JINI YAFI RUWA COMPLET BOOK BY D AUTA.doc

Author :  Hadiza D. Auta Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   4 / 69

9K to 12K   out of 206.5K words

take suka cika d'akin. Sai da na dauki kusan minti talatin kafin na farka bayan naka dogon numfashi, sannan na bude idanuna ina kallon su.

? ?? "Sannun Allah ya baki lafiya" inji Innah, gyada kai nayi tare da cewa.
"Yawwa, Amin Ya Allah"
? ?? Shafa kaina Mama tayi tana jin babu dadi a ranta wannan matsalar yaushe yarinyar nan zata huta.

?? Allah ya kawo mata mafita kawai, amma tabbas Umm-e-Rooman tana cikin matsalar rayuwa.

? ? ?? **
Gombe.
State lowcost.

? ?? Kofar gida ne me dauke da manya manyan gefe,har guda uku. Kasancewar babban unguwa ce wanda za a kira shi da karamin estate, duk da cikin tsarin rukunin gidajen gwamantin tarayya yake, kafin ka shiga cikin gidan akwai babban masallacin Juma'a, wanda yake dauke da hawa biyu na gini, sama can gurin zaman mata. Awa na biyu wurin zaman matasa da yara maza ne kasa kuma kuma wurin zaman dattawane.

? ? ? ? Sannan a gefen masallacin akwai Makaranta wanda ake kiran shi Madarasatul Sheikh Ja'afar Mahmud Adam. Shima gidan sama ne me dauke da Class har bakwai, kasa ma Class bakwa ne. Daliban makaranta na sanye da unifoam brown. Da farin hula maza mata kuma da farin hijab.

? ? ? ? Gaba kadan da makaranta akwai wani makaranta wanda shi kuma Makarantar Boko ce me suna.
Markazul Da'awa Memories Academy School.
Duk wadannan makarantun suna farkon shiga Estate din ne. Idan ka shiga cikin unguwar kuwa,

? ? ? ? ? ? A hankali idan ka bar makarantar da masallacin juma'a,.akwai Nana Aisha Specialize hospital. Me dauke da gidan sama, babban wuri aka tanadarwa asibitin,? idan ka tafi kadan a cikin unguwar akwai manyan shaguna har guda biyar. Masu ji da kyau da kuma kayan kawai wanda aka rubuta. M&M Shopping Mall.

? ? ? Daga nan idan ka dauki titi daudar rukunin gidajen ne na Familyn Moddibo Malami, wato Babban Chef Judge. Na garin gombe. Khadi Adamu Moddibo.

? ? ? ? ? ? Unguwa ce me dauke da gashin kanta domin idan zaka shiga unguwar sai ka wuce get uku, get din farko yana dauke da yan sanda da civil depends,? get na biyu yana dauke da Mopol, kasancewar a cikin yaran Khadi Adamu Moddibo yana da Mataimakin IG na kasa, sai get na biyu, Dr Hadiza Abdulwahab Moddibo, Karamar minister ilimi ce. Sai Professor Saifullah Adamu Moddibo,? yana jami'ar Bayero University.

? ? ? ? ? ? Idan aka ce za a fito da yaran Khadi Adamu Moddibo, da matsayin su toh tabbas? za a gama Pagen baki daya ba a gama ba, yaran shi maza da mata Biyar. Ban da Yaran yan uwan shi da suke zagaye cikin Family.

? ? ? ? ?? Sannan rukunin gidajen daya na bin daya ne, Alhaji Abdulwahab, shine Babban dan shi kuma mataimakin IG na kasa, yana zaune a garin Abuja da matar shi Dr Hadiza Abdulwahab Moddibo. Bafulata? ce yar garin Nafada. Kuma yar boko ce da ta taso cikin al'umma da arziki,jama'a akwai dan na gada shine wanda ba zai tab'a d'aga ido ya kalli dukiyar dake gaban shi ba har ya wulakanta wani. Akwai dan na koya wanda yake alfahari da dukiyar da bata shi ba, Amma Hajiya Hadiza ta haWu ta kowacce fuska ce, dukiyarta da aikin da matsayinta basu gabanta al'umma ce a gaban ta.

