JINI YAFI RUWA COMPLET BOOK BY D AUTA.doc

Author :  Hadiza D. Auta Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   9 / 69

24K to 27K   out of 206.5K words

cikin tukunyar mu ta tsafi."

? ? Girgiza kai ya fara tare da jin lallai dole ya rabu da Rooman, amma taya?

? ? ?? Kai mishi cafka tayi ya rintsa idanun shi, tare da fasa ihu kamar ba namiji ba, sai da mutanen gidan suka taru a dakin shi. Ya tashi jikin shi yana rawa.
"Lafiya?" Yadda yake haki zai baka tsoro,.dan haka kamar wanda ake razana ya shiga waige waige, tare da sauka a gadon.

? Kafin gari ya waye, ya fara zabura kamar wanda ya soma haukacewa. Dakyar aka samu yayi barci. Yana kwanciya kowa a falon sai kallon shi yake ya farka da ihu.
"Don Allah Karku kashe ni,wayyo Allah na, wallahi na fasa auren Rooman don Allah Karku min kome wallahi na fasa"

?? Nan take kowa ya fahimci abin da yake faruwa. Dan haka babu b'ata lokaci aka nufi falon meeting da shi, tare da kallon yadda ya koma kamar Mahaukaci karfi da yaji. Ina sallama ma shiga falon ya mike tare da niman maboya,. yana faWin.
"Wallahi na fasa auren ta, na rantse da Allah na fasa, idan na kuma ki kashe ni." Sake baki nayi ina kallon shi.

? ? ? Takawa nayi tare da nufar inda yake.
"Wayyo Allah na, na mutu na lalace wallhi ba zan kuma ba, don Allah ki kyale ni, na fasa auren ki nace" ya zube sumamme a wurin, kallon shi nayi tare da zuba gwiwata a kasa ina me jin wani irin bakin ciki mara iyaka.

? ? ? ? ?? "Tashi ki bar min Yarona idan ma maita ce ki tsallaka shi, amma aure kan an fasa ba dai wannan kurwan ba." Inji Innah Yarinyah, mik'ewa nayi tare da komawa gefen guda na zauna tare da kifa kaina a tsakanin cinyoyina, baka jin kome a falon sai shashekar kuka na, babu wanda yayi min wani abu ko magana. Sai ma tashin hankalin da aka shiga yayi da wasu suke ganin ai ba mamaki maita ce naci shi yasa nake wannan lamarin, amma idan maita ce ai da tuni na gama da yan dakin mu.

Wasa wasa aka samu rabuwar kai a cikin Ahalin mu,duk sabida ni, yayin da wasu suka yarda maita nake wasu basu yarda ba, musamman Yaran Alhaji Babba, babu kamar Baffa Chindo, domin shi har cewa yayi zai kai mutu kotu idan aka kuma jifana da kalmar maita.? ? Ganin haka yasa na samu sau?in tafiya bautar ?asa,? a can ma manime ne suka fito rututu.

? ? Amma ban d'ago kai na kalle su ba, har na gama bautar ?asa. Na dawo Yola. A nan muka hadu da Khalid Dan Yayan Yadiko Salamatu.? Aikuwa ya makale min kamar zai cinye ni. Naki kula shi naki yarda mu kulla ala?ar soyayya, asalima sai na gaya mishi gaskiya akai na.

? ? ? Amma dake soja ne bai da hankali sai gashi yace ya ji ya gani, koda maganar ta shiga cikin gidan mu, ai Gwaggon shi tayi tsalle ta dire tace ba jinin ta ba.

? ? ? Allah ya taimaka dai haka zancen shi ya lalace.

Ina zaune haka Baffa Chindo ya nima min aikin bank. A lokacin ina da shekaru kusan ashirin da bakwai, dan haka kwatsam muka hadu da, Adham dan gidan Baba Haidar.? Yadda bawan Allah nan ya nace tare da nuna zai iya aka kyale shi.

? Sai dai me! Ko wata biyu ba ayi ba, ya fasa niman tare da turo min zungureriyar sakon na bani hakuri akan ya fasa aurena, dariya nayi domin zuwa yanzun bana jin kome akan haka, wannan shine namiji na hudu da aka saka aurena da shi.

