JINI YAFI RUWA COMPLET BOOK BY D AUTA.doc

Author :  Hadiza D. Auta Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   3 / 69

6K to 9K   out of 206.5K words

ku barni" ta daka musu tsawa, tare da koran su. Suna fita ta dauki wayar ta, tana me niman Number Innahr Rooman. An gaya mata ana waya dan haka ta dakata, bayan minti biyar ta kuma gwadawa ya shiga.

?? "Hajiya Mariyah!" Ta kira sunan Innah da kaushi,
"Na'am! Azeemah" Innah ta amsa mata a hankali,
"Yarinyar nan bata da lafiya! Na kuma kiranki na gaya miki a karo na biyar, Yarki bata da lafiya, na gaya miki. Tun shekara goma da suka wuce Yarki bata da lafiya baki tashi ba, na kuma gaya miki Yarki bata da lafiya baki tashi ba, toh bari na gaya miki matukar kika zauna shiru. Wallahi rayuwar ta yana cikin garari. Dan haka ki san abin yi. Allah yana tare da mu?"

? ? ? Jin motsi tayi a bayan ta, ta juya.
"Mama karki raba ni da ita, idan kika kuskura kika saka aka yi wani abu a tsakanin mu, sai mun kashiiiiiiiiiiiiii" jifa tayi da wayar tare da kiran sunan Allah da karfi take ya b'ace. Da gudu yaranta suka shigo d'akin, ganinta suka yi jingine da wardrob dinta, tana haki.

?? "Mama lafiya?" Suka kalle ta, tare da tambayar ta,? had'iye yawun tsoro tayi tare da cewa.
"Babu kome"
"Meye ya samu Mama?"
"Wallahi Addah Rooman gata nan dai sai haki take kamar tayi tsere." Ajiyar zuciya ta sauke tana kallon su, kafin tace musu.
"Babu kome fa" ta mike, tare da amsar wayarta, ta ajiye a gadon, sannan ta wuce ban daki tayi alola. Sannan ta shigo cikin dakin ta same ni ina zaune.
"Mama kina boye mana wani abu?"
"Ban boye kome ba, kawai dai."
"Ina ruwanki da Rooman? Waye ya aike ki shiga rayuwar ta, baki ji ba ko? Abin da ya faru da duk me taurin kai shi ya faru da Babangida dan haka ki tsaya akan Yaranki da mijinki, ki mai da hankali gurin kare kanki da muguwar kishiyar ki, Rooman mallakar mu ce, dan haka ki ja bakin ki yi shiru ko kuma mu saubantaki"

? ?? Murmushi tayi sannan tace.
"Rooman!" Bude kwayar idanun nayi tare da kallonta, cikin idanun yayi sak da na kura. Ta razana amma kuma dakiyar da yake ranta yayi yawa. Murmushi tayi sannan ta ce.
"Waye kai?"
"Ban sani ba?"
"Me yasa duk lokacin da aka fasa aurenta kuke damunta?" Ta kuma tambayar Rooman da take tsaye jingine da wardrob,
"Indan kika shiga hurumin mu zamu baki mamaki;"
"A yan shekaru na, dan na mutu ba wani abu bane domin na sha ruwa, dan haka ku fita ku bar ta ta huta"
"Hmm! Zamu tafi da kome ma. Da abin da kike shirin aikatawa ba sai kin tuna da shi ba" daga haka na d'aga hannun dama na, na wani haske ne, a can kuma na zube a gurin, tare da ajiyar zuciya.
A hankali Mama ta taimaka min ba haura gadon, na kwanta. Sallah ta gabatar tare da addu'a, tana idarwa ta kalle ni, ta rasa meke faruwa ma, domin kamar an wanke mata kanta take ji.

? ?? A hankali ta gyara min kwanciya, sannan ta fita tana kallon Yaranta a falo amma bata kula su ba, kitchen ta nufa. Anan ta hadu da Aunty Bintu. Murmushi tayi mata, sai lokacin kalaman aljanin nan ya dawo mata. Hmm. Tace a ranta rana me had'a abubuwan da zata had'a bata dai yarda da batun aljanin ba, domin tasan su kan su, munafukai ne suna iya had'a husuma.

? ? *
A hankali kowa ya manta meye ya faru baki daya, satina biyu na koma aiki,? a wannan satin naji labarin Khamil Jafar Muhammad Muri zai yi aure, itama yar Gwaggo mu ce, dan haka nayi musu fatan Alkhairi.

