JINI YAFI RUWA COMPLET BOOK BY D AUTA.doc

Author :  Hadiza D. Auta Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   8 / 69

21K to 24K   out of 206.5K words

ji babu iyaka, dan haka suka mai da zancen kamar wasa, dan haka suka watsar da al'amarin tare da korata,

?? Abin mamaki baya karewa, har kusan sha biyun dare babu Babangida babu labarin shi, dan haka aka bazama niman shi.

Ina kwance a d'akina, na ji kamar ana shafa kaina, buWe nayi tare da kallon sama na, matar nan ce. Tana murmushi tare da kai hannun ta ta shake wuyata, kokarin numfashi nake amma baki daya na kasa,domin tayi min mugun shaka ne.

"Ke kamar mallakar mu ce, duk lokacin da kika fara kokarin ganin kin kawo wanda zai taimake ki zamu kashe shi,muyi ta azabtar da ke ta yadda kowa sai ya manta da..."? Hasken nan ne ya bayyana yasa ta b'acewa. Yana zuwa ya d'ago ni zaune yana me shafa min wuyata.

"Me yasa kike da taurin kai? Gashi nan kin ja ya bar gidan dan? haka daga yau kar na kuma ganin wani ya shigo rayuwar ki,muna da rayuwa dake me kyau"? kallon shi nayi bakina yayi nauyi, a hankali ya shafa goshina, komawa nayi na kwanta. karfe biyar na asuba gidan mu ya dauki labarin b'atar Babangida.

?? Duk inda ake saka ran za a same shi babu labarin shi,haka yayi mugun d'aga hankalin mutanen gidan, sai lokacin wasu suka fara daura ayar tambayar su akan fasa auren da nace ayi, dan haka kafin wani lokaci Al'amarin ya girmama a cikin Familyn mu, kananun magana da tashin hankalin ya kara ta'azara, har gani ake kamar akwai abin da nake a boye shi yasa nace ba fasa auren.

? ?? Auran da ba a daura shi ba kenan, domin dai ango ya b'ata, kuma an fasa auren. Kallona Alhaji Babba yayi sannan ya ce min.
"Me yasa jiya kika ce a fasa auren?" Kallon shi nayi tare da zaro idanu waje.
"Hmm! Ban sani ba." Abin yayi mugun b'atawa Iyayena rai.
"Ba zaki gaya mana ba?"
"Wallahi ban san kome ba, ina Hamma Babangida yake?"

Kauuu, Daddy ya kifa min mari, sai da na daina ji da gani, wani shuuu ya cika kunne na, kafin na dawo daga hutun wucin gadin da na shiga na rashin ji.
"Me yasa kika ce kin fasa auren shi?"
Cikin shashekar kuka nace.
"Wallahi ban san kome ba?"
"Zaki yi magana ko sai na shiga jikin ki"inji Baffa Aminu,

?? Girgiza kai nayi tare da cewa.
"Wallahi ban san kome ba" ina fada tare da shashekar kuka,
"Babu kome da zata sani, kawai a Cigaba da addu'a, tare da rokon Allah. Koda zaku Shakara ana abu daya ba zamu tab'a samun kome ba, addu'o'in shine ya dace." Inji Baffan Chindo mahaifin Babangida, rarrafawa nayi gaban shi, ina kuka tare da cewa.
"Ban san kome akan b'atar shi ba, amma wallahi ba zan tab'a cutar da shi ba,Baffa ka yarda dani."
"Karki damu Rooman babu abin da yafi ?arfin Allah,dan haka dai na kuka." Uzurin da Baffan Chindo yayi min yasa na dauke shi a wani aji na musamman, lokacin da ake nawa rikicin a falon Alhaji Babba.

? ? ? ? "Innoh sai da na gaya miki ki jawa yar uwarki kunne,na gaya miki ba sau daya ba, ba sau biyu ba.? Wallahi sai na gayawa Alhaji Babba abin da yake faruwa."

Mama ta faWa cikin kuka domin bata zargin akwai wani dalili ta bangaren Rooman, ta fi zargin Innah barmani.