***
Sai da na shekara uku cif babu wani mafarki ko wani abu da zai nuna akwai wasu masu bibiyar rayuwata. Sai ga Hamma Khamil.

?? Kamar da wasa dake an ga babu abinda ya kuma faruwa, kuma lokacin Innah ta dage min da niman taimako, musamman da taga ya fito ta shiga niman taimako ta ko ina. Allah da ikon shi sai ga maganar aure ya tabbata har mun shirya kan mu.

? ? Dake ba mazaunin kasar bane yana kasar Russia ne, dan haka yayi al?awarin idan aka yi bikin mu zai wuce can ya nima min aiki daga baya nabi bayan shi.

? ? ? ? Alhamdulillahi kowa yaji dadin samun lafiya ta, kuma mutum ne da yake da kokarin ibada da addini, ko mafarki bai tab'a yi ba, idan ya kwana biyu a mubi zai dibo jiki yazo Yola, haka muke fita tare da yawo. Akwai ranar da muka fita tare da da zama a wurin shakatawa, kallona yayi sannan yace min.
"Akwai abin da yake damunki?"
"Babu idan ma akwai toh Hamma Babangida ne" na bashi amsa a takaice,
"Har yau babu labarin shi?" Ya tambaye ni.
"Eh babu gaskiya sai dai muna kyautatta zaton yana raye domin duk lokacin da nayi addu'a akan shi ina jin kwarin gwiwar yana raye ban tab'a jin yana mace ba"

?? "Me yasa baki manta dashi ba?" Ya tambaye ni, murmushi nayi sannan na gyara zama ina kallon shi.
"Kai ka fara sona ne bayan kaji labarina da yadda nake, ka ganni da idonka sai ka ji na burge ka, daga nan ka fada soyayya dani. Shi kuma ya fara sona ne tun Daga ranar da aka ce an samu cikina yake murnan yayi Kani ko kanwa, bai da wurin kwanciya sama da jikin Mahaifiyata gudun kar ta tab'a mishi Kani ko Kanwar shi!? Ya soni tun daga lokacin da yaji labarin an same ni.

?? Mahaifiyar shi tayi tafiyar ?addara domin Allah ya shiga al'amarin Mahaifiyata, taya kake ganin zan manta soyayyar shi? Lokacin da aka haife ni, sai da aka yi kwana uku baya fita ko cikin gida gudun kar a dauke ni. Yaso ni tun daga ranar da aka fada akwai ni, har ranar da na diro duniya bai fasa sona ba, abu na karshe da ya nima don Allah a bashi aurena duk lokacin da ya dawo meye yasa Alhaji Babba bai rike alkawarin shi ba? Yafi son ya karya al?awarin shi ko? Toh idan ban so shi ba waye zai so? Ina son shi da dukkan zuciyata."

Kura min ido yayi sannan yace min.
"Na fahimci yadda kike ji! Don Allah ki manta dashi zaki soni fiye dashi ma"

Murmushi nayi domin ya bani dariya gyara zama nayi sannan na kura mishi ido, sanan nace mishi.
"Ba zan so wani bayan shi ba gaskiya."

? ? Haka muka bar maganar tare da barin wurin, bayan kwana biyu. Hamma Khamil ya koma Russia, bayan kiran gaggawar da aka mishi. Dole aka dakatar da bikin akan lallai sai ya dawo.

? ?? A hankali kome yake tafiya min na manta da kome, shima Khamil din sai muyi wata uku bana waya da juna kuma lafiya lau, sannan kuma ba wani abu bane kawai yanayin aikin shi ne.?? Bani Mantawa ba tafi wani bikin abokiyar aikina muka hadu da wani gaye me zafi.

Yes nace me zafi ne sabida haduwar shi, yana cikin abokan angon, kasancewar abokiyar aikina Christer ce,sai gashi ya fito cikin abokan angon. Dake yan matan amare mun saka gown ce Dari purple, su kuma mazan sun saka suit grey colour. Sai aka yi dace kowanne mu ya kama abokin tafiyar shi da inda zamu zauna. Tunda muka zauna yake kare min kallo sai gyara kayan jikina nake domin ban saba ba. Karshe ciro mayafi nayi daga jakata, na yafa. Murmushi yayi sannan ya ce min.
"Amma wannan shine saka kayan nan na farko ko?" Kallon shi nayi sannan na sunkuya kaina ina gyada mishi.

