Author : Jamila Janafty Category : Romantic Hausa Novels
Kafafu Da Sauri ya Sallame ya Dauki Fitilansa da Sandansa zai Fita Sai maryama ta Farka ganin zai Fita yasa Ta Tambayeshi sai yace mata yana Zuwa ya Fita da Sauri Yana Fita kawai yaci karo da Wani katon Mutim Cikin bakaken kaya ya Haskeshi da Fitila yana Tambayan waye Kafin ma yaji wani Abu Daga Bayansa yaji an sakarmai Harshashi aciki nan Take ya Fadi matattace Jin wannan karan Harbin Shi ya Rikita Maryama Ta Fito Da Gudu Ga Ciki Tana kuka Itama nan Take wani ya sakarmata Harshashi aciki Itama Ta Fadi ba Rai.
Innalillahi Wa"inna illairaju"un wannan ahali Sun ga Tashin Hankali kwarai yan Fashi Sun Shiga Har Shashen Alhaji Usman basu dai kashe kowa ba ammh Sun Karbi kudaden Daya Dawo Dasu Daga Tafiya yana Shirin Washegari zai kai Banki,sai kuma Dan kunnayen Zinaren su Nene da wasu kudaden Dake Hannunsu Sukayi ma Alhaji Usman Dukan Tsiya sai da ya Suma kana suka Tafi Su Nene suka Rude sai kuka Ga su Zain Suma kukan suke Zaina da Zafeera kuwa sai kuka Suke na Tashin Hankali Umman Zareena ita Tayi Hausan Kiran Wayar Dr.Saulawa ta Na kuka Tana gayamai Halin daSuke Ciki Cikin Tashin Hankali Shida Hajiya Mama suka Nufo Gidan Domin Daman Kaf an anguwan ba wanda bai ji karan Harbi Biyun Da sukayi ba.
Abun Tsausayi Suna Zuwa Gidan suka ga Get a wangale Hankalinsu ya Tashi ai basu Rude ba sai da suka ga gawan Maryama da Abdullahi kwance afarfajiyan Gidan cikin Jini Sai Zuciyoyi Suka Raunana Idanuwa Suka Zubda Kwallah Su Nene sun Rude matuka ga Halin da Suke Ciki ga mutuwar Maryama da Mijinta Sun Rasa Ina zasu Tare Hawayensu ne,Wanda ke zuba ba kama Hannun Yaro ganin Alhaji Usman baya Cikin Hankalinsa ne yasa aka Tattarashi Zuwa asibiti Dr.Saulauwa ya Kira yan Sanda suka zo Suna Ta Binciken gawan su Maryama Abun gwanin Ban Tsausayi Hajiya mama Kuwa Ta Rude sai kuka Take tsakanin ita dasu Nene an Rasa mai bama wani Hakuri.
Sai da yan Sanda suka gama Bincikensu kana suka Tafi da Cewar Insha Allahu za"a kama Yan Fashin da sukayi wannan aikin Sai alokacin Dr.Saulawa ya iya Kiran Chan Gada suma ya Sanar dasu wannan Mugun labari Fadar irin Tashin Hankali da Suka Shiga bata baki ne Mota Guda sukayo suka zo Goggo Halima da Hajiya Mama suka Yi ma Maryama Sallan gawa yayinda Wasu mazan Daga Gada sukayi ma Abdullahi wankan gawa aka Sallacesu Zuwa Gidansu na Gaskiya Allahu akbar.
Duka da su Bashir akayi Sallar gawan Domin Duk sunzo Hannatu ne kadai bata zo ba Ammh Rukayyah itama ta iso Tuni Zukata suka Raunana Sai ma in ka Tuna da Ciki Maryama ta koma ga Allah ga Yarta Karama wacce ko Shekara Biyu bata gama kaiwa ba Sai kaga yadda Zain da zareena da Haddir suke kuka Kamar Ransu zai Fita Duk da Suna Yara sun Fahimci Mama Maryama da Abdullahi Sun Tafi Tunda Hajiya Mama Ta gayamusu sun Tafi inda ba Dawowa Umman Zareena Goye da Zafira Zain kuma ya kama Halima ya kamkame yana kuka Abun gwanin ban Tsausayi.
