JINI YAFI RUWA COMPLET BOOK BY D AUTA.doc

Author :  Hadiza D. Auta Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   5 / 69

12K to 15K   out of 206.5K words

kanta kasa kafaffunta a sama gashin kanta yana lullube da fuskarta, a hankali ta daidaita tsayuwar ta a kaina, kafin ta shake wuyata tana zuba min wasu irin abu da suka fito bakin ta.

? ? Kai mata duka wani irin haske yayi ta fadi can gefe, tana muzurai, wani mutum na gani fari fat har yana kore kore, farin gashin kan shi ya lullube fuska shi.
? ? ? Shafa kaina yayi tare da cikina, yana me kallon fuskana, yadda nake zubda hawaye ya dashi saka hannun shi ya dauke hawayen yana mi b'acewa.

? ? ? ? ? ? Tun daga lokacin ban kuma samun lafiya ba, sai dai mugayen mafarkan da nake yi, wani lokaci ina son nayi amai amma dai na kasa ko naji abu yana yawo a? cikina, haka yasa kullum sai nayi yunkurin amai, tun ina zuwa aiki har MD din mu ya bani hutun nayi jinya, ganin Haka Baffa Chindo, yayiwa Baban Abba magana yazo ya duba ni, yana zuwa ya kare min kallo ya ce musu.
? ? "Gaskiya al'amarin Rooman akwai matsala, dan hakan ku had'a mata da na gida, domin da alamun abin da yake boye ne zai bayyana kan shi."

? ? "Meye yake boye da bamu sani ba?" Kallon shi suka yi bayan sun tambaye shi.

"Akwai Duhu da Haske a tare da ita, dan haka ban san yadda zan muku bayani ba, amma akwai banbancin a tsakanin mu da mugayen mutane" ya gaya musu bayan ya had'a min magani da ya bukaci a kawo mishi.

? ?? Kasa magana suka yi dan bayan fitar shi, kawai da minti biyar aka shigo da sauri yayi hatsari Allah ya takaita bai mutu ba, amma ya jikkata. Baffa Chindo ya dauki nauyin jinyar shi da dawainiyar gidan shi, yana asibitin ya bawa Baffa Chindo karin hasken a maida ni gida ayi jinyar a can. Shine dalilin da aka dawo dani gida. Kafin a dawo dani Baffa Chindo da Daddy suka gayawa Alhaji Babba, kuma dake yana da kyakyawan fahimta da kanshi ya samu malam Haruna, da yake unguwar mu. Yayi mishi bayani, shiru dattijon nan yayi sannan yace mishi.
"Kayi hakuri, bayan sallah isha zan maka magana"

? Aikuwa haka ce ta faru,bayan sallah isha da suka haWu ya mika mishi hannu suka gaisa.
"Alhaji Hashim! Yarinyar nan tana zagaye ne cikin tashin hankali. Ban san yadda zan maka bayani ba, amma akwai fararren al'amari a kan ta, wanda ba sabo bane. Dan haka maganin da zamu mata da wanda zamu bata bai kai wanda Ubangiji zai mata ba. Idan aka yi hakuri waraka yana nan zuwa gare ta amma sai an yi hakuri an kai zuciya nesa."

Abin da ya faru kenan.

? ? ....
Takowa malamin yayi tare da Almajiran shi, suka saka ni a tsakiyar su, sannan aka kawo ruwa da buta aka min alola, sannan aka zaunar da ni bayan an jingina baya na da jikin kujeran falon. Suka fara addu'o'in kafin aka fara karanta ayoyin ruki'a daga Alqur'ani me girma.

Tun da aka fara nake zaune, ina jin a mai, amma babu wani abun da ya shafi jikina. Shi kan shi Malam Haruna yayi mamakin yadda abin ya faru, domin ko jiya da suka yi magana da Alhaji Babba sai da suka yi artabu da miyagun, amma yau gashi nan suna addu'o'in babu alamar wani shaidani.

? ? ? ?? Yunkurin amai da nake yi ne, yasa suka dakatar da karatun,? ganin na kasa kome yasa suka cigaba da karatun su, wani irin zufa nake jikin yana rawa kafin na fara kwara amai duk da banci kome ba, haka nayi ta amayar da wasu irin abu.? Sai da nayi sosai kafin na koma na jingina da kujeran ina ajiyar zuciya. Yan uwan Daddy abin ya basu tsoro domin amai ne bakikkirin, sai motsi yake tare da juyi, aka Cigaba da karatun ruki'a sai da suka ga na fara barci suka kyale ni, Malam Haruna Yasaka hannu ya yayi Bismillah ya kwashe dukkan aman ya zuba a tire.