? ? Lokacin da na koma aikina dayawa abokan aikina sun ta tambayana meye ya faru, murmushi na musu sannan na cigaba da aikina babu dare babu rana.
? ? Dake ina aikin Bank ne shi yasa bani da lokacin kowa sai na aikina da kuma abubuwan da suka shafi yan uwana.
"Rooman Yakub Yero!" Muryan MD din mu ne, d'ago kai nayi ina kallon shi.
"Na'am Sir"
Na mike tsaye ina kallon shi,
"Naji an fasa aurenki da dan uwanki." Waya ta ce tayi kara na duba.
Mehd! Murmushi nayi tare da duba wayar, kallon MD nayi da ya daki table din da nake zaune a kai.
"Ya ina magana zaki mai dani dan iska?" Ya tambaye ni a tsawa ce.
"Sir wannan fa rayuwata ce, kuma ban ga dalilin da zai saka ana binciken abin da ya shafi privet life dina ba." Na fada ina kallon kasa.
"Lallai toh same ni a Office"
"Babu inda zata!" Mehd ya bashi amsa, kwarjinin da yayi mishi yasa ya kasa mishi tijara.
"Yan mata! Ya aiki tuba nake"
"Kai dan gidan Uban waye zaka shigo mana banki da gadara"
"Kayi kuskuren kula Budurwan da Mehd ya fada soyayyar ta, dan haka ka kome Office dinka zan zo naji da kai. Kin ga gama aikin nan kizo ki raka ni"
"Toh" na fada tare da had'a aikin gabana akan lokaci, ina kallon shi lokaci zuwa lokaci, domin ya kara kiba da kyau.

Bayan na gama ya ce min.
"Zamu iya tafiya?" Murmushi na sakar mishi sannan na fito na nufi office din MD. Ina zuwa na same shi sai gumi yake.
"Sir!"
"Don Allah ki tafi" ya fada min muryan shi na rawa, tab'e bakina nayi tare da barin shi a gurin, ina fitowa na kalli Abokan aikina nace musu.
"Don Allah bari naje na dawo,"
"Sai kin dawo" suka fada min,
"Bari na shiga gurin MD na mishi kashedi"
"Don Allah ka kyale shi."
"An gama Gimbiya" ya saka kai muka fita, aikuwa kamar jira abokan aikina suke mu fita suka dasa gulmar mu.
"Aikin kenan, ina zata yi aure ta zama gwamjo daga wannan yazo ya kwasa sai wannan yazo ya kwasa,bata da aikin fari sai dai idan an shirya aurenta ta fasa."

Fitowar MD ne ya saka su dukkan su, suka yi shiru.
"Munafukan banza munafikan wofi, akan uban waye take? Shegu marasa abin yi"

Sannan ya bar su a gurin yana hararan su, shiru suka yi babu wanda ya kuma magana.

--
Muna fita kuwa bamu tsaya ba, sai wurin shan ice cream,nan ya sayo min chocolat ice cream, sannan ya kawo min ya zauna yana kallona.
"Me yasa tun da na gaya maka batun auren da zan yi baka kuma juyowa ba? Ai ko babu kome nayi min fatan Alkhairi!"

Murmushi yayi sannan ya kalle ni da kyau, kafin ya ce min.
"Duk wanda zai so ki bayan ni ne, akan me zan zo nace miki sai an jima? Bayan ina tare da ke? Ko hakura da auron nan ina sonki" ajiye ice cream din nayi tare da kallon shi.
"Akan me zan hakura da auren?" Na tambaye shi, wayata ce tayi kara.
Dubawa nayi na ga Daddy.
"Assalamu alaikum! Dad" dakyar ya ce min.
"Na'am Rooman! Kina ina?" Yadda yayi magana sai da ya bani tsoro, mik'ewa nayi tare da cewa.
"Dadda! Ina nan me yasa meka?"
Yadda na rud'e yasa Mehd shima mik'ewa,
"Na'am. Hannuna ne yake ciwo gani A Yola nazo ganin likita"
"Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun!"
Da sauri na ture ice cream din da ban kai ga sha ba, na fita da gudu. Biyo ni yayi tare da cewa.
"Lafiya?"
"Baba na ne hannun shi yake ciwo"
"Toh Allah ya sawwaka" ya fada min, tare da bude min kofar na shiga motar, ganin yadda na rud'e yasa shi tukin da sauri, muna isa asibitin ban kai ga mishi magana ba na fice da sauri kamar wata tab'abbiya, ina shiga Emergency, na kira wayar shi, Innah ce ta Wauka.
"Dadda kuna ina?"
"Gamu a dakin da yake dan gama da inda ake tiyata"
"Innah" na shiga niman dakin da sauri, kafin na samu. Yana zaune a tsakiyar gadon hannun na bisa kan shi, Innar mu tana mishi fifita. Na karasa gefen shi na zauna.
"Dadda na?"
"Hmm! Umm-e-Rooman!" Kuka na sake mishi da shi,.hannun sai wani sheki yake yana motsi kamar a cika ruwa a cikin abu ana juya shi haka hannun yake motsi. Kuka nake har ina shasheka.