? ? Murmushi yayi sannan ya ce min.
"Toh kuwa dole ki damu da kanki" sai lokacin na kuma kare.mishi kallo kafin nace mishi.
"Baka yi kama da Musulmi ba" dariya yayi sannan yace min.
"Eh haka ake ganin amma kuma ai suna na, Mehd Moin Indimi!"

Kallon shi nayi kafin na sunkuyar da kaina, ina tuna inda na tab'a jin sunan, a bankin mu. Da sauri na d'ago kai ina kallon shi.
"Mehd Moin Indimi" d'age min gira daya yayi tare da mik'ewa lokacin da aka kira shi,.mika min hannun yayi na girgiza kai tare da mik'ewa tsaye muka nufi inda aka kira shi, sai da ya gama bada tarihin Angon sannan ya koma komawa inda muka taso tare, zama yana murmushi yace min.
"Abokina ne tare muka yi secondry school, ita kuma Yarinyar yar nan Yola ce, shi kuma Ubanshi Sarki ne a Imo, shi yasa na zo domin mun zauna a Mexico City, na united state."

?? "Ita Amaryan abokiyar aikina ce, muna aiki a Zenith bank, shi yasa ka gani a wurin bikin." Nafada tare da kallon shi.

Mika min hannu yayi tare da cewa.
"Nice to meet" girgiza mishi kai ina murmushi.
"Rooman Yakub Yero" kallona yayi sannan yace min.
"Wow! Kina nufin kin fito a Familyn Aliyu Hashim Hassan Yero" murmushi nayi sannan nace mishi.
"Eh Ya'yan Baba na ne"? girgiza kai yayi sannan yace min.
"Masha Allah! Amma kin hadu!" Murmushi nayi tare da cewa.
"Ai ban kai ka ba, ka duba da kyau, domin kuwa Yan mata suna bin ka? da kallo ne"dariya yayi sannan yace min.
"Kina da abin dariya"

Haka muka cigaba da hira har aka tashi, gaskiya ban tab'a haduwa da mutumin da ya tafi da imani na ba kamar Mehd Moin Indimi ba, ya hadu domin ko magana yake sai ka ga kamar bada bakin shi yake ba, hmm haka muka yi musayar waya. Shi ya kawo ni gida.

Kafin kace me mehd ya shiga alamarina yayi kane kane, tare da? nuna min zallar madaran soyayyar shi.? Ya iya kashe zuciyar mace da soyayya tare da nuna min nan duniya babu wata dama dani, sai dai kash an riga da am yi mana baiko da Khamil....

#Mai_Dambu
EXQUISITE WRITERS FORUM.
JINI..!
? ?Ya fi Ruwa Kauri?
? *Base on true life story*

*Sadaukarwa ga Family Hasssan Yero Family da Madakin Muri Family*

? ? ?? Mai_Dambu

BABI NA SHA ?AYA

Kamar yadda na gaya muku Khamil ya tafi bai waiwaye ni ba, ban kuma jin duriyar shi ba, kai ko gida ya daina kira, sai da muka kwashe wata biyar sannan ya fara kirana, tare da gaya min uzurin shi. Ban wani ji haushi ba, kawai dai naji babu dad'i shi ya tafi ban san rayuwar da yake ba, ni kuma Nan iyaye sun hanani sukuni ba halin a ganni da saurayi da ayi ya min fada da surutu.

Haka yasa na mishi magana akan yadda maganar auren mu ya lalace, bai wani bani uzuri ba, amma ya gaya min cewa. Wallahi nan ma hidima ce tayi mishi yawa, dan haka nayi hakuri zai zo.

? ?? A gefe guda kuwa shakuwar mu da Mehd yayi yawa, domin kuwa kowa yasan cewa muna soyayya duk da ba wani soyayya bace na can. Sai dai kawai wata rana zai iya dauke kafa shima na wasu watanin.

