JINI YAFI RUWA COMPLET BOOK BY D AUTA.doc

Author :  Hadiza D. Auta Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   6 / 69

15K to 18K   out of 206.5K words

suke dama a layin su, ita tayi ta kula da ita har cikin ya fito.

?? Abin mamaki cikin nada wata shida ya kwanta, kamar ba a tab'a halittar cikin ba, hankalin Mama ya tashi dan haka ta nufi gyambo, taje ya saka gwaggon su a gaba tana kuka.
"Gwaggo don Allah ki had'a bi da Shalle, cikin Mariyah ya kwanta."
Shiru Gwaggo tayi kafin ta ce mata.
"Ba wai ba zan kai ki bane, amma ai ke kin san abin da yake faruwa me yasa ba zaki dakatar ba? Don Allah ki yi wani abu mana"

? ? ? "Wallahi ba zan iya wani abu. Kai ba, tun tuni Mariyah ce ta zab'e haka don Allah." Ta faWa tana kuka,
Rike hannun Gwaggo tayi da mamaki ya kama ta.
"Iyayen ku sun sani?"
"Basu sani ba, amma ita ta zab'i dukiya akan haihuwa. Don Allah ki rufa min asiri, ki bar abun haka." Mik'ewa tayi sannan ta dauki mayafi suka fita, sun yi tafiya me tazara, sannan suka isa gidan Shalle tana zaune a gindin bishiyar tsamiya.

"Kina son yar uwarki, son itama Wayar tun ranar na fahimci haka, me yasa? Kinsan ai da yarinta a tare da ita akan me zaku dage ita ta zab'e bayan zab'ar mata aka yi"

? ? ?? Cikin kuka take kallon Shalle.
"Ta ko ina zagaye muke da su, don Allah kiyi wani abu." Mik'ewa tayi sannan ta tsinko ganyen tsamiya ta had'a da wasu ciyayyi. Ta mika mata.
" Dafa ta zauna akan tsohon turmin tsakar gidan ku, ta sha Insha Allah zata sauka lafiya daga kan shima sai ta bukaci hutawa."

"Mun gode" ta ciro kudi zata bata tace mata.
"Bana karban sadaka. Idan kin tafi tasha ki bawa Almajiri. Idan namiji ta haifa a sanya mishi Abdullahi, idan mace ce kuma ku saka mata sunan da zai dace da rayuwar ta. Amma kice karta yi kuka fa! Naso da zanyi rayuwa tabbas da zan tsaya na taimakawa abin da zata haifa."

? ?? Gyada kai suka yi. tare da mata sallama, suna tafiya. Ko minti talatin ba ayi ba, wasu mutane suka kawo jikan su dan kimanin shekaru goma baya, babu Lafiya. Karban shi tayi tana murmushi tace musu.
"Kun sha tafi, gashi kuma toh bari na gan shi"

? ?? Shafa kan shi matar tayi sannan tace musu.
300? ... Insha Allah'
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A'ichah
+22784506476
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank
#Mai_Dambu
? EXQUISITE WRITERS FORUM.
JINI..!
? ?Ya fi Ruwa Kauri?
? *Base on true life story*

*Sadaukarwa ga Family Hasssan Yero Family da Madakin Muri Family*

? ? ?? Mai_Dambu
*Talla! Talla!! Talla!!!*

_Akwai turaren wuta dan Maiduguri da Chad Ubansu me sanyin dadi idan ka saka sau daya sai ka kuma nima idan har kin yarda ke ?asaitacciyar mace ce me aji jaraba turaren wuta na zamani me yayi ba iya nan ba hatta? Humra me sanyin dadi akwai. Ga masu bukatar bikin ko amaryan karni tuntube Aishah Shuwa da kanki zaki bani labarin kamshi...+234 812 535 5554 sai an gwada akan san ba kwarai_


BABI NA BAKWAI.

"Toh Allah mai yadda yaso, ku dan bani minti biyar mu gani." A hankali take shafa mishi wasu maganin da ta kwab'a tare da had'a mishi ruwan tana bashi yana sha. Kafin ta juya ta kalle shi tana faWin.