Ayarin likitoci ne suka shigo duba hannun, kafin suka koma gefe, suna faWin.
"Toh gaskiya sai mun nime shi! Ko mu tura shi Federal medical center Gombe"
"Dr me zai hana mu kira shi, zai iya zuwa koda na kwana biyu ne tunda muna da cases dayawa akan irin wannan abun!"
"Ka fadi gaskiya"
" Alhaji kayi hakuri, ba zamu saka maka ko ruwa ba,.bari mu dauki hoton hannun mu turawa Babban likitan mu, ya gani. Zai zo ya duba ka"

"Dr yanzun babu abin da zaku iya mishi?" Na tambaye shi,
"Kiyi hakuri zamu abin da zamu iya amma Insha Allah zamu kira shi."
"Toh" na fada ina kallon su,
"Allah ya bashi lafiya"
"Amin Ya Allah" muna faWa.
Fita yayi na kalli Innah.
"Taya haka ya faru?" Na tambaye ta,
"Hmm! Bayan tafiyar ku da kwana uku, yace yayi sartse, da na duba hannun babu kome, toh sai muka bar shi a haka, bayan kwana uku sun tafi sallar juma'a, Deen ya buge mishi hannun da Murfin mota. Kinji sanadin kenan." Hawaye ne ya zubo min..
#Mai_Dambu
https://www.wattpad.com/1144426297?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_published
EXQUISITE WRITERS FORUM.
JINI..!
? ?Ya fi Ruwa Kauri?
? *Base on true life story*

*Sadaukarwa ga Family Hasssan Yero Family da Madakin Muri Family*

? ? ?? Mai_Dambu
*Talla! Talla!! Talla!!!*

_Akwai turaren wuta dan Maiduguri da Chad Ubansu me sanyin dadi idan ka saka sau daya sai ka kuma nima idan har kin yarda ke ?asaitacciyar mace ce me aji jaraba turaren wuta na zamani me yayi ba iya nan ba hatta Humra me sanyin dadi akwai. Ga masu bukatar bikin ko amaryan karni wato me jego tuntube Aishah Shuwa da kanki zaki bani labarin kamshi...+234 812 535 5554 sai an gwada akan san na kwarai_


BABI NA HUDU.
"Innah toh shine baku gwada na islamic ba, ni dai yanzun mu fara gwada na gida"? na fada musu ina kuka,

"A'a kawai zasu duba idan asibitin bai yi ba zamu koma gida" inji Daddy. Kallon Innah nayi domin tayi magana, bata ce kome ba, kawai sunkuyar da kai tayi haka ya tabbatar min da cewa tana bin bayan mijinta.? Kasa jure ganin shi nayi cikin wannan yanayin na kuma rushe musu da da kuka ina faWin.

"Don Allah ku bari a maka maganin Islamic zaka ji dadin shi." Share ni yayi kamar bai damu da halin da yake ciki ba yace min.
"Hmm! Da dai kin tafi kin gayawa Hamma Chindo ne da yafi akan ki zauna kina mana kuka kuma nasan Mariyah tana bukatar abinci ko?"

? ? Ya fada tare da kallon ta cikin karfin hali, gyada kai tayi. Baki daya sun haWe min kai, haka na fita tare da jan kuka na.
"Rooman!" Dawowa nayi ina kallon su.
"Ki share kwalla babu dad'i ki fita kina kuka."
"Toh Dadda." Goge fuskata nayi sannan na saka kai na fita ina jan kuka na.
Mehd na hango a waje yana jirana, a hankali na isa wurin motar shi na kalle shi.
"Akan me yasa baka biyo ni cikin asibitin ba?"
"Oh ai ban zata zaki yarda na shiga cikin bane naga kamar ke daya kika damu da iyayen ki"
"Ayya kayi hakuri" na fada tare da shiga motar ya shiga shima.

