Author : Jamila Janafty Category : Romantic Hausa Novels
makaranta Tunda Zain yana zuwa Wajen AIKI bai zama ba lalle Tafiyansu tazo Daya ba,Shidai Zain ya bata Gudummuwar Siya mata Tsaleliyar Waya sai ta bama Zainab Tsohowar Tata wacce Abba Ya siya musu ita da Zafeera tun suna gida
Tun Zuwanta makaranta Suka Hadu da Laila Adam,Course Dinsu Daya,Kuma Sai Halinsu yazo Daya Tunda itama Lailan akwai kokari anan garin Bauchin take da zama ita da iyayenta Duk ba masu Hali bane Suna Da Rufin asiri,Bayan Zafeera Laila ce kadai Halima ta yarda Ta sake kawa da ita Tunda Zafeera Tana makaranta sai dai in sunyi Waya,Duk wanda ya zauna da Halima Dole yasan Waye Firstlove agereta,Laila Taje har gidan Halima Tasan Zain Shima yasanta Tunda Yana zuwa Daukanta Wani Lokacin in bata je da Motarta ba,Har gidan su Umma Taje,Tasha kuma Raka Halima Gidan Alhaji Tsohi suje su gaishesu Yarinyar tana Da Hankali Shiyasa Har Zain ya yarda Halimar Tayi kawance da Ita.
Halima Bata Taba ganin Dina ba Sai sau Daya Da Zain zai kaita makaranta Ranar Motarta ba Lafiya tana Wajen gyara sun Fito sai ya samu Kiran gaggawa Daga asibitin sai ya Fara Biyawa da Ita asibitin Har Cikin Office Dinsa awannan Ranar ne wasu Suga Firstlove dib Dr.Zain,Aranar zaina taga Dina Ta ganta Ido Cikin Ido Tunda batasan da zuwanta ba Ta Shiga Office din Zain din ne Ta ganta ganin Ta Tsaya Tana kallonta ne yasa Shi Zain din ya Gabatar da Halima ga Dina Itama Dinar ya gabatar da ita akan cewa abokiyar aikinsu ce Dr.Dina gaddafi Sherrif.
Hannu Dina Tabama Halima sukayi musabaha kowanne na Kallon kowa da Wani Tunani Dabam Ita Halima aganin Farko Taji Zuciyarta ta Fara rawa Akan Dina Haka kurum taji Matar bata kwantamata ba Duk Kokarinta na tayi mata Dariya kasawa Tayi sai yake,Shima Zain din bai yarda Zainar Tasa ta gano wani Abu ba,Ya Tattarata suka bar asibitin a Hanya da zai kaita Makaranta sai da Halimar tace ita Kuwa Taji Zuciyarta bai kwanta mata da Wannan Dinar ba,Da ta Fadi Haka yaji mamaki ammh sai ya Shanye mamakinsa yace mata Dama Haka Allah ke Abunsa ba kowa bane zakaji ya kwantamaka ba Ammh Dina Bata da matsala Daganan bai kara mgana ba itama Bata kara mai Zencen Wata Dina ba ammh Abun ya Tsaya mata arai Har Haddir ta Tambaya yace mata Karta Damu Juz kawai abokiyar aiki ne Shi ina zai yarda aji mutuwar sarki abakinsa ba Domin Har ga Allah Tsausayin Halimar yake ji Yana Tsoron Faruwar wani abu indai Sirrin Boye ya Fito Fili.
*******
Fitowa Tayi Daga Library Ranta a matukar bace da kalaman Laila agogon Fatan Dake Hannunta na kamfanin Gucci takai Duba Taga har pass 10 kuma sai 11am zasu Shiga Lectures Din Dr.Tafida ne Baya son Wasa ammh da ba Haka da gidan Umma zata wuce kawai.
Departement Dinsu ta koma ta Samu Waje ta zauna Ta Fito da Wayarta Tana latsawa Zafeera take son Ta kira sun kwana Biyu Basu yi mgana ba,gabadaya Walwalarta Ta Ragu akowani Dakika kalaman Laila gareta Suna Dawowa mata kuma Suna sanya mata Faduwar gaba da Wani Rauni wanda Ta Rasa Daga Ina yake Fitowa.
