JINI YAFI RUWA COMPLET BOOK BY D AUTA.doc

Author :  Hadiza D. Auta Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   16 / 69

45K to 48K   out of 206.5K words

ta rufe ta sa mugun duka, dan haka ta mike a hankali, tana faWin.
"Aikin gama ya gama, domin nan da sati biyu zaki zama matar shi,.ki dauki kayan kiyi amfani dashi ko kuma kina ji kina gani ki zama bora"

? ?? Kallon mahaifiyarta tayi tare sa cewa.
"Idan da nasan haka zaki min wallahi da ban zo ba, haka ma bata b'aci ba, ga su nan babu abin da zanyi dasu" ta fada tare sa barin dakin. Haka kawai za a bata wani bakin sihiri ta samo shi daga baya ya kwace mata ina shi take so ba wani abin shi ba.

Dan haka tunda ta shiga dakin ta ta gama booking din jirgin sassafe na gobe Monday.
Bayan fitar ta Hajiya Rushediyya ta sake murmushin takaici ta yiwa kayan kyakkyawar adana domin zata dawo Indai ita ta haife zata dawo tana kuka lokacin zata yi treating taurin kanta.
? ?

? ?? Bata kuma lekowa waje ba, domin bata son ganin Mahaifiyar ta. Addu'a take Allah ya kai ta gobe tabar Abuja.

? ? **
Gombe.
An gama kome cikin yarda Allah, aka saka bikin kamar yadda Khadi yaso wato sati biyu zuwa. Sannan ya ware kudi na musamman ya bada akan ayi sayayyar kayan aure a cikin kwanakin.

? ?? Lokacin da labari ya fad'a kunnen Hajiya Hadizah, tayi matukar farin ciki duk da mutanen da aka basu kudin had'a kayan Gwaggo Fa'e ce sai yar koranta uwar Munafukai Umma Dahare, sai kanwar Mijin Gwaggo Fa'e Sailuba.

? ?? Tare suka tafi kasuwa aka yi ta sayayyar kayan akwatin. Yayin da Hajiya Hadizah tayi nata sayayyar dan oda tayi daga dubai, sauran kayan ta bawa kawarta Hajiya Fareedah tayi mata anan abuja, har Kaduna aka tafi had'a hijabai masu masifar kyau aka kawowa mata.? Tura mata hoton kayan Abeedah tayi dan dole ta ajiye na wurinta sai abin da babu ne ta tura mata, domin an a family group.

? ? ? **
Lokacin da Darrah ta dawo gida Gombe bata yi tsammanin zata samu kulawa daga Maccido ba, sai dai yana kulata har yana tambyarta me zata yi na bikin su. Tace mishi.
"Na bar maka zab'i"

"Shi kenan saura kwanaki nasan zaki so kamu, bride show, mothers night, and dinner." Gyada mishi kai tayi tare da jin wani kwalla na cika mata idanunta.
"Toh ki samu adam yayi had'a ki da masu kome"
"Why Adam?"
"Baki bukata ne?"
"Ina bukata" ta fita. A cikin motar shi ta nufi cikin gidan. Jan motar shi yayi tare da nufar inda mara lafiyan shi yake, duk da ya sallami sauran mutanen shine dai har yau bai fara magana ba, Asalima kamar ya manta kome na shi ne.

? ? Kuma irin wannan matsalar yana iya shafar kwakwalwar mutum. Dan haka yake kara bashi kulawa tare da mai dashi asibiti ana duba ?wa?walwar shi.

? ? Sai da ya fara zuwa asibiti ya duba mara lafiyan, sannan ya mishi addu'a kafin ya fito. Ya nufi wurin motar shi da yake Park space. Ya shiga tare da kunnata amma taki ta shi. Sake gwadawa yayi, bata tashi ba jikin shine ya bashi akwai wani a bayan motar shi Wan haka ya kalli mirror motar.

Sam Allah bai daura mishi tsoro ko shakkar wani abin halitta ba, dan haka yayi Bismillah ta tadda motar aikuwa ta tashi, ya ja motar shi yana me kunna wakar Zain, yana bin shi cikin nutsuwa da kwarin gwiwa. Dawowa gaba halittar yayi.

