JINI YAFI RUWA COMPLET BOOK BY D AUTA.doc

Author :  Hadiza D. Auta Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   7 / 69

18K to 21K   out of 206.5K words

Ubansu me sanyin dadi idan ka saka sau daya sai ka kuma nima idan har kin yarda ke ?asaitacciyar mace ce me aji jaraba turaren wuta na zamani me yayi ba iya nan ba hatta? Humra me sanyin dadi akwai. Ga masu bukatar bikin ko amaryan karni tuntube Aishah Shuwa da kanki zaki bani labarin kamshi...+234 812 535 5554 sai an gwada akan san ba kwarai_

BABI NA TAKWAS.

"Na sani ba zaki yarda da ni ba, amma wallahi ba haka bane, babu abin da zai faru, na miki al?awarin haka, a duk na mune babu abin da Barmani zata musu."

"Na dai gaya miki ki ja mata kunne, wallahi wani abu ya faru sai na fadi abin da zai sakata jin kunyar zama a cikin al'umma da cikin gidan" inji Maman Babangida.

Kasa kasa da Murya Inno tayi tare da cewa.
"A'a bana tunanin za ayi, kiyi hakuri" ta faWa cikin damuwa.

?? Bayan ta kashe wayar ne, ta kalli dakin shiru.
Abin da ya faru shekarun baya yana dawo mata. Daki daki,
Shekaru Ashirin da bakwai baya.

Wasa suke a bakin kofar gidan su ita da Mariyah kasancewar an yi ruwan sama sosai, dan haka suka nufi kofar gidan tare da tsugunawa suna kallon ruwan da yake gudana.
"Addah Salaha,. Kalli yadda dandali kwadi suke yawo a cikin ruwan. Karar motar katako suna ji, a hankali suka d'ago kan su, tare da kallon matar da tazo ana sauke kayanta.

"Laa Innah Barmani! Sannun da zuwa Sannun da zuwa" rike kayan hannunta suka yi tare da kallon ta.

? ?? Biyan kudin tayi bayan ta mika hannu zata dauki kayan, Yaron motar ya kai hannu tare da cewa.
"A'a bari na kai miki cikin gidan mana" kyale shi tayi sai da ya kai cikin gidan sannan ya juya zai fita ta dafa kafadar shi tare da cewa.
"Nagode Allah ya saka maka da gidan aljanna." Tana sake shi ya juya tafi ita kuma ta kalli hannunta yayi damshi, kallon kasa tayi sannan ta durkusa ta dauki kurwan yaron ta? nufi cikin gidan, dake yaran sun shiga cikin gidan domin sanar da zuwan ta, tana shiga zauren gidan ta dauki kurwan yaron ta d'aga wani kututture ta saka sannan ta mai da iccen ta mike tare da shiga cikin gidan.

Tana isa asalin cikin gidan ta ciro maitar ta sab'a a bishiyar gwaiba, sannan ta nufi cikin gidan da fara kwance bisa fuskarta. Nan gidan ya hautsine da murna,

? ? Tana hango kananun yaran gidan harshenta ya fara zazzagowa, tana jin ina ma da bata cire maitar ta ba, da ta samu kurwowi dayawa, amma babu kome zata adana abinta tasan gaba? zai mata amfani, dan haka aka shiga gaisuwa.

?? Ita din yar uwa ce ga Yadiko Delu,? dan haka suka shiga cikin dakin ta, kallon juna suka yi bayan sun kuma gaisawa.
"Ya zaman gidan na ku?" Kasancewar ita a taraba take aure, dan haka bata cika zuwa na sosai.

? ? ? ? "Lafiya lau, da fatan kin baro gida lafiya?"
"Lafiya lau"
"Toh madalla" Yadiko tasan halin ta, kara kallon ta tai sannan tace mata.
"Ina fatar kin rabu da wannan mugun abin?"
"Eh mana, na rabu da shi. Tunda kun ki amsar shi."
"Allah yayi mana tsari" inji Yadiko Delu,

"Kai Delu sai kace na baki wani abu mara kyau, toh Allah ya baki hakuri mai ta aiko baka ci dan kanka ba, zaka ci kodan kare rayuwar ka da ta iyalin ka,"

? "Hm! Keda ya zama miki dole ba, amma yadda nake da saurin fushi idan naci maita sai na gama da kowa" ganin Yadiko Delu ba zata fahimta ba, ya sata share zancen ta nufi waje tayi alola tana kallon Yawuro da take ta kwashe abinci tace mata.