? ? Sai da ta kai ta kawo a cikin gidan mu na Mubi, an fara kananun magana, wanda ban san daga inda ta fito ba, wai naki aure ina yawon gantali. Ranar Jabir ya ganni a can abuja a wani hotel. A lokaci ne Hammah yusef shima ya fada musu ya san ta tab'a mafarkin ina yawo amma bai tab'a gani na ba. Sai da takai maganar har kunnen Alhaji Babba. Abin da ya kawo zancen ba kome bane sai dan yadda aka tado da zancen aurena da Khamil, nan ne fa magana ta sake kwab'ewa har aka kira shi aka gaya mishi ya ce bai yarda ba.

?? Lokacin za ayi bikin Yaran Yadiko dan haka ta saka Innah a gaba da habaici da kananun magana.yau ake cincin Munnah da Falisat.? Tana cikin mutane ana aiki kasancewar sun girme Hamdiya da Shkuriyah.

? ? ? ? ? Ita Hamdiya take bin Abdul Malik, shamsudeen yake binta sai Shkuriyah, take bin shi. Kuma dama Abdul Malik ya da Munnah ne sa'o'in juna, Hamdiya da Falisat akwai dan yan watani a tsakanin su, Falisat ce babba sai Tsakanin Shkuriyah da Jannart akwai shekara biyu, amma dake suna da jikin girma zaka rantse da Allah sun fi mu girma.

? ? ?? "Wasu suna bugewa da karuwanci ne a kare da sunan aljanu ko Mayu ke bibiyar su,nan kuwa an Cigaba tunda ta kai har an fara haduwa da su a hotel hotel dake cikin Yola da Jimeta." Dariya masu aikin cincin din suka saka, Innah kan bata kula su ba, domin bata dauke su a mutnen da suka san ciwon kan su ba. Haka suka ci-gaba da habaicin su.

? ? ? ? ? Can da suka ishe ta tace musu.
"Ina ganin a duk macen da ta haifi Y'a mace bata da bakin da zata zagi wata Yar, bar ganin ?atara, ka kiyayye mai nima, idan Uwa ta cika uwa huta zagin dan wani sabida ciki me haife haife."

?? "Kwarai Mariyah, idan da ana sauya ?addara tabbasa ni da kai na zan sauya ?addaran Rooman, amma al'amarin na Ubangiji ne wani baya sauya. Ku kuma ku tabbata haka babu abin da Allah zai jarabce ku, ai abin alfahari ne ma Allah ya jarabce ka. Ana maka tabbacin kana da imani ne mara imani kam sai dai mu mishi fatan rabauta" inji Yawuro.

?? Jikin su ne yayi sanyi domin sun san cewa tunda tayi magana tabbas ta gaji da mugun halin su ne, domin tana jin abin da suke faWa.

?? Ire-iren waWannan abubuwan yana kara fusata Yadiko Salamatu domin kuwa tana ji tana gani bakiWaya mutane suka juya da laifin da take ganin na Innah ce.

? ? ?? Koda lokacin bikin yazo duk mun zo daga Yola,nan ma nasha bakar magana tare da fadar duk abinda ya fito bakin su, haka bai saka naji a raina zan yi fushi da kaddarata ba,kawai na yarda babu wanda ya wuce ?addaran shi. Haka aka yi bikin ana gaya min magana, wallahi ban d'ago kai nayi magana ba,? a wurin Dinner ba karamin rikici aka yi ba domin kuwa an kama Nasim? Annur mijin Falisat da wata yarinya, ba karamin tashin hankali muka shiga ba.

? ? ? ? ? ?? Sai abin ya zo mana banbarakwai, domin duk cika bakin su, ga dai mijinta an kama shi a wurin bikin su da mace,

?? Dan kar maganar ya zama babban magana a take aka juya zancen tare da cewa, ba wani abu suke ba kawai? ya taimaka mata ne,. Baki daya suka rena mana hankali muka tafi a hankali.

?? Muna dawowa aka ce ana nima na,wallahi ban dauka wani abu ba kawai na fito, sai ganin Annur nayi ya zo wurina,dan haka na nufi wurin shi tare da tambayar shi Lafiya?

