiyar shi, ya d'ago ta. Suka shiga dakinta.



? Dr Nu'aiym yana shigowa, ya amshi dan shi, ya kai mota. Tare da kallon matar shi. Komawa motar yayi tare da rubuta mata takardan saki daya, shi kam Dr Hayat dama a cike yake da ita yayi mata dukar fitar rai, sannan ya gaya mata da ?atuwar murya ya sake ta saki daya. Aure babu fashi. Yadda ta daki Addah Jebu haka ya dake ta, nata sai da yafi na Addah Jebu illa domin sanadin dukar cikin da basu san dashi ba ya zube. Karshe Addah Jebun ce ta fito tare da rufe Dr Hayat da faWa.

"Baka da hankali ne? Kana ganin yadda take zubda jini!"

Muryn shi na rawa ya ce mata.

"Yadda ta dake ki, haka data daki Ummina, yadda ta Miki haka zata yiwa Uwar da ta haife ni. Wallahi ba zan taba raga wanda bai ragawa manya ba, dan haka ta nufi gidan Ubanta ba gida ba, tunda bata da tarbiyyar bata san darajar manyan ba, ni ba asararre bane da xan zuba mata ido.300? ... Insha Allah'

+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A'ichah
EWF*

JINI...!
? ? ?? ?Yafi Ruwa Kauri?
Mai_Dambu

BABI NA ARBA'IN DA?TAKWAS

_AYI HAKURI SAURA KAD'AN NA KAMMALA FREE PAGES INSHALLAH_


?? "Baka da hankali ne? Wannan wani irin hauka ce? Zaka ka kashe ta ne?" Inji Dr Nu'aiym lokacin da yaga yadda yake jan Darrah, zuciyar shi ta gama fusata take ya amsa mishi da cewa.
"Na hauka ce" ya fada tare da ajiye ta yayi tafiyar shi, asibiti aka wuce da ita, wannan abin da ta faru ya d'aga hankalin Family baki daya, domin kuwa kowa hankalin shi ya gama tashi. Da aka ji abin da suka aikata take aka basu laifi tare da nuna rashin jin dadin dukar da yayi har ta rasa cikin jikinta. Amma a bangaren Khadi Adamu Moddibo bai ce kome ba, kuma bai mishi magana ba.

?? Akan wannan al'amarin sai gashi nan a had'a gagarumin meeting da ta janyo tashin hankalin da ya kusan raba kawunna iyayen su, karshe shi kan fushi Mahaifin shi yayi da shi domin a gaban jama'a yayi mishi fada yana blaming Ummi da cewa itace ta sake har Hayatuddeen yake dukar mace, karshe itama Hajiya Rushediyya tace bata yarda ba.

"Kawai tunda ya sake ta, Allah ya haWa kowa da rabon shi. Akan ta daki yar aiki ai sai a mata uzuri, tund ba ita daya bace ko mu da muka haife ta bamu tab'a mata irin wannan dukar ba, amma kasa yarinyar gaba kayi ta duka sai kace kasamu jaka? Alhamdulillahi tunda cikin ya zube kaje ka auri Rooman take ko ruwa take oho"

? ? ?? Bai ce kome ba, haka kowa yaji haushin sa, karshe aka ce an tashi Addah Jebu su bar estate din. Shiru yayi tare da mikewa zai fita.
"Ina zaka?" Inji Ummi ta tambaye shi a mugun tsoro.
"Zan bar gidan nan ne, akan me zata daki Matar da ta haife ta? Sannan kowa ganin laifina yake? Dan muna da arziki sai mu wulaknta na kasa da mu? Ba zan zauna ba domin matukar dan zauna toh tabbas Adam yana cikin estate din nan ne!"

"Dawo ka zauna. Babu inda zasu tafi domin kuwa abin da kayi baka yi kuskure ba, Addah Jebu ba sa'ar ta bace ka min daidai da ka hukuntatta, dama na gaya muku cewa matukar aka kuma kawo min rigima akan auren su, toh an gama auren shi da ita, dan haka Hamza ka dauki yarka Allah ya bata wani namijin da yafi Maccido, kai ma tunda kana da wacce kake so a Yola ka tafi ka musu magana zan tafi da kaina na nima maka auren ta."