? ? ? ? ? "Kiyi hakuri wallahi barmani bata da hannu a cikin wannan lamari,. Da kaina na mata magana ta daina maita tun ba yau ba." Ta faWa tare da sauke nannauyar ajiyar zuciya, kafin ta kalli yar nata.
"Ki yarda da ni!" Ta faWa a sanyayye, domin bata da wasu kalaman da zasu yi tasiri a kan Salaha.
"Ki Fahimce ni, wallahi babu hannun barmani"
Cikin shashekar kuka Mama tace.
"Taya zan yarda dake? Bayan kin san ta tab'a cutar yar kishiyar ki baki dakatar da ita ba, kina sane matar lawandi da ta rasu a wurin haihuwa itace ta kama ta.'"

"A'a ita ma taimaka mata aka yi. Don Allah ki bar wannan zancen idan kika cigaba da magana abubuwa zasu fito rai zai b'aci"
"Ina ruwana da b'acin ranaku?? Meye zai dame ni da b'acin ranku ? Akwai b'acin ran da ya kai wanda nake ciki? Akwai bakin cikin da ya kai nake ciki? Yaron da ya dace yana tare da matar shi yau kuka salwantar min dashi. Idan na kyale ku Allah ba zai kyale ku ba, Inno yar uwanrki." Ta mike cikin kuka tare da kallon Mahaifiyarta.

"Ko babu kome zaku kashe shi na ga gawar shi zai fi min sauki akan ace baya nan ba a san inda yake ba." Ta faWa cikin sautin kuka me cin rai. Uwa ce kawai zata fahimci halin da Mama take ciki. Domin da za a ce za a cire zuciyarta da babu mamaki za a iya hango halin da take ciki.

?? Haka ta bar dakin duk da Mahaifiyar ta ce, sai da taji ta tsane ta kamar ta mutu, bata kaunar ganin ta baki daya, a hanyar shigowa suka haWu da Barmani.
"Ayya ashe abin da ya faru kenan?" Wani irin fusataccen kallo ta mata me dauke da bakin ciki da b'acin rai tace mata.
"Wallahi bani da iko kisa ne amma da nice ajalinki"

? ? Daga haka ta nufi gidan Alhaji Babba, ita kuma Barmani ta kalle ta jiki a mace ta shiga dakin Yar uwarta, ta zauna.
"Me yasa ta tsane ni? Tun tashin ta bata kaunata?"
"Saboda halin ki na ganin abu ba zaki barshi ba? Barmani don Allah idan kece kika tab'a Babangida na zuba gwiwata a kasa ki kyale shi"

?? Cikin damuwa da tashin hankali ta ce mata.
"Wallahi ban tab'a? kama kurwan yaron nan ba, don Allah ki bata hakuri bani bace akwai wani al'amari a tare da yarinyar wallahi ban tab'a ba, sai dai maganar gaskiya ba iya nice nake bibiyar ta ba, har da wasu a cikin gidan wallahi kawai nawa ne kawai Salaha ta gani bata ga na sauran ba!" Ta faWa rai a jagule.

? ? ? Kura mata ido tayi sannan ta ce.
"Ance min mayyu munafukai ne, dan haka har dake ban yarda baki da hannu a cikin b'atar Babangida ba, idan wani abu ne don Allah ki gawar shi ku bamu"

Cikin jin haushi tace mata.
"Mun ci mun ki mu bada, idan kika sake min magana sai mu kara samu turo miki gawar kiyi? uwar da zaki yi da shi"ta faWa tare da fita daga dakin tana isa tsakar gidan ta haWu da matar Sha'aibu da tsohon cikinta, a kuwa ta ce mata.
"Lamiyo miko min butar can"
Da sauri ta miko mata tare da bata, ai kuwa ta had'a da kurwanta, tayi gaba abin ta sai da tayi kamar zata shiga ban daki ta kuma juyo abin ta, tana fita ta dauki kurwan ta nad'e a jikin bishiyar maina da yake kofar gidan yayi ta fitar ta. Gidan Alhaji Babba ta shiga jajjanta musu, tana shiga ta samu wasu bakin da suka zo bikin. Kallon matar tayi da yar jaririyar ta, ai kuwa ta kalli yarinyar,. Kallon ta kawai tayi yarinyar ta fara kuka tare da mimmikewa. Bata damu ba ta bar su a nan kawai domin yadda take jin b'acin rai babu abin da ba zata iya aikatawa ba.

