JINI YAFI RUWA COMPLET BOOK BY D AUTA.doc

Author :  Hadiza D. Auta Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   45 / 69

132K to 135K   out of 206.5K words

su yayi tare da tofa mata addu'o'in, kafin ya juya tare da gyara kwanciyar shi yana me janyota jikin shi.

?? **
Ruman.
"Kina ganin dama Hayat zai iya kawo Miki mafita ne? Da kin hakura dani da na kawo cika Miki zuciyar ki da kauna" ya fada tare da gyara min gashin goshina. Kallon shi nayi tare da janye kaina a hankali, kallon wurin Camera yayi sannan yace min.
"Basu gani na, amma ke duk motsinii suna gani kuma suna fahimtar haukar da kike." Tofa mishi yawu nayi, ya goge, sannan ya sake murmushin mugunta, yace min.
"Bari na miki abinda ba saba Miki"
"Insha Allah ba zaka kuma cutar da ni ba, domin Allah yana tarre dani." Na fada ina mirza karfen hannuna, cikin shammata tare sa kiran sunan Allah, na cikka mishi karfen bayan na kira sunan Allah, wani irin zabura yayi tare da b'acewa yana gurnani,

? ? Ban kuma sakewa na zauna a babu addu'o'in ba, domin nasan kowani lokaci zai dawo, haka na tsinci kaina mai da son maida hankalina wurin bautar Allah, bana wasa da Ibada. A hankali lokacin yai ya tafi kamar da wasa, wata rana aka sallame ni. Hamma Babangida ne ya zo da kanshi, yana min kallon kamar ya wata dodo. Cikin jin kunya na koma gefe idanuna ya cika da kwalla, komawa yayi gefe yace min.
"Ya jikinki?"
"Da sauki" na fada cikin rawan muryan kuka.

"Toh muje" ya fada a tsoro ce, Allah sarki, baki daya sai naji kuka yazo min, haka muka shiga taxi, tunda muka bar asibitin? nake kuka, har muka iso gida. Biyan kudin yayi tare da shigowa gidan, haka na koma cikin gidan ina rab'e rab'e. Babu wani dogon surutu ko alaka a tsakanin mu sai zaman kurame.

? ? Rayuwar babu dad'i, baki daya sai naji ina kewar Innah dan haka na shiga rokon shi ba dare ba rana akan ya mai dani gida, amma fir bawan Allah nan yaki, sai ma wani salon da ya dauka bata dawowa gidan sai tsakiyar dare, idan zai fita kuwa kafin gari ya waye ya fita. Sanin halin da nake ciki, ya sani shiga mugun mugun tashin hankali, domin kuwa zama wuri guda tare kadaici ya haifar min da tsoro kamar ana tare dani, firgice kamar za a tab'a ni, sai a hankali na fara ganin kamar gidan da nake yana sauya min, domin kuwa xan ga kamar ba cikin gidan da nake bane, sannan zan ga mutane suna hidimar su. Kamar gidan su, kuma idan da zan musu magana toh babu me kula ni, wannan yanayin yasa ko barci nake zan farka, domin hayaniyar mutane, ban fasa gayawa Allah kuka na, ba domin haka xan najin wani lokaci kamar ibadar ba zata karbi ba, ko bata amsuwa ce addu'o'in na. Amma daidai da rana ban tab'a bari ba.

? ?? Yau kwana bakwai da mishi magna, yana zaune a gaban me gidan shi. A matukar takure kamar zai yi kuka ya ce mishi.

"Kayi hakuri sir zan koma gida ne da mata ta, bata da lafiya!" Ya fada kamar xai yi kuka, shi kadai yasan halin da yake ciki, wallahi yafi rumanah shiga tashin hankali, domin shi ido da ido yake ganin tashin hankalin.