? ?? Sannan ya fita bayan ya haWa mana magani da wanda kullum za a na kawo min ina sha, da wanda za ayi min hayaki goshin magarib, lokacin ana kiran sallah farko za a yi min. Sai wanda kullum za a min salala da garin jar dawa. Da ruwan rubutun da zan na wanka da shi.

? ? ? ?? Sanan yayi musu sallama, ya fita.. kallona Alhaji Babba yayi sannan ya ce min.
"Rooman a ina kika kwaso aljanu haka?"
**
Asalin abun da ya faru..
*Wannan book din na kuWi ne*
+2347035133148 Zahrah Addah Ramla or Nijar+22784506476.? 300 500CF
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank
#Mai_Dambu

*Ayi hakuri da yanayin Hausar da nake amfani dashi domin ni yar Bauchi ce kuma Hausar Bauchi nake amfani dashi! Kuma kowa yasan Bauchi baya cikin Hausa Bakwai=?O??? EXQUISITE WRITERS FORUM.
JINI..!
? ?Ya fi Ruwa Kauri?
? *Base on true life story*

*Sadaukarwa ga Family Hasssan Yero Family da Madakin Muri Family*

? ? ?? Mai_Dambu
*Talla! Talla!! Talla!!!*

_Akwai turaren wuta dan Maiduguri da Chad Ubansu me sanyin dadi idan ka saka sau daya sai ka kuma nima idan har kin yarda ke ?asaitacciyar mace ce me aji jaraba turaren wuta na zamani me yayi ba iya nan ba hatta? Humra me sanyin dadi akwai. Ga masu bukatar bikin ko amaryan karni tuntube Aishah Shuwa da kanki zaki bani labarin kamshi...+234 812 535 5554 sai an gwada akan san ba kwarai_


BABI NA SHIDA.


Tushen Labari.

Fadar Sarkin Gombe shekarun baya.

?? Cirra ya?e jikin shi yana rawa, karkarwa kuwa, kamar wanda aka watsa mishi ruwa, yana kallon yadda suke zarta da hukuncin bisa rashin adalci, duk da yaji labarin Mai Martaba Sarkin Gombe bai da lafiya Amma yana ganin tsagwarancin son zuciya da son kai a kwayar idanun su.

?? "Malam Kamal muna baka hakuri zamu bawa dan uwanka Malam Hatayuddeen Sarkin Malaman Gombe, tunda shi ya fi cancantar zama sarkin Malamai."? D'ago kai yayi sannan ya ce.

"Taya ina sama dashi zaku zab'i tozartani? Bayan kunsan shi din ba toh amma maganar Gaskiya wannan ba hukuncin adalci bane domin ni na san sarautar Sarkin malamai da gidan mu ya dace."
Shiru suka yi suma sun san gaskiya ya fada, wanda zasu bawa Sarkin Malamai din yana da nashi matsayin a gefe guda, sabida son zuciya irin tasu yasa suka dauki mu?amin suka bashi.

? ? Ba dan kome ba sai dan ya kasance Dan Boko, shi kuma bai yi karatun boko ba, amma a haka sai yayi hakuri tare da mik'ewa yana faWin.
"Babu kome, kowa rabon shi yake tsira da shi." Daga haka ya fita daga fadar.

? ? Shi kan shi Malam Hatayuddeen bai san cewa shi zasu bawa Sarkin Malaman ba da ba zai amsa ba, domin Y'ayan Maza suke da shi da Kamalu, kuma basu wuce sa'anin juna ba, kasancewar tare suka taso, banbancin su da Malam Kamal shine shi yayi karatun boko, domin da karfin tsiya aka tafi da shi karatun boko, shi kuma Kamal an saka shi ya gudu. Kasancewar a lokacin shigowar turawan biritania kasar Nijeriya,? kama yara suke da karfin tsiya ana tura su makarantar boko, sai gashi Hatayuddeen har kasar Birtaniya yayi karatun shi sosai a gurin.

? ? Lokacin Bauchi da gombe suna hade da juna.