? ? ? ? A hankali ta nufi cikin falon Alhaji Babba ta samu suna tattaunawa ta gaida su, tare da basu hakuri da musu nunin su kaiwa Allah kukan su.

?? Duk wani mutumin banza musamman Mayu haka suke da wannan dabi'ar nuna maka suke sun Fika sanin Allah. Yadda take nasihar zaka dauka bata da wata fuska bayan wanda take ado da shi. Sannan ta mike tana faWin.
"Ubangiji ya bayyana shi a duk inda yake."

?? "Amin Ya Allah, Amin dan Alfarman Annabi"? suka fada baki daya, suna jajjantawa. Tana fita ta nufi cikin gidan ta kwashi kurwowin da ta cire bayan ta kulle a mayaninta, wato wani tsuma ne kamar hanky, ta fita a hankali ta nufi hanyar gidan Yar uwanta. Tana shiga tagan su cirko cirko, zasu nufi asibiti.

"Lafiya?" Ta tambaye su kamar babu kome a ranta.
"Lamiyo ce babu lafiya,aka nufi asibiti da ita,"

? ?? "Toh Allah gamu gare ka, ai sai muje ko" ta faWa bayan ta sabi mayafinta.

? ? ? ? Tana fitowa kofar gida ta tsaya jikin bishiyar maina ta dauki kurwan lamiyo, suka nufi asibitin tana zuwa daidai kofar dakin haihuwa ya janyo dutse ta daura akan kurwan Lamiyo, ta zauna a kai, tana me murzawa.

? ? ? ? ? Tun ana saka ran haihuwa har zuwa dare, bata tashi ba, tana zaune a kan kurwan. Dake akwai mutane dayawa a kusa da ita suma kuma sun yi yadda tayi ne,. Wato dauko dutse su zauna a kai.? Kwatsam sai ga wani mutum irin maharba nan, tun daga nesa yaganta. Dan haka ya nufe ta, tare da cewa.
"Iya tashi mana, ai kin gama da ita barta ta sauke nauyin da yake tare da ita." Yadda yayi maganar kasa kasa babu wanda yake jin su yasa ta mike a hankali, tare da cewa.
"Don Allah ka bar maganar a nan"
"Babu abin da ya dame ni, domin wata rana zaki tab'a wanda zai dame ki" yayi wucewar shi,? ko minti biyar bai yi ba, aka sanar da haihuwar Lamiyo, amma ita kan babu. Ga farin ciki ga bakin ciki abin ya d'aga hankalin mutane dayawa, musamman yan uwanta da mijinta.

? ?? Haka aka dawo da gawarta, Kallon juna suka yi da Yakura Adama, domin ta san haka kawai ruwa baya tsami banza,? kallon Barmani tayi sannan tace mata.
"Ba yau na fara jin labarin wacece ke ba, amma na yau ya kara tabbatar min da cewa zaki iya aikata kome, ki fita a cikin gidan nan kafin na sanar musu cewa kina da Hannu a abubuwan da suke faruwa!"

"Adama meye laifina? Ina ruwana da abin da yake faruwa?" Kau Yakura Adama ta dauke ya da mari, tana nuna mata hanyar waje, juyawa tayi sannan ta ce mata.
"Insha Allah sai na rama abin da kika min domin bana yafiya baya manta ranar daukar fansa."

?? "Kije kiyi duk abin da yayi miki algulgunguma munafuka me fuska biyu, ja'ira kawai wacce bata san akwai Allah ba. Ubangiji sai ya saka mana. Kuma abin da kika daure ki sake ko kuma na gayawa Ahijo," tana kiran sunan Ahijo ta kalle Yakura Adama tana mamaki.
"Toh ina ruwana da wani abu? Kawai zargina yake." Sake turawa ta Yakura Adama tayi tana fadin.
"Ba zaki sake ba kenan?"
"Amma Adama wannan cin fuska ne da cin zarafin Yar Uwata." Inji Yadiko Delu,
"Wallahi ta sake ko kuma na tura a kira ahijo" ta faWa da karfi,
"Jikokina ma baki bari ba, balle na wasu, Adama kin yi min dai-dai" inji Yawuro Uwargida Alhaji Babba, kakar mu.