? ? ? Suna da yara Biyar Maza biyu mata uku. Dr Hayatuddeen Abdulwahab Adam M, shine babba a Familyn baki daya, kuma shine mutum na farko da har yanzun ya kasa auruwa, domin idan aka ce mishi aure kamar an zage shi ne, yake zai fara wani yanayi. Yana da shekaru talatin da tara, kuma babban Malamin addinin Musulunci ne, uwa uba likitan musuluncin ne, bayan na boko ya had'a baki daya, a yadda ake fada a Familyn Moddibo ana zargin cewa aljana ta aure shi domin an tab'a mishi aure Moddibo ya nima mishi mata amma ya kasa zama da ita, bai da lokacin ta ita kuma ta fara wasu abubuwan dole Moddibo ya kira shi da ya sake ta.
? ?? Sai Kanwar shi da take bin shi Fatima tana aure a Katsina dan Sarkin Katsina yana aurenta,, sai Aalim yana aiki da Office din embassy na Malawi. Sai Abeedah tana karatun ta master American University Abuja. Sai Yar karamar su, Nana A'ishah tana Karatu a Novena University warri delta State.

Sai Dan kasuwa Alhaji Abubakar Adamu Moddibo, Babban dan shi Dr Nu'aiym ne, aboki na kuW da kud din Hayatuddeen,. Suna matukar son juna, Dr Nu'aiym yana da aure har da Yara biyu matar shi me suna Hoor domin shuwa arab ce, banbancin abokin shi tuzuranci yana keta mishi hazo.

Sai Abdul Hamid yana kwara yana aikin a babban kotun can domin ya gaji kakan su. Yana da mata da Yaron shi daya, Matar shi ne suna Abla itama yar Fulanin kumo ce.

? ? ? ? ?? Sai? Badhriya tana auren soja suna Jos, yaranta Uku. Sai karamar su Behnaz. Tare suke karatu da Barrah. Da Nana A'ishah, amma sabida sun fita rawan kai Macidd'o ya ce kar a Kuskura a hadu su makaranta guda, domin ba zasu barta tayi karatu ba.

Sai gidan professor Saifullah Adamu Moddibo, yana V.C ne na jami'ar, yana da yara hudu duk mata. Nana A'ishah. Itace Babba tana aure a nan gombe. Baban mijinta yana rike da control na NNPC. Mijinta kuma Babban jami'in tsaro ne na sama.

? ? ?? Sai Hawwa'u tana aure a Bauchi. Sai Yar karamar su, me suna? Barrah yanzun take karatunta na degree

? ? ? Gidan Dan Majalisar wakilai Alhaji Hamza Adamu Moddibo, duk cikin Familyn babu wanda yake da yara marasa jin magana da takadiranci kamar Alhaji Hamza yaran shi ba a musu fada. Babban su yana Jamaica, yaki dawowa domin a gulmace gulmacen da yake yawo an ce Yana can ne yana saffaran miyagun kwayoyi daga kasar Mexico zuwa Afrika.

Sai kanwa shi Me suna Darrah likita ce a Nana A'ishah hospital, sabida Macidd'o tayi karatunta, kuma ta sha alwashin sai ta aure shi ko ana ha maza ha mata, kowa a Familyn yasan wannan burin shi yasa ta zama mutuniyar kirki na fitan hankali ce, irin sune ake cewa Mage mai? kwanciyar daukar rai, matukar tana son abu bata hanzari bata gudu ta iya bin kome a hankali hankali har dai ta cimma nasara akan ta,? Mahaifiyar su Hajiya Rushdiyya, sakada yalla? ce, fara ce kal har tana ja ja, sai Nuruddeen yana nan yana aiki a Ministery of Economic...
Da saura... Domin akwai abin da ba zamu fahimta ba a cikin wannan yanayin tafiyar.
*Wannan book din na kuWi ne*
+2347035133148 Zahrah Addah Ramla or Nijar+22784506476.? 300 500CF
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank
#Mai_Dambu
https://youtu.be/i45MWo6gIh4

EWF

JINI..!
? ?Ya fi Ruwa Kauri?
? *Base on true life story*

*Sadaukarwa ga Family Hasssan Yero Family da Madakin Muri Family*

*Fatan Alkhairi ya isa gare ki Nimcy'luv=?? my Snow White! Na kara Miki da Princess Moana! Domin kina nan kamar Moana Yar barbie doll dina! Wato Yar tsanar roba irin babyn wasan yaran nan>?)? Nagode Sosai*

? ? ?? Mai_Dambu
*Talla! Talla!! Talla!!!*

_Akwai turaren wuta dan Maiduguri da Chad Ubansu me sanyin dadi idan ka saka sau daya sai ka kuma nima idan har kin yarda ke ?asaitacciyar mace ce me aji jaraba turaren wuta na zamani me yayi ba iya nan ba hatta? Humra me sanyin dadi akwai. Ga masu bukatar bikin ko amaryan karni tuntube Aishah Shuwa da kanki zaki bani labarin kamshi...+234 812 535 5554 sai an gwada akan san ba kwarai_

BABI NA BIYAR.

