JINI YAFI RUWA COMPLET BOOK BY D AUTA.doc

Author :  Hadiza D. Auta Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   65 / 69

192K to 195K   out of 206.5K words

da kika jiwa kanki ya ishe ki har karshen rayuwarki."

Zama yayi tare da kifa hannun shi a fuskar shi yana wani irin kuka, a karon farko da yaga abinda ba zai iya yin kome ba, da sauri yayi waje. Gidan shi ya nufa ya fara had'a magani sai ya had'a sai maganin ya lalace. Tunda ya yi na uku bai kuma ba, sabida yadda gaban shi ya fadi tare da jin kar'ar wayar shi. Dauka yayi tare da sakawa a kunnen shi.
"Hmm!" Ya faWa.
"Kazo muna bukatar ka" wani irin kwalla ne ya zubo mishi.
"Ta rasu ko?" Ya fada cikin matsanancin tashin hankali, yana jin kamar ya? samu Darrah yayi ta dukar ta sai ta mutu.

A hankali ya bar dakin bayi tunanin ya rufe ba, sam zuciyar shi tayi wani irin taushi da kumburi,haka ya nufi asibitin. Lokacin da ya isa ne ya samu Darrah tana ihu, tare da cewa.
"Wallahi sai na rama domin ba zaki kashe min Yarinya na kyale ki ba, muguwa." Wani irin shake ta yayi tare da niman dukarta , dakyar su Adam suka kwace ta a hannun shi. Cikin fushi ya bar asibitin tare da rantsuwar sai ta ga bayan su kamar yadda suka mata sanadiyyar Yarta.

?? Gidan da suka zauna, tana shiga ta samu gidan a rufe. Kamar wacce ake umartatta, ta shiga fasa kayan dakin maganin shi tare da bude wasu kwalaben, duk ta jima kanta ciwo. Ta nufi bayan gidan inda yake binne mugayen aljanu da yake cire su a jikin mutum, ta shiga tone su.

A idanun ta wani shudadden lokaci yana wucewa akan ta,.

Wacece Hajiya Rushidiyya.

Yar wani kauye ce dake iyakar najeriya da chad, mahaifin ta mutumin kirki ne, sai dai rashin dace da aka yi mahaifiyar ta, irin
Matan ne masu mugun son abin duniya, kasancewar akwai fatara da talauci, yasa suka dawo Gombe da zama.

?? Kasancewar Rushidiyya kawai suka haifa, yasa suka dauki soyayyar duniya nan suka daura mata ita kuma ganin haka yasa ta tashi cikin son abun duniya, itama Uwarta ganin yadda Allah ya yanka mata yarta da araha, yasa ta daura buri akan Yarta.

? ? ? ?? Har yarinyar ta girma burinta ta auri me kudin ban mamaki ko wani futacce, tana da shekara goma sha uku aka kaita makaranta kwana na Government Girls School Gombe,.a lokacin anyi auren Ummin da Abdulwahab, lokacin tana Koyarwa a makarantar, bata wuce shekara daya da aure ba, domin a tana gama bautar kasa aka yi bikin su, sai ya zama shi baya zaman gida domin lokacin da akayi auren su yana makarantar yan sanda dake ?asar england.

Domin zai yi shekara uku ne a can kuma a lokacin akwai karancin wayewa kamar Yanzun da ana kai aamarya kamar ta kamo mijin ta cinye shi. S???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ai ya zama Hamza shi yake kawo ta makaranta, a motar Moddibo lokacin yana alkalin shi ga kudi ga ilimi ga dukiya, duk inda zuri'ar shi suka shiga sai an fadi sunan su.

? ? ?? A hankali lokaci ya tafi,har Ummin ta fara jin labarin Rushidiyya a bakin mutane na tsananin kyawunta, wannan abin yasa itama take son ganin Rushidiyya, lokacin da da ta ga Rushidiyya ba wani abu bane yasa tayi haka sai dan sanin halin kanin mijin ta, da son kyakkyawar mace, sai ta ga yarinya ce dan itama ta bada wasu shekaru, dan haka ta same shi da maganar Rushidiyya, aikuwa sai da yatsa ya ganta, tun daga ranar ya makale mata, haka yayiwa Ummin dadi.