Ta kira Zafeera 2missedcalls bata Daga ba sai ta kyaleta Tana Tunanin kila itama Tana Class ne Tana kokarim maida Wayarta Cikin karamar Jakarta Laila ta kariso Wajenta bayan Ta gaji da nemanta Kafin ma Ta samu Zama Halima tayi Saurin Dagowa Lokaci Daya Tana Dakatar da ita Hannu.
"Wai bana ce miki ki kyaleni ba Laila..? Don Allah ki barni Dazu najure kin Fadi maganganu Son Ranki Buh by now Zuciyata bazata iya Jure waba gwara ki Kyaleni kamar yadda nace Simple...! Tafada Lokaci Daya Tana Mikewa Cikin Bacin Rai da Sauri Laila Tasha Gabanta Tana Fadin"Naji zan kyaleki Halima..Ammh plz ya kamata Ko Sau Daya ne kima mganata kyakyawan Fahimta ba Nufi...!
"Ya isa Laila..Sai yanzu na gano Inda kika Dosa Wato Kina son mijina,Shiyasa kika Fito da wannan Hanyar da Rashin Jituwa zai Fara Shiga Tsakaninmu saboda ki samu Wata Dama ko..? Tafada tana Watsa mata wani kallo Waro Ido Laila Tayi kafin Tace"Wa...? Innalillahi Wlh banzata ba Halima Banzata zaki min Wannan kallon ba..Ammh komai ya Faru ba laifinki bane ni naja..Allah ya baki Hakuri Insha Allahu haka bazata kara Faruwa ba kuma ina so ki sani yau ko Mutuwa kikayi bazan iya Cin Amanarki ba Ballatana Kina Raye Halima..!
Ta karishe Fada Idanuwanta na kawo kwallah kafin ta Juya Ta Fara Tafiya Halima da kalaman Laila suka kashe ma Jiki ta Daga Kafa Tana Tafiya ga Lailan Tana Fadin"Haka zalika kamar yadda Ko Da bana Raye bazaki iya Cin Amanata Haka ma Firstlove Ko Gawata bazai iya Cin Amana ba Laila Ballatana Da Rai na da lafiyata Bazan Taba yarda Dake ba..Domin Firstlove ya Fara Min Kauna ta gaskiya Tun ina Cikin Mahaifiyata..!
Cak Laila Ta tsaya ammh bata Waigo ba sai Halima ce Tasha Gabanta Tana Fadin"Nima am Sorry In mgana ta bata miki Rai I did Mean to hurt u..! Tafada Tana Riko Hannuwanta Mirmishi Laila Ta saki kafin tace'Na Fahimceki Kawata..Samun Wannan kaunar ta Firstlove dinki gareki sai An Tona Irin Labaran da muka Sha karantawa ne English Novels Da Hausa Banta Tsammanin akwai Ira iransa a xahiri ba..! "
Halima Ta saki wani kayattacen Mirmishi Tana Fadin"Gashi kin gani Wajen ZAINAZAIN..! laila ta Jinjina kai Tana Fadin"Kwarai kuwa na Shaida wannan kaunar Daga Allah ce.."Dariya suka Saki Lokaci daya kafin su Fara Tafiya Tare Hannayensu na Cikin na juna suna mgana Sama sama Wanda duk wanda ya gansu zai Fahimci Suna da kyakyawan alaqa akwancensu.
Cafteria suka je suka Sha Lemo da Snacks kafin su Wuce Class sai 1pm suka Fito Daga lectures Daganan Halima tayi ma Laila Tayi Zuwa Gidan Umma bata yi musu ba Ta Bita ammh Bayan ta Kira mamarta Ta gayamata Suna zuwa Gidan Umma su Saudart suka Fara Ihun Murnan ga Anty Halima ga Anty Halima Tun kafin ma Tagama Daidaita parking Dayake suna Haraban Gidan ne sai ga Zainab ta Fito suka Rumgume juna cikin Ladabi Take gaida Laila wacce Darajan Halima yasa Duka yaran ke Kiranta Anty Laila.