? ? "Toh Mr Yero zamu sallame ka, amma da fatan zaka dawo mana, domin mun ji dadin aiki da kai" gyada kai yayi tare da matse hannun shi, idanun shi ne cika da kwalla. Hadiye yawun yayi lokacin da Baturen ya mika mishi kudin shi, a hankali ya mike tare da godiya kudin da ya tara ma aikin shi zai kai su gida tare da matar shi.? Ana bashi yayi godiya tare da nufar waje, ya gyarawa kudin zama, bai tsaya ko ina ba sai Bus stop.? Anan ta ga wani mutum me wata irin riga a rufe da kan shi, k'amk'ame kudin yayi idanun shi yana zuba kwalla, domin yasan wannan mutumin shi yake bibiyar shi. Yana shiga cikin motar ya hango mutumin yana zaune, ji yayi kamar ya dira a motar haka ya k'amk'ame kudin shi, ya sunkuyar da kan shi jikin shi yana rawa, juyawa yayi ta hango mutumin yana tawowa wurin shi. Kafin ya iso kusa da shi. An isa unguwar su, da sauri ya mike tare da biyan kudin bus din ya sauka, yana fita ya arta a guje ya nufi gida, abin tausayi yana gudu mutumin yana bin shi, yana bin shi, sai da ya isa kofar gidan dai dai fitowata, muka yi gamon kamar zamu fadi daidai abin da ya biyo shi.
"Ruman mu shiga cikin!" Ya shiga tare da rufe kofar yana dauke ajiyar zuciya. Amma ya bar ni a wajen. A hankali nake kallon shi tare da isa gaban shi, yana tsaye akan iska. Sauka yayi tare da kallona. Hannun shi ya kai sai kuma ya fasa.

Juyawa yayi tare da tashi a iska, ya bar wurin.
"Me yasa yake bibiyar al'amurana? Me yasa yake bibiyar Rayuwata? Me yasa ya gallabi rayuwata? Akwai hujja haka kawai ba zai samu rayuwata ba." Na fada ina kuka. Cikin gidan na shiga na samu yana ya haWa mana kayan mu. Kallon shi nayi.
Dafa kafadar shi nayi nayi, da wani mugun sauri ya zabura, tee da ja da baya.
"Me kake so dani?" Ya fada muryan shi ne rawa,
"Hamma Babangida meye ya same ka?" Na tambaye shi ina shanye kuka na.
"Ki tafi! Ki shirya" haka na juya domin ita haka da na gani yana tsorona, yasa ni fita ina had'a kayana. Bayan na gama ne ya kuma bayyana.
"Ba zaku tab'a komawa ba!"
"Kana wasa da wanda ya yarda da Allah ne? Kana tsoro ne" komawa yayi maciji katon gaske fari da shi, kallon shi nayi domin zuwa yanzun bana jin kome a raina, hawaye na zuba min.
"Azzalumi mara imani inshallah kome zai zo min karshe"

? ? Na ja kayana na fita daga cikin dakin, na samu Hamma Babangida har ya fita, daga shi har ni idan ka gammu zaka fahimci cewa a firgice muke, a haka muka samu taxi har airport. Bamu samu jirgin Nigeria ba, sai Dubai.

? ? ? ? ? ? ? ? Daga ni har shi muna zaune tsamo tsamo, har Allah ya taimaka aka fara kiran fasinjoji, muna shiga cikin jirgin muka sauke ajiyar.

? ? ? ? **
Karfe biyar na asuba muka isa Abu Dhabi, lokacin da muka sauka, da ajiyar zuciya na sauko daga cikin jirgin ina ji kamar na iso gida ne, muna barin wurin wani jirgin na isa, muna zaune sai gashi suma sun iso, har suka gama zasu wuce ya dawo gaban mu ya tsaya.
"Ummu Ruman! Hashim!" Ya fada da dan karfi,
"Na'am!" Hamma Babangida ya fada da mugun sanyin murya, tare da mika mishi hannu, kasa kallon su nayi tare da shanye kukan da ya zo min.

?? "Amma Meye ya faru?" Ya kalle mu, tsaki matar shi ta ja, tare da cewa.
"Honey muje don Allah, ban san wani irin heart ne gare ka? Mutanen da suka wulakantaka, zaka tsaya kana magana dasu" ta fada tare da tura bakin ta.
Bude baki yayi zai min magana na d'aga mishi hannu.
"Mun gode, zaka iya tafiya matar ka tana da muhimmanci sama da mu." Taunar lips din shi tayi tare da rintsa idanun shi, sannan ya saka kai zai tafi Hamma Babangida ya rike hannun shi yayi tare da cewa.
"Don Allah! Kayi wani abu muna cikin tashin hankali"
"Dallas sake shi, gwara ku mutu da ya taimaka muku, marasa kyauwun dabi'a."