?? Lokacin da Abdulwahab ya cika shekara daya da rabi,.yazo hutu. Lokacin da yazo hutun, aka sha amarci. Sai dai bai wuce wata daya yayi ya koma. Inda ya barta da cikin Hayatudeen..?? sai bayan tafiyar shi da wata biyu, ta fara mahaukacin lailai, wanda ya gigita. Tayi fama da cikin shi sosai kafin ta daina laulayi.

? ? Bayan watanni tara da wasu kwanaki ta haifi Hayatudeen, idan Moddibo da kan shi yayi mishi huduba da sunan kakan shi.

Bayan shekara daya da wasu watanni Abdulwahab ya dawo, lokacin Hayatudeen yana zama.

?? Soyayyar Rushidiyya da Hamza tayi karfi, har ta kai iyayen sun shiga maganar, a lokacin tana aji biyu.

? ? Sosai Mahaifiyar ta take kaita wurin malamai, suna bata magani na yadda zata kame Hamza, har lokacin da Rushidiyya ta gama makaranta, aka sha bikin su da Hamza, Hayat yana da shekaru hudu zuwa Biyar, wanda yayi daidai da komawar su Lagos da zama, yana da shekara shida aka haifi Abeedah,? bayan sun koma USA da zama.

? ? ? ? ? ?? A lokacin Rushidiyya ta haifi Jawaad, Adamu Hamza Moddibo,? tana goyon Jawaad aka yi auren Abubakar da Murja,.inda ta haifi Nu'aym, wato Lamido. Sai karshen maza Saifullahi, da matar shi Umma Mariya, ita bata haihu da wuri ba, amma Yaranta mata ne. Kasancewar Ummin itace yar gida dukkan su bare ne, kuma tafi su matsayi sosai,.ga ilimi ga dukiyar da mahafanta suka bar mata yasa ake ganin kamar wani abu ne, a hankali hassada da kyashi ya bayyana a ran Rushidiyya, inda bata boye kiyayyarnta da ummi.

Duk da mijinta ya bata kome tayi rayuwar amma haka bai hanata hango Hadiza ba, a Irin wannan bin malam ne ta hadu da wata kawarta da suka yi bording school tare, take gaya mata matsalar ta, ita kuma ta ce mata.
"Toh Yanzun ina zaki?"

"Zan tafi wani kauye ne wurin wani boka" murmushi tai sannan ta ce Mata.
"Zo muje na nuna miki inda ba zaki kuma batar da kudin ki ba"
"Muje" ta kaita gidanta, suka shiga dakin ta, ta ciro madubi, tare da kwabe mata kayan ta, suka shiga ta mudubin,.suka bayyana gaban mata tana aikin ta.
"Ba zaki tab'a nasara akan Matar da ta miki rana ba, domin bata wasa da ibada, idan kika nace zaki iya samun matsalar hauka, mijin ki kadai zaki iya juyawa sauran ki bar su, domin suna nima ne a wurin Allah, shi kuma yana son siyasa dole zai kaucewa hanya, dan haka ki kula da wannan, sannan zan baki karfi amma cikin jikinki zaki bamu"

?? Shiru tayi sannan ta ce .
"Na bada shi"
Itama madubin ta bata sannan ta ce mata.
"Karni damu zaki iya komawa gida ta wannan mad''ubin kowa yayi tafiya shi."
Haka ce ta faru, kowa ya koma ta madubin shi,.bayan awa daya da komawar ta, ta haifi yarta matacciya. Bata damu ba domin tasan inda Yar ta tafi.

? ? ?? Haka tai ta samun ciki domin bayan Jawaad da Nur bata kuma haihuwa ba, dan haka sai da ta bawa Dodo yara uku cif kafin ta samu cikin Darrah, a lokacin ta roki dodo ya bar mata Yaron tana son shi. Shi kuma yaji dama zai bar mata,. shi ne aka haifi Darrah,. Sai Hawwa'u sai Nusrat da Nusayr.

? ? Har zuwa lokacin da kawarta ta mutu, sabida kin bawa.dodon su abinda ya bukata,.sai gashi sun sakata tayi hatsari suka dauko gawanta, suka tsafacce shi. Wannan abin yana masifar yiwa kurwan matar ciwo, domin sun zo kama kurwan su kashe shi amma ta gudu, suna aiki da aljanu sosai, domin ko maganin da aka bawa Darrah Akwai wani aljani a jikin shi. Shi yake rab'arta idan zata aikata sharri.