Anan Gidan Alhaji Usman aka yi Karban gaisuwa Duk da Shi yana asibiti sai da akayi uku ya Dawo Gida Domin ba Laifi Ya Daku Allah yasa ba karaya sai Gocewar Kashi,Shi kanshi Yayi kuka Zuciyarsa ta Raunana da Wannan Mummunar kaddaran Data Fada musu,Sai da akayi bakwai kana yan Gada sukayi Shirin komawa nan Goggo Halima tace abata Halima ta tafi da ita ta Riketa,Tana ta kukan Bayan Maryama Bata da kowa Duka iyayensu Sun Rasu Su bata ita ko In ta ganta zata Dinga Tunawa da ita Da Farko Dr.Saulawa ya karbi Rokonta yace Umman Zareena ta Hadoma Halima kayanta ta bama Goggonta Tatafi da ita Umma Sai ta Fara kuka Tana Rokon Itama abar mata Ashe Zain yalura Da Sanda Goggo Halima Ta karbi Zainarsa Sai ya Fara kuka yana Kokarin son Karbanta Duk yadda akayi Tunanin Abun ya Wuce wasa Dr.Saulawa yabama Umman Zareena Hakuri yace Ta barma Goggo Halima Rikon Halima Tunda Ita ga Zafeera ma Tana Raina Hakanan ta Hakura Tana ji Tana gani Ta Hado kayanta tabama Goggo Halima Dakyar Aka Rike zain wanda ke kuka yana Birgima kan ba"a Tafi da Zainarsa ba Ganin Har Goggo Halima ta Shiga Mota sai Numfasa ya Fara Daukewa kafin kace kwabo ya Suma Wannan Dalilin Shi Ya Hana Goggo Halima ta Fasa Tafiya da Halima ta Sauko Ta Damkama Umman Zareena ita tana kuka Tana Fadin'Naga Soyayya da kaunar Halima I idanuwan wannan yaron Tun Ranar datazo Duniya..Bazan so na Raba wannan kaunar ba..Gata Hajiya Fatima Allah ya baki ikon Riketa da Amana..!
Ba wanda Baiyi kuka ba awajen Zain kuwa yana Farfadowa Daya ga Zainarsa sai ya Karbeta ya Rumgumeta yana ta kuka Zareena da Haddir ma suka Taru Kusa Dashi Suma Suna kuka ahaka yan Gada suka koma Chan garinsu daDacin Mutuwar Maryama da Abdullahi.
*Comments
*Share and vote*
*Janafty...*
*Intelligent writer"s asso..*
*ZAINAZAIN..!*
_(Is a love Story and Betrayal)_
*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janaftyshakira*❤️
*BOOK 1*
0️⃣6️⃣
"Haka Halima Zaina Tatashi Ta ganta a Hannun Iyayan Rikonta,Musamman Alhaji Usman Daya kasance Kamar Uba Gareta Umman Zareena Ta zama Tamkar Uwar Data Haifeta Da Cikinta Saboda yadda Take Nuna mata kauna.