"Idan kika ce mijinki kar ya taimaka mana babu laifi, amma ba zan iya lamuntar wata mace tana haushi ga mijina ba,"

?? Na fada tare da kallon Hamma Babangida, da yake rawan jiki nason yayi magana da Dr Hayat, dafa shi nayi a matukar fusace ya juya tare da shake wuyata. Buge shi hannu Dr Hayat yayi, murmushi yayi sannan yace mishi.
"Barka Hayatuddeen Abdulwahab Adamu Moddibo!"
"Waye kai?"
"Mun kwana biyu bamu hadu ba" ya fada tare da dage mishi gira Waya.
"Waye kai?"
"Canka?"
"Safdar Hajbir!"
"Kaji manyan masu manyan kwanya ka lura da inda muke na tsayar da tafiyar kowa. Idan naso sai na saka kowa yayi ta faduwa, a sume karshe na daura laifin akan wancan da tasaka zuciyarka bugawa" dariya ya sake bayan kai Ayar maganar shi.
"Kasan me yasa ka samu nasara akan su? Allah ya ?addara haka sai ya faru, amma bari na gaya maka wani abu ko kad'an bana jin akwai abin da xaka yi ya ba wani tsoro, kuma ina da yakinin wata rana xaka biya bashin da ka ci. Wallahi zaka biya dan haka ka kyale bayin Allah suyi rayuwar su kafin na waiwaiye ka!"

"Idan naki fa? Nayi rantsuwa sai na cika shi sai na saka mata tsoron haduwa da wani namijin kai kuma nasan yadda zan yi da kai domin ka gama addabar rayuwata " inji Safdar.

Murmushi Dr Hayat yayi sannan yace mishi.
"Ina nan ina jiran ka, yau, gobe, jibi, gata, har wata sati ina jiran ka jahili wanda bai san kome ba sai asararan shi, dakiki gidahumi. Banza wawa dabba kawai kasake mutane ko na kama ka." Dr Hayat ya fada da karfi sai da Airport din ya amsa, da sauri ya fita a jikin Babangida, luuu yayi zai fadi Dr Hayat ya rike shi, ganin yadda nake wani dari dari, yasa shi zama a kusa da Hamma Babangida, har zuwa lokacin da aka? Turi security su tambaye shi lafiya.

"Lafiya lau, ya gaji ne!" Ya fada tare da riko Hamma Babangida har? masaukin da ya kama, tun a can muma ya kama mana daki daya, tun da ya kai shi dakin ya kwantar da shi, ya saka kai ta fita bai dawo ba sai kusan karfe bakwai, yana dawowa ya same ni zaune a jikin Hamma Babangida, na sarkafe hannun mu wuri guda, ina barci. Ajiye maganin yayi tare da fita bai dawo ba, sai wajen karfe goma na safe. Ya buga kofar na taso na bude mishi. Kurawa juna idanu muka yi kafin na matsa mishi a hanya ya shiga cikin dakin, sannan na tsaya ina kallon shi ya fara shafa mishi magani. Yana addu'a, balle rigar shi yayi a hankali sai ga wasu irin kuraje,? a hankali yake kasa mishi rigar har ya gama, sannan ya ce min.
"Ki kula dashi, nan muna bakon wuri ne, da zamu isa gida Insha Allah zamu yi aiki akan ki da shima" ya mike tare da cewa.
"Karfe biyu zamu bar garin nan insha Allah zamu isa karfe tara na yamma dan haka ki kula sosai."
Jinjina kai nayi, har ya fita ban iya kallon shi na mishi magna ba, sai ma kokarin kauracewa zuciyarta nake, domin sai kara hasko min da canjin da na gani a tare da shi.
Dakin su ya koma, yana shiga ya samu Darrah tana kuka.
"Kin san dai bani da case idan mina bararr da cikin jikin ki? Dan haka matukar baki kula ba, TOH ba makawa zaki muka daukar lokaci kina kuka, sannan yan uwana ne baki isa hanani kula da su."....