? ? ? ?? A Yanzun bokanyar ta samu ganin Safdar ne ta madubin tsafinta.
lokacin da ta samu ganin shi yaki mata magana, sai da tayi ta damun shi cikin fushi ya ce Mata.
"Duk wanda ya samu damar fitar dani? cikin wannan ukubar alkawarin mishi? biyayya, amma kafin nan sai an tono Aljanun da Hayatudeen ya binne, sannan zan saurara mishi. Karki sake wannan damar ta wuce ki"

Wannan dalilin yasa tayi amfanin da Darrah, domin ta samu damar Aljanun su Ku ce Safdar,

? ? ? ? ?? Da wannan yanayin ta ingiza zuciyarta ta mari Ruman domin idan tayi haka Ruman zata mutu, lokacin da Hayat sai yi kokarin niman maganin tayi kokarin zuwa gidan domin a rikice yake,. Lokacin da ta shiga cikin gidan da zumman marin Ruman Hayatu ya fito shine ta fita tana masifan rashin nasarar da bata samu ba.
Har zuwa marin Fareeha,
**
Bata fasa tonon ba, sai da tayi ta cire kwalabe babu iyaka, tana gama zaro su zoben hannunta ya fadi garin farfasa kwalaben,.tana dariya tana faWin.
"Hahahah, ta kare miki Ruman zaki tafi ki bar min Hayatudeen dina, zaki tafi inda kika sa na tura Fareeha Yarinyar kirki" tana gama fadar haka tana fasa kwalaben baki daya. Wasu irin bakaken hayaki ne suka tashi sama,.tare da curewa wuri guda sannan suka dawo da masifar karfi,.suka daki tsakiyar kanta. Sulalewa tayi tare da zubawa a kasa tana fitar da wani irin kumfa ta hancin ta da bakinta.

....
? ? A hankali ya shafa fuskar yarinyar yana jin wani irin kewarta, hawayen tausayin kanshi yana zuba mishi, bai san wacce irin uwa ce ba Darrah, domin sabida kishi ta kashe yarta ta kashe kanta mana, ya zai yi da Darrah yaji dadi. Wannan shine ake ce mishi sakayya. Kallon zoben hannun shi yayi tayi wani irin ja, wani sabon tashin hankali....
92
*Fatan Alkhairi me tarin yawa Momyna Aunty Sa'ah >?#?=??*

Kallon saman zoben yayi wani irin tsoro da fargaba yana kara ninka zuciyar shi, a gaggauce ya fita da gawar Fareeha,zuwa wurin su Adam. Daidai shigowar wani irin iska me had'e da guguwa, bin iskar yayi da ido yadda ya nufi dakin da aka kwantar da da Ruman, tabbas yaji a ran shi hakan zai faru. Zubawa guguwar ido yayi tare da kokarin bayan shi, amma sai ya ga ya dawo da karfi ya tsaya a gaban shi cak. Yana wani irin spark tare da gunji ya kuma fita da mugun gudu ya koma inda ta fito, "Alhamdulillahi" ya furta lokacin da ya ga guguwar ta fice, haka suka nufi gida da Fareeha da fuskarta ya sauya halitta, wannan abin duk wa Rumanah taso ya faru sai gashi ta koma Yarinyar da babu ruwan ta.

? ? ? An mata kome sannan akayi jana'izar ta, tare da kaita gidan ta ba gaskiya, sannan suka dawo aka dan zauna. Sai lokacin aka tuna da Ina Darrah ta shiga, har dare babu labarinta.? Shi kam Hayatu asia koma lokacin na farka, ina zaune tare da jin wani irin abu yana yawo a cikin zuciyata, yana shigowa naga yayi min wani irin zuru zuru, gwanin ban tausayi. mika mishi hannu nayi ya zauna a bakin gadon, ya zuba min ido tare da kwantar da kan shi a kan cinyinta. Yana me zaga hannun shi ya rungume ni sosai.
"Ya jikin ta?"
D'ago kai yayi yana kallon yadda nake firgice.
"Allah da ya bamu ita ya amsa" damke hannun shi nayi tare da jin kamar zuciyata zata fado, ajiyar zuciya nake saukewa tare da jin kamar zan mutu,.har wani lokaci shafa bayana yake yana rarrashina.
"Ta mutu? Allah sarki wallahi ban san zata kashe.... A'a ban san marin da ta mata zai kawo sanadin rayuwarta, wallahi ta bani tausayi ne na kaita wurin mahaifiyarta ta, sai gashi haka ya haifar da tashin hankalin da bazan tab'a mantawa da shi ba." Na sake wani irin kuka,.ina jin kamar na mutu na ko zan huta da bakin cikin da nake ji, uwa uba danasanin kai ta yake kara girgiza min zuciyata.