Bude Bayan Mota tayi ta Dauko Cake din suka Dunguma Cikin Gida Da Umma suka Fara cin karo Halima Tatafi gareta ta Rumgumeta Tana Fadin Tayi Kewarta Itama Rumgumetan Tayi Tana Fadin Itama Tayi kewarta Nene na gefe Tana Fadin Ayi dai mugani Umma tace anyi kuma Sun gani Laila na gefe Tana Dariya Cike da Sha"awan wannan ahalin Kafin Halima ta saki Umma Taje ta Rumgume Nene tana gaisheta ta Shafa kanta tana saka mata albarka Laila ta gaishesu suka amsa Cikin Sakin Fuska Suna Tambayanta karatu Daganan zainab Ta Shiga nuna ma Halima da Laila Vidio da sukayi ma Su Umma da Safe Lokacin da Zain yake yanka Cake sai da suka gama gani Halima tace kowa yazo suyi nasu Shagali Yanka Cake din akayi kowa yaci Halima Ta Diba Dayawa tace Na Alhaji Tsoho ne da Hajiya Mama su Umma nata Dariya Sallah sukayi sukaci Abinci kana Laila Tayi musu Sallama Tatafi Gida Saboda Mamarta zata Fita tace ta Dawo Da wuri Tunda kannenta Duk kanana ne suna Makaranta Gidan ba kowa.
Sai da Halima Tayi La"asar kana Ta bar gidan Shima Firstlove ya Kirata yace ta koma Gida Hakanan Daganan Gidan Alhaji Tsoho ta Biya ta gaishesu Shi da Hajiya Mama da Tabawa ta kuma basu nasu Cake din Hajiya Mama naci Tana Fadin"Shidai Zanullahi dan gata ne..Kowacce Shekara sai munci wannan Abun mai Dan karen Dadi da Sunan wai Bazday dinsa..!
Gabadaya Halima da Alhaji Tsoho suka sakamata Dariya Halima na Fadin karta Damu zata Shiryama Alhaji Tsoho ammh sai ya Cika Shekara 100 aduniya kana Zata Shiryamai Suna Ta Firansu suna Dariya Bata Jima ba tayi musu sallama Tatafi Alhaji Tsoho na kara Jadaddamata ta kula ta Dinga Tuki a Hankali tace Insha Allahu akoda yaushe tana Alhafari da Alhaji Tsoho Domin Tana kallonsa kamar kakanta ne ya Kure mata Dukkan Rashin kakanni Shi da Hajiya Mama.
Daganan Motarta Ta Shiga Ta koma Gida ta Fara Tunanin me zata Dafa musu na Dinner ita da Firstlove gefe Daya kuma Lokaci bayan Lokaci kalaman Laila na Dawo mata Ganin ta saka Abun Aranta zai Dameta sai ta Watsar da wannan Tunanin ta kwabe kaya ta Shiga tayi wanka ta Saka Saukakkun kaya na Zaman Gida Riga da Wando ta Fada Kitchen.
*Janafty...*
*ZAINAZAIN..!*
_(Is a love Story and Betrayal)_
*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janaftyshakira*❤️
*BOOK 1*
0️⃣8️⃣
"Dina na Fita Daga Cikin asibitin bata Zarce ko"ina ba sai Dan madaidaicin Gidanta wanda mahaifinta ya Siya mata take zaune aciki Daura da asibitin yake ba Nisa Wanka Tayi ta Sauya kaya zuwa Wata Doguwar Rigan Abaya baka tayi Rolling din Vail Din gyalen Bisa kanta kana ta Dauki Wayarta Ta kira Zakiya tace mata Tana Office ne ko Tana gida..? Nan tace mata Tana Office,kawai sai ta yanke Kiran Wani Hill din Takalmi ta sakamai mai Tsawo Ta zari key dim motarta Wanda ke Hade Dana gidanta ta Fito ta Kulle kana Ta Fada Motarta ta Bata Wuta kai Tsaye Babban Ofishin Kamfanin Sadarwa Ta MTN ta Nufa Zuciyarta Cike da Tunanin Yadda zatayi Da Zain Domin bata Jin zata yi Sanyi kamar yadda yake Bukata agaresa.