Nuruddeen wanda suke mishi lakabi da Nur, tacceccen dan bariki ne, dan iska ne manemin mata na bugawa a jarida, matukar zai ga Mace toh komin munin ta matukar tayi mishi tabbas zai bita.? Shi yasa abokan shi da sauran na kusa dashi suke kiran shi kusa baka haramun.

? ? ? ? Mutum ne da Allah ya daura mishi masifar sanyi,zai yi wuya ka ga yana magana ko yana hayaniya,

Sai Tagwaye Nusayr da Nusrat Nusayr namiji ne, Nusrat kuma mace, suma dalibai ne a matakin secondry school,? Yar autar Adamu Moddibo Malami, Fatimah wacce suke kiranta da Gwaggo Fa'e. Tana da Yaran Uku Mulham da Muayyad, sai Mace me suna Sarrah ita ma tana jami'ar Ahmadu Bello domin nan ta samu.

? ? Sannan akwai wasu ?a?an Yan uwan Moddibo a gefe guda, Kawu tukur da Kawu Rabi'u,sun tattaro sun zauna a gidan tare da shiga sha'anin gidan baki daya.
?? Kawu Tukur yana da Yara Maza. Biyu Jamal da Abdul Mannan, Jamal shi yake rike da albashin ma'aikatan Asibitin baki daya, Yayi da Abdul Mannan kuma yake gefen koyarwa yana rike da Markazul Da'awa Momerio Academy School. Matar Kasu Tukur irin mutanen nan ne masu masifar son abin duniya, Umma Sadiya, amma bata da gulma ko kananun magana,ganin haka yasa ta dauko Yar kaninta me suna Nuwwaratu, dake Allah yayi yarinyar da araha shi yasa ta saka buri dayawa. Idan ka cire wannan dabi'ar Umma Sadiya bata da matsalar kome.

? ? ? ? ? ? ? Sai Kawu Rabi'u yana da Yara uku, Bashir shine Babba kuma yana aikin soja ne, sai mai bi mishi Nurse ce tana aiki a Nana A'ishah hospital, Sai karamar su wacce itama tana karatun microbiology, a a.t.b.u Bauchi. Matar Kasu Tukur me suna Umma Dahare, irin munafukan matan ne da suka kware a kai gulma da kutungula, ta san hanyar da zata had'a makirci a tashi bom a cikin al'umma, Hajiya Hadiza ce kadai taki bata fuska amma ba karamar munafuka bace.
??
...
A bangaren can na estate din akwai yan aiki maza da mata suma a wurin ba kananun munafukai bane, sai wata Mata ce da mijinta da Yaranta Allah ya tsiratar dasu. Suna kiranta Adda Jebu, mace ce da tasan ciwon kanta tana da Yara da mata wasu na cikin garin gombe sun yi aure.? ?anta na Uku shine hannun damar Dr Hatayuddeen. Yana tare da shi a gida ko a waje, ya zama kamar tail din shi, duk inda ya saka kafa tare suke.

? ? ? ?? Sai Yar Kanwar ta da ta dauko daga hunna kaye, me suna Umma Hani, Addah Jebu tana da matukar hakuri domin ta kwashe shekaru talatin a cikin gidan Khadi Adamu Moddibo. Kuma har yanzu bata daina aikinta ba, domin duk gidan da aka yi Haihuwa itace take musu zaman biki, har ayi arba'in,? sanan dan irin su daka yaji da su abubuwa haka itace take musu mace ce yar amana. Akwai Yar uwan mijinta tunda mijin matar Ya rasu ta dawo wurin ta da zama, itama tana aikin sosai matar me suna Iya Lami, basu da magana ko shiga gulmar yan aikin gidan babu ruwan su, duk wasu masu aiki sun zo bayan su ne, dan haka basu cika shiga harkan kowa ba. Mijinta me suna Malam Musa tsohon driver Khadi Adamu Moddibo ne, kuma har yau idan baya son tafiya me nisa shi yake jan shi a motar shi.