? ? A tsaye yake kamar one, kafar shi daya tal, yanayin shi na sadaukan maza ne, yana da kai kamar na saniya. Sai gangr jikin shi irin ta yan adam. Cikin muryan firgitarwa yace mishi.
"Ka cire kanka akan mara lafiyar nan"

? ?? Cigaba yayi da maganar shi Dr Hayat yayi kamar bai gan shi ba, sai da suka kusan shiga unguwar su ya taka wani wawan birki kamar an watsa aljanin waje haka ya watsar da shi waje. A hankali ya fito daga motar lokacin aljanin ya koma siffar shi ta asalin rabi mutum rabi saniya.

? ?? "Nasan baka san ni ba, kar na kuma ganinka a cikin da'irar nan domin mallaka ta ce, idan na sake ba kuma ganin ka, kai da wanda yake turo ku zan lalata muku halittar ku"
Ya fada yana d'aga mishi gira Waya..

? ? Da wani irin fusata aljanin ya nufi kan Hayat, aikuwa kamar wanda aka wurgo mishi tsawa haka ya b'ace tare da kara da rugigi.

? "Alhamdulillah" ya fada tare da komawa cikin motar shi, ya zauna sannan ya tashe ta ya nufi gida.

?? **
Yola.

Kwanan Alhaji Babba biyar aka kasa gano matsalar shi Wan haka yaran shi suka kawo shi babban asibitin da nake aiki, tunda aka gaya min nayi ta shige da ficce har Allah ya taimaka aka samu damar kawo shi cikin asibitin, ciwon ciki yake fama dashi amma da aka duba babu shi babu alamar shi.

Idan ciwon ya tashi kamar zai yi hauka a cikin wannan yanayin nima na fara irin ciwon cikin. Amma ina boye nawa, idan na shi ya fara mishi haka zan ji a jikina kafin nima na fara.

?? Ganin basu da wani masaniyar yasa a babban likitan asibitin ya tura sako zuwa asibitin Nana A'ishah hospital da kokon baran su Dr Hayat yazo yayi musu wani taimakon.

? ? ?? Sun samu duba sakon su kuma ya gaya musu gaskiya ana bikin shi a wannan satin, dan haka suka yi ta rokon shi don Allah ya zo ya duba al'amarin su..

Ya amince zai zo amma kwana Waya zai yi ya koma.
Allah da ikon shi nawa ciwon cikin yayi sauki sakamakon wani magani da Mujaddadi ya bani, domin kwana uku ina fama da ciwon sai gashi a kwana na hudu yazo har gida ban san ya aka yi yasan gidan mu ba, ina kwance baba iliya yayi min magana na fito ina tafiya da kyar.

?? "Ayya kai ne da yammacin nan?" Na fada mishi ina daurewa,
"Kamar baki da lafiya?"
"Eh wallahi ciwon cikin nake fama da shi, amma da sauki"
"Idan na baki magani zaki sha?" Ya tambaye ni, murmushi nayi mishi sannan nace mishi.
"Me zai hana? Ai zan amsa, kuma zan shan"?
"Ok, kawo min kofi da ruwa."? Juyawa nayi na shiga cikin gidan,

Can na dawo da ruwan, yana amsa ya ciro wani kunshi a cikin aljanin shi ya saka a cikin ruwan, sannan yayi addu"a ya tofa. Sannan ya bani.
"Kisha da Bismillah"
Fada ni ma nayi tare da Bismillah na sha.
"Zan tafi zuwa gobe Insha Allah xan zo na duba jikin ki"
"Nagode Sosai, Allah ya kai mu" ya juya tare sa barin gidan, nima na koma cikin gidan, wato wani mugun ciwon cikin da ya kuma tirnike ni, na cigaba da juyi ina jin kamar wani abu zai fita ta kasa na,? tashi nayi tare da sauka kasa. Ban taba jin haka zai faru dani ba, kamar wacce na suma, ban san yadda zan kamanta abun ba amma na fahimci kamar wani abu yana fita a gaba ne da mugun ciwon ciki da zafin, Bani da ikon hanawa.

? ?? Kamar a zahiri ne ko a mafarki aka mika min baby nad'e a shawel pinky, tare da nuna min shi ban ga fuskar wanda yake nuna min ba, amma naji kamar ana cewa.
"Sannun kinji, sannun da dakon kayan mu, kinga dawa yake kama?"