"Kwana nawa kenan da faruwan haka?"
"Kwana Uku, nazo biki ne dashi bamu tab'a zuwa ba sai yau" murmushi tayi sannan ta ce mata.
"Zan baki zab'i amma ki bani nera biyar" duba jakarta tayi dakyar ta hango nera biyar ta bata. Juyawa tayi sannan tace mata.
"Zaki shahara sosai, zaki daukaka sosai. Sannan kukanki ba tsawon shekaru zaki cigaba da yi, kafin Allah ya kawo miki me share miki shi. Sai dai zan muku aikin nan kyauta da kuma wani abu Waya. Wancan matar ta tafi bana son zaman ta a nan."

Juyawa matar tayi ya rage daga Shalle sai matar da ta kawo danta, sun yi magana me yawan gaske,tare da mikawa Uwar yaron wasu abubuwan sannan ta ce mata.
"Shi din zai zama gaggara badau ne, kuma zai zama mutum na farko me yawan Alkhairi, kiyi ta addu'o'in, Allah zai tsaya muku, domin kina cikin makiya, shi kuma Karki damu da yadda rayuwar shi take, kiyi kokarin ganin kin fahimce shi. Wannan na bashi ne, domin ya zama adali a cikin al'umma, mai tausayi da jin kai, karki damu da lallai sai yayi yadda kike so, bayan Mayun sun shafe shi, akwai abin da ban gane ba, amma kiyi hanzarin barin nan da shi."

? ?? Mik'ewa matar tayi tare da mika mata sadaka.
"Ki tabbatar yau kuka bar garin, karki kwana a cikin shi, sannan ki bawa Almajiri sadaka kune mutane na karshe da nayi muku aiki akan gabba"

?? "Mun gode" ta faWa tare da saba'a yaron a kafad'ar ta, suka bar wurin Shalle. Bayan kamar minti biyar ta shiga had'a sauran abubuwan tare da daure ciyawar da yake wurin. Wani irin rugugi ne da wani katon tsawa ya diro a wurin, wasu irin manyan halittu suka bayyana a gaban ta.
"Yau ta kare miki"
"Alhamdulillahi burina ya cika kuma na sadaukar da kome ga wanda nasan al'umma zasu amfana da su, duk abinda zaku min sai kuyi"

?? "Shalle me yasa baki jin magana? Kinsan" shake wuyar jibgeggen halittar tayi sannan tace.
"Hukuncin shekaru nawa zaku dauka kuna min, na gaya muku ba zan yi ku ba, ku kyale ni mana" watsa mata wani irin Chain suka yi tare da daure ta suka tafi da ita.. duk yadda ta juya tsinin Chain din ne yake soke ta dan haka ta hakura da motsi.

A ranta tana ayyanawa idan har matan nan me cikin ta haifi Ya mace Ubangiji ya nufe su da saka Umm-e-Rooman. Domin sunan ya tasirantu da wargaza wasu abubuwan. Allah nuna mata wannan karshen zaluncin.

? ?? **
Basu kwana a gyambo ba, Maman Babangida tana bayan motar, Matar da ta kawo danta itama tana gabanta, ganin ya rage saura mutum biyu matar ta biya kudin motar baki daya ta ce mishi.
"Idan ka sauke ta A Yola zaka wuce dani gombe."
"Allah Sarki Hajiya mun gode"
"Babu kome"

Haka suka yi ta tafiya har Allah ya kawo su Yola, dare yayi sosai. Dan haka matar tacewa driver.
"Ko zaka kai ta garin su, ina ga sai gobe mu wuce kaga dare yayi zan kara maka kudin sama da." Jin kudin da za a biya shi yasa shi Amincewa sai gashi har Mubi, bude ido yaron matar yayi sannan ya ce wa Driver din.
"Tsayar da motar" yadda yayi maganar kamar umarni ne dan haka mutumin ya tsayar da motar.
Kurawa wajen yayi idanu, tare da kallon yadda ayarin wasu irin bakakken macizai suke tsallake titin, su kansu wani irin sanyi ne yake kad'awa, tare da tsoro ya kama su,? amma shi yana ganin macizan. Sai da suka gama wucewa sannan ya cewa driver.
"Muje" haka suka ci-gaba da tafiya har suka isa gidan su Mama.
Kallon su tayi sannan tace musu.
" Ba zaku tsaya ku kwana ba?"
"A'a ina son gari ya waye mana a gida ne ba bar yara a gida,"
"Toh shi kenan" haka ta fita tana musu godiya, sai da ta buga kofar gidan aka bude, har Baffa Chindo yaje yayiwa matar godiya, sannan suka juya abin su, bayan ta shiga cikin gidan.