*Kuyi hakuri don Allah idan na wallahi kusan yanayin ne sai a hankali naso yafi haka, amma babu lokaci insha Allah gobe zaku gani kamar kullum*
300? ... Insha Allah'
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A'ichah
+22784506476
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank
#Mai_Dambu
Mai_Dambu
Paid book300?
62

Takawa yayi tare da isa gaban ta, yana kallon yadda ta sake baki tana kallon shi.
"Baki da ikon hanani abinda niyya, taimakon Al'umma a jini na gane dan haka ki tsaya matsayinki na mata ta, karka ce zaki wuce iyakar domin ranki zai b'aci ni kuma ba zan fasa ba"

? ?? Kura mishi ido tayi kwalla na zubo mata, kirjinta? yana wani irin bugawa, juyawa yayi tare da Waukar abinda zai dauka ya sakai zai fita, ta bishi da sauri tare da rungumar shi ta baya. Cikin shashekar kuka ta ce mishi.
"Ina jin tsoron ganin ka da Ruman ne? Ina tsoron haduwar ku ne, shi yasa nake magana ba wai dan kome ba, don Allah don Allah don Allah, kayi hakuri ba zan kuma ba, idan na kuma ka min duk abinda ya dace"

? ?? Juyawa yayi tare da sumbatar goshinta, yana fadin.
"Ganin Ruman bai saka na daina ganin ki a matsayin abokinyar rayuwata ba, itama baki ga da abokin rayuwarta take ba? Toh shi ?addara haka take, don Allah a daina duba kishi"

?? Sakalo hannun tayi kafadar shi.
Da cewa
"Kayi hakuri"
Had'e ta yayi da jikin shi, tare da kallon fuskar ta. Sumbatar goshinta yayi sannan ya kuma kaiwa gefen idanun ta ya sumbata, sannan ya kuma rungume ta, yana jin wani irin abu ya tsaya mishi a rai. Idan ya tuna da yadda Ruman ta koma, sai yaji wani irin abu na yawo a ranshi, sumbatar kafadar yayi yana faWin.
"Thank you darling"
Wani k'amk'ame shi tayi tana jin wani irin dadi a ranta, sai karfe sha daya da rabi ya tashi, hada mishi ruwan wanka nayi ya shiga yayi wankan sannan ya fito na cire mishi kaya, abincin aka kawo na ajiye mishi tare da jiran yayi Sallah, yana idarwa bai ko yi addu'a ba, ya mike.
"Kasan halin da muke ciki, bai dace kana sakaci da addu'a ba" na fada mishi.wani mugun kallo yayi min sannan ya juya tare da cigaba da cin abincin shi babu basmala. Ai kuwa yana kai lomar farko ya kware, sosai fa tare da faduwa kasa yana niman ruwan sha, koda na mika mishi ruwan fisga yayi tare da kaiwa bakin shi, sake shake wuyar shi akayi tare da had'a shi da jikin bangon. Kakari yake tare da niman ceto.

?? Da sauri na fita zuwa dakin Dr Hayat, na buga sau biyu. Sai gashi ya buWe min.
"Ya dai Ruman?"
"Zai mutu" na fada tare da kallon kofar mu, da sauri ya fito muka nufin. Hmm muna shiga abin mamaki shine kamar babu abinda ya faru. Zaro idanu nayi tare da toshe bakina.

"Amma!"? Wani irin kallo yayi mana tare da kai ya cigaba da cin abincin shi, Dr Hayat ya kalli ni. Yasan ba zan taba mishi karya ba, dan haka ya ce min.
"Jeki wurin Wife"
Fita nayi ban tsaya ba, kallon shi yayi sannan yace mishi.
"Safdar!!!"? Da sauri ya d'ago kan shi zai magana Dr Hayat ya murza zoben shi, tare da kai bakin shi yayi addu'o'in, kafin ya ce mishi.
"Ina Babangida?" Nuna mishi kan shi yayi, wato da Dr Hayat ya. Finciko kafadar shi ya gwara shi da bangon b'acewa yayi sai ga Babangida a kasa dakin kaca kaca abincin.
Tasar dashi yayi tare da zaunar dashi a bakin gadon, sannan ya fita ya kira Ruman ta gyara dakin. Nan ya ya had'e mishi magani sanan ya saka kai ya fita, bamu kuma haduwa ba, sai karfe daya da zamu tafi, muka hadu dasu. Har a cikin jirgin Hamma Babangida abin yana yi yana tab'a shi.