? ? "Innalilahi! Rooman sannan ciwon cikin ne?" Inji Mama da ta shigo ta same ni kwance cikin mawuyacin hali, kallona tayi tare da cewa.
"Wannan jinin fa?"
"Ban sani ba," na bata amsa a wahale, haka ta kula da lafiya ta tare da kasa nutsuwa dan haka ta kira Innah ta gaya mata halin sa nake ciki. Allah Sarki Uwa kenan.

? A cikin wannan yanayin, tazo muka tafi Maiduguri, gidan wani Malam Aminu Goni,? yana gani na ya shiga had'a min magani tare da cewa.
"Lafiyar ki tana gab da samuwa, sai dai fararren ?addara zata iya ratsa zukatan mu, hakuri da juriya zai kai mu ga cin nasara, amma tabbas lafiyar ki ta kusan samuwa ga wannan Insha Allah zai wanke miki cikinki ba zaki kuma daukar nauyin wani shaidani ba, sai na abokin rayuwar ki."

Kwanan mu daya muka dawo anan muka ji labarin ai likitan da zai ga Alhaji Babba ya bada uzurina ayi hakuri ba zai samu zuwa ga iyayen shi sun hana shi. Abin tausayi haka dattijon sai makala mishi alluran barci da na rage zafin ciwon suke kawai.

? ? *
Gombe.
Ranar Asabar aka daura auren Hayatuddeen Abdulwahab Adamu Moddibo tare da Hafsat Darrah Hamza Adamu Moddibo, akan sadaki nera dubu saba'in. Daurin auren da ya tara dubanin al'ummar Musulmi daga Sangaren uban amarya da kuma Sangaren Uwar ango da Uban Ango.

? Bikin ne na Who is Who, Dan ma Hajiya Hadizah taki yarda da bidia, an yi bikin dai dai gwargwado, tare da shagali. Ana gobe daurin auren wato ranar juma'a, ya tadda rigima zai tafi Yola ana niman shi ai kuwa, mahaifin shi da Mahaifiyar shi sun san zai tsarewa aurenne kuma sun fahimci hake daga wani irin rigima da suka yi da Darrah har ya mare ta, ranar kamu. Aikuwa ran mahaifiyarta ta yayi masifar Saci domin tana ganin tun yanzun ya fara saka hannu a jikin yarta ina kuma da anyi auren sai me ba zai faru ba, wato idan ta nazarci akan abin da bai taka kara ya karya ba ya mareta, amma tuno da sharadin shugaban su sai jikin ta yayi sanyi ta rufe yar nata da fada.

Dama akan Ummi ce kanwar Adamu yar rikon Addah Jebu, wai kawai dan ta shiga cikin taron kawayen ta, shine fa ta mari yarinyar akan idanun Adamu, shima ran shi ya Saci ya gaya mata magna dake bata da kunya sai gashi ta d'aga hannu zata mare shi akan idanun Maccido, shi ya rike hannunta ya gaura mata mari, abin kenan ya zama kananun magana a cikin Family din Gwaggo Fa'e da tafi kusanci da uwar amaryan ta daka tsalle ta tuna tace bata iya ji ba.

? ?? Akan me zai tozartata a gaban jama'a, nan suka yi ta kananun magana har dai Hajiya Hadizah ta fito tayi magana shine aka samu sau?in al'amarin amma na ciki yana ciki. An bar shi ne a ga kamun ludayin zaman su. Ranar juma'a yace zai tafi aiki Yola, sai da ran Mahaifiyar shi ya Saci sannan ya hakura kan Insha Allah nan da sati biyu zai zo domin ta mishi gargadi da bata yarda y tafi a kan lokacin ba, dole ya kai tafiyar sati biyu masu zuwa.

? Haka aka yi shagali tare da yan uwan shi, duk da yana fara'a da farin ciki amma Khadi kadai yasan bayan kaunar auren sai Dr Nu'aiym..300#@Mai_Dambu
EXQUISITE WRITERS FORUM.
JINI..!
? ?Ya fi Ruwa Kauri?
? *Base on true life story*

*Sadaukarwa ga Family Hasssan Yero Family da Madakin Muri Family*

? ? ?? Mai_Dambu

BABI NA ASHIRIN DA BIYU.