"Yawuro Uwargida a gidan Malam Mamman Muri, naga abu ina son da fatan ba zaki hanani ba." Kallon ta Yawuro tai dan bata matan wani sha'ani ta ya tab'a had'a su taji ana cewa kowa ya maka dan shi ya rike Barmani ta iso idan ka shirya zaman makoki a gidan ka toh. Jin haka yasa ya fara kokarin fahimtar Barmani tana maita kenan. Dan haka ta kuma saka ido sosai akan Yaranta tare musu addu'a sosai. Tana kuma karb'a musu jiko da hayaki.

? ? "Ayya Barmani, me kika gani kike so?" Ta tambaye ta a hankali tana kwashe abincin ?arshe.
"Mariyah"
"Barmani" Yadiko Delu ta kira sunan ta a tsawa ce.
"Kai Delu wasa nake mata" ta wuce tayi ban daki bayan ta kama ruwa ta fito, sannan tayi alola ta samu yaran suna cin abinci.
? ? Dakin yar uwarta ta shiga, ta zauna tare da shiru kafin ta mike ta gabatar da sallah da yake kan ta, tana idarwa ta nufi hanyar waje bayan ta zauna domin matan gidan a wurin Alhaji Muhammad Muri suke cin abincin su.

? ? Kallon Yaran tayi bayan ta zauna tace musu.
"Kowa ya zab'i abin da yake so ni kuma ba bashi." Dake Salaha tana da masifar wayo kuma Yadiko Delu ta mata fada akan karta yarda Barmani ta ce ta zab'i abu zata kashe ta ne, ta daina ganin su, aikuwa tuni tsoron Yar uwan Mahaifiyarta ya shiga ranta. Ganin Mariyah tana kallon Innah Barmani yasa ta rike hannun Mariyah tana girgiza mata kai.

? Rashin wayo, sai ta kai hannunta zata zab'i hannun da Barmani ta dunkule. Salaha ta buge hannun, kallonta Barmani tayi sannan tace mata.
"Ina ruwanki tunda ke ba zaki yi ba." Yadda tayi mata maganar tana hararanta yasa baki daya tsoro ya kamata, dan haka ta koma gefe tana kallon su, har Mariyah ta zab'i dukiya bayan ta ce mata.
"Wannan kudi ne, wannan kuma Yara ne wanene kike so?" Abin ka da kuruciya sai ta kai hannunta kan dukiyar tana faWin.
"Addah kullum zan ci dad'i na barki yara kuma zasu dame ni, tare da su zamu yi ta cin daWin."

?? "Yawwa Shalele, zan zaki ci dad'i." Tana fadar haka ta kalli Salaha tare da zabga mata harara, har iyayen su, suka dawo.? Bakin Salaha bai yi nauyi ba ta gayawa Uwarta, itama bata yi kasa a gwiwa ba, tayiwa barmani fada da cewa matukar bata kyale yarinyar ba zata gayawa Alhaji Muhammad Muri, jin haka yasa baki daya tsoro ya kamata ta ce.
"Kai wasa nake fa, ban mata kome ba, wallahi babu maitar ma yanxun."

? ? ? ? Sanin halin Alhaji Muhammad Madakin Muri yasa ta fadi haka domin zai iya sawa a mata wulakanci akan Yaran shi.

? ? Cikin dare bayan kowa ya kwanta ta, mike tare da nufar inda bishiyar gwaibar nan ya?e ta dauki maitar ta, ta had'iye sannan ta nufi zauren gidan ta dauki kurwan yaron driver nan, ta fita tsaya tare da kallon shi tana murmushi, tunda ta had'iye maitar ta zama wata irin tsohuwa me ban tsoro da kyama, dan haka ta nufi hanyar waje bayan ta koma tsuntsuwata duji (wato Mujiya kuyi hakuri da Hausar nawa)

? ? ? ?? Tashi tayi sama tare da cillawa can samaniya, ta nufi wani tsubiri, ta sauka sai ga wasu ma sun sauko, mikawa shugaban su tayi kurwan yaron ta kalle shi kafin ya mikawa sauran aka kwantar da shi, aka fara rawa.