Aminu shine Babban dan su yana koyarwa a cikin makarantar Markazul Da'awa Momerio, sai Nana tana aure a can jeka da fari, sai Adamu takwaran Khadi, yana tare da Hayatuddeen, suna Masar yanzun haka, sai kanwar shi itama tana nan cikin estate din tana auren wani ma'aikacin asibiti kuma itama aikin da take kenan, dan Nurse ce.

Khadi Adamu Moddibo yana da mata daya Hajiya Aisha wacce suke kira Nenneh,mace ce da tayi nisa a hidimar Addini da daukaka kalmar Allah, mace ce me tarin ilimi da sanin ya kamata,mace ce da bata damu da Waukar gutsiri tsome irin na yan bani na iya ba, sai dai a gefe guda Allah yayi mata baiwar fada mafadaciya ce.

? ? ? ? ? Kuma itama bafulata ce gaba da baya, wacce idan har zata yi magana sai dai kaji ta surka da fillanci, domin mace ce mai mugun kishin kabilar ta bata cika Hausa ba, idan zata yi kuwa toh lallai rabin Hausar fullanci ne. Ita ta haifi yara biyar rus din nan babu haWin gwiwa da kowa sai taimakon Ubangiji.

? ? ? ? ?? Kusan yaran Khadi Adamu Moddibo basu zaman gombe idan ka cire Hatayuddeen da Moddibo ya mayyance mishi ya dawo gida yayi aiki domin yana aiki ne a asibitin jami'ar South Korea.? Ganin yaki aure yasa Moddibo yayi mishi kiranye sai gashi babu shiri domin da wasa suka yi musu da Nu'aiym wanda suke kira da Lamido, kasancewar shi din sunan shi sunan wani Baffan? Moddibo ne,? suna zaune da dare suna hira a lokacin sanyi. Dake Dr Nu'aiym irin mutanen nan ne masu mugun barkwace, ya sha shayin da Nenneh ta kawo, ya lumshe idanun shi ya cewa Moddibo.
"Khadi! Na rantse da Allah mata na zata iya wannan shayin yadda kake gwarzanta tsohuwar nan"

"Sha dai" ya ce mishi idanun shi yana kan aikin shi.
"Moddibo! Shin taya zaka iya dawo mana da wancan Imam Win?"
"Kana bukatar haka ne?" Moddibo ya tambaye shi.
Gyara zama yayi sannan ya ce mishi.
"Idan har kayi yadda ya dawo nan da jibi ni kuma zan saya maka sabuwar mota "

Murmushi yayi sannan ya ce mishi.
"Ubanka wancan dan siyasan, na haife shi lokacin ina da mota na bakwai ne"
"Kaga abin da yake had'ani da kai ko? Baka da aiki sai Ash'aria!" Ya fada fuskar shi a bad'e. Yana wani kumburi da hura hanci.

? ?? "Tunda abin ya zama da cin fuska sai da safe" ya miki yana kad'a key din shi tare da nufar hanyar waje.
"Lamido!" Dama sun saba haka idan ya taso suka yi fadar su, yaga sun yi fushi. Saukowa yake tare da nuna musu babu kome a dawo a cigaba da hira.

? ?? "Dawo nan Ubana" dawowa yayi ya zauna tare da b'ata rai.
"Kai ne kake da renin hankali, wata mota ce ban hau ba a shekaru na din nan? Kana tsammanin na kyale Maccido ne haka kawai? A'a na zuba mishi ido ne naga yadda zai kare gudun shi. Kowa yasan Yarinyar nan Yar gidan Ubanka dan siyasar nan tana masifar kaunar shi, na kira shi nace yayi mata magana yace bai da lokacin ta. Amma idan na kira Uwar shi zata mishi magana,? ban san me zanyi wa Maccido yaji dad'i ba, na nima mishi ya'yan manyan mutane da malamai yaki amsar su, na koma gidan sarautar Buba yero na duba mishi Yan mata yaki karb'a. Shi yasa da aka ce Korea ta rike shi ban yi mamaki ba.

? ? Idan shi ba namiji bane ya gaya min gaskiya na nima mishi magani, Darrah tana nan tana jiran shi domin babu fashi akan auren shi da ita, kai kuma kace na kira shi?"