? ? Lokacin da Malam Kamal ya dawo gida, ya fadawa yan uwan shi halin da ake ciki, sun yi bakin ciki. Matuka gaya amma sai suka dauki haka a matsayin ?addara ce. Bayan haka da dare sai ga malam Hatayuddeen har gida yazo.? Ya gaida mutanen gidan tare da shiga wurin dan uwan shi ya zauna akan buzu yana faWin.
"Yero kayi hakuri, wallahi ban san haka zai faru ba, da ban zo Gombe ba."

? ? Murmushi yayi sannan yace mishi.
"Moddibo kenan, wallahi babu kome. Allah ya nufa kai ne zaSaSSen, mu ai faffutika muke Allah ya tayaka riko"? inji Malam Kamal Yero, kasancewar family daya ne amma kuma suma suna da lakabin su.
? ? ? Kowani family da inkiyarta.? Shiru ne ya gifta tsakanin su, kafin Malam Hatayuddeen Moddibo ya ce mishi.
"Idan nayi kuskuren ka gyara min karka barni nayi ta lallube cikin duhu, ka haska min fitilar da take hannun ka, don Allah karka barni haka."

? ? ? ? ? "Insha Allah zan yi ?o?arin tayaka riko, domin kazo da abu me girman gaske ne"
"Nagode sosai"

? ? ? ? Haka suka yi hiran kamar babu abin da ya had'a su, a gefe guda akwai wani dan uwan iyayen su, kasancewar shi din Kamar Uba yake musu, dan haka shima yana niman a bashi sarautar Sarkin Malaman,sai gashi an zab'i Hatayuddeen, sanin cewa Hatayuddeen bai san kome akan sha'anin addini sosai ba, yasa shi shigewa Hatayuddeen.

? ? ?? Tare da mishi saran b'oye, yadda ba zai fahimci waye shi ba, ya boye asalin shi ya bayyana wata fuska na daban, tun da jimawa basu shiri da Malam Kamal Yero, basu ga maciji duk da kuwa dan uwan Iyayen su ne, amma baki daya basu shiri da Malam Kamal Yero. Sabida yayi laifi har sau biyu ana kawowa Baffa Hatayuddeen Adamu Moddibo karan shi, shi kuma ya kawo karan wurin Alhaji Abubakar Yero mahaifin Malam Kamal Yero.

? ? ? ? Sun same shi da maganar yayi rantsuwa duk wanda ya kuma mishi magana a bakin ran shi, Baffan Hatayuddeen ya ji tsoro sosai kasancewar shi ne babba a gidan su, tunda babu iyayen su. Sai ya ja Abubakar Yero tare da cewa.
"Kaga kyale shi ba zai tab'a ji ba, idan muka matsa mishi hatsabibi ne zai iya cutar da lafiyar mu har da rayuwar mu ma."

? ? Gyada kai yayi sannan ya ce mishi.
"Toh shi kenan, nayi shiru." Haka suka zuba mishi ido, tunda su ne manyan. A irin wannan abubuwan da yake aikatawa har aka tab'a kai karan shi gidan Sarki, shi ne aka kira Sarkin Malamai wato Alhaji Abubakar Yero ya tare da Alhaji Baffan Hatayuddeen Moddibo, suka nufi gidan sarki aka yi magana, koda aka gama tare da koran shi a cikin gari. Shine ya kulla ci yan uwan shi tare da alkawarin dai ya kashe su har lahira.

?? Kuma alkawarin shi bai fadi banza ba, sai da ya kashe su.? Shima gidan su Babban Family ne, shi yasa Malam Kamal ya rike shi a ran shi har kwanan gobe, baya magana dashi domin an dakatar da shi ne da shima ya rama kisar da aka yiwa Baffan su.

? ? ? ?? Domin lokacin da hankalin shi dan yana samartaka abun ya faru. Dan haka ko kanen shi ya haramta musu soyayya da yaran gidan Baffa Lameer.

? ? *
? ? Bayan kwana takwas,sai ga sako daga fadar Mai martaba,? dan haka bai yi kasa a gwiwa ba, ya isa fadar yana shiga ya samu Baffa Lameer, ya gurfana a gaban Sarkin Gombe ga Malam Hatayuddeen Moddibo zaune.

? "Mai martaba ina son la shiga tsakanin mu da Malam Kamal Yero, domin yayi alwashin sai yaga bayan Hatayuddeen Moddibo, sabida Sarautan da aka bashi. Dan haka kuyi mishi iyaka da Hayatu, domin ina da shaidar shi ya kashe mahaifin shi da Mahaifin Hatayuddeen, idan kuka sake zai aikata kome.