Tana zuwa ba wani Neman izini Domin Duk wanda yasan Zakiya acikin ma"aikatan Dole yasan Dina Saboda kawaye ne na Sosai koda ba Bangaran karatu Daya suka karanta ba aikansu ya kawosu gari Daya kuma Halayyansu da Dabi"ansu tazo Daya Shiyasa Bond Din kawance su har yanzu yana nan Zakiya Babba ce awajen tana matsayin Matakiyar Md kenan Wato Manaja Shiyasa Tunda Dina ta Shigo ma"aikatar take ta samun gaisuwa yake kawai Take Tana Daga Hannu Domin bata Cikin Hayyacinta Gudu Gudu Sauri Sauri ta karisa ga Babban Office din zakiyan wanda ya zama Tamkar gidanta Wajen Zarya kamar yadda Shima Office din Dina na asibiti ya zama Dandalin Zakiya din.
Tana Shiga ta isketa Hakimce kan Kujeran ta mai Juyawa da Mutum din nan katon Office ne wanda bayan katon Tuberin aiki da kujerun karban baki akwai Kujeran gida wadanda Suka karama Ofishin kwanya sai karamin Firaza sai Kofar Tiolet inda Mutum zai Shiga in Lalura ta kamashi.
Dina na Shigowa ta Watsar da Key din Hannunta da wayarta Saman Daya Daga Cikin Kujerun wajen ta Nufi Fridge din ta Bude Ta Dauko Ruwa Swan mai Sanyi akwai kananan Kofuna a kife saman Fridge din ta zari Daya ta Tsiyaya ta kafa kai Tana Sha Cikij gaggawa Duk zakiya Dake Hakimce Tana Waya idanuwanta na kanta,Sai da Ta kusa Shanye Rabin Ruwa kana ta Dakata tana Sauke Numfashi Lokaci Daya kuma ta maida komai Cikin muhallinsa ta Baro Wajen zuwa Kujeran Dake Fuskantan Zakiya ta Zauna Tana maida Wani karamim Numfashi.
Ita kuwa Zakiya kai ta Cigaba Da kadawa Tana kuma Wayarta Lokaci Daya Kusan Mintina goma da Shigowar Dina Office din ammh bata gama ba sai wani narkema wanda Take wayar Dashi Take tana Tsarashi Da kalamansu na yan Duniya Ran Dina ya Fara baci Ta kai Duba Zuwa ga Agogon Guccin Dake Tsitsiyan Hannunta Lokaci Daya Ta saki Tsaki Tana Fadin"Ko in koma Inda na Fito ne..?
Tafada Tana Sakarma Zakiya manyan Idanuwanta Mirmishi ta Saki Tana Girgiza mata kai Kafin Tayi Saurin sallaman wanda Suke wayan Lokaci Daya Tana kallon Dina Cikin Shakiyanci Take Fadin"Dr Dina Gaddafi Sheerif...'
Karamin Tsaki Dina Taja kafin Tace"Karki Batamin Rai..wai don Allah zakiya yaushe zaki Daina Harka da yan Barikin nan Tsoffin Banzan nan ne..? Me kike nema Kudi..? Suna..?matsayi..? Duka fa Allah ya baki Zakiya Wannan Rayuwar Da kikeyi sam Bata Dace da mace mai aji kamar ki ba..!
Wani Shu"umin Mirmishi Zakiya Tayi kafin tace"Allah ko.? Ke bari ni nayi Tsoffin Banza Da kike mgana Duk fa yan Siyasan munr mu Dina gwara na karbe kudaden Tunda Duka kudin aikinmu da"aka basu suke Shashancin Dasu,gwara na karbi Rabona Domin ko Dangote na zama a kudi Wlh bazan hakura Da Nema ba Dina Kudi Sune Rayuwa Kinji..!
Tafada Tana wani Rausayar Dakai Dina ta gyara zama Tana Fadin"Yan Siyasa fa kikace Zakiya..? Zakiya tace"Yes Sufa nace..Ai sune yan Harka ke bari nayi Miki gwari Gwari Wlh Duk yan Siyasan kasan nan namu Kadan ne na Allah Sauran duk yan Bushashe ne.."Da sauri Dina Tace"Ammh banda Ubana ko..?