Janye hannun shi yayi tare da takawa gabana.
"A'a Rooman ba zaki iya daukar kasadar da nake ba, zaki rabu da ni."

Cikin rashin sanin madafa na kuma isa gaban shi.
"Bani da wanda ya fahimce ni, Babu wanda ya gane halin da nake ciki, karya tani suke, yau naga ciki a jikin matar Baffa, kuma da na fito kace na koma na ciro gashinta, na hango wani abu a jikin Matar Babana,. Na hango mutuwar Auren Falisat. Kai ne kawai ka yarda dani. Me yasa zan wasa da damar da na samu?"

? ? Cikin matukar damuwa ya kalle ni, sannan yace min.
"Duniyar mu sun bambanta, kaddaran mu daya ce, ina sonki kiyi min alkawarin zaki tsaya a bayana" rike hannuna nayi gam tare da kura mishi ido nace.
"Nayi maka alkawarin da Allah ba zan tab'a a juya maka baya ba, amma akwai abin da yake faruwa dani da zarar na samu wanda nake so" takowa yayi gaba na.
"Ko kud'a sai na so ta cutar dake zai cutar dake, ki kwanta kiyi barci, amma karki manta alkawarin mu kar wani abu ya dawo ya juyawa kaddaran mu baya"

? Gyada kai nayi tare da rike hannuna ina jin hawaye na kuma tuttulomin.
"Insha Allah duk rintsi duk wuya ina tare da kai" a hankali ya bude min hannun shi na shiga cikin kirjin shi yana buga bayana.
"Ina kaunar ki"
"Nima haka"
"Kiyi min alkawarin zaki rayu dani"
"Insha Allah na maka alkawarin zama da kai da dad'i ko babu dad'i."

? ? "Ni kuma zan baki mamaki domin babu wanda ya isa ya rabani dake"? haka ya janye ni sannan yayi min sallama ta tafi.? Tun daga lokacin ban kuma samun matsala da kome ba, Asalima na daina mafarkin da nake ne. Matar nan ta daina zuwa min sai barci na nake cikin kwanciyar hankali da nutsuwa.

Nayi kyau na kara kiba, fatatta tayi mugun haske duk wanda ya kalle ni sai ya fahimci nutsuwa ta zo min,tsakanina da Mujaddadi wata mahaukaciyar soyayya ce muke kamar zan zaucce, har a wurin aikina kowa yasan na fada soyayya na fitar hankali, ba dare ba rana sakon dare daban, sakon rana daban, gashi idan yazo gidan yakan b'ata lokaci kafin ya tafi dan haka ranar da Shahid ya gaji da shegen hiran da baya karewa ya fito yayi mana sallama.
"Addah Rooman! Ki shiga cikin gidan," ya fada min tare da mikawa Mujaddadi hannu.. kin mika mishi hannu yayi tare da tsare juna da idanu.
"Malam ina son ka fahimci wani abu a matsayin ka na mutumin kirki bai dace kana zuwa kana b'atawa yarinya lokaci ba, sannan idan har da gaske kake toh ka fito idan kuma baka shirya ba, toh kar na kuma ganin kafarka? a kofar gidan nan"

"Idan naki fa?" Ya tambayi Shahid a gadarance.
"Tabbas zan gayawa me faWin mu kar na kuma ganin ka a cikin gidan nan" ya fada shima da danyen kai.
"Hmm, zan fita ba zan kuma dawowa ba, amma ka sani ba a bina bashin da ya rage a kaina da na biya da yadda ba zaka iya kwacewa ba, sai dai ina kaunar ta, kuma nasan kayi haka ne dan kare mutuncinta da na baka mamaki." Bai kula shi ba ya shige tare da rufe gidan.

Bayan nayi wanka tare da alola nayi sallah, na kwanta.? Ban jima ba na kwanta. Kamar mafarki haka nake jin yanayin dan haka ba shiga ambaton Allah har barci ya dauke ni.

? ? "Mujaddadi lafiya kake huci baka tafi bane?" Duk lokaci guda na wurga mishi tambayoyin da suke bakina.
"Kanin ki nan ne ya min rashin kunya, ba dan ina son ki ba, wallahi sai na bashi mamaki."