?? Har kusan karfe biyu na dare muna zaune, shafa bayana yayi tare da mikewa ya nufi ban daki yayi alola tare da Waukar abin sallah, ya fara nafillah, ko zai ji sauki a zuciyar shi har wurin karfe hudu saura.
03:50am.

"Ummu Ruman!" Juyawa nayi tare da isa gaban ta.
"Ina jiran ki! Gata zata kawo ki gare ni ina jiranki da saka ran zama karkashin ku"

? ? ? ? ?? Na bude baki zan yi magana ya tab'a ni. A hankali na bude, ina kallon shi. Magana nake so naji wani abu ya cika min nakina, hannuna na kai da niyyar ciro shi, haka nayi ta kokarin ciro shi.
"Ma'idah!" Ya fada a hankali, kallon shi nayi naga inda yake kallo, mace ce sanya da farin doguwar riga me ratsin ja.
"Ku shirya nan da kwana huWu zan zo mu tafi. Ina muku ta'aziyar rashin da kuka yi"

? ...
"Me yasa sai mun je can?" Na tambaye ta,
"Ana biyar halacci da halacci, karki zama daya daga cikin butulci idan kika yi haka ba zaki tab'a yafewa kan ki ba"
Gyada mata kai nayi sannan ta juya tare da tsaga bango zata tafi. Juyowa tai tare da goge kwallar da yake bin fuskar ta..
"Idan ya dawo karka jin tausayin s Drhi ka kashe shi idan haka zai samar da zaman lafiya toh a batar da shi yadda babu wanda zai kuma jin labarin shi" ta fada tare da sake kuka, me cin rai domin da ciwo abinda kake so ya kasa fahimtar ka.

"Mahaifiyar Fareeha kuma a kyale ta halin da take ciki ya ishe har karshen rayuwarta, ita din ta zama mazauni, wasu ne a barta kar ayi saurin rabata da su domin haka ya zama iznina akan wasu masu kokarin ganin sun ga bayan wasu domin dadin ransu" ta fada tare da barin wurin, kallon juna muka yi, lokacin ana kiran sallah farko.

? ? ? ? "Darrah!!" Na fada da ?arfi tare da rike hannun shi jikina yana rawa, tare da sauka daga gadon, zan fita daga dakin.
Dawo dani yayi yana girgiza? min kai.
Kuka na saka Mishi tare da cewa.
"Abinda nake gudu ne ya faru da ita,.barta ta girbi matsalar ta." Ya fada tare da rungume ni,
"Me yasa?" Na fada tare da dukar kirjinta, ina kuka kamar raina zai fita a jikina.
"Don Allah ka cece ta"
"I can't" ya fada tare da wucewa ban dakin domin ba zai iya da al'amarin ba. Alola yayi yazo ya wuce masallaci, ina kuka ko a jikin shi.

? ? ? ? ? ? Karfe bakwai ina zaune, idanuna sun yi sumtum sumtum. Ina zaune A'isha da Abeedah suka shigo da Aslam, yana gani na? ya mika min hannu? tare da jan zuciya, amsar shi nayi tare da lumshe idanuna. K'amk'ame ni yayi yana ajiyar zuciya.
"Ya isa my son!"
"Ya jikin?"
"Da sauki sosai"
Bude baki A'isha tayi zata min magana na watsa mata wani irin banzan kallo.
"Rike gaisuwarki, hankalin ki ya kwanta? Kin yi farin cikin da halin da Darrah take ciki, kema kiyi a hankali abinda da yaci doma ba zai bar awai ba, wallahi ba zan iya mu'amala dake ba, domin ina da yakinin idan ki ka samu wanda zai kashe ni ke zaki bashi abinda zai kashe ni, meye amfanin rayuwar da kika yi da ita baki bata shawara na gari ba,.Yes ita yar uwarki ce ni kuma? bare ce, amma bari na gaya Miki tir da wannan halin naki"

..na gaya mata magana masu zafi, ashe Ummin mu tana bakin kofar tana jin mu, yadda nake gaya mata ai da laifin ta wurin abinda ya samu Darrah. Haka kawai na zama masifaffiya, wunin ranar ban gan shi dake Ummin da Hajiya Murja, suna tare da ni. Sun ki yarda su kawo zancen Darrah.