?? _Tun bul tun bul!_
? ? ? _Tun bil tun bul_
? ? _Mun kashe Yaron nan_
? ? _Tun bul tun bul_
? ? _mun ciye kurwan_
? ? _Tun bul tun bul_
Suna rawa kayan su na kwaSewa, har sai da suka yi tsirara, sannan suka fara aiki yanka kurwowin mutane, bayansu gama suka watsa a katon tukunyar da yake gaban su,

? ?? Wani kwalbar shugaban su, ta bude bayan ta diga wani bakin ruwa. "Fuuuuuuwa!" Hayakin dark pink ya tashi sama, kafin suka had'a baki wurin cewa.
"Wureraaaaaa!"
Suka d'aga hannun su, sama tare da kara furta "Wureraaaaaa". Bayan sun gama,? kowa ya fadi bukatar shi. Itama Barmani ta fadi bukatar ta tare da mika mahaifar Mariyah.

Kallon ta shugaban tayi sannan ta ce mata.
"Ba zan amshi mahaifar ba, ki ajiye can domin zata haihu ko bud'ade ko bijima, zata auri me arziki ba wai fatar ki bace ta kai ta haka ?addararta ce dan haka babu bukata domin haihuwa zata yi. Sai dai mu ajiye wannan muyi ta gana mishi azaba koda ba zata haihu da wuri ba. Kuma Uwar Yarinyar bata wasa da addu'a ban san wata irin sa'a kika ci har kika raba da mahaifar ta ba"

? ? ? Da haka suka gama kai kukan su, sannan aka dauko wasu irin kwanuka aka zuba ana zuba musu kurwowin da aka dafa.

? ? ? A hankali kowa yake shan nashi sannan suka wani irin ihu, tare da fadin.
"Wureraaaaaa!" Har suka gama kowa ya kama gaban shi,

? ?? **
Lokacin fitar Barmani akan idanun Salaha ce, dan haka bata san lokacin da ta dawo ba, domin tayi barci, amma kuma ta kudira a ranta ba zata tab'a barin ta cutar da Mariyah.

? Wannan shine abin da ya faru, har zuwa ranar da aka da akayi auren su, tana rike da abin lokacin da Allah ya budawa Yakubu ne abin ya fara bata tsoro domin yayi Mahaukacin kudi,kafin Allah ya had'a su da Shalle ta basu makarin wancan abin.

? ?? ...
A dawo labarin.

?? Yau kwana biyar ya rage dan haka ina kwance, naji kamar ana kirana. Mik'ewa nayi tare da fitowa kofar part din mu, wani haske na gani ya bayyana, a hankali na tako har wurin hasken da yake inda bishiyar rimi yake na tsaya,? tun ina yarinya nake ganin wurin ban cika ganin abin da yake wurin ba, amma yau naga wani mutum da ya juya bayan shi, farin gashin kanshi ya sauka a gadon bayan shi.

? ? ? ?? Yana zaune kamar yadda na saba ganin shi ya lakwashe kafar shi yayi zaman yogo, dafa kafadana aka yi, na juya tare da sake wata ?atuwar kara.
"Addah!!!" Abdul Malik ya kira sunana na, lokacin na suma.

? ? Daukata yayi tare da nufar cikin gidan da ni.

? ? "Lafiya Abdul?" Inji Daddy,
"Ina lafiya naga taje ta kafe wancan bishiyar rimin da ido bata san nazo ba, na tab'a kafad'ar ta shine ta suma,"
nan da nan aka shiga yayyafa min ruwan sanyi,? ajiyar zuciya na sauke tare da kallon su.

"Meye ya faru?" Suka min tambayar. Dafe goshina nayi tare da cewa.
"Babu kome"
"Toh meye ya kai ki wurin bishiyar rimin can?" Inji Daddy,. Kallon su nayi kafin na shiga ?o?arin tuni abin da ya faru, na manta baki daya.

"Wallahi ban sani ba, ni kamar kira na aka yi ko meye oho ban sani ba fa" na fada musu ina kokarin mik'ewa.
"Toh Allah ya kyauta" inji Daddy,

"Amin Ya Allah" Innah tace tana kallona, ina shiga dakina na kwanta tare da sauke ajiyar zuciya,ina kara jin wani sanyi a kaina zuwa kirjina,, lumshe idanuna nayi barci me mugun karfi yayi gaba dani.