Alokaci Daya Suka Taso Su Uku Halima,Zafeera da Umar Faruq Duk da Ta Girme musu da Wasu Wattani Sun kawo Ta Girma Tunda Ita Haka Allah yayi ta mai karamin Jiki ce,Tunda Halima ta Fara Wayau Ta Fara Cin karo da matsancin Kauna Da Soyayyah da Zain ke Nuna mata Tun yana Lokacin kuruciya Shiyasa Ta Fara Bude Ido Dashi Duk Gidan Bayan Umman Zareena Halima Bata yarda da kowa ba Sai Zain Ko Makaranta Da karfi Da Yaji aka Sakasu Suna da Shekara Biyu da wani Abu basu Cika uku ba Saboda kukan da take yi Duk Sanda Zain zai Tafi makaranta ya Barta Wannan Dalilin yasa Alhaji Usman ya Saka su Nursing Section Saboda dai Halima da Zain su kasance Waje Daya Hakan kuma ba karamin yima Zain Dadi yayi ba ko achan makaranta Da ya samu Faraga sai ya Leka ajinsu Halima Lokaci kalilan Su kansu yan Makarantar suka Shaida Halima zaina yar gatace kuma Ta gaban Goshi a Wajen Zain
Kwanci Tashi ba Wuya awajen Allah...Yau da gobe bata bar komai ba Gashi Har Su Zain Sun kamallah Secondary School Dinsu Lokacin Zain nada Shekara 19 aduniya shi da Zareena da Haddir,ayayinda da ita kuma Zainarsa Take Cikin Shekara na Tara aduniya ita dasu zafeera Zuwa Lokacim kuma Abubuwan Duk Sun karu an samu Cigaba Sosai Ta Bangaran Haihuwa Nene Ta kara Haihu Yarta Mace mai Suna Zainab Wacce Tsakaninta Dasu Halima ba Nisa,sai Umman Zareena ta kara yin Bashir Wanda Suke Kira Junoir sai na Karshen Allah ya bata Ya mace Wacce Tacii Sunan Saudart.
Ayayinda kuma Bashir Wanda Suke Kira Da Baban kaduna Bayan Sadiq karami Sai Kuma Amina Wacce suke Kira Hajiya,sai Karaminsu Muhammed Amin,suna Kiransa Amin Kawai,Aliyu kuma Wanda Suke Kira Dadyn Abuja kuma Bayan Hamdiya,Ta kara Haifan Waleeda da Kuma Lauratu,yayan Su Inna Rukayya Ta kano da na Inna Hannatu dai ba Wacce Tayi Aure Dayake ya"yan nasu suna karatu mai Zurfi ne.
Zuwa Lokacin kuma Girma ya Fara kama Dr.Abubakar Saulawa,sai ya Damka Ragamar komai a Hannun ya"yansa Asibitinsa kuwa ba koda yaushe yake samun zuwa ba sai dai ya Damka Amanar komai Hannun Amintattun Likitocin Dake Asibitin Suna aiki..sai kuma Burinsa kan Jikikinsa Guda Biyu Haddir da Zain Wadanda suka ce zasu Karanci aikin Likitanci ammh kuma Bangare Dabam Dabam Wannan Abun yafi komai Mai Dadi Farincikinsa sai da ya kasa Boyuwa,Yana ji acikin Ransa ko ayau ya Fadi ya bar Gidan Duniya Allah ya Cikamai Burinsa.
Halima Tataso ba Hannun iyayenta ba ammh Babu Abunda Ta nema na Rayuwa ta Rasa,Umman Zareena,Nene, Zain,Da Alhaji Usman Kowa Sonta yake Kada Hajiya Mama Taji Labari da Dr.Saulawa Wanda Jikokinsa Ke Kiransa Alhaji Tsoho Har Duka ya"yan sa Suma sun kama ganin Girma ya kamashi Har ya Fara Farin gashi.
Ashekarun Halima Tara aduniya Ta Fahimci Tsanatsanin Son da Zain yake mata,Domin Tun kafin takai Haka Komai nata Zain ne,Tun Tana yar Shekara Biyu Tare suke kwana Shi ke bata abinci abaki Yayi mata wanka komai Shi yake mata ko Su Nene sun ce ya bari sai ya saka kuka Dole suka Kyaleshi Itama ta Bude ido da Wannan Kaunar Nashi ne Da Allah ya sakamai Tun Tana Cikin Mahaifiyarta.