Washi Gari
Sa sassafe ta dafa maganin ta kaiwa Mariyah, sannan ta dawo ta Cigaba da ayyukan ta, haka suka yi ta yi har aka kwana aka wuni, tsawon wata biyu ana abu daya, sai ga cikin ya fito bul, abin mamaki. Haka suka ci-gaba da tattalin cikin, duk da samun shi yaja baya, amma kuma akwai na rufin asiri.

Kafin ta haifi cikin nan kuwa, sai da jini ya Salle mata, kamar zata mutu, haka Alhaji Babba ya shiga niman magani kamar gobe duk inda ya shiga za a gaya mishi ai matsalar a cikin gidan yake, ba a wajen gidan ba. Gashi nan idan yaje ya tara Familyn din su yayi musu kashedi. A sake mishi kurwan Surukar shi.

? ? ? Yana zuwa yayi musu hauka na fitar hankali,? tare da cewa sai ya dauko Sarkin Mayu yayi musu tonan silili.

? Jin haka kuwa bai gama fita a kwayar shi ba, aka ce jinin da yake zuba ya tsaya. Da haka aka samu cikin ya kai labari, shi yasa da ta tashi haihuwa babu wanda ya sani daga Mamar Babangida sai mazajen su, sai Alhaji Babba.? Shi da kan shi ya tsaya da addu'a, har Allah ya dauke ta lafiya.

? ? Ana kawo mishi yarinyar yayi mata addu'o'in tare da mata Huduba, sunan da zai saka mata ne yake ta wasiwasi, a hankali ya ji kamar ana ce mishi ka saka mata UmmuRuman,? ai kuwa ya rangad'a mata Ummu Ruman,? kowa yazo Barka har da kakanina yarinyar, kowa ya dauke ta sai yayi magana, gashi a lokacin aka bawa Yakub auren Salamatu.

? ?? Murna a cikin Zuri'ar babu wanda bai yi ba, bayan suna aka? Umm-e-Rooman ta kama wani irin kuka mara dadin ji. Haka aka yi ta tunanin ko wani abu ne, kafin su yi arba'in yarinyar ta koma kamar Kwarangwal,sai da Alhaji Babba ya kai yarinyan can kauyen numan wurin wani me magani, mutumin ya duba ta sosai, kafin ya basu magani tare da cewa.
"Akwai Mayu a cikin gidan, ta ko ina suna son yarinyar suna bibiyar rayuwar Uwar da yar Uwar tafi ?arfin su, suka koma kan Yarinyar. Dan haka ga wannan ayi ta mata hayaki aka bata tana sha itama Uwarta a bata ta sha, wannan ta wanke nononta da shi"

Ya amsa tare da musu sallama ya bar kauyen ya dawo gida,. Lokacin da ya dawo ne ya bada aka fara maganin, sannan ya tara meeting. Bayan la'asar.
Sun taru baki daya, shiru yayi sannan ya mike tare da cewa.
"Na tara ku ne a nan ba dan kome ba, sai dan wancan yarinyar! Tun kafin a haife ta kowa yasan yadda muke ta fama har zuwa yau. Sai da na gama yawo na, aka ce min ciwon yarinyar a cikin gidan nan yake. meye Umm-e-Rooman tayi muku? Ku idan har rayuwarta kuka bukata toh ku dauki nawa ku barta ya rayu! Don Allah ku sake kurwanta." Yadda yayi maganar yayi kashe musu jiki dan haka aka shiga kananun magana.
"Ai kowa yana fama da matsala babu wanda ya sani a she a cikin mu ake mana haka, toh gaskiya ya isa haka matukar a ka cigaba wallahi kome zai faru. Domin ba za a tab'a mana dan uwa ba, itama Yarinyar a kyale ta haka ko kuma muyi abin da zai hana kowa sukuni sai a dauko Sarkin Mayu yayi mana tonan silili a cikin gidan." Jin haka yasa duk suka shiga hankalin su. Miyagun cikin su, suka shiga hankalin su kamar me. Tare da alkawarin sake kurwan yarinyar.