Yadda matan suka had'e mata kai tare da niman fallasa asirin ta, yasa ta ciro mayaninta tare da warware sai ga kuda suna tashi sama, tare da kama gaban su.
"Fita mana a cikin zuri'ar mu, karki lalata darajar mu, domin zama dake kamar zaman kura ce a garken awaki"

? ?? Gyada kai tayi tare da cewa.
"Sai na rama"
"Insha Allah ba zaki iya mana kome ba, domin Allah yana tare da mu"

? ?? Zata fita muka hadu da ita ban san me yake faruwa a cikin gidan ba, kallona tayi sannan tace min.
"Sannun kin ji" ta kai hannunta tare da tab'a hannuna, da sauri ta cire hannun ta, tana kallona tare da cewa.
"Wai! Lallai ma kuwa, gidan Madakin Muri da Hassan Yero zasu yi aiki babba, toh Allah ya tishe mu Alkhairi"

? ? Gyada kai nayi tare da shiga cikin gidan, na samu suna tattaunawa. Ban saurare su ba, na a shige dakin Yakura Adama na kwanta ina kuka kasancewar itace Kakata da ta haifi Uwata. Yawuro Balkisu ta haifi Ubana,. Shigowa suka yi tare da maimaita abin da ya faru na mike zubur.
"Ai kuwa ta rike hannu na ta sake yanzun da zan shigo." Na basu labarin abin da ta fad'a.

? ? "Lallai ma! Dole na kai ta wurin Ahijo, domin ba zan kyale haka ba, zata iya cutar da ita babu gaira babu dalili."

?? Kallon su nake a hankali,kafin na kumshe idanuna,nace musu.
"Naga tsoro a idanunta ba zata iya min kome ba, Allah yana tare da ni,duk da wani sharrin ta zai koma kanta.? Damuwata Hamma Babangida" na fada hawaye na zuba daga idanu na. Nan kuma jikin su yayi masifar sanyi,suna kara jin tausayina, rarrashina suna fara, amma haka bai hana ni kuka kamar me ba, ji nake kamar bani da gata, kome ya tsaya min cak.
#Mai_Dambu
https://chat.whatsapp.com/GhM2louNlbeJSgwVtluonQ
EWF.

JINI..!
? ?Ya fi Ruwa Kauri?
? *Base on true life story*

*Sadaukarwa ga Family Hasssan Yero Family da Madakin Muri Family*

? ? ?? Mai_Dambu

BABI NA GOMA.

?? Duk yadda lamarin yake sai da ya wuce tunanin kowa, domin a cikin kwanaki uku babu labarin Hamma Babangida babu dalilin shi. Kwanciya jinya Mama tayi nima a tsatsaye nayi nawa, kafin a cika sati daya labarin Hamma Babangida ya sha ruwa. Mun yi kuka har mun godewa Allah.

?? Dan haka muka dawo Yola bayan mun bar Mubi, dama kuma a nan nake karatuna, sannan na dawo, gidan su Hamma Babangida na? cigaba da zama, a hankali kome ya sauya mama da yan uwan shi basu tab'a fushi dani ba,asalima kyauttta min suke kamar nice Babangida.

? ? ? Kwanci tashi asaran me rai, Babangida ya cika shekara daya da barin gida, ni kuma ba kammala karatuna na degree, a lokacin manima sun min caaa. Dan haka Alhaji Babba ya saka aka kira ni lokacin da na dawo hutun kafin a tura mu bautar ?asa.

? ?? Zama nayi a gaban shi ina zaune, Hamma Yusuf ya shigo shima ya zauna.
"Gashi nan ku daidaita kanku, tun bayan b'atar Babangida naso miki magana, domin shi ya bukaci haka, toh yanzun dai gashi nan da kan shi"

?? Kaina a sunkuye na cewa Alhaji Babba,
"Alhaji na zata zaka bari har Hamma Babangida ya dawo ne, don Allah kayi hakuri"

"Toh abin da na gani shi nayi, Babangida ba abokin rayuwarki bane, shi yasa na zab'a miki Yusuf" ya fada cikin lallashi da lalluma,tare da kalmomin masu dadi da daraja.

? ? ? ? ? ? ?? Mik'ewa yayi tare da bamu wuri, kai na a sunkuye. Hamma Yusuf ya gyara zaman shi tare da isowa gabana.
"Rooman" d'ago kai nayi na kalle shi, kafin ta Cigaba da cewa.
"Na jima ina son na tinkare ki da maganar soyayya, toh Allah bai nufa ba."