? ? A wani katon fili babu kome a wurin sai Flowers.
"Kina son su ne?" Aka fada a bayana, da sauri na juya tare da kallon shi, gefen shi wasu yan mata ne, suke shafa shi tare da bin jikin shi suna mishi wani irin romancing, kallon shi nayi fuskar shi lullube da farin gashi. Juyawa nayi da sauri domin daya daga cikin yan matan ta mike tare da hawa jikin shi, tana wasa da al'auran shi.

? ? ? ? "You like then?" Ya kuma tambaya na, gyada mishi kai nayi duk da na juya mishi baya, jin shi nayi yana dab dani, na d'ago kai na ina ?o?arin kallon fuskar shi. Amma na kasa hango fuskar shi,. Hannun shi ya d'aga tare da kallon wurin Flower ya nuna da shi take wuta ta kama Flower.

? ?? "Me yasa?" Na fada da karfi ina kallon shi, bayan na kalli yadda flowers din suke ci da wuta.
"Ni ya dace kice kina so,duk namijin da ya kuskura ya ce sai ya rab'e ki haka zan mai da shi, ke mallaka ta ce."

? ?? "Ni? Ina ruwa na da kai? Meye ya had'a ni da kai? Babu abin da zai tab'a had'a ni da kai dan haka ka kyale Ni." Na fada tare da kaucewa da gudu, sai dai duk gudun da nake ban iya wuce shi ba, iyakata a wuri guda nake ta falla gudu, sai da ya riko hannuna, tare da daka min tsawa, wanda ya sani daina ji da gani, na yi baya zan zube ya tare ni.

? ? "Ke mallaka ta ce. Ina kare ki ne domin kar a cutar dake daga ranar da na matsa sai buzunki, dan haka karki kuskura raina ya b'aci kuma, idan ba haka ba zaki ga izayar azaba sai kin mika wuya zan kyale ki" ya fada min haka yana kallon jikina. Kai hannun shi yayi zai tab'a ni na farka daga mugun mafarkin da nake, kallon gefe da gefe nayi,tare da addu'a na koma na kwanta.

? ? ?? Yola.
Kwanciya yayi sabida ya gaji, baki daya wunin yau yayi shine a zirga-zirgan bikin shi da su, sabida ya gaji ainun yana kwanciya barci ya dauke shi. Yana fara barcin ko minti talatin be yi ba, yaji ana daure shi.

"Har ka isa ka shiga cikin rayuwar ta? Ita din namu ce, idan ka sake aka daura auren baka fasa ba, zamu kashe ka kamar yadda ka gani, wurgaka zamu yi a cikin wancan tukunyar azabar."? Bude idanun yayi tare da kallon sama.

?? Wata tsohuwa me ban tsoro ce a saman kanshi gefen ta,wasu manyan karannuka ne, suna haushi.
"Zamu kashe ka! Idan ba...." Bayyanar hasken da yayi a dakin yasa suka b'ace, yana zuwa ya shake wuyar Babangida.

"Duk wanda ka ga zai zo maka bayan ni ne, zan kashe ka ko na shafe tarihin ka, ka rabu da Rooman ko na salwantar da rayuwar ka.". Yadda ya shake shi ne,yasa shi zubda kwalla a hankali bakin shi ya motsa tare da cewa.
"Rooman tawa ce, ba zan tab'a barwa wani ba" sake shake shi tayi tare da daka mishi tsawa.
"Karya kake tawa ce" ya cigaba da shake shi har sai da ya daina numfashi sannan ya sake shi, domin ya zata ya mutu nez yayi b'acewar shi a dakin.

? ? ? ?? Babu wanda ya san abin da ya faru har kusan washi gari, ba a gan shi ya tafi masalaci ba, shine Mama tazo duba shi,? yana sume. Salati tare da kiran Yan uwan shi, suka kai shi asibitin.? Dakyar aka samu ya farka.

? Yana bude ido, ya fara kokarin tashi yana ture mutane, yana faWin.
"Wallahi bakin isa ba, Rooman tawa ce" ganin haka likitocin suna danna mishi alluran barci.

Ga bikin saura kwana hudu, basu fada a can mubi ba, aka cigaba da kula shi shi har, ana gobe daurin auren yaji dauki kamar bashi ba.