? ? ? ? "Banki ko Gida?" Ya tambaye ni,
"Kai ni gida" na fada mishi ina kauda kaina, tare da kallon window.
"Meke damun shi?"
"Hannun shi ce ta kumbura kamar an hura balloon"
"Allah ya sawwaka"
"Amin"
Haka muka isa gida ya sauke ni.
"Nagode sosai"
"Allah ya bashi lafiya" ya fada tare da kallona.
"Amin Ya Allah Nagode sosai" na fada mishi ina shigewa gidan. Yadda na bude get din na shiga ina jin kunci a rayuwata, ban san meke min dad'i ba, na wuce zuwa cikin gidan, a falon na samu Mama. Zama nayi ina jin damuwa a raina.
"Yau kin taso da wuri" murmushin yake nayi, sannan na ce mata.
"An kawo Daddyn mu asibiti ne, bai da lafiya"
"Toh Allah ya bashi lafiya"
"Amin Ya Allah," na fada, fitowar Aunty Bintu yasa mu, kallon ta tana latsa wayar ta.
"Mutanen banki an dawo lafiya?"
"Alhamdulillahi!" Na bata amsa,
"Dawa suka zo?"? Mama ta tambaye ni.
Jim nayi kafin na kalle ta na ce mata.
"Da Innar mu"
"Toh ai ya kamata ki shiga kitchen a nima musu abin da zasu ci"
Mik'ewa nayi lokacin Aunty Bintu tana kokarin wurgo min tambayar ta,
"Waye ba lafiya?"
"Mahaifinta" mama ta bata amsa a takaice,
"Toh Allah ya kyauta"
"Amin Ya Allah" muka fada lokaci guda.

?? D'akina na wuce nayi wanka tare da cire kayan jikina, na fito na nufi kitchen na daura abincin da zan dafa musu. Ina aiki hankalina yayi nisa akan aikin naji kamar an shafa kafana, a matukar razane na kalli kasa na, ajiyar zuciya na sauke tare da kallon magen Mama.
"Boss kai ne haka?"
"Meow" ya fada min, dan haka ban kula shi ba, na cigaba da aikina har na gama had'awa na fito.
"Har kin gama?" Aunty Bintu ta tambaye ni,
"Eh na gama had'awa"
Daga haka muka shiga hira, sai wajen karfe biyar na yamma muka nufi asibitin,? dukkan mu.

Koda muka shiga cikin hannun ta motsa sai yadda kai yake yana wash wash, ni da ban da juriya na fashe da kuka, ina me rike shi tare da jin kamar zan cire ciwon a jikina. Shigowar likitocin ya sa muna zuba musu Ido.
"Kuyi hakuri, Dr ba zai samu zuwa ba baya gari, dan haka zamu sallame ku, idan har ya dawo zamu nime ku"
"Toh ya zamu yi da hannun shi? Kuma kuce zaku sallame shi bayan ciwon ba ta gida bace."

"Gaskiya da ace Dr Hayat yazo toh da tabbas shi iya bada wani abu akan ciwon shi, amma bai zo ba asalima baya kasar yana kasar egypt, idan ya dawo zamu tura mishi sakon ku." Dr din ya fadi haka, kamar nayi kuka haka nake kallon mahaifina da ciwon hannun shi, haka muka tattara muka dawo gida, har Baffa Chindo ya dawo domin an gaya mishi halin da ake ciki, kuma ta tawo, kallon kanin shi yayi sannan yace mishi.
"Ina ga bari na kira Makocina shima naga yana da dan sani akan matsalar makarai." Ciro wayar shi yayi ya kira Makocin mu, Baban Abba domin yana da yaro Abba,. Can kuwa sai gashi ya shigo zama yayi sannan ya kalle mu bayan mun gaishe shi.
"Rooman!"
Da sauri na d'ago kai ina kallon shi.
"Ya aiki?" Ya kuma tambaye ni,
"Alhamdulillahi! Muka had'a idanu."
Sarawa kaina yayi na mike a hankali na bar falon, juyawa yayi sannan ya ce.
"Alhaji bani da maganin ciwon shi, sai dai kuma zan had'a mishi maganin da zai rage mishi zafin ciwon nashi da girman, amma bani da wani abu a kai. Sannan taya haka ta faru?" Ya tambayi Daddy, nan ya gaya mishi abin da Ya faru.
"Karka kuma dukar Umm-e-Rooman. Idan kuma ka cigaba zaka iya rasa rayuwar ka, shi yasa na kore ta, gaskiya ban da wani sani akan matsalar ta, amma tabbas? akwai lokuta da wasu manyan abubuwa zasu fito ta sanadin ta, amma kuyi hakuri. Na jima ina son nayi magana amma kamar rufe min ba?i ake yi.