Wata Shegiyar Dariya Zakiya ta Saki Harda Buga Tebur kafin ta Dakata Tana kallon Dina Cikin Iya bariki ta Daga mata Gira Tana Fadin"Ammh ai kema kinsan Barewa batai gudu Danta yayi Rarrafe ba ko.?
Cikin wani irin kallo Dina Tace"Bangane ba..! Zakiya ta kara wani Sakin Dariya kamar Wata Shashasha Tana Fadim"Dina kin sanni na sanki...Zan tsage miki gaskiyata kema zaki Tsagemin ita koda bazatamin Dadi ba ki Rantse da Allah me mahaifinki ki zuwa garuruwa yanayi da Sunan Taron Siyasa..? Shifa ba Dutse bane Tun muna yara sai ya Shafe sati Bashi agida to yana ina..? Ke Namiji fa sunansa Namiji Tawajena ni kin ganni nan Ko Ubana ban yarda Dashi ba Ballatana Uban Wata..!
Ta karishe Fada Tana sakin Wata karamar Dariya Tsaki Dina Ta saki Kai ta Dauke tana Fadin"Zakiya bana som iskanci..Ni Dad dina ba irin Kazaman Da kika saba bi bane...Na yarda dashi Taron Siyasa yake zuwa Fakat..!
Zakiya na Dariya tace"Yes Shima ya yarda Dake..Aiki kika zo Bauchi ba Sheke ayarki kikeyi keda Dr Zain ba ko...? Tafada Tana kallonta ido kawai Dina ta sakarmata ta kasa Mgana Ganin Haka yasa Zakiya ta kara saka Dariya Kafin ta Tsagaita Tana Fadin"Is Ok....Tuba nake Tawan Babanmu ba Dan isk..!
Bata karisa ba Dina Ta Wawuri Wani Littafi ta wargeta Dashi kaucewa Tayi Tana karamar Dariya Tana Fadin"Ahh..Meyayi zafi haka..? Toh Allah baki hakuri ban karawa Tawajena..!
Tafada Tana kokarin Hadiye Dariyarta Cikin Kufuluwa Dina ke Fadin"Ammh dai kinsan ance mu Nemi Duniya kamar bazamu barta ba ko..?
Zakiya TaDaga kira Tana Fadin"Yes haka kuma muke Neman lahira itama kamar bazamu Risketa ba.."Hararanta Dina Tayi Tana Fadim"Toh ke Ai Duniyar kadai kike Nema kin manta da zaki Lahiran Wata Rana..!
Zakiya Tace"Duniyan Dai muke Nema Ba nake nema ba..Duk wani Zunubi Danake aikatawa kema kina aikatashi Dina Kinga kuwa miye maraban Dambe da Fada ai Duka Sunansu Fada..! Dina Takadai kai Tana Fadin"A"a muna da Bambamcin Ni Tunda Nake wa Zain kadai na yarjema Gonata Zakiya kinsani ina Son komai nawa ya kasance Specail ne ke kuwa nayi nayi na Raba ki da Rabama kowa ni Jig and Jag Jikinki kinki jina Zakiya in ma Kina so ne kiyi irin nawa ki Zabi Wani Daga cikinsu kawai kice ya Fito kiyi auranki yafi Wannan Rashin Madafan..!
Zakiya Ta Daga kanta Sama na wani Lokaci kafin Tace"Ai Duka Zina Zina ce Dina..Da wanda yasha Giya ta Dubu Daya da wanda yasha ta Dubu Dari Duka Dai sunanta giya sukasha.Dake da kike Harka da Mutum Daya Dani Da nake baza Hajata Duka A mizanin sunan Zunubai Daya ne Dina ko ki yarda karki yarda Tare zamu gyara Halinmu im ma Haka kikeso kice..mganar kuma na samu wani na Aura nifa ba wanda yamin ne..Dama zaki mim Hanya na samu wannan Cute and Handome Dan"uwan Farkan ki dinan Allah zan Tuba na Bishi muyi Aure na Tabbata yadda Zain yake Cika ki tsaf nima na Tabbata zai Cikani Har ya kure Kwadayina..!