? ? ? Bayan an gama taron tare a kafa sharadi idan yarinyar ta kuma wani ciwo wallahi koma wacece sai an fitar da ita, dan Alhaji Babba yayi rantsuwa idan ba zasu tab'a shi ba, toh a sake mishi kurwan Jikar shi, tun da suka ji abin da sauran yan uwan shi suka fada tare da gaya musu zasu dauki mugun mataki matukar suka tab'a Alhaji Babba.

? Shine yarinyar ta samu lafiya, a hankali da kome ya sauya har yarinyar ta kai shekara daya da rabi

? ? ? Bata kuma wani lalura ba. Wani abin da Mariyah take yi duk lokacin da magarib tai zata saka Babangida ya rike hannunta su je cikin gidan, wurin Yakura Adama,? Kakar ta na Uba. Tun yarinyar bata da wayo har tayi,. Wani lokaci da kanta take tafiya, kafin ka shiga cikin gidan, akwai bishiyar rimi, a cikin gidan kullum tazo wucewa sai ta tsaya tana kallon wurin.

? ?? Tun abin yana bata tsoro idan tazo sai ta tsaya, har ta daina tsoron. Amma haka kullum sai ta zo wurin bata da yawan magana, haduwar ta da wurin yasa ta kuma zama mara magana, idan tazo wurin zata iya zama har isha tana kallon abubuwan al'ajabi.

?? A hankali take girma har ta kai lokacin da aka saka ta a makaranta, a lokacin aka yi auren Yakub da Salamatu. Allah da ikon shi tana shigowa sai cikin Maimunari, wacce suke kira da Munnah. A lokacin Mariyah tana da cikin Abdul Malik, kusan a tare suka haihu.

? ? ?? Daga nan suka shiga haihuwa kamar gasa, har lokacin da Umm-e-Rooman ta gama Primary school, ana goyon Hamdiya. Lokacin Babangida yana ?o?arin shiga jami'a.

? ? ? ? ? ? Tun daga lokacin wata irin shakuwa ta shiga tsakanin su,? wani abu da ba kasafai ake gani a wurin yaran Fulani ko hausawa ba, shine gashin Umm-e-Rooman ja ne, me sirki da fari fat, wanda ya karkato ta goshinta. Wannan ya faru ne lokacin tana da shekaru biyar,? tazo zata wuce wurin bishiyar rimin cikin gidan su, wani katon bakin kare ya taso mata, yadda ta fasa kara, tare da zuSewa a sume. Ihunta da aka ji ne yasa aka fito a nan a ka same ta, ta suma. Daukar ta Innah tayi,. Lokacin Yadiko Salamatu tana aiki a tsakar gidan,Maman Babangida ta fito dan tana sallah taji ihun. Shine ta fito, Innah ta na shiga cikin gidan ta mikawa Mama Umm-e-Rooman, ta wuce dakin ta.

Bayan ta dauki Umm-e-Rooman, wani farin haske ta fito da mugun gudu, ya caki karen ihu yayi tare da b'acewa, dama tunda Rooman ta fadi karen yake zagaye ta, ganin haka hasken ta kuma bayyana kafin zuwan Innah ta tafi da gudu ta sami karen. Tartsatsin wuta ne ya zube a kan Rooman a hankali ya shige cikin gashin kanta. Innah tana zuwa kuwa ta dauke ta bakin ta dauke da addu'a.

? Bayan Mama ta kaita d'akinta ne ta fara mata alola ta daura da addu'a, cikin ikon Allah ta farka da lafiyarta.

? ? ? ? Haka yasa basu damu, sai da ta fara girma ne aka lura da farin gashin da yake jikin gashin kanta, sai aka Wauki haka a matsayin yar baiwa.

? ? Lokacin da aka kai ta Makarantar kwana, watan ta biyu aka dawo da ita gida sakamakon rashin lafiyar da ta fara, inda suka tashi da addu'a,? asalima Rooman ta taso bata da wadattacen lafiya. Kuma jikinta a buWe, shi yasa da zaran wasu miyagun sun kalle ta ko sun mata wani. Shi kenan babu lafiya, sai dai lokacin da aka dawo da ita gida, suka kai ta numan anan aka? basu magani tare da rufe mata Jikinta. Ta cigaba da zuwa wani privet school anan Mubi.