"Kayi hakuri zan mishi magana ai kai ba sa'an shi bane, don Allah kayi hakuri kaji Insha Allah irin haka ba zai kuma faruwa ba" na fada tare da rarrashinsa, rike ni yayi tare da cewa.
"Sai kin sumbace Ni" juyawa nayi naga babu kowa kawai na sumbace shi.? Rungume ni yayi tare da cewa.
"Zanyi tafiya na tsawon wata guda,an turo min Ammyna bata da lafiya, zan je na duba ta, ki tayani rike amanar kaina"

?? "Ayya Ubangiji ya bata lafiya ja gaishe ta, sannan zan rike maka amanar da ka bani." A hankali ya saka hannun shi cikin aljuhun shi ya cire wani zobe ya saka min a hannuna. Sannan ya ce min.
"Ki kula da bakon lamarin da zai zo miki ba haka kawai ake amsar kowa ba, karki manta ki ajiye min zuciyar ki tana da me iko da ita"

? Gyada kai nayi sannan na ce mishi.
"Insha Allah" rungume ni yayi tare da sauke min sumbata a goshi, sannan ya ce min.
"Ki kula min da kanki"

? ? Sallama muka yi yayi tafiyar shi ni kuma ba cigaba da barci na.
? *
Washi gari.
Da na tashi ban lura da zaben ba, nayi ta hidima na, sai da na zo tafi asibiti na kalli Aunty Binta da take kwance a falon.
"Aunty ya dai?"
"Babu"
"Ki daure domin zaki iya samun masu bibiyarki, idan har haka ta faru cikin jikinki zai zube" tashi tayi yana kallona sannan tace min.
"Da gaske ina da cikin ne?"
"Akwai da gaske akwai, sai dai ki boye domin xa a iya rasa shi "

?? Jin haka yasa ta yin shiru tana kallona.
"Baki aikin bokanci balle nace ke din bokayan ce, amma bakin ki yana sake.magana da yawa."

Tashi nayi xan bar falon na ji na rike abu ina, dubawa sa mamaki na ga zobe ne mai kyau, kuma ta dace da hannuna. Sai lokacin abin da ya faru ya dawo min, kamar a mafarki kamar a zahiri kawai sai na ajiye shi a zahiri ne domin ai muna cikin magana ya gaya min zai bani kyauta sai ga Shahid.? Ina cikin wannan yanayin Shahid ya fito kallon shi nayi naga fuskar shi a kumbure. Ban yi mamaki ba sai dai na ce mishi.
"Bana son rashin mutunci akan me zaka gayawa Mujaddadi bakar magana?" Tsaki yayi domin baya jin dadi jikin shi.
"Ki rabu dashi bana jin mutumin kirki ne, idan kanwar shi aka kuma tsarewa da hira har goma zai ji sai ne??? Addah Ke ba yarinya b'ace balle a ce da kuruciya akan ki, idan da yau kinyi aure da tun lokacin can babban yanki ko danki zai kai shekara goma, amma kin zauna kina abu kamar wata adult ko su ba zasu yi abin da kike ba, kai ya waye an daina wannan yanayin don Allah domin mutuncin ki da ta gidan nan k???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?i rage hiran dare"

Wallahi maganar shi tayi tasiri a raina amma kuma, yadda nake jin Mujaddadi ba zan iya hakuri ba, dan haka na tsaya cikin masifa na gaya mishi magna tare da mishi gargadi ya fita hanyar Mujaddadi. Karshe sai da Mama ta shiga maganar ta mishi fada, sannan ya hakura bawai dan yaji ba.

? ? ? A cikin kwanakin Fanan tazo mana wuni, kamar ba zamu rabu ba, na had'a mata kayan mata da na sayi na aurena duk na bata tayi ta murna har tana nunawa Mama, murmushi kawai tayi da zata tafi na ciro mata wasu rigunar barci, ajiye mata sai gata har da kuka, ina son Fanan domin bayan kannena sai ita, sabida duk abin da zan yi babu me saurin bada shaida aka kaina sama da ita. Zuciya tana son me kyautatta mata tana kin me kuntatta mata, shi yasa ko kannena ban ji na basu ba sai ita, na bata kome.

? ?? Haka muka tafi asibiti da ita Alhaji Babba

16 / 69