?? Ajiyar zuciya Dr Nu'aiym ya sauke sannan ya kalli Khadi.
"Alkali idan har dawowan shi babu matsala a dawo mana dashi, ko d'azun sai da Nenneh ta min magana. Wai yaki aure bata son ta mutu ba yi aure ba"
?
Murmushi yayi sannan ya ce mishi.
"Insha Allah zata ga auren shi" ya fada tare da kallon Alqur'anin hannun shi.

? ?? Dan haka bayan Dr Nu'aiym yayi mishi sai da safe, ya mike tare da shiga ban daki yayi alola sannan ya fito ya fara gabatar da sallar nafilla, a daren bai rintsa ba sai da ya gayawa Allah kukan shi akan Jikar shi mafi soyuwa a zuciyar shi.

? ? ?? Tsawon kwanaki uku ya dauka yana rokon Allah akan Dr Hatayuddeen sai gashi tare da Adam Jelar shi. Suka dawo domin a can ma yana tare da shi ne Jelar shi, tun gama secondry din Adamu yasa Dr Nu'aiym ya tura mishi Adam, yanzun haka yayi karatun shi a fannin computer.

? ? ? Bayan dawowa shi ne ya kuma tafiya Cairo dama a can yayi degree din shi da likitanci, kuma yana samun damar komawa shine ya fara karatun shi a fannin likitanci a Muslunci. Kuma har lokacin suna tare da Adam.

? ? ? Bayan ya gama domin karatun ya dauke shi shekara uku ne, yana dawowa ya mai da hankalin shi akan aikin shi yana aiki da Babban asibitin Gombe Federal Medical Center.

**
Yola.

Hannun Daddy sai godiyar Ubangiji kawai, nima ba lafiyar nake dashi ba, yau fari gobe? dan har aikina bana zuwa.

? ? ? "Ina ganin zamu tafi da ita gida kawai, domin nafi zargin ciwon bana asibiti bane dan ga Baban su ma." Inji Innah jikinta a matukar sanyayye, domin al'amarin ya ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?bata tsoro kamar ba zata iya ba take gani.

? ? ?? Ajiyar zuciya Mama tayi sannan ta ce mata.

"Allah ya basu lafiya"
"Amin Ya Allah"
? Dake suna cikin dakina ne, had'a kayana suka yi, tunda mehd yayi maganar aure ne baki daya nake wannan yanayin, ban san yadda zan fada ba. Amma duk lokacin da wani da namiji zai min magana akan aure kafin zuwan yau ban tab'a shiga makamanacin halin da nake ciki ba.

?? Dan haka shima ya kafe domin dai shekaranjiya ya shigo kuma an yi magana da shi, rashin lafiya ta ce kawai ya hana ayi dogon magana. Sai da Mama ta had'a min kayana tsaf tare da Innah, sannan aka kira Shahid yazo ya fitar da kayan, ni kuma Mama ta rike ni muka fito waje, aka saka ni a baya. Ina kwance jikin Innah.

? ? ? ? Bankwana muka yi da mutanen Yola muka wuce Mubi. Tun a hanya Daddy yake cewa.
"Alhamdulillahi. Hannun nan dai da sauki sosai, kamar bashi bane ya kumbura sumtun din nan ba"

? "Allah ya baka lafiya!" Inji Driver da zai kai mu Mubi. Ina kwance jikin Innah, baki daya jikina ciwo ya ke min, na rasa inda zan a rayuwata. A hankali na kalli Innah.

"Anya zan sami lafiya?" Rufe min bakina tayi tare da girgiza min kai.
"Insha Allah zaki samu lafiya, cuta da mutuwa duk na Allah ne"? kwalla ce ta kuma zubo min, dan haka koda muka isa wuraren karfe biyu, kai tsaye Falon Alhaji Babba aka kai mu, musamman ni.

? ? ? Tunda aka kwantar dani, suka zuba min ido nayi wani irin fari fat, domin sai da muka iso ne Innah ta lura da haka, gyara min kwanciya aka yi, sannan suka zuba min ido.

?? Flash Back.

? Ranar da na fadi a dakin nan, ranar Daddy yaji kamar an cire mishi ciwon hannun shi, ina kwance. Wannan mummunar matar ta taso zuwa kaina ta tsaya

4 / 69