?? Ram Malam yayi masifar b'aci jikin shi yana rawa, ya mike tare da riko wuyar Baffa Lameer.?? Sai da fadawa suka taru a akan shi kafin ya sake shi. Mai martaba ya ce.
"Malam Kamal Yero, meye yayi zafi haka? Da har zaka yi kisa akan sarauta, toh na maka iyaka da ?asar gombe, ka tafi ka bar min yankina. Idan har na ganka tabbas za a kashe ka" wannan kalaman yasa shi mik'ewa tare da cewa.
"Nagode" ya saka kai ya fita, jiya matar shi Harira take gaya mishi Kanwar shi Labaraba tana tare da Bashir.? Kanin Hatayuddeen ba karamin farin ciki yayi ba,ya dawo gida kenan suna tattauwana aka kuma taso shi a gaba da tashin hankali. Da yasa shi komawa cikin gidan aka tattara tare da barin garin gombe.

? ? .Da asuba suka bar garin gombe,sai da suka kusan mubi aka fahimci babu Balaraba a cikin su, ita kuma an sake mata sunan ne kasancewar ta fara kal aka haife ta, kanwar shi da suka Uba daya ce, mahaifin su ya rasu ya bar uwarta da karamin cikin ta, kasancewar Mahaifiyar su Malam Kamal ta jima da rasuwa, tun suna yara ta rasu,

Su shida ne a cikin dakin su, sai dakin Matar baban su, Yara biyu. Balaraba itace Babba, sai Sabitu. Ganin kamar ta bata ne, Malam Kamal yabi sawunta, har ya shiga gombe babu labarin ta, dan haka ya dawo tare da bawa mahaifiyar ta hakuri suka cigaba da tafiya, basu zame ko ina ba sai garin Muri da yake cikin Mubi.

? ? Dake suna da yan uwa maza da mata dangin su. Yasa suna komawa garin basu jima ba..aka. Aurar da Jamai ga Dan Gwaggo Hakama Harisu. Shine aka bashi Madakin Muri, kasancewar Malam Kamal shi ya kafa garin Muri.

?? Sannan ya bawa yan uwan shi sarautar muri.

? Bayan shekaru.

Zuri'arsa ta kuma bun?asa, tare da taimakon Allah,? suka rike auren zumunta, kuma wani ikon Allah babu wanda zai ce maka an tab'a samun matsala.

Kanen shi biyar nan duk sai da ya had'a auren ?a?an su da juna.? Sunayen kanen shi ya had'a da Aminu, Nasir, Muhammad, Habibu, Hauwa'u, Fatimah, sai ya had'a dan Aminu da Yar Fatima, Yar Habibu da Dan Muhammad,Yar shi da Dan Nasiru. dan Hawwau da yar Sabitu.

? ?? Dangin su baki daya sai ya zamana auren zumuncin yayyi karfi a cikin zuri'ar. A hankali suka hayayyaf can gidan Madakin Muri aka samu yan mata da Samarika dan haka suka ci-gaba da had'a auren zumuncin su.

? ? **
Bayan wasu shekaru.
Allah yayiwa Malam Kamal rasuwa inda ya kuma jadadda musu karfin zumunci, da kuma bai yarda su koma Gombe ba, ko suyi alaka da yan gombe.

?? Gidan Harisu kasancewar shine Madakin Muri,sai aka samu auratayya a tsakanin gidan shi da gidan Sarkin Malamai, wato gidan malam Kamal.

? ?? Suma kenan malam Kamal sun rasu bayan sun hayayyafa. A hankali manyan suna yi ta karewa, ana kuma Cigaba da had'a auren zumunta. Har bayan shekaru casa'in cif.
Alhaji Hashim Hassan Yero.
Kakan shi shine Malam Kamal Yero. mahaifin shi Hassan Yero, shine Wan autar Malam Kamal Yero domin su biyu aka haifa, Ya macen ta rasuwa.

? ? ?? Hajiya Yawuro ita kuma Yar Jikar Habibu Yaro ne,? Kabiru Muri ya haife ta. Dan su karfafa dangantakar su, aka bawa Alhaji Babba ita domin shi ya kasance Babba a cikin Familyn.
Ya haifi yara tara.