? A ranar suka nufi Mubi,. Kallon Mahaifin shi yayi sannan ya ce.
"Abba! Idan ina raye Insha Allah Rooman mata ta ce,"
"Insha Allah zaka rayu ma" ya fada mishi,suna isowa aka fara shagali tare da hidima sosai, sai dai bai zauna a cikin mu ba, falon Alhaji Babba ya nufa, ya zauna yana faWin.
"Dattijo! Don Allah ka min al?awarin babu Rooman! Iya haka zaka min ka tabbatar min da ina kaunar Rooman"

"Takwara na baka Rooman har abada!" Ya fada tare da kallon shi.
Murmushi yayi sannan ya ce mishi.
"Toh Insha Allah, duk inda na kasance zan waiwayo gare ta, ni dai ka tabbatar min da Rooman ta zama tawa"
"Na baka Rooman bata da mijin da ya wuce ka."
"Nagode sosai, Allah ya sadamu da Alkhairi"
Ya fada tare da mik'ewa yana jin kamar idan ya bar gidan bai zama dole ya kuma daina ba, domin shi daya san yadda yake ji a jikin shi baki daya, ji ya?e yayi ta tafiya ko zai samu sauki da yake nima akan rayuwar shi.
300? ... Insha Allah'
+2347035133148 a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A'ichah
+22784506476
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank
#Mai_Dambu
EXQUISITE WRITERS FORUM.
JINI..!
? ?Ya fi Ruwa Kauri?
? *Base on true life story*

*Sadaukarwa ga Family Hasssan Yero Family da Madakin Muri Family*

? ? ?? Mai_Dambu

BABI NA TARA

Daukar motar shi yayi tare da nufar hanyar gari, yana ji kamar ana kad'a shi tamkar yadda ake koran shanu ana zuga musu bulala haka yake jin shi. Ji ya?e kamar duniyar ce bata da ce da shi ba, shi yasa zai tafi zai tafi haka yake ji kamar ana koran shi daga garin Mubi.

Sai da yayi dogon tafiya, tare da isa tasha, ya tsaya yana kallon motar da yake jin ana faWin.
"Lagos!!! Ibadan!!!" Motar ya fada tare da kifa kan shi a jikin kujeran."

? ?? **
A can kuwa hak kawai naji raina yana b'aci sosai, dan haka na shige daki na fashe da kuka, sosai nake kuka ina jin wani irin kunci.? Shigowar kanwata Hamdiya ta zuba min ido.
"Addah Rooman meke damun ki?"
"Babu kome Diyah" dake haka muke kiranta.
"Toh ai sai ki taso a saka miki lalle"? ta faWa min, kallonta nayi domin na fara jin haushin ta, a hankali na mike tare da nufar kofar, ina fita Yagwalgwal Kanwar Alhaji Babba ta yab'a min lallen me shegen yawa haka suka feshe ni da turaren kamshi.

Ina kuka gefe guda masu kidan garaya ce a gefe da molar su, ana kid'an garaya,. Sarawa kaina yayi dan dole na kwace kai na, na gudu falon yadiko Salamatu,tana zaune ta ganni na shigo ina zare ido.
"Uwar me kika shigo yi?"? Ta tambaye ni, kallon ta nayi, sannan na wuce dakin ta, na kwanta a saman dogon kujeran da yake uwar d'akinta, duk da suna falo, kuka nake wanda baki daya ya d'aga musu hankali, duk jarabarta da bala'in ta, sai da ta sauko tana kallona.

"Ke ni bana son munafunci da kinibibi, uwar me aka miki" d'ago kai nayi tare da kallonta da kwayar idanuna sa suka yi fari kal.
"Subhanallahi! Rooman!" Ta kira suna na, d'ago kai nayi da fararren idanuna.
"Yadiko don Allah kice a fasa auren nan" na fada ina rike hannun ta. Wani kallo ta min tare da juyawa tayi ta bar dakin. Kafin minti talatin maganar ta karad'e Familyn mu dama gamu da yawan bala'i.

? ? ? Kamar za a cinye ni haka aka tura ni har falon Alhaji Babba, ina zuwa na zube ina kuka.
"Toh bamu kira ki kiyi mana kuka ba, me ye hujjar ki ba kin Babangida?"

"Wallahi ban sani ba, amma don Allah ku fasa auren, ina jin kamar zan mutu" na fada musu haka, Haushin da wasu suka

7 / 69