?? ...
Dake ance a bakin wawa ake jin mutuwar sarki, mahaifiyar ta a haukace tazo tana ihun tare da fadar abubuwan da aka fada nice zan kawo mata karshen su. Ita abar ta kashe ni, ko na gaya mata wani boka ne yayi min asirin da na raba yarta da mijinta da Yaranta. Ashe kuka rahama ce, bakina ya bushe ko yawu babu a bakina, sai ajiyar zuciya nake tare da jin zafi kamar zuciya zata kama da wuta.

? ? ? ? Har zata fita tace min.
"Wallahi sai kin roki ki mutu da halin da zaki tsinci kanki"
"Allah ya maida muku sharrin ku Rushidiyya idan mun cutar dake Allah ya bi miki hakkin ki, idan kuma kece kika nemi ganin bayan mun, toh Insha Allah baku ga kome ba."

?? Tashin hankali yayi yayiwa a cikin family mun.
Duk me Imani idan ya ga halin da Darrah take ciki sai tsoron Allah ya kama shi, domin lokaci guda ta koma wata irin halitta, lokacin da Dr Hayat ya fara ganin ta, sai da yaji wani irin tsoron Allah ya kama shi, domin kuwa lokaci guda kome nata ya jirkice, sai wani irin gurnani take tana karce yatsunta da kasa, zuba mata ido yayi tare da fara addu'ar da yake yi. Ihu ta kwala Aljanun suna fadin.
"Ba zamu bar jikinta ba, dan ko ka fitar damu zamu dawo ita din kamar gida ce a wurin mu babu ita zata, idan ka cika damun mu zamu dauke ta ka nime ta ka rasa, wannan me mugun nufin zaka taimaka mata,.ko ka cire mu sau dari zamu dawo sau dubu!"

Wannan abun ya dame shi kamar zai yi hauka yana ji yana gani babu yadda ya iya dasu, domin zai cire su zai azabtar da su.. amma dake kafirai ne marasa imani zasu cigaba da zama a jikinta, domin suna fita basu wuce kwana Waya zasu dawo. Karshe Uwarta da tafi kowa hauka tazo ta dauke ta.
Farin cikin yayi domin an rage mishi nauyi daga ranar da iyayen su suka zo, nan suka saka shi a gaba da rikon ya hakura yayi mata maganin, toh gashi ma Uwarta ta dauke ta.
**
Darul azab.
Gidan Yarin da Safdar yake zaune ya fashe da dariya, tare da kakkausar murya. Yana kallon yadda Ruman da Hayatudeen suke ciki. Dariya yake tare da kallon wasu daga cikin dakarun da suke gadin shi.

?? "Nawa zan baku na yanta ku, na biya ku?" Kallon juna suka yi kafin suka fita,.nan suka gama shawarar su,.kafin suka koma.
"Shugaban mu matukar ba zaka ci amanar mu ba, mun Amince zamu bude ka ranar shagalin bauta."

?? "Lallai kun cika masu lissafi ina jiran ranar, kafin nan ku isa wurin Durf ya baku kafin alkalami."

? ? ? ?? Haka suka amince. Murmushi yyi. Sannan ya? juya tare da kallon.
Yana zubda wasu irin hawaye Masu Kama da bakin jini.
"Rooman ina nan tawowa gare ki" ya fada tare da juyawa yana kallon kofar. Matukar ya fita anan sai ya karar da baki daya ahalin shi,.kafin ya tunkari Rooman wacce zai dauke ta cak ya dawo da ita duniyar shi ya kashe tsinannen cikin jikinta, sannan ya dauki fansar abinda Hayatudeen yayi. Tsinannen mara mutunci da sanin ya kamata.

Duk sabida shi ne aka tattara shi a nan, ban da rashin irin na dan adam da ya

65 / 69