Mun sami jirgin da zai sauka a garin Abuja ne, dan koda muka isa Abuja, sai da muka jima kafin muka samu jirgin Yola, dukda Dr Hayat yaso mu kwana biyu amma naki gwara muje gidan kome zai faru ya faru a gaban jama'an gida.

? ?? Muna isa Yola taxi har gida ya kai mu, muna sauka muka shiga da kayan mu, Baba megadi ne ya biya kudin motar domin ya gan mu kamar an koro mu, muka fada falon. Gara ni da sallama na shiga gogan naku kamar an koro shi.yana ganin mahaifiyar su a kitchen ya nufi wurinta tare da fashe da kuka. Kamar Yaro karami,fitowa yayi ya ga ina tsaye.
"Barkan ku da hanya sannun,"? ta fada tare da amsar kayan hannuna.
"Karki amshi kayan, tunda muka tafi yarinyar nan take yawon bin maza, dama an gaya min ban ji..."

Tass Mama ta wanke shi da mari, tare da kara tsinka mishi mari, sanan ta juya tare da kallon shi.
"Tun daga lokacin da ka b'ata nasan da wannan masifar, sannan da ka dawo sai da na gaya maka ka hakura da ita ka barta tayi auren ta, kace min idan baka aureta ba, mutuwa zaka yi, ka sani muka b'ata da yar Uwata, ka ce min bata sonka Hayatuddeen take so, wallahi billahi azim Allah sai ya saka mata, kuma Aure yanzun ka fara tunda Salamatu ta zama uwarka" ta ka raso wurina tare da riko hannuna. Muka nufi dakinta, kuka nake tare da jin kamar zan mutu domin kirjina har zafi yake, babu wanda yasan mun dawo.

? ? ? Zaunar dani tayi sannan ta ce min.

Na kasa magana na kasa kome kuka nake kamar raina zai fita.
"Don Allah ina son naje wurin Innah ta"
"Kiyi hakuri ba a cikin wannan yanayin ba" ta fada min tare da rike hannuna, ta rasa me zata ce min haka nayi kuka ya saukar min da zazzabi me zafi, sam ban san me yasa rayuwata ta zama haka ba, amma akwai Allah. Nasan yana ganin kuma baya barci baya gyangyandi.

? ? Haka nayi ta kuka ina jin kamar da mutuwa nayi zai fi min dadi sama da ace ina raye ne, tare da wasu irin mutane, tsawon shekaru ina fama da jaabawar rayuwa, amma a bangare na babu wanda ya damu dani domin kallon abin suke kamar ai ba wani abu bane, shi yasa kowa yayi watsi dani amma ai nima ai ina da nawa laifin, domin gashi ban damu da Ibada har haka ba, dan haka na mike tare da shiga ban daki nayi wanka da alwala, sannan na zo na gabatar da sallah,ina idarwa na jima ina addu'o'in. Kafin Na mike zan kwanta Mma ta kawo min abincin. Zama nayi naci kadan sannan na koma na zauna ina kallon yadda Hamma Babangida ya juya min baya, haka na kwanta har barci ya dauke ni,

Ban tashi ba sai karfe biyar, nayi tashi nayi sallah, sanan na saka dogon riga, na nufi falon muka gaisa, yana gani na ya mike tare sa barin falon, zama nayi Shahid ya kalle ni, sannan ya dauke kanshi. Da alamun sunyi magana ta da dan uwan shi.

**
Sun sauka a garin Abuja, Aalim yaje ya dauke su, suka wuce gida.
"Adam ka tanadi kayan aikin idan nazo zamu wuce Yola ka haWa min kome." Cikin wani irin fushi take kallon shi, suna had'a ido ta dauke kanta tana hura hanci.
"Zaki zauna na kwana biyu, anan zan tafi Yola gobe insha Allah Adam zai kwana a can" bata ko

45 / 69