Chindo wanda sunan shi Aliyu, sai Mahaifin Rooman Yakub, sai Zainab tana aure a gidan Madakin Muri,? sai Jamil wanda yake soja ne yana can kudu yana auren yar baffan shi, Sai Lawizah tana nan a cikin garin tana auren Jikar Aminu,, sai Nusaiba tana aure jikan Fatimah amma ta rasu shekara biyu kenan, sai Balkisu. Tana auren jikan Sabitu, sai Hassana da Hussainah,? Hassanah tana auren Jikar Muhammad, suna cikin gidan, Hussainah tana auren a gidan Madakin Muri, sai gambon su yana Abuja yana auren Kanwar Mariyah.

? ? ? ?? Yakura Adama Kanwar Alhaji Babba ce, ita kuma aka bawa jikan Harisu wato Alhaji Muhammad Madakin Muri. Ita ta haifi Mariyah.

Baki daya family din auren zumunta suka fi kullawa.
? ?? **
Kasancewar Chindo shine babba dan Alhaji Babba, sai aka bashi auren Mama ita ta haifi Babangida wanda sunan shi Hashim ne, sai kanwar shi da take bin shi, Jiddah sai Shahid da Hisham sai Fanan. Kasancewar Ita Mama Yar Yadiko Delu ce, ita kuma Mariyah Yar Yakura Adama ce.

? ? ? ? ? Gidan Yakub kuma an had'a shi aure da Mariyah, Kanwar Maman Babangida ce, sun jima basu haihu ba. Sai da suka tafi gyambo bikin wata yar gwaggon su, wacce shima mijinta kanin su Alhaji Babba ne, a gidan bikin ana? sha'ani wata ta ta shigo cikin gidan.
Kai tsaye ta nufi wurin Mariyah,. Mika mata hannu tayi.
"Bani biyar" kallon mutanen wurin tayi, kafin ta ciro biyar ta mika mata.
"Arzikin mijin ki zai lalace amma sai dai zan baki damar zab'i haihuwa ko Arziki?"

Kallon matar tayi sannan ta kalli Maman Babangida,? da take goyon Babangida lokacin, dan yana yawon shi bai wuce shekara uku ba, sunkuyar da kai tayi.
"Shalle baki ganin bakuwa ce, don Allah ki kyale ta Y'ata ce."

"Sumaye! An rufe mata bakin haifarta ce. Sabida arzikin mijinta. Sai dai basu san cewa Allah ya halicci irin mu a doran kasa ba. Ba zata haihu arzikin da yake da shi zai lalace. Domin ba ta Allah bace shima tura mishi aka yi. Dan haka ki zab'a idan arziki kike bukata na yi tafiya ta, idan kuma Haihuwa kike so tsaya muyi magana."

? ? Dayawa mata a wurin kansu rabuwa yayi wasu na cewa ta zab'i dukiya ta bar haihuwa wasu na cewa ta zab'i haihuwa ta bar dukiya. Wata dattijuwar mata ce ta fito ganin yadda jikin Mariyah yake rawa tace mata.
"Meye dalilin ki Shalle? Idan ta zab'i daya ta bar daya?"
"Idan ta zab'i dukiya, har abada ba zata tab'a haihuwa ba, idan ta zab'i haihuwa har abada ba zasu tab'a tsiya ba,domin zasu fi karfin kome mijinta ba zai yi Maula ko roko ba, amma arzikin shi ba zai wuce wanda zai dauki nauyin iyalin shi ba. Domin a yanzun ai bin shi ake yayi aure yaki yi."

? ? ? ?? "Toh na zab'a mata haihuwar!" Ta faWa tana kallon yadda Mariyah take sauke ajiyar zuciya.
"Yawwa Insha Allah zaki haifi abin da zai janyo miki arziki har cikin dakin ki, sai dai kuma zaki tashi a tsaye, domin ana bibiyar rayuwar ki,? gidan ku akwai masu bibiyar ki. Ba iya gidan mijinki ba, har gidan iyayen ki"

?? Kallon Maman Babangida tayi tare da cewa.
"Sannun da ?o?arin dakatar da wasu abubuwan, sai dai kiyi hakuri. Duk tsanani yana tare da sauki." Ta juya kan Babangida tana shafa kanshi.
"Yaro, ki yawaita mishi addu'o'in. Allah ya kare shi mugun ji da mugun gani" daga haka tayi ficcewarta daga cikin gidan.

Nan suka shiga hiranta da yadda take taimakawa mutane, ita dai Mariyah bata yi magana ba, tana dai kallon abin kamar almara, baya bikin sun dawo gida ne, wannan watar tayi b'atar wata, tun daga lokacin daga ita sai Maman Babangida

5 / 69