Tun Tana yar Shekara 5 aduniya Zain yake kiranta da Firstlove Dinsa,itama kuma Sai Take Kiransa da Hakan,Duk wanda yake Cikin Wannan Ahalin ya Shaida wannan Kaunar Dake tsakanin Halima da Zain,Sai da Zain din ya Fara mallakan Hankalinsa ya kai Matakin Shekara Sha Hudu Umman Zareena ta Hanashi kwana Daki Daya da ita Saboda Halin Rayuwa Da Farko ya Nuna Fushinsa Sai da Mganata takai kunnan Alhaji Tsoho ya Kirashi yamai mgana kana ya Hakura Zainarsa Ta Daina kwana Dashi Shakuwa ce Wacce Bata da Karshe ta Shiga Tsakaninsu in Daya bai Ga Daya ba,ba kwanciyar Hankali In Daya na kuka Daya zai Fara ne komai nasu dai Daya ne in Daya ya samu Abu Toh bazai iya ci ba sai da Daya Suna Kara Girma Tsananin kaunarsu ga Juna na kara Tasiri acikin Ransu kuma Duk Wanda ke Tare da Zain Dole yasan Labarin Halima matarsa ko da Mutum bai Taba ganinta Ba ba"a zaman Minti Biyar Dashi bai ambaceta ba Haka Islamiyansu da Suke Zuwa Sai da Hukumar Makaranta ta kawo karar Zain kan yana Zuwa ajinsu Halima yana Daukanta zuwa ajinsu Baya barinta Tayi karatu Dalilin Haka Umman Zareena ta Saka aka Cire Zain din da Haddir da Zareena aka Sauya musu islamiya Saboda Zain ya samu kwanciyar Hankalin yin karatu Shima Din sai da aka Sha Fama Dashi kana ya Hakura ammh da yace Bazai bar makaranta ba Sai dai in inda aka maidasu Din Su koma Tare da Zainarsa.
In Homework aka bata Amakaranta Shi ke koyamata Komai in bata gane ba kafin Ta Fara Ma Umma mgana Shi zata Fara nema,Dama gashi da kwalkwalwa Zain irin yaran nan ne masu kaifin kwalkwalwa da Kokari Ita kadai yake koyama Karatu,Zareena Tayi ta Jin Haushi Shi kuwa Haddir Baya Damuwa,Tunda bamashi ba kaf abokansu na makaranta Sun san da Zaman Halima amatsayin matar Da Zain zai Aura in ya Girma ya gama karatu,Saboda koda yaushe ko kuma a ina ya zauna Bai da Labari sai nata Allah ya Riga ya Dasa wannan kaunar junan a Tsskaninsu.
Lokacin da sukayi Candy Zain yana Gida Tunda Batare da Saninsu ba akayi musu Cukun Cukun Fita Aborad Su Dora karatunsu Zareena kuma Alhaji Tsoho ya Hana yace ta zauna agida Nageria Tayi karatunta,Zain ya gama Sakankancewa ATBU bauchi zai yi Saboda Bayason Nisa da Zainarsa sai dai kuma Yaga Sabanin Hankalinsa Domin sai da komai ya kamallah Suna gabda Tafiya Shida Haddir suka Tsinci Labarin.
Haddir Kadai yake ta Murna Banda Zain wanda ya Fara cewa Shi ba Inda zashi Saboda Zainarsa Tun ana Dauka Wasa ne Har aka ga Da gaske yake Ganin Yaki ce shi bazashi ba yasa Baban Kaduna yazo Har Gida yana ta yimai Fada Daga baya kuma ya koma Lallashi ammh Sai da akayi mai alkawarim Daya Dawo Bayan ya gama Karatunsa Za"a Daura musu Aure da Zainarsa kana ya yarda akwanakin da suka Rage musu na Tafiya duk batasu yayi wajen Sallama da Zaina da kuma Daukan ma Juna alkwarinka da kuma Sharadai Sharadai masu Dama Da ba wanda ya sani sai shi sai ita Duk da Tana da karancin Shekaru ammh Ai tasan mai Sonta Ta kuma Shaku Dashi Tayi kuka Sosai Lokacin da zasu Tafi Ammh sai ya Lallasheta da Fadin Ta tsaya Tayi karatu Dakyau In ya Dawo Zai Tafi da ita Bayan An Daura musu Aure suje chan su zauna Allah Sarki Rayuwa Suna Makarantar Ranar Wata Talata Jirginsu Zain da Haddir ya Daga zuwa London Ta Abuja ya Tashi In da suka samu Rakiyan Dadyn Abuja da Mommy Iklima Sai Zareena Wacce tasha kukan Rabuwa Da yan"uwanta wannan Shine karo na Farko da zasu Rabu da juna Tun Bayan Haihuwansu....