?? "Gwara da baka min magana ba, domin bana son ka" na fada tare da kallon shi kwalla na zubo min.
"Mutumin da nake so ya b'ata, taya zan zo wani bayan shi, taya zan kula wani namijin bayan shi na ajiyewa rayuwata don Allah ka hakura da ni"

? ? ? ? ? Murmushi yayi sannan ya ce min.
"Ina sonki zan kuma jure duk abin da zaka min"
"Ba zaka ka iya ba"

? ? ?? Na mike zan fita, ya dawo dani gaban shi tare da kura min ido.
"I love You"
"Na jima da jin kalmar a bakin Hamma na" na gaya mishi tare da kallon shi, hawaye na zuba min,

? ?? Sake hannu na yayi sannan ya barni na tafi.
Tun daga ranar ya addabi rayuwata, hidima kala kala. Shima dan cikin dangin mu ne, dan haka aka yi na'am da zancen shi. Kafin kace kwabo kowa yasan da soyayyar mu.

? ? Tun da aka fara magana manyan mu suka tsayar da magana. Shi kenan mafarkai tare da wani irin damuwa ya shige ni.

?? ....
Suna zaune da abokan shi a Yola wani gidan cin abincin,? bayan sallah isha, domin abin da ya kawo shi wurin cin abinci, kasancewar a Yola yake da aiki.

? ? ? ? Hango ta yayi ita da wani mutum,? sanye take da wando iya gwiwarta sai wani riga bai kai cibiyarta ba, kallon ta yayi daga sama har kasa zuciyar shi tana tsannaninta bugawa.

? ? Fita yayi cikin abokan shi ya bi bayan ta, koda ya shiga bai gansu ba, dan haka ya fito yana kyautatta zaton gizo ne, ya dawo wurin su ya zauna ya gasun fito.

?? A hankali ya taka tare da nufar inda suke, har sun tadda motar su, dan haka da sauri ya shiga nashi tare da bin bayan su, sai da suka yi tafiya me nisa, kafin suka tsaya,? zuba musu ido yayi sannan ya fito,koda ya isa jikin motar gaban shi ne ya fara faduwa, sabida glass din motar a bude take, kana jin muryan na ciki. Isa yayi tare da bude motar. Yaji an shake wuyar shi.

?? Tare da fito???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?war wani jibgeggen halitta, sosai ya rike wuyar shi.
"Ka rabu da ita ko kuma na kashe ka har lahira" ya fadi haka tare da buga shi da kasa, sai da ya daina numfashi, bude idanu shi yayi tare da rike wuyar shi da yake jin numfashi na mishi wuyar shaka.

? ? ? ? ? ? ? ? ? Daidai kunnen shi aka ce mishi.
"Ba mafarki bane, ka kiyayye kanka akan Rooman"? da sauri ya tashi zaune, domin bai zaci haka ba.

? ?? Bai sauka a gadon domin yayo alola tare da niman tsari ba, gyara kwanciyar shi yayi tare lumshe idanun shi. Aikuwa wani barcin yayi gaba da shi. Ko minti talatin bai yi ba, wasu bakakken karannuka su uku suka taso shi a gaba da gudu ( Mayu sun fi amfani da Mage da Kare, sun fi kwarewa akan tsafin su da suddabarun su akan wadannan halittar.).

? ? ?? Dan haka koda yayi gudun shi, a wani rami ya tsaya tare da share gumin da yake keto mishi, da farin ciki ya kalli Rooman da tazo fuskar ta, babu walwala tana isowa gaban shi ta kalle shi tana faWin.
"Hamma na gaya maka bana son ka, Hamma Babangida nake so, gashi nan yana ramin nan dan haka duk wanda yazo matukar ba ciro min shi zai yi ba, har abada ba zan tab'a son shi ba," tana gama fadar haka ta tura shi da dukkan karfinta ya fada ramin.

? ?? Wani zabura yayi da mugun sauri zai tashi aka shiga daure shine. Kallon saman kan shi yayi wannan mummunar matar ce.
"Baka isa ba, idan kana son ranka da lafiyar ka, toh dole ka rabu da ita ko kuma mu yanka ka mu zuba namar ka a

8 / 69