? A hankali girma ya bayyana a tare da ni, lokacin ina shekara na goma sha bakwai, ina aji biyar na secondry school, dake makaranta a aji biyar ake zana Waec, ina gamawa ban tsaya ba na nufi jami'a, a nan ne samari suka min cak har da masu turowa gida, duk wanda yazo da a dakatar da shi a gaya mishi an yi min miji.

A ka'idar gidan mu, Yarinya ta kai aji biyu na jami'a ake mata aure lokacin Hamma Babangida yana master din shi.? Lokacin wayar salula sai wane da wane, lokacin da aka bawa Baffan Chin okdo karamin jakadar Nigeria a Ukran ya kawo mana kananun waya, da shi muke cikin soyayyar mu.

? ? Lokacin da ya gama aka saka bikin mu, inda aka fara hidima sosai. Tare da fara biki.

? ? ? Lokacin sun koma Yola da zama, akan idan aka gama bikin mu can zamu zauna tunda a Yola nake karatu, aka tsayar da maganar.

? ? * Tun aka fara maganar auren sun yake cikin tashin hankali, domin wasu miyagun mafarki yake.

?? Kuma ya rasa yadda zai yi dan haka ya sami mama ana saura sati Uku bikin su
? ? ?? Tana sallah isha ya zauna a gaban ta yayi shiru, tana idar da sallah tayi addu'o'in, sannan ta zuba mishi ido.
"Babana lafiya kake zaune haka?"
Shiru yayi bai ma san tana yi ba, can kuma ta sake mishi magana kamar wanda yake barci ya firgita.

? ? ?? "Mama Umm-e-Rooman! Anya tana da lafiya?" Duban shi tayi kafin tace mishi.
"Kamar Ya?" Ta mai da mishi tambayar,
"Abin da yasa na miki tambayar, Muna lafiya da ita tace wai kar na Kuskura nace zan aure ta, idan ba haka ba zan mutu." Kallon shi sosai tare da ta??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ke cewa.
"Ban gane ba?" Ta kuma tambayar shi a rud'e.
"Ina nufin ita da kanta tace na janye auren ta ko ta kashe ni, idan bata kashe ni ba zata shafe Tarihi na, ta gaya min haka tun wata uku saura bikin mu, yanzun da ya rage saura sati Uku, na fara wasu miyagun mafarkai, wasu mata suna bina zasu kashe ni,tare da wani wanda ban sani ba.

? ? ? ? ?? Mama ina jin tashin hankali akan haka don Allah meke faruwa."

? ? ? Jinjina kai tayi sannan tace mishi.
"Kasan tayi matsalar rashin lafiya, ina ga shine yake bibiyar ta"
"Ai na zata ko wani abu ne yake damunta."
? ? ? ? ? ?? Ya fada yana mai da ajiyar zuciya, girgiza kai take gabanta yana mugun faduwa. Haka tayi ta bashi shawara, kafin ta sallame shi yana fita ta kira Rooman.
Bayan sun gaisa tace mata.
"Meye ya ke had'a ki da Babangida, har maganar kisa take shigowa?"

"Wallahi ban tab'a cewa zan kashe shi ba, akan me zan fadi haka ga mutumin da yake sona, wallahi ban fada mishi haka ba." Duk yadda mama taso jin ko akwai wani abu amma bata fada ba, har suka yi sallama.

? ? ? ? ?? Bayan ta gama ne ta kira Mahaifiyar ta, suka gaisa. Tace mata,
"Inno ki jawa Barmani kunne wallahi ta sake, wani abu ta faru da Babangida na rantse da Allah kome zai fito har ke zai shafa, dan haka tayi gaggawar fita harkan shi."

? Cikin kwantar da kai da murya ta ce mata.
"Karki damu babu abin da zai faru, ki kwantar da hankalin ki, Allah yana tare dake."

"Ba sai kin gaya min akwai Allah ba Inno na jima da sanin akwai shi...? 300
300? ... Insha Allah'
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A'ichah
+22784506476
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank
#Mai_Dambu
EXQUISITE WRITERS FORUM.
JINI..!
? ?Ya fi Ruwa Kauri?
? *Base on true life story*

*Sadaukarwa ga Family Hasssan Yero Family da Madakin Muri Family*

? ? ?? Mai_Dambu
Talla! Talla!! Talla!!!*

_Akwai turaren wuta dan Maiduguri da Chad

6 / 69