Tafada Tana yar Dariya Hararanta Dina Tayi Tana Fadin"Karma ki saka ma Ranki..Domin wannan Haddir din sai yafi Zain Taurin kai...Kullum.Fuskarsa ba Fara"a ba Ke ba,nikaina ya Tsanane kamar ya Fahimci da wani Abu Tsakanina da Dan"uwansa in ya ganmu Tare ya Dinga Hararata kenan Kamar na Tsaremai wani abu.!
Zakiya Ta Tabe baki Tana Fadin"Kinga Abunda yasa naki yarda da Shawaranki kenan..Ka tsayama Namiji Daya ya zame maka Ciwon ido gwara ki barni Ahaka gida goma mganin kashe Gobara."Kai Dina ta Jinjina kafin Tace"Allah ko ya kyauta..!
Zakiya Tace"Nagaba..Domim wannan ya Riga da ya Faru..Lafiya na ganki a Hanzarce..?
Tafada Tana Tsareta da ido kai Dina Ta Dafe kawai batare da Tayi mgana ba Cikim Mirmishi Zakiya Tace"ZAIN again..?
Kai Dina ta gyada mata Cikim Rauni Tace"Zakiya kin sani Kaf Duniya Ba Namijin Da nike so kamar Zain..Ammh kuma Shi yana Bani ciwon kai kullum Kalaman bakinsa bai Taba sona ba kuma bazai Taba Aurena ba Mace Daya yake so kuma itace Kadai matarsa Firstlove Halima Zakiya na Tsani jin Wadandan Sunayen zuciyata na kuna Jiya nan mukayi Fada dashi wai kamar ni Zaim zai kalla yace Bayajin Dadina Halimarsa na Sakashi Kuka Tundaga Farkon Dare Juz Imaging fa Zakiya Ni Wai Zaim ke Fadama haka Nida maza Dadama suke son na basu irin Damarshi ban basu ba ammh Shi ya samu yana min Wulakanci yana Hadani da wannan Banzar matar Tashi Wacce Daga ganinta Jikinta ba Ruwan da yake isanta ma Ballatana ta jika wani Dashi..!
Tafada Cikin Jin Haushi da Kishi Dariya Zakiya ta saki Har tana Mikewa Tsaye Galala Dina Tayi Tana kallonta ganin Yarda Take Dariya kamar wani Abun Dariya ta gayamata Cikin Takaichi ta kauda kai sanin Halin Zakiya na Dariyan mugunta Tana Cikin dariyan ne ta kware Ta Fara Tari Cikin Kufuluwa Dina tace"Allah ya kara.!
Da karfi Fridge Zakiya ta Nufa ta Bude ta Ciro Ruwa ta kafa kao Tasha sai da ya isheta kana ta Sauke Goran Ruwan Tana Sakin Ajiyar rai Cikin Mirmishi Dina Tace"Gud...Dama ai mganin mai Dariyan mugunta kenan..Nakawo miki matsalata ammh Sai kika Fara min wannan Banzar Dariyan Taki..!
Zakiya ta murmusa kafin ta kariso Ta zauna Kujeran Dake fuskantan Dina gab Da gab Cikim Danne Dariyanta Take Fadin"Ya zanyi..? Wlh Nakasa Danne Dariyata ce Wai Shi Zain din yace ke baki sakashi kuka Daga Farkon Dare sai Matarsa..? Tafada Cikin som karta Saki Dariyanta Cikn Jin Haushi Dina Tace"Wlh..Jiyan nan ya Fadamun wai ya gaji da Tararrayanmu..Dama na gaya miki koda yaushe Cikin Fadin haka yake so yake na Rabu da Dashi yaci Bulus Zakiya ni kuma Kinsani Duk Duniya Zain kadai nake so kuma Shi nake mafarkin ya zama Mijina ko Ta Halin kaka...!
Zakiya Tace"Ikon Allah ai bai Kamata ki Damu ba Sanin Dama Aikin Boka ne ke Tafe dashi.
ammh ba Domin Haka ba da Tuni ya Rabu Dake..."Dina ta Rausayar Dakai Tana Fadin"Duk nasan wannan Zakiya plz ki gayamin ya zanyi..? Wlh bazan iya Rabuwa da ZAIN ba Shine kadai Namijin Dake gamsar dani..!
Zakiya