Itama Din Tafiyarsu ba Dadewa Ta Tatattara zuwa Zaria Inda Ta Fara Karatunta na Aikin Jarida Wato Mass Com,a nan cikin ABU zaria Cike da kewar yan"uwanta Wanda suka Riga suka zama Jikin jikin Juna,Hakuri kawai Take Tinda Daman ko ba Karatu akwai Aure wanda Dole zai Rabasu.
Sai bayan Tafiyarsu Su Umma Da Nene suka Fahimci Yadda Shakuwa tayi mugun Shiga Jikin Halima Domin kwana Take kuka Tana Kiran Sunan zain Dalilin Haka sai da tayi zazzabi Harda kwanciya a asibiti Da aka Sallamota Sai ta koma Shuru Shuru bata Mgana sai dai ka ganta ta zauna Tayi Tagumi Kawai Chan kuma sai ta Fara kuka Sai a Hankali a Hankali Ganin Zafeera da Faruq suna Kokarin Janta ajiki Saboda ta Saki Jikinta da Ita kanta Umma da Abba Wadanda basa Son ganin Damuwarta Da akayi Hutun Makarantar Wannan Shine karo na Farko Da taje Gada Tayi musu Sati biyu ta Dawo,Domin Lokacin da Zain yana nan Baya barinta Taje ko"ina in ma Abba ya matsa Dakyar yake yarda Suje da ita tayi kwana Daya Su Dawo Goggo Halima Ta gaji da Mitan ta Zura ido Ammh Bayan Tafiyar Zain sai Alhaji Tsoho yace Taje chan Tayi musu Hutu Saboda yan"uwa su ganta Koda Taje Din bata wani Sake ba Duk da tasan Sune Dangin Mahaifanta ammh kuma Rashin Zain a gareta Tamkar wani Gibi ne na Rayuwarta.
******
Rayuwar Haddir da Zain a Jami"ar Oxford Universty London Tasha Bambam Domin Dama ko Ahalayya da na yau da kullum Suna da Bambamci Haddir Mutum ne mai Mugun Zuciya Kuma So Silent gashi bai Cika Shiga Shirgin mutane ba,In ka ganshi ya Sake to da Dan"uwansa Zain ne,Duk da ba Abu Daya Suke karanta ba,Shi Zain yana Bangaran Gyneacologist ne,ayayinda Haddir yake Bangaran Paediatric ne,ammh yanzu Suna Hade ne sai Tafiya Tayi Tafiya ne kowane Bangare zai Ware kanshi.
Tun Zuwansu Makarantar Basu Dade ba Sunan Zain Usman Abubakar Saulawa yayi Fice Saboda Zamowarsa Guru a bangaran Kokari Shi kanshi Haddir ya sani bai kama kafarsa ba Dalilin Haka sai ya Sanu Tarin Masoya da abokai kana kuma gashi Handome Matashin yaro mai Kokari,nan da nan ya Shiga Ran maza da mata kafin kace me Zain ya Shiga Click na mata da Maza ba Adadi Tunda Gaskiya Haddir yafishi irin wannan kamewar Ammh Shi Zain yana son Rayuwa da Jin Dadi.
Tun Farko Sai da Haddir yamai mgana kan ya maida Hankali ga Abunda yakai su Ammh Zain bai Ji ba,sai ma yayi Biris da Mganar Haddir din yana Ganin ai yana ganin Karatunsa bazai Hanashi Jin Dadin Rayuwa ba,Ganin Haka yasa Haddir ya Fita Batunshi Saboda karatunsu ba Koda yaushe suke samun Kiran Gida ba Sai bayan Wasu Satittuka Dama Shi Zain Ba da wanda yake waya sai Halima Waya Dakeki..? kina cin kaza..? Kin yi kuka..? Umma na baki madara..? Tambayoyi Dai gasunan sai Ta Rasa wanda zata amsa mai ma aciki Dama Shi yana Kiran Gida ne saboda ita Domin Duk Duniya bayan Iyayensa Itace agabansa kuma aransa.