"Dama naga kawai kinyi min kyau ne a cikin kayan ankon yasani zuwa ganin ki, wato? Rooman da nasan kin fisu kyau wallahi da ban fara niman Falisat ba. Sabida Allah yayi miki baiwa irin matan da suka san darajar kan su, wallahi yau da na ganki ba karamin matsanancin damuwa na shiga ba."

Kallon shi nayi tare da murmushi,sannan nace mishi.
"Toh yayi kyau. Amma kafin nan ina son na tuna maka kanwata kake aure da muke Uba daya, idan ka Kuskura ka janyo min tashin hankali." Takawa nayi gaban shi tare da kallon shi sosai sannan nace mishi.
"Sai na baka mamaki domin wallahi sai na hanaka barci ka juya ka tafi bana son Iskanci"

?? Na bar shi a wurin, a hankali shiga ta cikin gida ne naji kamar ana bina a baya, da sauri na shiga cikin gidan, ina isa wurin bishiyar rimin, naji na kasa motsi. Na tsaya kamar an dasani, juyawa nayi na kalli bishiyar rimin.? Kofa ce ta bude, a hankali na hango wani fili sosai, kamar irin lambu nan, dan haka na taka a hankali tare da kai hannu zan buWe.
"Rooman!" Da sauri na juya tare da kallon Alhaji Babba.
"Me kike a wurin?"
"Hmm. Ganin kofa nayi" na juya ina nuna mishi, babu kome sai kokon bishiyar.
"Ina kofar yake?"
? Ya tambaye ni, sai lokacin na kuma kallon kofar na ga babu kome, a tsora ce na kalle shi.
"Alhaji wallahi kofa ce"
"Muje ciki" a hankali nayi gaba ina waiwayon kofar.

? ? ? Jikin shi ne yayi masifar sanyi, koda na nufi gidan mu nuna min hanyar gidan shi yayi haka na shiga falon shi, na zauna. Shima ta shigo ya zauna.
"Ina zaki a jikin itaccen?" Ya kuma tambaya na.
"Babu ko ina, kawai naji ina son zuwa wurin ne" jinjinq kai yayi sannan yace min.
"Idan wani abu ya same ki fa?"
Sai lokacin na zaro idanu.
"Hm"
"Karki kuma zuwa wurin kinji, maza tashi ki nufi gidan ku."

Haka na nufi cikin gidan mu na kwanta, tare da jin wani irin tsoro da damuwa, me yasa ba a ganin abin da nake gani? Me yasa mutane basu lura da abin da yake faruwa dani? Ni kadai ce nake ganin kome ba kowa ba? Anya ni yar Adam ce kuwa!?

Na tambayi kaina, kai na ne da ya fara sarawa na koma na kwanta ina jin babu dadi a raina, a hankali bakina yake karanto ayatul kursiyu,. Iya shi na karanta ban kuma karanta kome ba, sabida nauyin barcin da ya dauke ni.

? ?? ... 2:am
A hankali nake takawa har jikin bishiyar rimin, a hankali na tura kofar tare da bude kofar, wani irin sanyi ne ya huro tare da dusar ?an?ara, a hankali na bude tare da hango step, sauka nake a hankali. Can na hango wani mutum zaune yayi zaman yogo, gaban shi wuta ne yake ci. A hankali nake matse jikina, sabida sanyin da ake kad'awa, jikina yana wani irin rawa, haka na nufi inda yake domin koda nayi tunanin juyawa babu kofar babu dalilin shi.

? ? ?? Da sauri na isa wurin wutar, na durkusa, bude idanu yayi tare da kallona yau kan ya daure gashin sa a tsiyar kan shi, Allah yayi halitta, kyakyawa ne na gaban kwantaccen,? garin gashin sa yana tufke a tsakiyar kan shi. Kallona yayi tare da warware kafar shi ya tashi tare da tab'a wani wurin sai ga ?atuwar rigar sanyi.

?? Takowa yayi tare da saka min a bayana, sannan ya zauna tare da kallon yadda nake jin sanyi, dafani yayi,. Can na fara zufa saboda zafin da nake ji. Ina son nayi mishi magana amma bakina yayi nauyi dan haka na zuba mishi ido. Janye hannun shi yayi yana kallona.

? ? ? ? ?? Jin sukuwar dawakai ne ya sani

9 / 69