"Wayyo Allah na, wallahi ina son mijina ba zan tab'a rayuwa babu shi ba" wannan shine ake kira jaraba, tana son Dr Hayat amma bata san yadda zata zauna da shi ba, baki daya ta birkita musu falon dakyar aka shawo kan Khadi akan ya amince Dr Hayat ya dawo ita domin yaki ya ce ba zai zauna da ita ba.

?? Haka suka tafi da ita, bayan sun watse Khadi yayi mishi magana.
"Kayi hakuri ka maida ita, ta gane kuskuren ta, kayi hakuri Allah yana alfahari da masu hakuri!"
Cikin sanyin murya ya ce mishi.
"Tun lokacin da na sake ta, Addah Jebu ta sani na mai da ita, amma ta tafi can gidan su zata gane muhimmancin rayuwar gidan miji da rayuwar gidan su."
"Haka ma da kayi yayi kyau, amma maganar Yola nan ka tabbatar ka tuntube su"

Gyara xama yayi sosai, sannan ya ce.
"Dattijo, maganar auren Yolan nan akwai gagarumin lamari me mugun tashin hankali, tun daga lokacin da na fara ganin Hashim, na ji hankalina bai kwanta da shi ba, sai Darrah take ce min ita bata son ganin shi tsoron shi take ji, dana bita cikin hikima da dabara, anan take gaya min cewa. Ita idan ta ganshi wani irin tashin hankali take ji, wanda bata san dalilin ba, sai da na fara ganin Rooman a asibitin Yola nan na lura da aljanun da suke bibiyar ta sune suke bibiyar shi, da na tsannanta bincike sai na samu ai dukkan su kusan abu daya ne, Lokacin da naje jinyarta sai na fahimci dukkan zuri'a daya ce, kuma a daren da zai tafi yake gaya min cewa. Malam Hayat Nagode kace min Rooman bata yi aure ba, da alama Alhaji Babba ya ajiye min alkawarin mu ne, Dattijo wallahi sai naji baki daya na sare, suma kowa yasan da alqawarin shi idan ya dawo zai auri Rooman, gashi ni kuma Alhaji Babba ya bani ita na tura da magabata na!"

Murmushi Khadi Adamu Moddibo yayi sannan yace mishi.
"Karka sare! Ka cigaba da faffutikar niman ta, insha Allah Ubangiji zai baka ita. Kayi hakuri ka kuma rike ta hannunka."

"Ai na hakura ne, ta auri dan uwanta zai fi dacewa da ita akan ta shigo cikin gidan nan ta samu tashin hankalin Zuri'ar ta, kawai gwara ta zauna a can zai fi mata."
"Never give up, shi rayuwa ba ayin shi haka, idan kace sai ka sare taya zaka karasa yakin da ka fara? Hmm akwai wani abu amma ba Yanxun zan gaya maka ba"

?? Dariya yayi sannan ya ce mishi.
"Batun matar nan kace ka kayi mafarkinta? Amma kuma baka dauki wani mataki ba"
"Eh toh kasan ance matukar muka hadu da Yarinyar a tare damu na ganin ta, toh ban sani ba ko ita ce Rooman ban sani ba."

?? "Amma ai mahaifiyarka zaka tambyarta domin ita ta gaya min." Inji Khadi Adamu Moddibo,
"Eh toh ai ita ta ki gaya min kome sai dai idan naje ta ce min akwai lokaci, kuma har yanzun lokacin nan dai bai yi ba, shi yasa na daina tambayar ta,"

?? "Hmm!"
"Kuma ban tab'a jin tashin hankali ba a rayuwata, ba sai da na hadu da Ruman, Wallahi bugun zuciyata ya girmama. Ban san yadda zaka dauka ba, amma idan na rasata xan yi hakuri amma kuma rayuwata zata iya zama koma baya."

? ? "Ka saka Allah a cikin lamarin ka domin idan ka biyewa mace zaka mutum ita kuma ta rayu da wanda take so." Mikewa yayi tare da nufar waje, har ya wuce gidan shi yana shiga falon kasa ya hango Safdar Hajbir zaune yana dariya!
"Ka zata zan kyale ne? Ai ni nake tinzara Matarka, itama Rooman bai zama dole ka same ta ba, domin duk wanda yabi inuwata sai naga bayan shi! Balle kai

34 / 69