Ko achan London zaku yi mamakin yadda Sunan Halima yayi Fice Sau Tarin Abokan Zain Turawan Suna mai lakabi da ZAINAZAIN ne kuma yana Jin Dadi Baya jin kunyar yace musu matarsa ce da zai Aura da zarar ya gama karatu ya koma Gida Shi Ba mutum bane mai ijiye Sirri A"a indai ya Hadu da kai ko na Wuni Daya ne Dole ka Shaida Wacece Firstlove a Wajen Zain.
Ba Dina Bace Sanadiyar Fara Lalacewar Zain ba Ita Dina Daga Baya tazo makarantar Domin Zain na gabanta da Shekara Daya sai akaci Sa"a kuma Duka Course Daya zasu karanta,Zain yana da Sakewa da Mutane Both Mata da Maza Sabanin Haddir Dake da kamewa da kuma Daraja Mutumtanka Gidansu da kuma Tarin Nasihun Iyayansu har ma Gargadin Alhaji Tsoho Garesu na su Tsarkake Zuciyarsu Suji Tsoron Allah Suyi Abunda ya kaisu ammh Zain ya watsar da Wannan Farkon Abun da ya Fara kaishi ga Kusanta ZINA shine Biye ma Matan Turawa Wadanda muke da Bambamcin al"ada dasu da kuma addini.
Tun Zuwan Zain makarantan Yayi yanmata da Kawaye mata Wadanda bai san iyakarsu ba In suka ce Suna sonsa baya Taka musu Burki Saboda Shedan ya saka Mishi Sha"awarsu Banda Son su Saboda So Daya ne Tak kuma Zainarsa yake ma Wannan Son Da wannan Abun yasa ya kan kyale su Tabashi Har ma Suyi Hugging Dinshi Su kuma yi Kissing Dinsa baya Damuwa Tunda ya gani a nan Duk Normal ne.
Dalilin Fara aikata Zinarsa Ta Farko Suna Shekara Na Biyu a Landon ne Wata Kawarsa Gloria,Baturiyace yar kasan London din ce itama karatu ya kawota makaranta Tun ganin Farko Da Tayi ma Zain ya Shiga Ranta Ta Dinga Neman kusanci Dashi Dayake bashi da Wuyar Sakewa Nan da nan ya Saki Jiki Da Ita suka Shaku suka zama kawaye suna Fita yawo Tare da Zuwa Wurare Dadama Kwatsam Ranar ta gayyaceshi Gidanta Cin Abincin Dare Wato Dinner Daya nemi Haddir yazo suje yace bazashi ba sai yayi Fushi ya Tafi shi kadai Ashe ta Shiryama Ranar Mganin karfin Sha"awa ta sakama Zain a Alemi yasha Domin ya Biya mata Bukatunta Tunda Tayi kokarin Hakan ta kasance ammh kuma Shi Zain din yana kwace ma Hakan.
Ranar Zain yayi Zina da Gloria kuma Abun Takaichi ma Bashi ne ya Fara saninta ba Ranar agidanta ya kwana Bayan komai ya Lafa yashiga Nadaman Abunda ya Faru yana kuka yayi mata Kaca kaca suka Rabu koda ya koma Gidan da iyayensu suka kama Musu Shida Haddir baya Cikin Natsuwar,Dama bai da Rike Abun Aranshi yana komawa ya kwashe komai ya Gayama Haddir Suka zauna sukaci kukansu Tare ammh Haddir yayi ta ma Zain Fada kuma yayi mai alkawarin Rufe wannan Sirrin ba Wanda zai Ji Bayan Shi Zain din yamai alkawarin zai Guji Faruwan haka.
Kamar Gaske Zain ya Fitar da kansa Cikin Wani Shashancin makaranta ya koma ya maida Hankalinsa kan karatunsa sai dai kuma Waasa Farin Girki Tunda Gloria ta Dandanamai kamar ta Jona mai Bala'i sai ya kasa Sukuni yayi yayi ya Danne Abun ya kasa Bayan Faruwar Haka da wattani kadan Zain ya Koma Ruwa Harka