? ? Alhaji Chindo ai na gaya maka ta sanadin ta, Allah zai iya kawo wasu abubuwan masu kyau da marasa kyau."

?? Yana fada tare da tofa addu'o'in a jikin hannun, kafin ya mike ya ce.
"Shahid muje na baka addu'o'in da za a shafa mishi."

?? "Toh" ya mike, sannan yayi musu bankwana, juyawa yayi tare da kallon su ya ce.
"Ku saka ido akan Rooman"
"Insha Allah" yana fita Shahid ya bi bayan shi har gidan shi, ya had'a mishi magani, sannan ya ce mishi.
"Akwai matsala a rayuwar Rooman, ko nima kasada nayi da na shiga wannan al'amarin,dan haka kayi baya da ita karka shige mata."
"Insha Allah"
Suka yi sallama, yana fitowa gaban shi ya fadi, kallon kofar gidan su yayi, daga inda yake. Ya hango wasu manyan manyan karanuka.
"Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun!" Ya furta lokacin da suka yo kan shi da masifaffen gudu, kare kan shi yayi, yana ambaton Allah,? tsit yayi tare da jin wani sanyi na kad'awa. A hankali ya bude idanun shi, yaga babu kome a kofar gidan, da sauri ya isa tare da shiga cikin gidan, yana shiga ya samu ana tattaunawa akan matsalar Baffan Umm-e-Rooman, mika musu maganin yayi suka fara amfani dashi ana shafa akan hannun.

? ? ? ?? *
Ina shiga daki na kwanta, tare da shiru ina nazarin abin da na gani a idanun malam, karar da wayata tayi ya sani dauka tare da sakawa a kunne na.
"Mehd"
"Hmm! Kana lafiya?"
"Lafiya lau, dama akan maganar auren mu ne nake son muyi magana, iyaye na sun dame ni"

? ? ? ? ? ?? "Hm! Yanzun an kawo Baffana asibiti jinya ne zan musu maganar aure? Ko an ce maka bani da hankali ne da zan same su da maganar aure?"? Yadda na tsaya ina mishi rashin mutunci sai ka dauka wani abu me ?arfi yayi min nan kuwa raina ne ya b'aci da maganar auren.

Murmushi yayi sannan ya ce.
"Ok kiyi hakuri ban kyauta ba, Allah ya bashi lafiya zan zo insha Allah na duba jikin shi." Ya fada min, kashe wayar nayi tare da jin takaicin ambaton aure da yayi. Ina kwance naji kamar ana goge bango kamar irin b'era na cin abu a dakin mutum.

? ? ? ? Bude idanun nayi a hankali tare da nazarin ta ina b'era ya shigo dakin. A hankali na juya tare da kallon inda nake jin motsin, rubutu naga aka yi a jikin bangon dakin da jini.
? ? *SAI MUN KASHE KO MU B'ATAR DA*

Wani irin tsoro ne ya kamani, na juya da sauri, ina kallon kofar da zan fita. Kofar ta rufe rub.

? ? ? Cikin tsananin tsoro na juya tare da kallon matar da take takowa gabana.
Tana isowa ta d'ago idanunta,
tana nuna ni tare da fashewa da dariya, kallon dakin tayi tare da hango kwaro da sauri ta mika dogayen yatsunta, ta kamo shi ta wurga a bakinta, tana taunawa. Ai kuwa na fara amai kamar nice nake taunawa. Kama wuyana tayi tare da d'aga hannunta ta fara spelling magical words.
Sai da tayi nisa har dakin yana girgiza, domin na fara hango duhu. Kawai sai gani nayi an yi sama da ita, zuSewa nayi a wurin na suma.

? ? Shigowar da Innah tayi tare da Mama duba ni, suka same ni a wurin kwance yasa baki daya suka rud'e,

3 / 69